Showing 69001 words to 72000 words out of 150033 words

Chapter 24 - Rabo Ya Rantse Book One Complete Hausa Novel

yi mana Dan bazan ajeta ba aikin fari bare na baƙi ba sannan na ɗauki albashi na bata ƙarshen wata Ɗakunan namu ma yaushe rabon data gyara mana ehe"
Ammi ta faɗa tana Hararar Farha data ƙi ɗagowa ta kalleta Murya a hankali tace mata.
"Ki haƙuri Ammi yanzu me zan dafa muku?"
Ta faɗa kamar zatai kuka.
Da sauri ya katseta da cewa
"A,a tashi jeki ɗaki bara a siyo musu kawai lokaci ya ƙure"
Ta dafa ƙasan tiles ta miƙe tana Cije baki ta bar falon Aliyu yayi wa wani yaron shi waya akan yayo masa order abinci Minti kamar talatin yaron nashi ya kawo abincin Da kanshi ya tashi yaje ya amso Ledojin da abincin ke ciki ya miƙawa Ammi wata daban kuma ya bawa safna yace ta miƙawa Farha ta amsa tana tura baki ta nufi ɗakin daga bakin Ƙofa ta wurga mata Ita kam farha kwanciya tayi tana kuka shiyasa bata ma ji shigowar Safna ba bare tasan abin da ta aikata matan.

Gaba ɗaya tunanin Farha shine yaushe zata sami ƴanci yaushe ze dena ɓoye ita matarshi ce abin da ya ƙara fusata ta shine halin Ko in kula daya nuna mata bayan ko wace mace idan ta tsinci kanta a ƙwaryar manya Mijinta yana tsayawa ya riritata ya kula da ita amman ita jiba yadda ya barta kamar ma ya manta abin da ya aikata mata tabbas maganar daya faɗa mata gaskiya ce daya ce mata baya son ta da gasken yake don inda yana son ta baze taɓa yi mata haka ba.

Ammi ta dubi Aliyu cikin faɗa.
"Amman baba me yasa zaka min haka? damu da ita ɗaya ne?"
Ya haɗe rai sosai ya watsawa su safna Mugun kallon daya sa suka miƙe jikinsu na ɓari suka bar wajan ya dubi Ammi har Lokacin Fuskar shi babu walwala.
"Ammi menene abin nuna fifiko ga wanda baka san waye a wajan Allah ba? danna ɗauka mata abinci acikin naku shine matsala to Ammi ki haƙuri Da laifin dana yi"
Ta hayo masa ka da maganarta mai ƙarfi.
"Naga fa abun naka yayi yawa ga Kitchen nan tazo ta girka nata mana dole abin da muka ci shi zata ci salon raini ya shiga tsakanin mu to wallahi ka kiyaye ni Ka shiga taitayin ka ka kama kanka ka fita daga sabgar yarinyar nan tun kafin na saɓa maka"
Ya rasa me yasa Ammi ta ƙi jinin fatima kuma de yarinyar ba rashin Kunya takewa Ammi ba amman baki ɗaya ammi tabi ta tsaneta ya fuskanci har yaran Ammi su safna ma sun Tsaneta.
"Ammi bazan kuma ba ki haƙuri"
Ya faɗa cikin mutuwar Jiki Ammi ta kauda maganar tana cewa.
"Niko me akaiwa Mami ne tunda ta dawo bata shigo Min ba nida ɗazu ma zanje naji lafiyarta"
Ya taɓe baki tare da cewa.
"Nima ban san meya hanata zuwa nan ɗin ba duk tabi ne ta damu kanta akan rashin haihuwa ɗazu ma kuka ta gama yi maybe ko wannan matsalar ce data ɗora damuwarta akai yasa ta ƙi shigowa kin san wani in yana cikin wani yanayi baya shiga cikin mutane"
Ammi tace
"Haka ne ai ba ita kaɗai ba kowa ma burin sa ai ka haihu kaima muga naka ɗan Allah dai ya nuna mana wannan rana in kaje ka turon ita nai mata nasiha"
Ya jinjina kai yana cewa.
"Da aure da haihuwa da mutuwa duk Lokaci ne Allah ya bamu waɗanda zamu iya dasu shi kuma Allah ya iya mana gaba ɗaya Kuka ai bashine ze bata ƴaƴa ba Allah ne mai badawa Ammi ina son haihuwa amman wallahi bana ɗagawa kaina hankali akanta dan nasan daga Lokacin yayi Allah ze bani"
Ya faɗa yana Lumshe ido.
Ammi cike da tausaya mishi tace.
"Haka ne baba Nina sanka akwai tawakkali In sha Allah mami zata cika maka gidannan da ƴaƴa masu Kyau irin ka harma da biyayyarka"
Yayi Murmushi yana shafa kai bai dai ce Komai ba.
Miƙewa Ammi tayi "Bara naje nai wanka naci abinci ka ƙaraso daga ciki mana naga kamar yau ba zaka fita Office ba"
Ya bita da ido be magana ba sabida yadda ya matsu ta tafi yaje Inda zuciyarsa take muradi...........

*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*

*A LOVE STORY 53*

Sakin ajiyar zuciya yayi mai ƙarfi lokacin daya tabbatar Ammi ta ƙullewa ganin sa a hankali ya miƙe tare da nufar ƙofar ɗakin yana murɗa handle ɗin yaji ta a buɗe ya shiga ya sanya key ya rufota yabar key ɗin ajiki a tsaye ya tsaya a kanta hannunsa duka a cikin aljihun trouser ɗinshi kukanta yake sauraro wadda ita sam bata ma san da shigowar shi ɗakin ba, Sannu A hankali ya zauna a gefen gadon yasa hannun shi ɗaya ya tallafe Fuskarshi dashi gaba ɗaya jikinsa yayi sanyi da yadda yaga lamarin nata har Kusan minti ashiri yana zaman jiran ta gama kukan suyi magana ganin bata san yana wajan ba yasa ya matsa Kusa da ita ya janyota jikinsa.

Idanunta har lokacin a rufe suke kuma se ƙoƙarin tashi daga jikin nashi take sedai yadda yabi ya kanainaye ta ya kasa bata damar Miƙewa.
"Shiii fatima, wai meye haka kukan ya isa haka kada kanki yayi miki ciwo"
Ya faɗa yana share mata hawayen nata da tafin hannunshi.
Juyawa tayi ta dena kallon saitin Fuskarshi yayi Murmushi.
"Au wai kukan nawa ne, To naji nayi laifi amin afuwa bazan kuma ba"
Ya faɗa sanda yake ƙoƙarin Juyo da ita facing ɗinshi ya taɓa wuyanta akwai zazzaɓi sosai ajikinta Miƙewa yayi bayan ya sauketa daga jikinshi ya koma toilet ɗin ruwan ɗumin ya kuma haɗawa ya dawo ya ɗagata cak shiya taimaka mata wajan rage kayan dake Jikinta duk Kunya ta gama kamata haka ya kuma dannata acikin ƙaton bawon dake shaƙe da ruwan Ɗumi ta jima aciki shikuma yana tsaye a kanta seda ya sauya mata ruwan har sau uku sannan ya ɗaukota suka fito cikin ɗaki saman gado tahau tana rawar ɗarin zazzaɓi ya ƙarasa gaban kayanta ya ɗauko mata Doguwar riga da ƙyar ta yarda ya saka mata.

Ya sunkuyo daidai Fuskarta cike da tausaya mata.
"Me zaki ci yanzu ina Break fast Ɗin da safna ta kawo Miki?"
Ta zubo da hawaye.
"Ni bazan ci komai ba bakina ma kwata kwata babu daɗi"
Ta faɗa tana jan Bargo ta rufe duk Jikinta.
Ya ƙarasa inda takeaway ɗin take yashe ya ɗauka Doya ce aciki da ƙwai ya tabe baki ya aje a saman Madubi ya fita daga ɗakin tare da rufota da Key gudun kada wani ya faɗa mata yaga halin da take ciki.

Mota ya shiga bayan ya saka face mask ya boye Fuskarshi da kansa yaje ya siyo mata ɗan abinda zata ci marar nauyi ya karɓo mata magani a pharmacy bayan yayi wa likita bayanin halin da take ciki Lokacin daya ƙaraso ana kiran sallar la'asar seda yayi sallah sannan ya wuce koda ya ƙarasa falon Ammi su safna na dinning suna cin sauran abincin ɗazu dan ba'ai girkin ba Ammi Kuma tana ɗakinta ya zauna a falo ya wayance da danna waya ganin yanayin sa yasa suka Miƙe har suna rige rigen barin wajan ya Tashi ya nufi ɗakin farha ya buɗe ya shiga ya rufo Ƙofar tana zaune ta idar da sallah a gabanta ya tsugunna bayan ya aje kayan hannun shi ya taɓa Goshinta yana cewa.
"Yaya yanayin jikin naki?"
Ta ɗan kalle shi gaba ɗaya taga ya sauya mata duk Jikinsa a sanyaye har faɗawa idanunshi taga yayi.
"Da sauƙi Alhamdulillahi"
Ta bashi amsa bayan ta kawar da kanta dan gujewa mayen kallon da yake faman binta dashi.

Ya Buɗe Ledar hannun shi ya fito mata da robar farfesun Kayan cikin rago da soyayyen dankali se kaza Wadda aka gasa mai romo se shinkafa da miyar hanta gaba ɗaya ƙamshin abincin ya cika ɗakin ya zauna a gabanta ya tanƙwashe ƙafafun sa.
"To wanne zaki ci anan Nasan baki ci Komai ba"
Ta lumshe idanu sabida yadda yayi mata maganar cikin kulawa yayi mata ita.
"Shinkafar nake son ci dan yunwa nake ji sosai"
Ta faɗa tan haɗiyar yawu.
Yayi Murmushi.
"Farfesun fa?"
"Shima zanci duka"
Ya ɗauki ƙaramin spoon ɗin cikin abincin ya buɗe robar yana ɗiba yana bata a hankali ta Noƙe taƙi amsa yaɗan harareta da sauri ta amsa tana ci tun tana jin kunya harta ware tana cin abincin ganin ta soma ƙoshi ya tura mata farfesun gabanta wannan karon da kanta taci Kuma taji daɗin bakinta ruwa ya buɗe mata tare da magungunan daya amso mata duka na gajiya ne da rage raɗaɗi ta amsa tasha zata kwanta ya hana yace ta bari abincin ya narke turo baki tayi ta juya masa baya itafa ya soma isarta haka ya hanata ta kwanta seda yaga ta soma bacci a zaune sannan yace taje ta kwanta aiku nan da nan bacci ya ɗauketa wanda bata samu a daran Jiya ba Ƙarfin Fanka ya ƙara mata sabida Ac'n ɗakin ta lalace ya tattare kayan abincin ya aje a gefe ya Rufe mata rabin Jikinta ya fita daga ɗakin bayan ya rufo shi.

Cikin gidansu mahaifin shi ya je Kuma ya sami ƙannen Babansu duka a gida zama yayi suna gaisawa Kuma da alamun sunji daɗin zuwan nashi nan da nan yara da manya sukai ta fitowa suna Mishi sannu da zuwa matan kawunan shi suka fara jere masa kwanukan abinci agaban shi ruwa kaɗai yasha ya fuskanci Hirar da Baba usman keyi masa.
Wadda Godiya yake masa akan hidimar da yake yi musu yaɗan yi murmushi.
"Baba kada ka kuma yi min godiya ai in ban yi muku ba wa zan yiwa Kune fa kuka fito ta tsatso ɗaya da mahaifinmu wallahi Ku nakewa kallon Baba a yanzu"
Albarka suka haɗu suna sanya mashi acikin Gidan sukai sallar magariba wadda Baba Usman yaja su bayan sun idar ganin ba wata matsala a gidan Komai suna da dan hatta sola ya sanya an Musu ko ina haske ga gida yasha gyara.
"Baba zan koma ko akwai wani abun?"
Baba Usman yayi Murmushi
"Haba Aliyu ba komai wallahi dan kayan abincin da ka sa aka cika mana store dashi ko rabi bai ƙare ba Komai akwai shi Alhamdulillah"
Sauran ma suka haɗa baki wajan yi masa godiya ya fita ya shiga Gidan kawun su Ammi nan ɗin ma yaɗan jima dan har isha'i yana cikin Gidan yana fitowa yayi sallah ya koma Gida ya shiga Mota ya kuma siyowa farha abinci da fruit, A mota yabar su seda Ya shiga Part Ɗinshi yayi wanka ya sauya kaya dan duk wanda ke Jikin shi sun dame shi ya sauko ƙasa Mami ya tarar zaune Cikin shiri da ƴar ƙaramar akwati a gabanta.
"A,a mamy lafiya na ganki kamar me shirin Fita wani waje?"
Kuka ta ɗan ƙaƙalo mai sauti.
"Mama ce ta faɗi a napep shine zanje dubata ƙila ma na kwana tunda Ta bugu sosai"
Ya zauna yana cewa.
"Subuhanallahi garin yaya yaushe hakan ta faru?"
Ta goge hawayenta tana cewa.
"Ɗazu nan Hassana take gaya Min gashi suma basa gida suna Ƙauye ita ma Amir ke gaya musu dole Ni zani na kwana dama kai nake jira kazo"
Ya kalleta.
"Ita ma dai ina motar dana bawa Amir ɗin nace ya dinga kaita Unguwa ya kamata ta daina hawa Motar haya"
Mamy da sauri tace.
"Ai ta lalace Motar"
Ya Haɗe fuska"Shine baki gaya min ba me yasa?" ta kama wasa da yatsunta don motar Tuni sun siyar sun Miƙawa Bokaye  Kuɗinta
"Ok Next week Musa ze kai musu wata Kije driver ya kaiki Ki mata sannu kafin nazo Musa ze kawo Muku saƙo Gobe"
Godiya ta fara yi masa ya ɗaga mata hannu dan baya so ta miƙe ta fita daga falon Driver ta kira ya tafi kaita Gidan nasu.

Ya miƙe bayan fitar Mami Saman shi yahau ya gama abin da zeyi ya rufo Ɗakin ya kashe hasken Falo har na ƙasa ya Rufe falon ya fita daga part Ɗin Ya je Mota ya ɗauko abin da ya siyo ya shiga Sashin Ammi ba kowa a falon dama basu fiye zaman falo ba Haka ya Shiga wajan Farha ya rufe Ƙofar ya kunna hasken Ɗakin..................*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa  wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank,  idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*A LOVE STORY 54*

Tana ta baccinta har Lokacin ya aje ledojin hannun shi ya ƙarasa gefen gadon ya zauna bayan ya zaro wayar shi daga cikin aljihunsa wadda ke faman yin ringing!
Momcy ce matar Marigayi Alhaji Hamishi uban gidan shi rejecting ɗin kiran nata yayi shi ya kirata.
"Assalamu alaikum"
Ya faɗa daga ɓangaren Momcy ta amsa cike da damuwa.
"Wa'alaikassalam, Aliyu baka samu ka shigo ɗin ba kuma ina ta jiran ka"
Ya shafa kanshi kwata kwata ya manta.
"Ki haƙuri in sha Allah zanzo na manta ne"
Momcy tace masa.
"Dama nasan ka manta ne dama maganar Hanan ce"
Aliyu yace.
"Ina sauraron ki ko dai sena zo ɗinne?"
Momcy tayi saurin cewa.
"A,a bari kawai na gaya maka, Yau kwana biyu da Hisba ta kamasu a Wani gidan shaye shaye ita da ƙawayenta dama shine wayar da nake ta yi maka Amman Alhamdulillahi Mijin Hasina yaje da ƙyar suka bada ita"
Aliyu yaji ya kaɗu da wannan magana wato har iskancin Hanan yakai haka.
"Innalillahi wa'innah ilaihirraju'un Allah ka shirya mana zuri'a ki haƙuri kada ki mata baki dan Allah addu"a kaɗai zamu yi mata"
Momcy ta fashe da kuka tana cewa.
"Ina wa Allah godiya daya bani Hanan Amman wallahi lamarin ta ya isheni dama zata mutu na huta"
Da sauri ya katse ta da cewa.
"Kada ki ƙara faɗin haka domin Kamar Kin gaji da jarrabawar Allah ne dan hanan jarrabawace gareki Kuma in sha Allah komai ze zamo labari"
Da sauri momcy tace.
"Aliyu yaushe wannan labari zezo kwata kwata na rasa halin wata ɗauko yarinyar nan mahaifinta Mutumin kirki ne kowa yabon sa yake wallahi Hanan bata yo halin mu ba"
Aliyu yayi murmushi me ciwo kafin yace.
"Momcy sedai ki haƙuri, Tun asali kece da laifi domin Kin sakarwa su Hanan batare da kina kwaɓar su a matsayin ki na uwa ba, Sau tari zanzo gidan Hanan tace Miki zata fita baki taɓa tambayarta ina taje ba Sau tari zaki ganta da ƙawa baki taɓa cewa ina ta samo wannan ƙawar ba sau tari zata fita school baki taɓa Bibiyarta a makarantar ba, Sannan kuma da mahaifinsu ya rasu mai yasa zaki damƙa Musu dukiyar mahaifin su batare dakin saka wani na juya musu ba to Kinga duk ire iren waɗannan Abubuwan sakacin daga wajan kine dama in uwa bata saka ido akan ɗanta irin hakan tana faruwa"
Ya faɗa a hankali.
Kukan ta cigaba dayi domin dukkan maganar shi akan tsari take.
"Haka ne Aliyu Amman yanzu ina kan gyara kai dai ka tayani addu'a"
A tausashe yace.
"In sha Allah ina hanan ɗin bani ita"
Momcy ta miƙawa Hanan wayar.
Shuru Hanan tayi tana hararar wayar.
"Nasan kina jina ko to wallahi Ki shiga hankalin ki kuma lallai acikin ƴan iskan mazan da kike bi ki gaggawar fito da Mijin aure in ba haka ba sadaka zan bada ke Sakarai marar tunani"
Kashe wayar yayi yana jin zuciyar shi babu daɗi bai so wannan ƙaddara ta faɗawa ƴar gidan mutumin arziƙi kamar Alhaji Hamishi ba.

Tunda ya kunna hasken ɗakin ta farka sedai tai shuru ne sabida tsoron haɗa ido take dashi Musamman daya shigo mata adaidai irin wannan Lokaci Rawar Jikin tace ta ƙaru.
Ƙara kasa kunne tayi lokacin da taji yana wayar ta rasa dasu wa yake wayar wadda tasan bada ƴan gidansu bane Jitai ta damu data san wacece Hanan ɗin data ji ya ambata tunda sunan matar shi Mami.
To wacece hanan meye halaƙar shi da ita da har yake zaƙewa akan lamarin yarinyar.
Taɓe baki tayi a zafafe ta tashi ta dira daga saman gadon toilet ta shiga wanka tayi sabida taji ƙarfin Jikinta ta ɗauro alwala ta fito har Lokacin yana zaune yana danna wayar shi ta sauya kaya a toilet ta fito fuskarta a ɗaure ta shinfiɗa darduma ta tayar da sallah ta idar ta miƙe ta tsaya a saman kanshi ganin bai da Niyyar magana.
"Ka tashi ni zan kaɗe gado na kwanta"
Ta faɗa tana hararar shi.
Bai kulata ba se ji tai ya janyota jikinsa ƙamshin turaren shi ya cika hancinta ta Lumshe ido gabanta yana faɗuwa.
Ya ja hancinta yana aje wayar shi a gefe.
"Fatima sarkin tsiya to anan zan kwana"
Zaro ido tayi tana Jin ƙirjinta yana mata wani irin duka da ƙarfin gaske.
Kafin ta aro jarumtar furta masa.
"Nidai kai tafiyarka dan Allah bana son kwana da Mutum a kusa dani"
Murmushi yayi tare da cewa.
"Sabida me bayan ni bargo zan zame Miki daman yau Garin sanyi ake"
Da sauri tace.
"A,a wallahi zafi ake shiyasa ma nake son kwana ni kaɗai"
Bece mata komai ba ya sauketa daga Jikin shi ya ƙarasa inda ya aje ledojin ya ɗauko su.
"Oya sauko kici abinci ki sha magani"
Turo baki tayi yadda taga fuskarshi babu walwala ne yasa ta sauko ya tura mata Doyace soyayya da miyar kifi se kayan marmari shikam kankana taga yana sha ta ɗan tsakuri Doyar taci Kifin sosai dan ya mata daɗi Miƙewa taga yayi ya shiga Toilet ya jima kafin taga ya fito a gaban Wardrobe taga ya tsaya ya tube jallabiyar jikinshi Daga shi se Gajeran wando ya ƙaraso gabanta taga ya wuce gado ya kwanta Jikinsa duk gashi ne Musamman Kirjinsa Jikinta ne yahau rawa bata taɓa ganin namiji babba a haka ba da ƙyar ta wanko bankin ta da hannunta tana fitowa ta ganshi zaune da alamun Jiranta yake Fisgo hannunta yayi ya ɗora ta a saman Ƙirjinsa ya lalubi Makunnin ƙwan ɗakin ya kashe duhu ya cika ɗakin Laluben Rigarta taji yana yi har ya sami nasarar Cilli da rigar ita dai zaro ido take sabida tsabar Tsoro Gaba ɗaya jitai ya gigice se faman Yamutsa mata Jikinta yake da zazzafan salon shi ya ɗora Harshen shi a dokin wuyanta yana cigaba da ruɗa ta da salon shi Wani irin baƙon lamari taji a dukkan sassan Jikinta Lokacin daze ɗauki hanyar shi Riƙe shi tayi da ƙarfi hawaye take saki wanda har ya jiƙa masa Ƙirjinsa.
"Please ban fa warke ba dan Allah kai haƙuri"
Ta faɗa muryarta tana rawa.
Cikin maye da shauƙin wajan taji yace.
"Ummmm zaki ƙara samun goge wa ne a wajan Plsss ki barni"
Daga haka wata irin damƙa yakaiwa Tudun kirjinta yana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login