Showing 39001 words to 42000 words out of 150033 words
Chapter 14 - Rabo Ya Rantse Book One Complete Hausa Novel
ta ƴan gwangwan wadda wani abokin sa yayi masa tayi a kasuwar ƴan gwangwan ta ƙofar ruwa awon Ƙarafan mota ake a fitar dasu lagos.
Ranar da Aliyu ya fara zuwa kasuwar yana bakin wani shago a zaune.
*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*RABO YA RANTSE*
*28*
*A LOVE STORY 28*
Wani Babban Mutum yazo zai wuce Sai ya yar da ƴar ƙaramar wata jaka adaidai ƙafafun Aliyu wanda yake gyangyaɗi sabida wanda abokin nashi ya haɗa shi dashi har Lokacin bai zo kasuwar ba Shi Kuma Aliyu tun safe ya dako sammako ya Zo kasuwar dan Burin shi Ko jari Bola ce yayi muddin zai sami Halaƙ ɗin shi.
Da sauri Aliyu ya buɗe idanun shi ya ga jakar sai ya ɗauka yabi bayan Mutumin Da sauri ya tare shi yana ce masa bawan Allah ka yada jakar ka Mutumin yayi farin ciki har ya bawa Aliyu kyauta wanda Aliyu yaƙi karɓa ya koma wajan zaman shi aranar ma dai Aliyu bai sami komai a kasuwar ba haka ya koma gida yana ƙunci dan ko ammi da tana masa magana banza yayi mata kuma yaƙi cin abincin dare haka da sassafe ya koma kasuwar still wannan Mutumin ya kuma zuwa kasuwar yazo ta gaban Aliyu ya wuce har ya yi nisa ya dawo ya dubi Aliyu.
"Jiya na ganka anan yau na ganka lafiya ɗan saurayi?"
Aliyu shuru yayi wa mutumin can kuma sai yace.
"Nazo neman aiki ne"
Mutumin yayi dariya.
"To ban da abin ka matashi ta ina ake samun aiki ana zaune ai sai ka motsa taso Muje Shagona"
Aliyu yabi Mutumin wani shago wanda ake sayar da kayan gyaran Motoci suka zauna mutumin ya kalli Aliyu.
"Ni sunana Alhaji Hamishi, Ni sana'a ta sayar da Motoci da kawo kayan gyaran su daga lagos da kwatano tunda na ganka ka bani tausayi ina zaune anan ƙofar ruwa matata ɗaya da ƴaƴa na mata Biyu Hasina da Hanan"
Aliyu yayi shuru.
"Baka ce komai ba"
Atakai ce Aliyu yace.
"Sunana Aliyu Ni kuma maraya ne da yayana da babata da ƙannena dansu ma na fito neman Aiki dan ina taimakon Ammi nauyi ya mata yawa"
Wannan shine mafarin Buɗewar idon Aliyu akan harkar motoci dan kunsan Komai akwai sila Alhaji Hamishi shine silar Komai na arziƙin Aliyu dan bai wa Aliyu Mugunta ba ya fara ajeshi anan shagon siyar da kayan gyaran motoci na ƙofar ruwa kafin daga baya daya ga amanar Aliyu ya ɗauke shi ya kaishi kamfanin sa dake Kan titin malam ƙato square Aliyu shine ya biya wa sadiƙ kuɗin makaranta a tare suka koma B.U.K Shida sadiƙ inda suka haɗa degree ɗinsu dama tun suna primary sunyi saukar su ta alkur'ani mai girma Suma su Bashir tuni Aliyu ya tsaya musu akan karatun su yana kammala service Ɗinshi ya fara fita kwatano yana shigo da motocin hannu yana siyarwa Ta dalilin Uban gidan shi Alhaji Hamishi wanda Aliyu ya mayar dashi uba a gare shi kullum arziƙin Aliyu bunƙasa yake lokaci Guda ya ɗauke nauyin ƙannen shi idanun shi ya bude sosai a harkar wadda harta kai ga ya soma zuwa yana siyo sabbi da kanshi ya ɗora riba ya siyar da kayan shi sabida yadda idanun shi ya buɗe a harkar.
Sannu a hankali arziƙin Aliyu ya bunƙasa tuni yabar kamfanin Alhaji hamishi ya Tsaya da ƙafar shi Haka ya siye ƙaton filin Kusa da gidan su shine ya gina wannan ƙaton gidan da suke ciki a yanzu ya dawo da ammi ciki kuma ya zuba mata ma'aikata Sannu a hankali har gidan su baba usman sai da Aliyu ya gyara shi tsaf lokacin kuma ya mayar da hankalin shi kan ginin kamfanin shi dake titin lawan danbazau wanda ya bawa sadiƙ manager Kuma rabi ma'aikatan shi ƴaƴan su baba usman ya ɗiba amman ba a san ran ammi ba.
Aliyu sun haɗu da musa kamar irin haɗuwar da sukai da Alhaji Hamishi shiyasa Aliyu yake ji da Musa sosai Kuma ya yarda dashi Kamfanin Aliyu mai suna Madaki Motors an services ya bunƙasa wajan kawo sabbi motoci na zamani dana hannu tare da kayan gyaran su Wanda kamfanin yayi suna a garin kano har ma da kewayan ta Aliyu na lagos da kwatano sadik na kano yana lura da wannan kamfani na Aliyu tare da Musa cikin haka Allah yayi wa Alhaji hamishi rasuwa Amman duk da haka Aliyu bai yada zuri'ar Alhaji Hamishi ba yana zuwa sosai matar shi mai Kirki ƴaƴan sane kaɗai sai a hankali Musamman ƙaramar hanan da sam bata da kamun kai wannan kenan.
Cikin haka Aliyu ya buɗe kamfanin sa a lagos wanda sadik ya koma can Taimakon Al'umma Aliyu yake da dukiyar shi musamman mabuƙata dan ya ɗanɗana rayuwar talauci yaji shiyasa bai taɓa wulaƙanta wani dan yana da shiba shiyasa idan yana kano kofar Gidan shi tam da jama'a Haka zalika a dangin su Kowa ya lalubo matsala wajan Aliyu zai tawo Kuma bai taɓa juyawa dangin mahaifin shi baya ba.
Taimakon su yake da su da gidan Kawun Ammi Dan duk matasan gidan daga sun taso Aliyu ke ɗaukar su aiki a kamfanin shi.
Salma tai aure wadda take Bin Aliyu zuwa wannan Lokacin Ammi tace wa su Aliyu su kawo matan aure Sadiƙ ya kawo sakina ƴar nan Ɗiso wadda ammi ta yaba Aliyu ya kawo najuwa course mate ɗin shi a B.u.k ammi taƙi amince wa sabida taga Najuwa wayayyace tace tana tsoron wadda zata raba su da Aliyu still dai bayan najuwa ya kawo wata ƴar nan galadanci nan ma ammi taƙi yarda sai yayi fushi yace ya fasa auren.
Cikin haka tajira yayar Ammi ta kawowa Ammi ziyara wadda rabon ta da ammi tun barin Ammi gidan su Lokacin da mahaifan ammi suka rasu Ammi taje fagge har ba adadi neman tajira amman bata same taba ita ko tajira tana sane da dukkan labarin halin da Ammi ta shiga amman taƙi zuwa sai da mahaifiyarta da mijinta suka rasu Taji labarin arziƙin da Aliyun Ammi yayi shine tazo dasu mami cikin wahala tana kuka Ammi ta tausaya mata suka jajanta rashin juna kafin ammi ta haɗawa tajira sha tara ta arziƙi tasa aka kaita gidanta wanda take ciki da ƴaƴan ta marayu a fagge.
Kusan koda yaushe tajira tana wajan ammi biyayya takewa Ammi kamar itace ƙanwa Aliyu yaji bai yarda da matar ba sabida biyayyarta da Kirkinta yayi yawa Amman yadda Ammi ta ɗaukake ta tana yayarta ce uban su ɗaya su kaɗai suka ragewa juna shiyasa Aliyu ya zuba musu Ido dan bama cika zama yayi ba dama.
Kamar wasa Tajira tazo wa Ammi da batun haɗin auren ƴaƴan su abin kamar aikin asiri ammi bata musa ba dole tasa Aliyu ya auri Mami ƴar wajan tajira sadik ya auri sakina suka wuce lagos Shikuma Aliyu anan yabar mami a part ɗinsa ba dan yana son mami ya aure taba sai dan Bin Umarnin Ammi amman yadda mami ke masa biyayya yasa ta sami Gurbi a zuciyar shi Ta sami ciki har sau Uku yana ɓarewa yanzu haka shekarar su ta goma da aure sadiƙ ƴaƴan sa uku duk mata salma ƴaƴan ta biyu shiko Aliyu shuru kake ji dan daga Mami ta sami ciki ɓarewa yake.
Matar Alhaji Hamishi Momcy tana ganin mutuncin Aliyu dan duk wata matsala tata data ƴaƴanta shi take Kira ta gayawa Babbar ƴar Alhaji Hamishi Hasina tayi aure ƙaramar ce kaɗai take bawa Momcy ciwon kai dan hanan bata ji kule kulen maza ga shaye shaye sabida kawai uban su ya rasu yabar Musu dukiya ta raina Momcy bata jin maganarta hakan tasa wani Bin momcy ke kiran Aliyu wanda Hanan take masifar Jin tsoron shi dan baya mata ta sauƙi ya ɗauketa kamar su salma dan baya da gate a gidan Alhaji Hamishi kuma komai na abincin Gidan shiya ɗauki nauyi hatta masu gadin Gidan shike Biyan su sosai yake kyautata wa Iyalan Gidan.
Aliyu yana son Ammi yana kyautata mata sosai baya ƙetare dokar ta ko kaɗan Sabida haka ma ko maganar daɗin aure baya wa Ammi dan bata ƙaunar yayi wa Mami Kishiya.
Ammi ita ma tana son Aliyu yadda ba'a zato ɓacin ran Ammi Biyu ne wanda take nunawa Aliyu ƙiri ƙiri in yayi na farko yazo mata da tsokanar zai wa Mami kishiya wannan Rufe Ido take ta nuna ɓacin ranta dan tana son Mami sosai sabida yadda mamin ke mata Biyayya a fili, yadda Ammi ke son mami bata son sakina matar sadiƙ haka dan ƙiri ƙiri Ammi take nuna fifikon soyayyar mami a gaban Kowa Na biyu kuma Ammi taji labarin Aliyu yayi wa dangin mahaifin shi abu yanzu zata rufe ido taita faɗa tace duk abun da sukai wa mahaifinshi baya tunawa shiko sam bai taɓa Ƙullatar dangin uban nasu ba wandaAmmi ko Ɓangaranta bata bari su shigo in sunzo sai dai suje sashin Aliyu Baba Usman ya bata haƙuri amman ta rufe idonta.
A lokacin da Suka cika shekara goma da aure tuni sunan Aliyu yayi fice a garin kano sabida taimakon sa ga al'umma yana da kamfanin sa a kano lagos da kuma abuja arziƙin sa ya Bunƙasa Yadda Aliyu keda farin jini ne yasa gwamnati mai ci a yanzu tai masa tayin siyasa da farko yaƙi amman ammi tace yayi haka ya marawa gwamnati baya wanda gwamna ya bashi Muƙamin mai bashi shawara a Ɓangaran harkarkokin matasa wanda matasan ke masa laƙani da HASKEN MATASA!
A daidai wannan Lokacinne mami ta kuma samun Ciki ya ɓare wanda shine Gidan radio ɗin da farha ke aiki suka zaƙulo labarin suka juya ya koma sharri wanda farha tai jagoran cin yaɗa labarin wanda hakan yasa Aliyu yaji gwara ya aureta kodan ya ƙuntata mata akan abin da tai masa wanda auren farha Shine kaɗai abin da Aliyu ya taɓa aikata wa wanda Ammi bata sani ba sadiƙ ma bai sani ba Kuma duka Ƴan uwan shi da suke ciki ɗaya basu sani ba mami matar shi bata sani ba, ko yaya zaman farha zai kasance da Aliyu Oho
*DAWOWA CIGABAN LABARI*
*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*RABO YA RANTSE*
*29*
*A LOVE STORY 29*
DAWOWA CIGABAN LABARI.
Cikin kasala ta miƙe daga saman gadon ta ƙarasa bakin jakar kayanta Zazzago su tayi ta ware su a saman carpet tana Ninke wa, Tana gab da gamawa aka bankaɗo ƙofar da ƙarfin gaske Farha ta saki bra ɗin hannunta tana zaro ido.
Sunkuyar da kanta tayi a ƙasa lokacin da taga Ammi a tsaye akanta fuskarta a haɗe.
"Fati"
Ammi ta kirawo sunanta.
Da sauri tace wa Ammi.
"Na'am ranki ya daɗe ina kwana"
Ammi ta ƙara tamke fuska cikin kakkausar murya tace wa farha.
"Kada kiga baba jiya ya hanani na koreki hakan ya baki damar kawo min iskanci ina son ƴaƴana duk abin da suka ce miki kiyi gaggawar yi in ba haka ba zaki tsinci kanki cikin wahala da ƙunci a tare dani"
Farha ta ƙara yin ƙasa da kanta gabanta yana cigaba da faɗuwa da sauri tace.
"In sha Allah Ammi zanyi muku dukkan abin da kuka ce"
Daga haka Ammi taja mata ƙofar tana mai ce mata.
"Ki maza kizo ki gyara mana ɗakunan baccin mu kafin ranki ya ɓaci"
Aje ninkin tayi tare da bin bayan Ammi Duk suna zaune a dinning suna break fast kallo ɗaya tayi musu sum sum ta nufi corridor ɗin da ɗakunan baccin su Ammi yake sai yau ta ƙarewa Ɗakin Ammi kallo haɗaɗɗan ɗaki kamar bana dattijuwa ba yasha kayan gado saitin farare masu tsada da kyau sai ƙamshi ɗakin yake yi Toilet ta soma wanke mata sannan tazo ta soma gyara gadon tana gamawa ta shiga ɗakin su Safna wanda anan taci wahala sabida komai yana zaune da gindinsa a ɗakin sai da ta gyara dukkan kayan su da suka birkito toilet ɗinsu kuma harda Jini duk sun ɓata shi Ta toshe hancin ta tana wanke toilet ɗin wanda kamar da gayya ma suka ɓata shi ajigace ta gama sabida tashin zuciyar da ya kamata sabida tana da ƙyanƙyami haka ta fita daga ɗakin tana mayar da Numfashi.
Har lokacin Ƴammatan suna dinning suna Cin abinci daga tsakiyar falon Ammi ce zaune da Aliyu wanda bai fita ba suna magana da Ammi tazo zata gifta taji yace mata cikin taushin muryar shi.
"Kije dinning kiyi break"
Yi tayi kamar bata jishi ba ta wuce cikin ɗakinta sabida yadda amai yake taso bata Ammi tabi Aliyu da kallo.
"Bangane taje tayi break a dinning ba ka manta akwai girkin su daban da sukeyi a ɓangaran masu aiki?"
Ya shafa kanshi sam yama mance Ammi tana wajan batare da yace wa Ammi komai ba ya cigaba da danna wayar shi dake hannun shi.
Wayar Ammi dake gefenta ce tayi ƙara ganin salma ke kiran yasa Ammi ta tashi ta nufi bedroom ɗinta su safna na ganin Ammi tabar wajan suma suka tashi da sauri ko wacce tayi hanyar Bedroom sabida ganin dodon nasu a wajan.
Miƙewa yayi duk da yana da Meeting da mai girma gwamna sannan kuma Momcy matar Mai gidanshi marigayi Alhaji Hamishi tayi masa waya akan tana neman shi.
Dinning ɗin ya nufa ya ɗauki plate ya zuba soyayyan dankali da Miyar source ɗin albasa da hanta ya haɗa tea mai kauri daya sha Ovaltine da madara ya saka tea spoon aciki ya juya ɗakin Da farha ke ciki ya nufa Bata cikin Ɗakin ya aje mata Break ɗin a saman madubi ya zauna a gefen gadon yana jiran ta fito duk da sauri yake yi amman ya rasa dalilin daya sa yake son yaga taci abincin wanda ya dangana hakan da tsananin tausayi da yarinyar take bashi shi mutum ne da baya son A bashi yarda Ya ci amana tunda tace tasan baze cutar da ita ba shikenan ta sare mata duk wata laka ta jikinsa wadda yaci buri akanta mai yawan gaske.
Tsaki Aliyu yaja yana duba haɗaɗɗan Agogon zallar azurfa na Rolex dake ɗaure a tsintsiyar hannun shi, Kafin ya miƙe ya ƙarasa Bakin ƙofar toilet yaja ta buɗe durƙushe ya ganta ta riƙe wuya tana kakarin Amai.
Ƙamshin turaren shi ne ya sanar mata tsayiwarshi a wajan.
Da sauri ta taro ruwa tana wanke fuskarta da wajan da bata iya aman bama Ta miƙe ya matsa mata hanya ta wuce zaune tayi a bakin gado tana mayar da Numfashi Ya bita da kallo bayan ya fito daga cikin Toilet ɗin.
A taƙaice yace mata.
"Wai menene hakan? ulcer ce dake kike amai baki ci abinci ba?"
Haushi ya kamata ta juya masa baya tai kwanciyarta tana cigaba da riƙe wuyanta dan har yanzu ƙarnin jinin da kuma ganin shi da tayi zuciyarta bata daina tashi ba.
Ya tako daidai saitin ta yana Facing inda ta kalla ɗin.
"Fatimah wai menene?"
Shuru tayi masa tai kamar Allah bai halittar shi a wajan ba.
Ya zube dukkan hannayen shi cikin aljihun wandon shi, kafin ya juya yabar mata ɗakin.
Yana fita kuma ta fashe da kuka ita kaɗai take magana kamar wata zararriya.
"Ya Allah! ka fitar dani daga cikin wannan hali wannan bawa naka ya cutar dani ina ji ina gani Mahaifiyar shi da ƙannen shi sun mayar dani ƴar aikin su"
Ta ƙare maganar cikin kuka bacci ne ya ɗauketa a haka ba ita ta farka ba sai azahar da wata irin haɗaɗɗiyar yunwa amman bata ko kalli inda taga abincin daya aje mata ba wanka tayi sannan ta sauya kaya ta fita Can sashin su hajjo.
Duk suna zaune wasu na Cire hancin kayan miya wasu na tuƙin tuwo ta ƙarasa tayi musu sallama Da far'a suka amsa mata murya a sanyaye tace musu.
"Hajjo ta nan dan Allah?"
Ɗahare da sakin fuska tace mata.
"Eh ga ɗakin ta can shiga tan ciki hutawa take dan bata jima da shigowa ba"
Miƙewa tayi ta nufi ɗakin Hajjo ta tarar da ita tana sallah, bayan hajjo ta idar da far'a ta dubi Farha.
"Ƴata yanzun nan nake tunanin ki fa araina bari na baki abinci nasan ba lallai kin karya ba"
Hajjo ta zubo mata kunun gyaɗa wanda yaji kwakwa tare da farfesun kayan cikin rago da doya da ƙwai.
"Maza kici ki ƙoshi ki mayar da kuzarin ki, Kinji marainiyar Allah"
Wata ƙwallah ta sauko wa Farha wadda bata bari Hajjo ta gani ba tayi sauri ta share ta ɗauki kunun sha take kamar magani gaba ɗaya tunanin Gida da Yadda tabaro Umma ya tsaya mata azuciyarta
Hajjo ganin datai kamar farha na cikin damuwa sai ta dinga bata labarai na abin dariya wanda kafin wani lokacin har ta shanye Kunun ta ci doyar sosai Anan ta shantake har la'asar tai sallah sannan suka jera da hajjo wadda zata ma su Ammi girkin dare Har Kitchen farha ta raka Hajjo wadda ta zauna tana taya Hajjo aikin Girkin haka kawai taji hankalin ta yafi kwanciya da hajjo taji hajjo kamar ƴar uwarta ta jini, Suna gama girkin wajan magariba Hajjo ta ɗiba musu nasu Farha takai kayan abincin dinning ta jera ta dawo ta gyara Kitchen Ɗin Hajjo nata shi mata albarka.
"To ƴata kije ɗakin ki kiyi sallah zan kawo miki naki abincin kinga magariba tayi"
Cewar hajjo.
"Farha ta tura baki gaba kamar yadda take ma umma in ƴan shagwaɓar suna kusa"
Cikin Muryar tausayi tace
"Dan Allah muje ɓangaranku ni anan tsoro nake ji ni kaɗai"
Hajjo tace mata babu matsala su tafi mana haka suka jera suka bar part Ɗin Ammi suka tafi nasu Hajjo a ɗakin Hajjo farha harda cire Hijabi bayan tayi sallah tayi kwanciyar ta aɗakin tuni sanyin fanka Ya saka taji wani bacci ya kamata Nan da nan ta soma baccinta a ɗakin hajjo ɗin.
Yana tafe cikin sauri sabida ya ɗan makara ya shiga motar driver yaja motar direct gidan gwamna suka je suka gama tattauna abin da zasu tattauna sai yayi kamfanin shi ya saka a hannu a wasu Motoci da za'a fitar zuwa Calaba anan ya zama busy bai sami kan shiba sai wajan bayan sallar magariba ya gaji iya gajiya ko Momcy ma sai waya yayi mata akan gobe yaje Gidan kokuma zai mata waya idan ya nutsu Kai tsaye Kuma gida ya nufa sukai sallah a