Showing 147001 words to 150000 words out of 150033 words
Chapter 50 - Rabo Ya Rantse Book One Complete Hausa Novel
bata sabbin kaya ta sanya.
Ammi da kanta ta haɗawa Aliyu abinci ranar ciwo ya ƙare seda ya gama cin abincin sannan take sheda masa mami bata nan mahaifiyarta tazo ta tafi da ita sedai in ya huta yaje ya dawo da ita.
Aliyu yayi Murmushin takaici.
"Ammi kawai mami tai zamanta Na sake ta saki Biyu dan na kama mami da tarin laifuka kafin nabar Gidannan kona zauna da ita ma akwai zargi Sabida dumu dumu na kama ta da laifin Yunƙurin kasheki ta hanyar zuba Miki magani agirki Kuma ban tabbatar ba seda na kamata da manyan Hujjoji wanda ni ban san dalilin ƙudirin hakan gare taba"
Ammi ta share hawaye nan take gaya masa Dukkan abun da ya faru wanda tajira tazo tai mata agida Tsaki yaja yana Allah wadai da wasu mutanan to mai wani ya isa yayi maka In ba Allah ba.
Ya jima suna hira da Ammi wanda washe gari yacewa Ammi ta shirya suje har gidansu mami ya miƙa mata takardar sakin nata tare da bayyana dalilin sa na sakin a gaban mahaifiyarta Sedai koda suka je Gidan su mami yadda suka ga tajira abin babu daɗi se ɗagawa Ammi hannu take amman ba damar Neman yafiyarta.
Mami ta bawa Ammi tausayi dama shi Aliyu tunda ya bata takardar ta ya bayyana mata laifukan ta wanda bata Musa ba ta saka Kuka tana neman yafiyar shi yace ya yafe mata Allah ya yafe masu gaba ɗaya ya fita Ko kallon ɗakin da tajira take beyi ba Ammi da tunanin tajira ta dawo Gida seta ƙara Jin tsoron Allah lallai Mutum ba abakin Komai yake ba.
Kuma a ranar Sadiƙ ya gabatarwa Aliyu riba da ci gaban da kamfanin nikan shi suka samu bayan baya nan Aliyu kuma bai ƙasa a gwiwa ba wajan tara ƴan uwan shi a wannan rana ya sheda cewa ya mallakawa Sadiƙ kamfanin shi na Lagos halak har abada ya mallakawa Bashir kamfanin shi na Abuja har abada shi Kuma ze mayar da hankali ana kano da wanda ze Buɗe a garin kaduna dan mutan kaduna sun zame masa dangi Ranar Ammi tai Kukan daɗi sadiƙ Kuwa yama kasa magana haka Bashir bayan gama Murna Aliyu ya kuma yiwa Bashir albishir da yaje ya Nemi auren Hanan ƴar Gidan Alhaji hamishi wadda yace se a haɗe dana Safna Bashir yayi Godiya sosai haka taron ƴan uwan ya tashi Cikin farin ciki.
Wata irin kulawa Ammi take bawa farha tun farha na jin kunyar Ammi har ta ware ta mayarta kamar umma dan shagwaɓa take zubawa Ammi wadda Komai tace Aliyu ya sauya na ɓangaran shi in farha ta haihu seta tare acan dan haka sabbin gyara aka soma yiwa part Ɗin Aliyu Daidai da sutturar farha ammi ta bawa masu aiki sabbin kaya aka ɗinka mata akwati akwati masu kyau da tsada Su safna Sun Haɗe kai da farha sun koma ƴan ukun Ammi.
Musa daya zo Aliyu ya karɓi wayar shi ya kunna tarin saƙonni Yayta bi Haka yaje Gidan gwamna ya sheda ya dawo dan sadiƙ ya gaya masa sunje Sun bada Uzirin yayi tafiya har gidan su farha seda yaje anan Su kawu sukai ta masa Godiya da mamaki ya kalli Musa bayan sun fito yake tambayar shi bayan baya nan ana aika masu da saƙo ne Musa yace Shiya ɗauki nauyi Aliyu yay wa Musa Godiya sosai Nan fa harkokin Aliyu da tafiye tafiyen sa suka dawo acikin satin Ya aika Musa kaduna dan ya Fara duba in da zasu siya su gina kamfanin su ma acan.
Sadiƙ ya koma lagos sedai yadda yaga sakina fa abin babu sauƙi nan Minal babbar ƴarsa ke gaya masa abin da maman su take lokacin da baya nan Abin ya ɗagawa sadiƙ hankali dan washe gari suka dawo kano Gidan su sakina ya wuce Ya sanarwa da mahaifiyarta dan sosai sakina hauka take da sumbatu jamila ce ta warware wa sadiƙ Komai na abin da Sakina ta aikata sadiƙ yayi Takaicin abin ya kalleta yace.
"Mai na rage ki dashi sakina gashi nan kin ɓata rayuwarki a banza abin da Kike so Gashi na samu dan Aliyu ya mallakamin kamfanin sa cikin sauƙi bayan Kin fita daga hankalin ki sakina Kin cuci kanki Kuma ni sadiƙ na sake Ki Saki ɗaya kuma ba zan bar Miki yarana ba"
Ya kwashe ƴaƴansa suka bar gidan sakina se dariya take Suna fita Jamila ta samo mota ta saka sakina sukai dawanau gidan mahaukata dan tace ba zata barta agida ba ta kashe su haka kawai Mahaifiyar sakina tai takaici da halin ƴar tata haka jamila takai sakina gidan mahaukata aka bata ɗaki guda dan A soma duba ƙwaƙwalwarta dan hauka take Tuburan tana Tone tonen asiri.
Sadiƙ duk yadda yaso seda yay Kuka sanda yake shedawa Ammi abin da yake faruwa Ammi ta tafa hannu tana cewa.
"Lallai Mutum mugun icce sakina tabani mamaki dama abin da ka shuka shi kake Girba Allah ya zaɓa maka tagari wadda zata riƙe maka yaranka yanzu Ka huta zuciyarka tai sanyi kafin ka koma lagos ka bar Min yaran a gabana kafin muga abin da Allah ze mana"
Nan take bashi labarin su tajira ma Sadiƙ yaji labarin tajira da Kuma abin da ya gani akan sakina ya ɗaga masa hankali Kuma ya ƙara Jin tsoron Allah aran shi.
Wayyo Allah Kaine mai iko akan kowa zuwa wannan Lokaci abin ya ƙazanta ga tajira dan takai tana ɗoyi tsutsa tana fita daga gabanta kwanan ta Biyu cikin wannan hali rai yayi halin sa an Mutu da Mugun Nufi arai Allah ka rabamu da irin ƙarshen su tajira Babu wani taro da akai haka tsirarun Mutane suka kaita Gidanmu na gaskiya aka gama addu'a aka watse su tajira an gama na duniya sauran nacan.
Seda akai kwana bakwai mami ta kira ammi ta sheda mata Ammi batai ƙasa a gwiwa ba wajan saka salma dasu safna a gaba suka Je gaisuwa harda abin arziƙinta takai Musu mami se Godiya take.
Sadiƙ ya koma lagos.
Cikin Farha nata Girma kullum Aliyu na Ƙuncin taƙi Zuwa inda yake ai tasan yana buƙatarta Ita ko dan rashin Kunya taje wajan Miji da wannan ƙaton cikin ta Tsallake mahaifiyar shi Dan haka tai masa banza duk da ba haram bane hakan amman ai da kunya.
Bayan wata biyu farha ta tashi da naƙuda wadda Nan da nan Ammi tasa aka ɗauko Mota suka tafi asibiti basu Jima da zuwa ba Allah ya sauketa lafiya ta haifo yaranta mace da namiji masu kama da Aliyu sak kafin kace me asibitin ya cika da ƴan uwa Aliyu da yaje kaduna dan Buɗe kamfanin shi albishir da Salma tai masa ba sanya yayo Gida yabar Komai wajan Dini wanda ya taimaka masa ya sami aiki a tasha to shi Aliyu ya Nema akan Harkokin kamfanin nashi na kaduna kuma ya ɗora shi a babban matsayi a kamfanin.
Zo kaga murna wajan Aliyu duka ya haɗe yaran nashi yana Musu addu'a yana farin ciki da yake bata sha wahala ba nan da nan aka sallamo su suka dawo Gida Ammi ta haɗa ruwa da kanta taiwa Farha wanka ta gyarata tsaf Aliyu se kallon farha yake yanzu da kanta ta haifa masa waɗannan manyan yaran kyawawa.
Musa ya aika gidan su farha aka sanar wanda Yaya sadiya da Nafisa da Umman zage yayar umma dasu babarsu Hadiza suka shigo Motar Musa suka tawo Gidan farha Hoho Duniya da duniya se a wannan Rana su Yaya sadiya suka san wa farha ke aure ashe Hasken matasa take aure wanda A kamfanin sa ma su Halifa suke aiki.
Sun sami karramawa daga wajan Ammi da su safna Farha kuwa harda Kukan murna ta rungume yaya sadiya wadda ta saki baki tana kallon farha Su yaya sadiya na gidan farha ta Koma sashin ta ashe basu ga komai ba domin sashin farha se ka rantse ba a ƙasar nan aka tsara shiba Umman zage aka bar mata su Kuma suka tafi Gida da labarin mijin da farha ta aura da kuma Duniyar alatun da suka gano.
Umman zage kewa farha wanka da yara wanda Koda yaushe se farha tai kuka in za'a mata wanka Umman zage taita tsokanarta Aliyu Kullum yana rungume da yaran shi yana kallon su yana jin farin ciki aran shi haka aka gudanar da taron suna gagarumi yara sunci Suna Amina ( Ammani ) da Abdullah ( Dady ) haka akai taro lafiya aka gama lafiya Se bayan suna umma tazo shima da ƙyar Su yaya sadiya suka takura tazo dan koda tazo a part Ɗin Ammi ta sauka Hmm zoku ga soyayya wajan farha da Umma dan ɗane jikin umma farha tai tana Sangarta kala kala Shikam Aliyu koda yazo gaida Umma yaga yadda farha tai abin ya bashi mamaki duk yadda yake zaton farha ta wuce nan.
Yara nata girma dan suna samin kulawa ta kowane ɓangare kwanaki arba'in umman zage tayi tanawa farha wanka wanda Aliyu ya mata gagarumar kyauta sanda zata tafi Hajja ce ta dawo ɓangaran dan ta taya farha raino da ƙyar yabarta taje Gida tai kwana Uku yadda taga an sauya gidansu tai murna taiwa Aliyu fatan alkairi taji ya ƙara ƙima a idanunta ashe haka ya kyautatawa mahaifanta kaji masu yi domin Allah amman bai taɓa gaya mata ba seda suka ƙulle da Umma ma take ƙara gaya mata abubuwan da yake musu tace wallahi Umma bai taɓa gaya Mini ba lallai ma Abban su ba Komai.
Ta zaga gidan yayinta kaf dan haka ta ɗauki Ikram sukai ta ziyara Wanda Aliyu yayta Mitar tana fitar masa da yara suna shan rana in yayi waya dasu har Gidan su Shema'u ƙawarta taje anci dariya ba ƴar kaɗan ba da suka Tuno aikin su na gidan radio Shema'u ta bawa farha labarin zuwan musa gidan su Farha ta bawa shema'u labarin komai har auren da sukai da Aliyu bayan ta bata Numbern wayarta suka baro Gidan su shema"u gida daɗi kamar kada su baro gida haka suka dawo washe garin data dawo Aliyu ya ɗauke ta da yara sukai kaduna abin mamaki ya bata dan ya gyarawa Inno Gidanta har mai aiki ya ɗaukar mata Ya kuma saiwa Mijin shafa gida ɗan ƙarami anan Kusa da na inno kuma ya ɗauke shi aiki a kamfanin sa nacan agidan Inno suka kwana cikin Ac da haske dan ya gyarawa Inno Gidanta ya sauya mata Komai washe gari sukai sallama da Inno da su shafa ta kamfanin sa nacan suka biya suka gaisa da dini ta zaga kamfanin Sosai sannan suka kamo hanyar kano tana Jinjina halaccin Aliyu wato Shi baya manta alkairi sabida duk waɗanda suka taimaka masa a kaduna seda ya koma ya taimake su.
Bayan sun dawo Gida ta kafa masa nacin maganar Mami wanda se Lokacin ya gaya mata Halin da ake Ciki tai Kuka dan bata ji daɗin rabuwar suba haka ta kafa masa nacin ya kaita gidan su mami ba dan yaso ba yakai ta wuni tai agidan su mami wadda bata Ɓoyewa farha Komai ba farha ta tausayawa mami haka suka wuni da daddare yazo ɗaukar su Tana masa ƙorafin halin da Mami da ƴan uwanta suke ciki yana mita yana Komai haka dai yasa Musa yakai Musu Kuɗi da kayan abinci kuma tunda ga nan Duk ƙarshen wata yana sawa akai Musu.
Mami nata wa Farha godiya a waya farha tace mata ba komai.
Rayuwa na tafiya bikin su safna yana ƙaratowa sajeeda ganin zata cutu ne yasa ta gayawa farha halin da take Ciki akan Nura kuma ta roƙi alfarma da ta taimaka mata akan shawo kan shi farha tai dariya tace ta kwana gidan sauƙi aikuwa ta kira Yaya Nura wanda tuni Aliyu ya sauya masa wajan aiki yana kaduna bayan ya sami ƙarin girma shaida masa tai halin da ƙanwar Mijinta ke ciki akan shi ashe shima tunda yaga sajeeda sanda suka je da Su Ammi kullum tana manne aran shi kawai gani yake kamar tafi ƙarfin shine Cikin Lokaci kaɗan Soyayya ta Ƙullu a tsakanin Su Wanda ba jimawa manya suka shiga maganar babar su Hadiza murna take nura ze auro ƙanwar Mijin farha itama ikram maganar aurenta da Salim tai ƙarfi sosai dan Lefe za'a kawo ma Bashir yaje Gidan su Hanan tuni sun sasanta Kansu Har an kai Kuɗin aure da saka rana.
Cikin wannan Lokacin akai Bikin jamila ƙanwar sakina wanda bayan auren nata ta sami Kira daga dawanau cewa Jikin ƴar uwarta ya tsananta naka nakane haka jamila da Mijinta suka ɗauko sakina yadda suka ganta abin babu sauƙi ta haukace Hauka take Tuburan agidanta ta ajeta sedai kwanan sakina Biyu ta rasu waya jamila taiwa sadiƙ washe gari yazo kano Ya ɗauki Aliyu suka je wajan ta'aziyya sannan yakai yaran sakina se Kuka suke har dare suna can Kafin su dawo Gida washe gari shema'u tazo wajan farha sun Fito farha zata rakata sadiƙ yaga shema"u bai wani yi Ɓoye Ɓoye ba yacewa farka surukata naga ƙawarki in ba wani ni ina ciki farha tai Murna sosai kafin sadiƙ ya koma akai maganar auren shi da shema'u ana bakwan sakina sadiƙ ya koma Lagos.
Shirin auren sadiƙ da shema'u Safna da kamal sajeeda da nura Bashir da hanan ya kankama kowani ɓangare Shiri ake dan Gidan su Farha Nura da Ikram za'a haɗa shiyasa Duk farha ta zama Busy ga kuma shirin Buɗe ƙatuwar Plaza wadda Aliyu yayo mata order kayayyakin sawa irin su dogayen riguna da takalma harda kayan jarirai dan ta dinga sai dawa Sunan Plazar fatiman Ali plaza tana nan kan babban Titin Hotoro anan ya buɗe mata ya zuba mata ma'aikata mata don su dinga taimakon ta to shirin Buɗe plazar da Kuma shirin Bikin da zasu yi duk ya sakata ta zama se a hankali dan hatta su Ammani watsar dasu take wajan Ammi Tun ubansu na mita har ya gaji damma yaran akwai haƙuri.
Alhamdulillahi anyi bukunkunan lafiya an kai amare gidajen su anyi shagali na ban mamaki dan hatta shafa seda tazo daga Kaduna ita da Inno haka zalika Mami ma da su Hassana sun zo dan farha seda takai Musu katin Biki har Gida a sabuwar motar daya bata wadda ya koya mata da yake tana da ƙwaƙwalwa tuni ta Iya ta ƙware a tuƙi dan da ita ta dinga shige da ficen Biki.
Farha tai rawar gani sosai dan ita taiwa Ikram komai wanda uwa da uba keyi sannan ta haɗawa Nura Lefe duk kuma a lalitar Oga Aliyu kuɗin suka fita Babar su Hadiza ta dinga wa farha Godiya kamar zata ari baki.
Mami ta sami Miji wani bawan Allah anan maƙotan su matar ce ta rasu da yaransa Biyu Har gida ta kawowa Ammi da farha katin Biki Kuma sunje harda abin arziƙin su anan Gidan su ta zauna sabida ƙannen ta waɗanda suma duk sun sami mazajen aure Shirin Bikin su ake kuma farha tace Aliyu ya taimaka yayi Musu kayan gado Bai Musa ba yace yadda kika ce haka za'ai ƴar amanata.
Rayuwa mai sauyi komai ya sauya a rayuwar farha wadda ta koma Babbar Mace Dan Allah ya sawa kasuwancin ta albarka Tana taimako sosai da wannan sana'a tata wadda nan da nan Sunan plazar ta yay suna a kano sabida yadda kayanta keda sauƙi da aminci.
Aliyu nata mitar taƙi yiwa su Ammani ƙanne shifa Seya ƙaro aure dariya take in taji ya faɗi wannan magana dan tasan ita kaɗai ce amarya uwar gida a gare shi.
Yanzu haka su Ammani nada shekara biyu suna Gudunsu ko ina haka ya ɗebe su harda Umma da kawu Da hajja suka Nufi makka dan suyi aikin hajji sabida yayi wa hajja alƙwari Kuma Allah bai yiba sabida tafiyar dayay kaduna.
Ita dai farha taje umara har sau biyu se kuma makkan daya kaisu a wannan Lokacin haka sukai aikin Hajjin su suka dawo Gida lafiya.
Bayan shekara shidda farha ta sake haifar yara Biyu duka maza Safna da ta haihu sajeeda ta haihu shema'u da suka haɗe kai da farha itama ta haifi ɗa namiji kuma ta riƙe ƴaƴan sadiƙ tsakaninta da Allah Hanan ma ta haifi Ɗanta namiji Wadda Itama Gidanta ke Abuja Ikram ma ta haihu dan seda ta haihu farha ta iya zuwa gidanta sabida kunyar salim wanda bai ko nuna mata wani abu ko a fuska ba, Anyi auren su ruƙayya Haka zalika anyi auren ƙannen mami.
Rayuwa na tafiya abubuwa masu daɗi da marasa daɗi Sun faru domin Inno ta rasu Haka zalika kawu ma ya rasu Se Cigaban da Aliyu ya ƙara samu dan koda mai Girma gwamna ya sauka daga kujerar dayay shekaru takwas ta zarce akan ta, jam'iyya tai masa tayin koze tsaya takarar gwamna seda yay shawara da Ammi da farha sannan ya amince aka fara yawon yaƙin neman Takarar Kujerar wadda Cikin Hukuncin Allah bayan kaɗa ƙuri'oin dubban jama'ar dake jahar kano Allah mai kowa da komai ya bawa Alhaji Aliyu Abdullahi Madaki nasarar lashe zaɓan Zama Cikakken gwamnan kano.
Anyi murna anyi shagali haka su farha sukai ƙaura zuwa gidan gwamnati Mulki yake cike da adalci da jin ƙan talakawa Farha An zama first lady abin se Godiyar Allah dama dukkan wanda yay haƙuri a rayuwa yana tare da nasara.
*ALHAMDULILLAHI*
Nan na kawo ƙarshen Littafina mai suna *RABO YA RANTSE*
wanda na fara saki da rubuta shi on 22 august na kuma kammala shi a on 10 act 2023 abin da nayi daidai Allah ya bani ladan shi kuskuren danai kuma Ya Allah ka yafe mini.
Waɗanda suka ɓatan a wannan tafiya na yafe muku waɗanda na ɓatawa a wannan tafiya nima su yafe mini Allah ya yafe mana gaba ɗayanmu ina roƙon ku da kuyi aiki da abu mai kyau da darasi da saƙon alkairi na wannan Littafi Kuyi watsi dana dukkan sharrin ciki.
Godiyata ga Allah maɗaukakin sarki daya bani rai lafiya kwanciyar hankali basira hazaƙar Rubutu nagode maka Allah baka taɓa gajiya da dukkan lamurana ba nagode Maka Ya rabbi!
Godiya ga tarin masoyana mabiyana masu Jimirin bina Ya Allah ka sakawa dukkan wadda ta sanya Kuɗinta tasai wannan Littafi nawa da dubun alkairinka.
Godiya ga ƴan private Allah ya biya Muku buƙatunku na alkairi.
Godiya ga ƴan paid grp Allah ya biya Muku buƙatun ku na alkairi.
Se mun a haɗu a wani sabon