Showing 105001 words to 108000 words out of 150033 words

Chapter 36 - Rabo Ya Rantse Book One Complete Hausa Novel

lamarin kiba kada ma kice zaki ɗaga masa hankali yazo yana ɓata miki ranki, Ki barshi da abin da ke damun shi Wallahi Fatima abin da yasa kika ga yana Wannan Ɓoye ɓoyen auren naku matar shi Wadda yake aure yanzu da babarta da Ammi babansu ɗaya ammi ce ta haɗa auren kimanin shekara goma tunda sukai auren In Aunty mami ta sami Ciki kafin ta haife yake ɓarewa anyi maganin har an gaji har ɗaurin mahaifa ammata abin ya faskara wanda kin san ta silar wannan matsala ma har Gidan radio ɗin da kike aiki suka sami Labarin Ƙarya suka watsa akan shi ko?" farha ta ɗaga kanta tare da cewa "Haka ne amman ban san dangantakar shi da matar shiba gaskiya ni iya labarin haihuwar shi Md ya bani yace na watsa" salma taja ajiyar zuciya sannan ta ɗora da cewa "Fatima Mun sha wiya a rayuwa Mun taso cikin rashin gata mahaifinmu maraya ne.............seta fashe da kuka cikin kukan take bawa farha labarin su daya shuɗe seda takai aya sannan tace " Allah shine gatan mu, Ya Aliyu shine gatanmu komai da kika sani shiya tsaya mana har muka kai wannan mataki, Ammi uwace yadda tai mana ne yasa Ya Aliyu baya son ɓata mata rai baya son saɓa mata Sabida mun taso ne a rayuwa bamu da kowa se ita, Ammi ta haɗa auren Mami dashi ne sabida tana ganin mami ƴar yayarta ce sabida yadda muka taso a rayuwa yasa Ammi take tsoron kada Yaya yaje ya auro matar da zata tarwatsa mana zumunci mami kuwa kinga ƴar uwarta ce Bata da matsala a tare da ita, Yaya Aliyu yana da wadda yaso a shekarun baya amman ammi ta hana shi auren Najuwa Ammi bata son Ya Ali ya ƙara aure ko yayi maganar aure in ma haihuwa ce tace ya jira mami zata cika masa gida da ƴaƴa amman maganar gaskiya ammi bata son yaya yayi aure sabida tsoron matan zamani yadda Allah ya ɗaukaka shi tana ganin ko wace mace da zuciya biyu zata aure shi bada zuciya ɗaya ba"

Farha taja ajiyar zuciya lallai inda ranka kasha kallo a fili ta furta "To Ammi ta lissafa ba daidai ba yawanci ma wanda kake zaton bashi da matsala a rayuwarka to daga ƙarshe shi yake zame maka illah, Ai bakawa Allah dubara ƙaddarar bawa kuma bata sauyawa wannan duk ba mafita bace In Allah yaso ya jarabci ɗanta da shu'umar mace wallahi ba wayo ba dubara seya bashi, sannan shi aure muƙaddari ne daga Allah Ni yanzu na taɓa kawowa zan aure shi toni ko a mafarkina ma ban taɓa kawowa ba dan ban sanshiba hasali ma akwai wanda nake so aka tsaida maganar aurena dashi amman ɗan uwanki ya kutso akai dashi wallahi Ammi tayi ganganci To yanzu bada ban yana da biyayyar ba in yaje yayi zina fa koya yi auren ya aje matar a wani wajan fa?" salma tai saurin cewa "To baga shi ba ma ya auro ki ya ajeki agidan kuma bata sani ba nima dai naga Wannan Ƙudiri na Ammi sam bai yiba wallahi" farha taja ƙaramar ajiyar zuciya tare da cewa "Ai a matsayin ta na uwa addu'a zatai masa akan Allah ya bashi mace tagari bawai ta tsaya akan mami kaɗai ba ita mamin wahayi akai mata aka ce lallai ta garin ce? zuciyar mutum se Allah, Ni dai Allah ya sani ina son Mijina kuma tun kafin nasan asalin shi waye na soshi, amman inna ga da matsala zan nemi ya sakeni dan wallahi nagaji kullum ina ɓoye a ɗaki Kullum ban da ƴanci Koda yaushe Cikin fargaba nake idan Ammi bata san auren mu yanzu ba yaushe zata sani toni nagaji shi ta zamewa dole yayi mata biyayya bani ba kawai ni ya sake ni yaje ya zauna da wadda mahaifiyar shi take so take kuma burin su haihu tare" farha ta faɗa daɗan Ɓacin rai salma ta sassauta Murya tare da cewa "Nifa ban gaya miki maganar nan dan ki je ki ɗagawa mijin ki hankali ba kija min masifa kuma kada ki sake maganar saki dan babu kyau batun Biyayya ga ammi kece zaki ƙara nusar dashi hanyar yiwa mahaifiyar shi biyayya Dan ya gama da ita lafiya abin da ya shafi yaya ke ma ai ya shafeki Bazan Ɓoye miki ba yaya ya auri mami ne dan biyayya ba domin yana son taba kuma auren ku da yaya ze zamewa Ammi izna taga duk yadda taƙi yayi auren daga ƙarshe ya auro mata matar da take zaune da ita batare data san matar sa bace ba wannan ma babbar izna ce gareta dan Allah ki kwantar da hankalin ki kada ma Ki sa damuwa aranki na gaya miki waɗannan maganganu ne dan hankalinki ya kwanta da wasi wasin da kike na hayar iyaye da yaya yayi sannan na gaya Miki ne dan Kisan waye Mijinki dan shi be zama lallai ya gaya Miki ba"
Farha ta kwantar da kanta a jikin Pillow lallai akwai matsala har salma ta gama maganganunta ta fita bata iya magana ba, Gaba ɗaya tunaninta ya tsaya ammi wace irin uwa ce Murmushi mai ciwo ta saki Su a iya fahimtar su kenan akan ammi Amman ita fahimtar datai Ammi ta hana Aliyu yayi aure ne dan kada acika gida da ƴaƴa Mamin ma abin da yasa ta saki hankalinta da ita dan tana samun ɓarin ciki ne amman ita fa a yadda ta Zarga kenan acikin ranta Hawayen tausayin Mijinta taji yana zubo mata lallai suna cikin gagarumar matsala ita dashi dan tun yanzu ta fara Missing ɗinsa dan tabbas data sami dama sedai yaga wayam dan zakara bata sa'a zeyi ita ba zata iya auren rashin ƴanci ba dan a yadda yake shakkar mahaifiyar shi ɗinnan bata hango narasar ƴancin su anan kusa to gwara tai ta kanta Tun wuri kada ma tazo ta sami Ciki Azo a sami matsala, Dama haka yasha wiyar rayuwa dama haka suka taso lallai duk wanda yayi haƙuri ze sami nasara ta tausaya masa a yadda taji tarihin sa lallai Bayan wiya se daɗi tana nan a kwance salma ta shigo cikin shirin fita taɗan kalleta.
"Ni zanje wajan ɗinki su Dady kuma zunje aski da Babansu gashi gidan yayi shuru ga wayata zan baki ko Mijinki ze kira dan ya kikkirani kina bacci ni kuma naƙi tashin ki"
Salma ta faɗa tana miƙa mata wayar ta sukai sallama salma ta fita kwanciya Farha ta kuma yi tunanin mafitar ta cike acikin zuciyarta tabbas ya zama dole ma ta samowa kanta mafita wata sabuwar tsanar Ammi taji acikin zuciyarta Har akai sallar la'asar tana faman tunani tashi tayi lokacin data ji Kiran sallah tayi sallah ta fita falo mai aikin Salma nata Gyaran kayan miya a kitchen gaisawa sukai da Farha wadda ta zauna taɗan kalli mai aikin salma cikin sakin fuska tace "Dan Allah Ko akwai tsakin ɗan malele agidan nan?" Mai aikin salma taɗan zaro ido tana dariya "A,a babu amman in kina so sena Miki da semo shima yana daɗi" farha taɗan haɗiyi yawu tare da cewa "To dan Allah ki sakan salak da tumatur ana shan ruwa shi zan fara sha" mai aikin salma tana dariya tace to farha tashi tayi ta koma ɗaki se gab da magariba salma ta dawo suko su dady ma seda aka idar da sallar magariba suka shigo Gidan Ana shan ruwa farha da wannan ɗan malele tasha ruwa tasha sosai kuma taji daɗin sa salma se dariya take mata lokacin data shigo ɗakin taga farha ta zage tana ta shan ɗan malele Tana kuwa gama sha gudawa tace salamu alaikum Ta dinga shiga Toilet tana yin sallar Isha'i ta kwanta cikinta se ƙugi yake mata ba komai bane yasa hakan face yaji data danƙara a ɗan malelen wayar salma dake Gefenta wadda har Lokacin salma Bata amsa ita ke Ringing ta ɗauki wayar taga special Number ce bama ta ƙasar nan ba ta mayar da wayar ta aje bata ɗauka ba.


Aliyu yana kwance.............*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*A LOVE STORY 86*

A cikin ɗakin hotel ɗin daya sauka Pillow ya danne da ƙafafun shi se ƙaton Bargo fari tas daya rufe jikin shi dashi gefen shi cup ɗin black tea ne wanda yake ta turiri tunda aka kawo mai bai shaba tunda ya dawo daga masallacin harami yake kwance Tunda bai samu wuce wa chaina ɗin ba ya zauna anan saudia addu'a yake tayi sosai akan lamarin shi da fatima da kuma neman Allah ya inganta mai cikinsa dake Jikinta Kuma Alhamdulillahi yaji tana ta kwanta mai aran shi ga kuma damuwar cikin nata da kullum ke manne aran shi ji yake dama da ita ya tawo sabida Baya tare da Mami a halin yanzu ita tana tare dasu Ammi.

Tashi yayi zaune tare da zube dogayen ƙafafun sa a ƙasa shi kuma yana zaune a saman gadon Jikinsa sanye da ƙaramin wando wanda ya manne masa a iya cinyarsa wadda ta cika da tarin Gargasa wadda ta kwanta tai luff baƙa siɗik se singlet fara wadda ta fito masa da gabaki ɗaya halittar dake faffaɗan ƙirjinsa mai cike da kwantacciyar Suma baƙa tai luf Nippy ɗinsa baƙaƙe zagaye da sumar suma kana kallon shi kasan lafiyayyen namiji ne mai ji da ƙarfi da lafiya wanda yake cikin ganiyar shi ta matashin namiji mai jini ajikinsa hannun shi yasa wanda yatsun hannun guda biyu suke ɗauke manya manyan azurfofi masu tsada ajikinsu ya tallafe ƙugunsa ya janyo Ƙasan leɓansa da harshensa yana tsotsa ita kaɗai yake gani a idanunsa Ji yake kamar ze rufe ido ya ganta wata irin wutar soyayyarta ke cin zuciyarsa Number ɗin salma yake ta kira har Lokacin ba'a ɗagaba tsaki yaja yafi kala goma idan baiji Muryarta ba akwai matsala gagaruma a tare dashi Muryarta kaɗai ce zata saukar masa da Azabar da yake ji a gangar Jikinsa.

Tsotsar ƙasan leɓanshi yake yana sake Kiran Number ɗin salma, Farha taja tsaki ƙarar wayar ta hanata bacci Mai yasa ma Aunty salama zata ajemin wayarta a wajena tasan ai ba kirana yake yi ba yau kusan kwana ashirin da Biyar ai bai kirani ba se yau taja tsaki sabo ta Toshe kunnenta da hannunta wayar dai na ƙara Ɗaukar sabon kiɗa na alamar ana kira kamar zata ce wayyo Allah! tai picking call ɗin shuru tayi Aliyu ya ja ajiyar zuciya tunda yaji shuru yasan Gimbiyar tasa ce ƴar rigimarsa dan inda Salma ce da sallama zata ɗaga da gaisuwa.
"Fatima Ina yini" taji Muryar shi Wayyo daɗi Nutso tayi a saman gadon taja Pillow ta matse tana sakin Numfashi a hankali shuru tayi masa iya muryarshi ma kaɗai ta wadace ta a halin yanzu.
"Fatimahhhh" yaja sunan wanda taji Numfashinta yana ƙoƙarin ɗaukewa yama za'ai ta barshi ai kawai faɗa tayi ba zata iya barin saba son sa a jininta yake tana sonsa kamar Bugun Numfashinta.
"Kina fa jina dan Allah ki kulani Kimin magana Wai meye haka sabon raini kika Ɓullo" ya ƙarasa maganar Cikin faɗa amman bawai mai nuna yaji haushi ba.
Sangarta shagwaɓa ta motsa se kawai ta ɓare masa baki tahau Kuka ƙasa ƙasa mai cike da ɗaga hankalin ma'abocin sauraron shi wayyo Allah! nan da nan ta ɗagawa marayan Allah hankali tashi yayi tsam daga zaman da yake ya shiga sintiri a ɗakin yana yarfe zufa kukan yarinyar ɗaga masa hankali yake tunda can ina ga kuma wannan Lokacin da take ɗauke da ajiyarshi Cikinshi Gudan Jinin shi.
"Shiiiiiiiii wai meye haka Okay so kike nima nayi kukan ko? ko so kike na Shiga cikin damuwa da tashin hankali?" ya faɗa da narkakkiyar Muryarshi mai kama data wanda yake jin tsananin sanyi ga kuma raɓa da tsananin sanyin na Bugun ƙashin sa da Jikinsa to haka muryar tashi tayi kala, "Nifa kawai kukan Daɗi yake min na rasa me yasa Ya zama abokina" ta faɗa tana turo bakinta gaba yayi Murmushi yana jin Nutsuwa da wata kasala tana rufe shi ya koma da baya ya zauna a saman gadon se Kuma ya kwanta tare da ɗaukar Pillow ya ɗauro a saman Ƙirjinsa ya matse shi ya damƙe wayar"Fatima ta rigimar ki se ni ɗin to yaya kike kullum idan na kira salama se tace kina bacci Dafatan kina lafiya?" ya faɗa yana lumshe ido "Lafiya lau Alhamdulillah yaya ibada Allah ya amsa" ta faɗa wayar tai shuru sabida su duka shurun sukai "Tom yaya Kika koma yanzu nasan Kin ƙara girma Ko Jikinki yayi kyau?" kunyar maganar tashi taji dan haka tayi masa shuru se can Kuma kamar wadda ta tina wani abun tai saurin Ce masa "Kasan me?" ya girgiza kai kamar tana gabanshi kafin yace "Sekin gaya min" ta ɗan yi raurau kamar zatayi masa Kuka "Wallahi Abu fa se ta'azzara yake shine nace gwara na gaya maka sabida kana ƙasa mai tsarki kayi mini addu'a" yaɗan Yamutsa fuska duk bai gano mai take Nufi ba "Ban fahimce kiba Fatima?" ya faɗa a hankali "Dama wannan tsutsar ta ciki daka ce nake cin ayaba ka tuna?" da sauri yace "Yes na tina tana girma ne Kokuma yaya ake ciki duk na damu da ita nima" ya faɗa yana toshe baki dan dariya ce taso Kama shi ta gyara kwanciya tare da damƙe wayar da ƙarfi kafin tace masa "To wallahi girma take yi Cikina yay ta Motsi Kullum gashi daga sama Yana kumbura Cibiyata ma Duk ta ƙara Fitowa gashi naita bacci Kullum sena ci ayaba da yawa ɗazu dai nake gayawa Aunty salama shine take cemin Ko ina da ulcer ne wai itama tana haka mutum yayi ta Jin ma kamar yanayin yana da Ciki" tashi yay ya zauna ya jima bai ji dramar fatima ba A hankali yace "Alhamdulillahi wannan tsutsar ciki mai abin al'ajabi haka ta koma miki kuma kice lallai semun tashi tsaye, to koke ma cikin gareki ne?" da sauri ta wani zaro ido kamar yana gabanta "Ciki kuma angaya maka a ruwa ake sha Daga aure se ciki to ko Yaya sadiyarmu ma seda tai wajan shekara Uku sannan ta haihu fa haka suma su Ya Nafisa ai daga aure ba'a samun ciki da wuri" Da sauri yace "Haka aka gaya miki kenan?" ta wani haɗe rai "Nidai kabar wannan maganar yanzu addu'a zaka min da magani Ko yaya?" yayi Murmushi "Duka zan Miki nima wannan Tsutsar da ita nake kwana nake tashi amman dai kina cin ayabar sosai ko?" Da sauri tace "Eh duk da bana son ta amman haka nan nake daurewa" yayi murmushi fatima da sauranta Shirme ne da ita ace kana ɗauke da Cikin Mutum ka kasa fahimta Lallai da sauranta Shikuma zeta Shigar da ita akan Tsutsar Ciki ce har sanda Cikin ze Fito a Lokacin ta farka daga baccin daya ɗauke ta.
"To Kina cin farar ki kuwa? dame dame kike ci yanzu?" ya tambayeta "Hmm yauma ɗan malele akai Min wallahi naci bakaji daɗi ba Aunty salama tana kula da ni kome nace mata tana Min yau ma ta amsa size ɗin kayana ta kai mana Ɗinkin sallah" Ya saki fuska cikin Jin daɗi yace 'Ai na gaya miki a kaf ƴan uwana ba kamarta wallahi Nasan zatai Miki fin haka Kuma nagode sosai Amman kin san dai ba anan zaki sallah ba" ta wani haɗe rai tana hararar gefe "To a ina zanyi?" ta faɗa kamar zatai kuka "Gidan Ammi nan da kwana Biyu Zan dawo ana Jibi sallah kuma dana dawo ma Ki shirya tanan zan Biyo ƙafata ƙafarki................*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*

*A LOVE STORY 87*

Ya faɗa batare da wasa a maganar tashi ba, Lokaci kaɗan hawaye suka wanke mata fuskarta "Baki jin me nake gaya miki ne kika min shuru fatima?" turo baki tayi gaba kamar yana gabanta "Ni kika yi wa shuru?" ta kuma jin muryar shi wannan karon a tausashe yayi mata maganar"Toni me kake son nace maka?" ta tambaye shi cikin sigar sakalci ya sauke ajiyar zuciya tare da cewa "Ce maki nayi dana zo zamu wuce gidan Ammi Naji kin min shuru ne baki magana ba" Ta shaƙi hanci tare da cewa "To naji Allah ya kaimu amman ni har ga Allah ana shiga haƙƙina" cikin sauri yace mata"I don't understand you, I am intruding on your rights like that kimin yadda zan fahimta" ya faɗa muryarshi can ƙasa kanta tsaye tace mai "Sabida ni nagaji da zaman gidanku mahaifiyarka bata sona babu sunan da bata haɗani dashi ba har Igiyar shanya ta kirani dashi sabida haka Ni wallahi na gaji Kullum ina ƙunshe a ɗaki Inna fito bauta na fita yi mata ita da marasa kunyar ƴammatannan To yaushe zan sami ƴanci kamar ko wace mace, Ni harga Allah in ba zaka barni anan gidan ba to sedai a rabu danna gaji agaskiya ana ƙwarata" ta faɗa tana murguɗa bakinta Aliyu ya sauke wayar daga Saman kunnensa ya kalli Number tabbas da fatima yake magana wato koda yaushe rashin Kunyar yarinyar ƙaruwa yake ya daure ya danne abin da yake taso masa sabida furucinta na se a rabu ɗinnan ya kaɗa shi matiƙa.
"Fatima"
Yaja sunan a hankali.
"Ina jin ka" itama ta faɗa muryarta babu sassauci.
"Cewa zaki na'am ba ina jinka ba tunda bada yaro ƙarami kike magana ba da Mijinki kike yin magana fatima"
Ya faɗa a hankali.
"To Na'am Mijina" ta faɗa a gatse ya saki murmushi mai ciwo wai kamar shi yarinya ƙarama zata mayar kamar sakarai shi kuma ya biyewa shirmenta lallai haka rayuwa take Kodan akan ta yasan so akan ta ya fara soyayya oho!
"Fatima na kiraki dan hankalina ya kwanta danna sami Nutsuwa amman shine zaki ɗaga min hankalina idan har zan kiraki Na sami ɓacin rai to inda kike ma sena guji zuwa sabida bana son ɓacin rai a rayuwata Kuma na baki haƙuri akan abin da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login