Showing 99001 words to 102000 words out of 150033 words

Chapter 34 - Rabo Ya Rantse Book One Complete Hausa Novel

halin da farha take ciki nace masa kuna waya da Mijinta kamar yadda yaya sadiya take gayan shine yace ai waya ba tabbas bace mu ganta shine tabbas tunda duniya yanzu babu gaskiya acikin Mutanan ta"
Yaya nafisa takai maganar cikin sanyin Jiki umma ta kuma goge hawayenta tare da cewa "Hidimar da Mijinta yake mana tayi yawa, na fahimci shi kuma kawun ku wannan wayar da sukai da mijin nata ya sami nutsuwa Nikam har yanzu hankalina baya kwance ga kuma maganar yaron nan da Ya nemi auren farha Jiya Kawun ku yake cewa Baban sa yace dai basu haƙura ba suna neman iri dai acikin gidannan a ƙara bashi guda ɗaya daga cikin yarannan ni nace ga Ruƙayya ko Hadiza amman kawun ku yace Ikram za'a bashi wallahi Jiya baki ga bala'in da a kwasa ba Nan Babarsu Hadiza tazo tagama cimin mutunci har da cewa waya sani ma ko anyi tsafi da farha kuɗin kanta Muke ci wannan abu ya ƙara ɗaga min hankalina Kin san shi maƙiyi kome zaka masa bazaka Burge shiba nina rasa mai nayi wa matar nan ta tsane ni nida ƴaƴa na wallahi babarsu Ruƙayya ta sakko har nan take zuwa muyi hirar mu wani bin sirrinta ma zata kwaso ta gaya mini"

Yaya nafisa ta numfasa kafin tace.
"Au umma salim ɗin ne dai bai haƙura ba wato yanzu kuma da ikram za'ayi to umma Allah yasa haka ne mafi alkairi sedai Kuma Tana makaranta katse mata karatun zaku yi kenan?"
Umma tace.
"A,a nifa hankalina har yanzu bai gama kwanciya ba, Kin san dai yadda muka ƙare da mahaifiyar shi babu kalar maganar da bata jefe mu da ita ba akan farha bada ban Allah yasa ma Mahaifin nashi a tsaye yake ba ina ga da har gidannan zata zo taci mana mutuncin maƙiya suyi dariya to Se Allah yasa mahaifin sa a tsaye yake shine ya taka mata burki, to kawun kune yaje har gida yana ƙara bawa mahaifin salim ɗin haƙuri dan yadda kawun naku ke faɗa ko a hanya baya yadda su haɗu da mahifin salim sabida yadda yake jin kunyar shi, to shine fa mahaifin salim ɗin kecewa kawun ku Shifa yana ganin acikin ƙannen farha a sake bawa salim guda ɗaya tunda ya gama ginin shi yayi komai matar dama ake jira"
Yaya nafisa ta katse umma da cewa.
"To shine aka bashi Ikram?"
Umma ta girgiza kanta.
"A,a shi kin san kawun ku in ze magana tara mu yake gaba ɗaya har yanzu shibe san ya ware mace ɗaya yayi shawara da itaba, To shine jiya ya taramu yake gaya mana Shine na buɗi baki nace to tunda haka ne ga Ruƙayya ko Hadiza tunda Wannan shekarar zasu gama makaranta, Amman shi kawun naku se yace a,a ga Ikram nan ƴar ɗakin su Farha in aka bawa salim seya fi jin daɗi, Kuma ma ikram tafi farha sanyin hali da haƙuri to tundaga nan suke ta ƙananun maganganu musamman ita babarsu Hadiza dan ba'a ƙare taron da ita ba tashi tayi tabar mana wajan tana Mita, nifa Nafisa bana Murnar wannan abu saboda Ikram duka nawa take ma da za'a mata maganar aure"

Yaya nafisa ta saki fuska cikin farin ciki tace.
"Umma bafa aja da ikon ubangiji ke dai addu'a zaki muma kuma mu tayaki duk abin da yafi zama alkairi Allah ya tabbatar sabida seta yuwu rabon ikram ɗinne ma Allah yasa akai haka data shiga gidan sa ita farha ɗin ta Mutu Ai da Ikram gwara da Allah ya kawo wannan masalahar sannan in batun shekaru kike yanzu ikram nada shekara kusan sha takwas a jiki fa tafi farha sannan tafi farhan ki Nutsuwa kawai in yana son auren ai yarjejeniya akan ze barta ta fita tai jarrabawar ƙarshe Shikenan sabida umma wata ni'ima Allah yayi miki kina kallo kece kaɗai mai ƴaƴa mata agidannan meye bamu gani ba wani irin hali ne bamu shiga ba, wallahi umma wani bin ko agidana ina son naci abu mai daɗi kona ɗinkawa yara amman inna tuno ku agidannan sena haƙura na ƙullo na kawo muku ranar da Farha taje take gaya min lokacin su Halifa sun sami aiki amman kowa babarsa yake bawa Abin cefane ranar har kuka nayi nace duk dan ke ake wannan sabida baki da ɗa namiji amman ki duba ni'imar Allah kaf ƴaƴanki Farha ce kaɗai takai shekara ashirin da ɗori batai aure ba amman duk ɗinmu muna shekaru kaɗan Allah yake bamu mazaje to ga Ikram ma farhan datai jinkirin a hakan ashe ajikinta za'a huta sabida haka Umma ki godewa Allah su ga ƴaƴan nan birjik agaban su Na gidan Mijin ma ba daɗi suke jiba mu ɗinnan wallahi Munfisu rufin asiri to zuciyarki wankakkiya Allah ya duba shiyasa ya Yaye maki damuwar ƴaƴan ki cikin sauƙi"
Dukkan maganganun yaya nafisa haka suke kuma umma taji ta sami Nutsuwa sosai da maganganun Nafisa sabida dama sune kamar abokan shawarar tata Umma ta dubi yaya nafisa.
"Haka ne maganarki to Allah ya zaɓa abin da yafi alkairi seku soma tari dan dama nace Ikram taku ce kune zaku aurar min da ita ni hutawa zanyi"
Yaya nafisa tayi dariya.
"Da yake kin aurar da farin cikin ki umma masoyiyyar farha oh wannan ƙauna amman umma yanzu kin dena Jin zazzaɓin ko?"
Umma ta wurga mata pillo tana dariya sannan tace.
"Ai wannan zazzaɓi bazan dena ba har se naga auta ta, Sannan kuma da kike batun na aurar da farha babu fa abin da nayi mata na uwa Kina kallon yadda wannan aure yazo abu kamar almara babu wani shiri haka aka tafi da yarinyar nan kamar Marar gata ko sabbin kaya babu"
Umma ta faɗi maganar cikin damuwa Hirar su suka cigaba dayi har zuwa lokacin da Ikram ta dawo daga makaranta ta gaishe da yaya nafisa ta wuce ɗaki ta cire kayan makaranta ta fito ta shiga kitchen ta zubo abinci ta zauna tana ci suna hirar su.

Aliyu daga masallaci fita yayi zuwa cikin gidan su mahaifinsu yayi Musu sallama sannan ya kira Musa Suka wuce office dan ya ɗanyi abin da zeyi kafin lokacin tafiyar shi ya cika dan Jirgin ƙarfe ukun yammaci ne ze tashi dasu in sha Allahu........
*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*


*A LOVE STORY 81*

Tun da ya shiga office ɗin shi yake faman aiki yana damƙawa Musa dukkan wasu abubuwan da zasu gabatar Idan baya nan seda akai sallar azahar a masallacin Dake cikin kamfanin nashi sannan ya rufe laptop ɗin dake gaban shi suka fita da Musa zuwa masallaci bayan sun idar da sallah Office ɗin dai ya kuma dawowa lokacin ya ɗago ya kalli Musa tare da bashi umarnin ya sai kayayyakin sawa irin dogayen rigunan nan ɗinkakku sabida lokacin ɗinki ya ƙure to ina ma yasan size ɗin ta in ma ɗinkin ne, yakai gidan salama sannan yaɗan yi siyayyar kayan motsa baki ya tafi dasu.
amman yayi sauri ya dawo sabida ze kaishi gidansu fatima kafin Jirginsu ya tashi da ladabi musa ya amsa mai sannan ya fita ya laluba wayar shi ya shiga kiran Layin salama kusan sau uku tana ringing bata ɗaga ba se daya kira na huɗun sannan ta ɗauka da muryar bacci ya hau yi mata masifar baccin me take bata ji kiran shiba Haƙuri ta bashi umarni ya bata akan ta miƙawa farha wayar salama ta miƙe ta shiga ɗakin da farha ke ciki bacci take sosai tace masa bacci take se cewa yayi ta tashe ta, ta bata wayar Salma ta cika da mamakin wannan naci haka amman taja bakinta tai shuru ta shiga tashin farha wadda ta Miƙe bakin ta cike da yawu taje ta zubar ta dawo ta karɓi wayar salma ta fita tabar mata ɗakin.

"Fatima kin tashi lafiya?"
Taji sassanyar muryar shi acikin kunnenta.
Ta turo baki tana wani kwaɓe fuska dan takaicin katse mata baccinta da yayi.
Tayi masa shuru, yayi ƙasa da murya.
"You are angry with me because I woke you up, so I am sorry" ya faɗa cikin ƙasa ƙasa da murya, still shurun nata ne ya kuma biyo baya yaji hankalin shi ya tashi ya kuma yin ƙasa da muryar shi "Kin zaɓi ki hukuntani ta hanyar yi min shuru idan ina miki magana ne kome fisabilillahi me yasa kike son ɗaga hankalina ne?" ya faɗi maganar yana sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi a hankali ta kwanta a saman gadon muryarta can ciki tace.
"Ina kwana?" ya saki murmushi me sauti"Se yanzu kika san yaya na kwana bayan da shuru kika min" ta turo baki kamar yana ganinta tare da cewa"Bacci fa nake yi mai daɗi kasa aka tada dani" yayi murmushi "Sallah zanji kinyi and kina azumin?" ta wani yi ƙaramar dariya "Ina yi mana ta yaya zan sha azumi babu wani dalili, sallah kuma tun asubah nayi kaima kasan ba wasa da sallah" yaja ajiyar zuciya tare da cewa "To Alhamdulillahi yaya kike jin zaman naki kuma yaya kike ji ajikin naki?" ta lumshe ido saboda har Lokacin baccin na kanta "Zaman nan yafi na gidanku daɗi sabida Aunty salama tasan darajar ɗan adam kuma tana girmama ni, sannan Jikina lafiya lau sema ƙarin kuzarin dana samu wanda yafi nada" ya Jinjina kai cikin rashin jin daɗin maganarta yasan magana ta faɗa a fakaice wato gidansu ba'a san darajar ɗan adam ba lallai ta riƙi su Ammi acikin zuciyarta seya kawar da maganar yace mata "Jirgin ƙarfe uku zamu bi wace addu'a zaki min?" tayi dariya "Allah ya kaika lafiya, idan kaje kayi addu'a Allah ya baka ƴan uku da ƴan huɗu a wajan Aunty mami" da sauri yace "Kefa bakya son ƴaƴa dani?" ta rufe ido cikin jin kunyar abin da ya faɗa mata sannan tace "Ni ai nai ƙanƙanta da yawa ina zan iya rainon ƴaƴa ai se su karyani ba yanzu ba ita dai Allah ya bata" ya cika da mamakin Furucinta "To idan Allah ya baki fa?" tayi dariya "Zan karɓa amman wallahi sedai kaji da ƴaƴanka dan bazan iya musu komai ba Inji ma da nauyin cikin kai in sha Allah bama zan haihu yanzu ba yadda mata keci wiyar ciki data haihuwa" dariya yayi sosai lallai wautar fatima takai ta kawo tan tare da cikin ma bata sani ba sannan har take faɗin ba zata haihu da wuri ba har sukai sallama dariya yake mata kuma hirar tasu tayi masa daɗi Sabida shirmen data dinga zuba masa Minti kaɗan musa ya dawo Suka wuce Gida wanka yayi ya fito cikin shirin sa har part ɗin ammi mami ta raka shi addu'a ammi ta dinga yi masa Sadiƙ da Bashir ne suka rako shi duk yadda jamila taso ganin Aliyu abin bai samu ba saboda yadda mami ta liƙewa mijinta sadiƙ da Bashir wata motar suka shiga daban driver yaja su shikuma ya shiga cikin wadda Musa yazo da ita suka wuce Gidansu farha seda ya gyara sosai ya saka face mask sannan ya sauka Yabar Musa a mota ya gane gidan duk da an gyara shi amman Yadda Gano gidan abin har mamaki ya bashi shi kanshi doka gate ɗin yayi ƙanin farha ɗan ɗakin su ruƙayya ne yazo ya buɗe Ya zubawa Aliyu ido yaga fuskar shi a toshe Aliyu ya zame face mask ɗin shi tare da cewa yaron "Ki ramin baba agida" yaron yace "Ai baya nan ya tafi gaisuwar Mutuwa" Aliyu yayi shuru kafin yace "To kace wa maman su Farhan tayi baƙo a waje" Yau ce rana ta farko daya faɗi sunan ta na laƙani dan yaron yafi ganewa aiko yaron ya koma ciki aguje yaje ya gayawa Umma wadda tace wa Ikram taje ta gano mata wanene Ikram ta saka Hijabi ta fita Tana zuwa gaban Aliyu taɗan saki fuska ta tsugunna ta gaishe dashi.
"Wai umma tace waye?"
Yayi murmushi yana kallonta.
"Kema wace koke ce Ikram mai ɗan malele?"
Dariya tayi tana Ɓoye fuska.
"Nice dai ikram amman bana ɗan malele"
Aliyu ya zubawa ikram ido lallai fatima tace yaga ƙannenta seya yi mamaki amman duk da haka Yara ne saurin girma ne sukai.
"Jeki cewa mama Aliyu ne yazo Mijin Fatima"
Ai ikram seta ɗago tana dariya.
"Lahh kaine ina farha to?"
Ya zuba mata ido Tafi fatima fari da kyau ya kawar dakai.
"Tana gida mana"
Da sauri ikram ta juya cikin gida ta sanar da umma wadda Ita kuma umma tayi saurin shiga ɗaki tana murna yaya nafisa ce tace wa ikram taje ta shigo dashi Ikram ta fita ita kuma yaya nafisa ta shiga gyara wajan.
"Wai ka shigo"
Ikram na gaba Aliyu yana binta a baya suka wuce babban falon gidan suka shiga ɗan ƙarami na umma.........
Yaya nafisa na zaune akan kujerun da aka zuba ƙananu a falon Aliyu yayi sallama ya shigo cikin nutsuwa yaya nafisa ta amsa mai sallamar kuma tana nuna masa gurin zama sedai yaƙi zama akan kujerar data ke nuna masa da sauri Ikram ta shinfiɗa mai darduma a saman ƙaramin center carpet ɗin falon ya zauna yaya nafisa se satar kallon shi take Kyau kamar shi yay kanshi Astagfirullah ga Nutsuwa wannan kuwa anya Mijin farha ne.
"Ina kwana yaya mutan gidan?" cewar yaya nafisa ya ɗago ya kalleta bata fi sa'ar bashir ba itama farar ce kuma suna kama da ikram yaya akai basa kama da fatima ya kawar da mamakin shi tare da cewa.
"Lafiya lau Alhamdulillahi"
Yaya nafisa taji yayi mata kwarjini tashi tayi ta shiga cikin ɗaki umma ta tarar da umma zaune a bakin gado yaya nafisa tayi murmushi.
"Umma yana jiranki kije ku gaisa"
Umma dama akwai jin kunyar surukai tace.
"A,a Nafisa jeki kira su Babarsu Ruƙayya su gaisa kafin na kintsa"
Yaya nafisa ta ɓata fuska.
"Haba umma gaskiya ki soma fita in yaso sena kirasu daga baya ai ya shaida kece mahaifiyarta ko"
Ba yadd umma tayi haka ta saka hijabinta har ƙasa ta fita Lokacin Yana ta jan Ikram ta magana tambayarta yake ajin ta nawa Ta dage tana gaya masa sega umma ta fito da sauri ya gyara nutsuwar shi kuma bai yarda sun haɗa ido ba yayi ƙasa da kanshi.
Umma ta sami nesa dashi ta zauna.
Da sauri ya ce mata.
"Mama ina kwana mun same ku lafiya?"
Lokacin ta ɗago da Murmushi da kuma alkunya a saman fuskarta tace.
"Lafiya lau yaya mutan gidan?"
Lokacin shima ya ɗago ya kalleta da sauri yayi ƙasa da kanshi Ko kaɗan ba zaka ce maman fatima bace sabida basuyi kama ba Itama fara ce tas.
Ɗakin shuru yayi.
Har yaya nafisa ta fita domin kiran mutanan gidan.....*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*A LOVE STORY 82*

Ɗakin Babarsu rukayya ta soma shiga ta gaya mata tazo ga mijin farha yazo sannan ta shiga ɗakin babarsu hadiza wadda dan tsananin ruɗewa seda zaninta ya kunce"Nafisa mijin farha ko mijin fa'eeza?" Yaya nafisa tai dariya tare da cewa "Mijin farha dai shine yazo ya gaishe daku" Da sauri ta juya ta koma falon Umma bata zauna anan ba Ɗaki ta wuce ta sami Ikram a zaune dan tunda Umma ta fita wajan shi Ikram ta tashi daga wajan taba su guri Falon yayi shuru dan duk cikin su babu wanda ya kuma magana tun bayan gaisawar da suka yi.


Aliyu jinsa yake wani iri ita ma umma haka Cikin haka Su Babarsu Ruƙayya sukai sallama umma ta ɗago da far'a ta amsa musu zama sukai suna gaishe da Aliyu Babarsu Hadiza tsabar ruɗewa ma cewa take "Ina farha ɗin?" murmushi yayi tare da cewa "Tana nan lafiya shima sallama yazo yayi musu zeje saudia" daga haka shuru ne ya biyo baya dan ko wacce tasha jinin jikinta Aliyu ba kalar wanda za'a masa baragada a gaban shi bane ba Ko wacce mamaki take ina farha ta samo wannan Miji na kere sa'a falon tsit yayi seda suka ji tashin maganar kawu sannan Babarsu Ruƙayya ta miƙe dan ta gaya masa ga baƙo A babban falo kawu ya zauna Aliyu ya tashi tare da ajewa Umma damin ƴan dubu dubu agabanta yayi mata sallama umma tai kamar ruwa ya cinyeta dan ta kasa Motsi sabida dama ita bamai sake wa bace da surukai wajan kawu yaje a ƙasan carpet ya zauna suna gaisawa.
"Muna ta ganin abin arziƙi fa Allah ya ƙara maka buɗi ina fatima?"
Kanshi yana sunkuye yace.
"Tana nan lafiya nima sallama nazo muku zan tafi saudia bana son ku shiga shakku akaina danna tabbatar Muku da gaskiya ne yasa nazo"
Kawu addu'a ya dinga zubawa Aliyu wadda tai masa daɗi sosai yaran gidan sukai ta zuwa suna gaishe dashi su Halifa ne kaɗai basa nan Amman hatta su Ruƙayya seda suka zo suka gaishe dashi kuma duk wanda yazo se Aliyu ya bashi kuɗi.
"Kaga fa waɗannan duka ƙannen fatima ne" cewar kawu yana dariya Aliyu ya zaro ido sabida sosai abin ya bashi mamaki daya ga su Ruƙayya Dan sun fi farha girma.
Kawu ne yace.
"Amman duka tsiran su babu yawa ita fatima tana da shekaru ashirin da huɗu ne, Su Ashirin da biyu na haifa Akwai wasu a ɗakunan su, ita fatima su Biyar ne a ɗakin su sadiya nafisa fa'ieeza fatima ikram ni bana barin ƴaƴana suyi karatu mai tsawo daga sun taso Indai sun sauke kur'ani aurar dasu nake akan Fatima ƴaƴana suka fara cigaba da karatu wadda ashe jinkirin danai ban bawa salim ba kaine mai rabon, yanzu haka ƙanwarta zan bawa salim ɗin nai masa Huce zuciya"
Aliyu dai bai ce komai yaɗan duba agogon shi ya zaro ido dan lokaci ya tafi.
"To baba ni zan koma duk abin da kuke buƙata ka gayawa mai kawo muku abinci Magana in sha Allah, sannan akwai shagon da nake son na saya maka shi anan Wajan Mandawari se a zuba maka kayan abinci ka dinga saidawa ya ɗan fi zaman haka baka komai"
Kawu ya washe baki cikin Murna yace.
"Kamar kuwa ka sani Wallahi bana son zaman nan haka tunda ina da ƙarfina da lafiyata Nagode Nagode Allah yasa kafi haka"
Aliyu yayi murmushi.
"Baba kada ka damu duk abin da zan muku kamar nayi wa mahaifana na ne Allah ya saka muku da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login