Showing 129001 words to 132000 words out of 150033 words

Chapter 44 - Rabo Ya Rantse Book One Complete Hausa Novel

gidan ta gabatar Musu Da Ammi a matsayin uwar Mijin farha wadda nan suma suka zauna suka gaisa dasu Ammi kafin su tashi subar wajan.

Ya Nura ne ya shigo ɗakin Umma yana kiran Ikram ta zuba mai Miya tunda ya shigo sajeeda ta zuba masa ido gabanta yana faɗuwa ta Lumshe ido har wata iska ke kaɗata sabida ganin Nura matashin saurayi fari ɗan dumurmur mai Jini a jika.
"Nura ga Mahaifiyar Mijin farha Ku gaisa" cewar Umma Ya Nura ya tsugunna ya gaishe da Ammi kana ya tashi ya Fita dama shi bamai hayaniya bane ba Kuma ba laifi yana ganin ƙimar Umma sosai.

Har Kusan Goman dare Ammi tana Gidan su Farha kafin ta direwa Umma ledar data zo mata da Ita sukai sallama Suka baro Gidan Aikuwa gaba ɗaya Yara da Manya A gidan suka rako Su Ammi har wajan Mota harda kawu wanda yake tayi wa Ammi godiya yana cewa a gaishe da sauran Na gida haka suka rabu Gaba ɗayan su cike da ɗaukin Juna Kowa na gidan su farha ya yaba da Mutuncin Ammi musamman yadda ta saki Jiki tasha Hirarta sosai ta zama Mutuniyar Kawu.

Ko a mota su Ammi labarin karamcin mahaifan Farha suke yi Musa yana Jin su yana ta Murmushi ya sauke Ammi da Sajeeda wadda gaba ɗaya Jikinta ya Mutu tunda taga Ya Nura shikenan taji kaf duniya bata da namijin data ke masifar so in ba shiba soyayyar shi Bugu ɗaya tayi mata Mugun kamu Ita babu ruwanta da Talaka ne shi kawai Nutsuwar shi da kamalar shine yayi mata Hmm anya sajeeda Kin gano Gidan shiga Kuwa Babar su Hadiza mahaifiyar Nura mace ƴar bala'i bare yadda ta ɗauki so ta ɗorawa Nura sabida shine Babba a ƴaƴan ta Maza!

Koda suka shiga gida ma falon Ammi babu kowa Ammi ɗaki ta shige tana Jin kamar ta sauke wani babban nauyi akan ta wannan ziyarar data Je wa surukanta masu Kirki da Mutunta ɗan adam Alwala ta ɗaura Zama tayi tana addu'a seda ta raba dare tana sallah tana wa Aliyu addu'a dan se wajan Asubahi Bacci ya ɗauketa a saman abun sallah Kuma zuciyarta  ta ɗan rage damuwar Rashin sa sabida zafin addu'ar da take yi akan lamarin.

*****************
Tunda suka shiga mota farha ta Jingina kanta da Jikin kafaɗar Aliyu tana tunanin ina ze kaisu Dama yana da ƴan uwa ko gida a kaduna ne Ita kam bata taɓa zuwa kaduna ba shiyasa gaba ɗaya tafiyar ta dame ta gaba ɗaya Jinta take a takure ga Fitsarin daya riƙe mata mara ga Ƙafarta duk ta dame ta sedai yadda take ganin shi a cikin damuwa mai tsanani ba zata iya gaya masa damuwarta ko guda ɗaya ba.
Shima a nashi ɓarin nazari yake akan jahar ta kaduna wadda bai da abokan mu'amala acikin ta wannan tasa ya zaɓeta a matsayin jahar dayay balaguro zuwa cikinta wadda yake fatan yayi rayuwa tare da fatima acikin Jahar kafin Allah ya kawo masa mafita sabida tunda ya baro Gida babu Fuskar wadda yake hangowa seta Amminsa Yasan tana cikin tashin hankali ba ɗan kaɗan ba se Kuma Mami wadda yasan ya tauye mata haƙƙinta tunda har yanzu matar shice akwai nauyin ta akan shi yasan bai kyauta ba ta wannan ɓarin sedai tafiyar tashi kamar Dole ce dan yana tsoron abin da Ammi zata zartar dan uwa ce baze ja da ita ba shiyasa ya zaɓi yayi mata ƙaura Kafin Allah ya kawo musu mafita akan lamarin.

Tunda dukkan abin da Ammi ta buƙata a tare dashi babu wanda yayi Kuskure dan yaƙi Bin umarninta akan su na farko ta nemi ya zubar da Ciki na Biyu saki wanda duka babu dalili bare Hujja mai ƙarfi abin da yasa ma yayi mata ƙauran dan baya son ja in ja da ita ne tana matsayin mahaifiya a gare shi wannan tasa yayi balaguro.

Tafiya taƙi ƙarewa Har zuwa sanda aka kira sallar Isha'i basu ne suka sauka ba se bayan sallar Isha'i a babbar tasha suka sauka Aliyu ya Fito Musu da kayan su ya laluba aljihun jallabiyar shi wadda ya sako Atm card Ɗinshi aciki se ƴan Kuɗin shi waɗanda basu da yawa sabida bai fiye aje cash ba shine yasa ya ɗauko Atm ɗinshi na bankin da yake ajiyar Kuɗi.

Sedai koda ya laluba aljihun nashi wayam ba Atm ɗin Ga wayar da yake transper da ita ya bawa Musa akan cewa ya kashe masa ita ya aje a wajan shi se ƴan Kuɗin daya cusa cikin aljihun shi marasa yawa.
Duk yadda yaso ya dake seda ya kaɗu sabida babban tashin hankalin shi Fatima yasan mai ciki da tsara be tsara be ga kuɗin hannun shi ba zasu Riƙe Shiba Dama ya taho da Atm ɗin shine dan yasan koda zasu shafe shekaru ba zasu tagayyara ba dan harda Niyar yasai ƙaramin Gida yazo sedai kash Allah baiyi hakan ba dan yafi zaton a ɗakin shi ya manta Atm Ɗin garin saurin haɗa kaya waɗanda Ko rabin kayan nashin ma bai ɗauko ba.

"Yallaɓai Kuɗin Mota ka tsayar damu"
Kwandastan motar ya faɗa a gadarance.
Drivern yace.
"Haba ɗalha kai masa a hankali wannan bai kama da mutanan banza ba"
Aliyu yayi murmushi tare da Ƙirgo Kuɗin motar ya basu yay Musu Godiya tsugunnawa Farha tayi tana Rintse ido da kulawa ya durƙusa a gabanta.
"Fatima yaya me yake damun ki?"
Ya faɗa mata Cikin kulawa.
"Fitsari nake ji washh bayana ƙafata"
Ya ɗan yi Jimm.
"Ni har ga Allah ban son Kishiga toilet Ɗin tasha sabida toilet  Infection"
Ta hau Kuka! tana cewa.
"To ni a ina zanyi wallahi ya matseni Sosai"
Ya kama Ƙugu kafin yaɗan saka hannu yana matsa mata ƙafar tata wadda ta tasa ta Kumbura Cikin sanyin Murya yace.
"Ki bari Mu fita sena sama Miki inda zaki Kinji"
Yadda ya furta maganar cikin sanyin Murya ne yasa ta miƙe ya ɗauki kayan su suka fita daga Cikin tashar..........

Autar manya ce marubuciyar......
*ƁOYAYYAR ƘAUNA*
*BA SON TA NAKE BA*
*ƊAN MAJALISSA*
*MURADIN ZUCIYA*
*ASHE ZUMA*
*TAURARO*
*KOBA SO*
*RABON WANI*
*FITAR RABO*
*DA IZZATA*
*BAƘON LAMARI*
*AUREN BARE*
*H A S K E*
*ZUMA A BAKI*
*BAƘAR FATA*
*RABO YA RANTSE*

*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa  wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank,  idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*

*A LOVE STORY 98*
Rabo Ya Rantse
Arewabooks autarmanya

A bakin titi suka tsaya inda motoci da babura ke ta faman kaiwa da kawowa Farha ta kalli Aliyu wani irin tausayin shi ne ke ratsa mata zuciyarta yana huda mata sassan Jikinta koda bai gaya mata ba tasan yana cikin ruɗani da tashin hankali tare da damuwa sedai da ike namijin duniya ne bai ko nuna mata ba.
"Ka bani wannan jakar na riƙe kayan sun maka yawa a hannun ka"
Ta faɗa a hankali ƙwalla mai zafi tana ƙoƙarin zubo mata.
"Nine nace miki kayan sun min yawa a hannuna?" ta girgiza mai kai tare da Kallon fuskar shi se kawai ya juya ya cigaba da kallon titi bai san ko ina a kaduna ba se yace in ba hanyar wucewa zuwa abuja ba bai taɓa zuwa wani abu cikin jahar ta kaduna ba taka maimai bai san ina zasu sauka ba zufa ce ta soma karyo masa ya duba agogon hannun shi Goman dare ta kusa dan motoci ma sun soma sauƙin wuce wa inda Yana da wadataccen Kuɗi ne daya kama musu Hotel sun kwana sedai yana tunanin in ya kama Musu Hotel yanzu to ze ƙarar da ƴan canjin hannun shi.

"Har yanzu kina jin fitsarin fatima ko ya koma kinga yadda Allah yayi damu bama wajan da zaki samu kiyi anan domin titi ne"
Ta girgiza kai.
"Kada ka damu dani Allah ya duba Mu"
Tana rufe bakin ta suka ga wata tsohuwa zata tsallako titi sedai Tsallakowar ta gagara sabida yadda wata babbar mota tayo kan tsohuwar da sauri Aliyu ya yada jakun kunan hannunsa ya tafi wajan tsohuwar a guje ya kamota suka tsallo Ɓangaran da farha take.
"Jikana nagode Allah yi maka albarka bada ban kaiba da tuni wannan mota ta murjeni"
Duk yadda Aliyu ke cikin ɓacin rai seda yayi Murmushi.
Mai hali baya fasa halin sa aljihun sa ya duba ya ɗauko naira dubu ya damƙa mata.
"Baba gashi Kici goro ba yawa"
Tsohuwar ta washe Gibi tana dariya tare da cewa.
"Kai amman nagode nagode madalla a ina kake jikana na dinga zuwa Muna gaisawa ka ganni tunda nake bantaɓa haihuwa ba dana ganka se naji kamar Nina haifi Mahaifin ka tunda nasan dai na girmi gyatumar ka"
Daga farha har Aliyu dariya sukai na dramar tsohuwar kafin farha tace mata.
"Mu baƙi ne daga kano muke"
Tsohuwar tai saurin cewa.
"Oh amman kuka tsaya a titi ai da kunyi saurin zuwa inda kuka zo sabida Titin nan akwai manyan Motocin dake yawo akan shi Nima daga Bikin Jikar ƙawata nake Shine na biyo tanan da tuni na zama gawa"

Aliyu yace.
"Baba zamu bar nan yanzu kema ki daure ki tafi gida dare yayi"
Seta kama haɓar zaninta ta ɗaure kuɗin tana cewa.
"To ku gaya min inda kuka sauka sena zo gobe wajan ku mu ƙara gaisawa"

Cikin ƙosawa da maganarta Kasancewar shi mutum marar son magana sosai yace.
"Bamu da masauki muna dai duba in da zamu sauka ne dan mu baƙi ne a garin"
Tsohuwar ta kama baki cikin mamaki.
"Baku da masauki fa jikana aikuwa ni ina da shi kaga gidana da Mijina ya rasu ya bari se dangin sa suka tausaya min suka bar mini ni kaɗai suka saka min ɗan haya sedai ganin bani da gata tunda ban taɓa haihuwa ba ga dangina duk sun ƙare yasa ɗan hayar yake Mini iskanci baya Biyana Kuɗin hayar Kuma da Kuɗin nake Cin abinci Jikana alkairin dakai Mini dan Allah nima zan kwatanta zan baka ɗaki guda wanda ke Jikin nawa ka zauna kai da matarka danna san matar kace Amman zance kai ɗan yayana ne kazo Kaga zaka dinga amsar Mini kuɗin hayata ma da baya bani"

Tsananin tausayin ta ya kama zuciyar Aliyu.
"Baba idan na zauna kamar na tauye kine sabida Zaki bani ɗaki ne kyauta Kuma Kinga na shiga haƙƙin ki"
Da sauri tace.
"Ni baka tauye niba kuma kai alkairi ne a gare ni dan Allah jikana in ba raina wa kai ba kazo muje ni har zuciyata na baka kuma bana buƙatar Ficikar ka, ka zauna daga nan har san da zaka tashi dan kanka daga gani bakai kala da Mutanan banza ba akwai Ɓoyayyar baiwa a tare dakai"
Aliyu ya lumshe ido yana hamdala a zuciyar shi na yadda Allah bai tozar tashi ba Godiya yayi mata ya ɗauki kayan suka bi bayanta tafiya suke kamar ta kurame seda suka zo dogon wani layi Gaba ɗaya ginin layin na marasa ƙarfi ne dan ko wutar Nepa babu ko ɗauke wa akai oho.

A bakin wani ƙaramin gida tsohuwar ta tsaya mai Ƙofar katako Aliyu ya ƙarewa gidan kallo aran shi yana hamdala ga sarki Allah.

"Jikana kaga gidana nan sunan wannan Unguwa sabon garin rigasa ni Kuma sunana Inno"
Aliyu yayi murmushi inno ta tura ƙofar ta shiga gidan duhu se kukan yara daga wani ɗaki mai fitilar ƙwai Ta ɗaga murya tana cewa.

"Shafa fito ina sunusi yau ga Ɗan yayana yazo"
Matar dake ɗakin matashiya dan ba wata Babba bace ta fito da sauri tana cewa.
"Maraban su sannun su da zuwa amman Sunusi baya nan yana titi"
Sedai se kallon Aliyu take wanda yay kamar bai ganta a wajan ba dan ko gaisuwar data ke masa bai amsa ba yana masifar jin haushin mace marar aji.

Inno ta nuna wa su Aliyu wani ɗan ƙaramin ɗaki wanda ko Kitchen ɗin part ɗin Aliyu ya ninka ɗakin Sau goma tace musu.
"Ga ɗakinnan dama a share yake Kullum sena share ga tabarma nan ga fitilar ƙwai seku shiga ga gidan namu babu abinci"
Da sauri shafa tace.
"Ina da sauran tuwon dasu Basma basu ci ba bara na kawo Musu"
Ta koma ɗaki Shidai Aliyu kayan su ya ɗauka Farha ta ɗauki Fitilar da Inno ta kawo Musu suka nufi ɗakin Suka Buɗe wayyo Allah Aliyu ya ambata a ran shi sabida ƙanƙantar ɗakin ga Shi duk raɓa ta kama bangon ɗakin har simintin ɗakin sauraye ne suka yo Musu caaa da kuka.

Farha da yake ta saba shinfiɗa tabarmar tayi a ƙasa shi Kuma ya aje kayan su a ƙasa bai zauna ba ya Jingina da bango a saman tabarmar farha ta zauna ɗakin yayi shuru.

"Yawwa baƙi ga tuwon da miya"
Shafa take magana daga bakin ƙofa farha ta yunƙura zata fita ta amso ganin kallon da Aliyu ke ai ka mata dashi yasa ta koma ta zauna jikin ta duk a sanyaye shafa taita magana taji shuru seta koma da tuwon ta.

Cigaba sukai da zaman kurame kuma yaƙi zama ko a saman tabarmar ma.

"Kana jina"
Ta faɗa muryarta a sanyaye kamar zatayi kuka!
Bai mata magana ba.
"In hakan akwai cutar wa a tare dakai wallahi ni ka sake ni bani da matsala Kuma in sha Allah zan raini cikin jikina har na haifa koda daga ranar dana haihu ne kazo kace in baka ɗanka zan baka in yaso se matarka ta shayar maka da duk abin da na haifa amman hakan akwai cutarwa a tare dakai sabida baka saba wannan rayuwa ba kaje kabi umarnin mahaifiyarka in ma zubar da Cikinne mafi alkairi duk se a zubar amman Yau ɗaya jibi yadda ka sauya baka saba rayuwar ba sam batai kama dakai ba"

Shuru ne ya kuma biyo bayan maganar tata wanda harta fitar da ran ze mata magana se Kuma taga ya Nufo inda take ya zauna a kusa da ita Kanshi ya sunkuyar yana haɗa kalmar daze mata magana da ita.

"Fatima! waye yace miki wannan rayuwar batai kama dani ba? kin san yadda nake a da kafin na zama haka? kin san wani ƙalubale na fuskanci kaina wallahi sam ba wannan rayuwar ce ta sakani a wannan yanayi ba kece kika sakani fatima anya ban cutar dake ba na kuma raboki da Jahar ki bayan na rabo ki da iyayenki anya ban so kaina ba? sannan maganar zubar da ciki da saki inda ina ra'ayin su da bamu zo nan ba fatima kun fiye min komai na rayuwa Zaki iya zama da Aliyu a wannan Lokacin da bashi da komai ɗakin ma da ya saka ki aro aka bashi? fatima zaki iya wannan rayuwar dani Tabbas Allah ne yaso jarabtata da hakan dan ya ƙara gwada imanina ina fatan wannan ƙaddarar ma Allah ya bani Ikon cinta dan bani da haƙƙin Ammi akaina sabida haramun ne kai biyayya ga abokin halitta dan ka saɓawa mahaliccinka Kinga dukkan abin da Ammi ta bani umarni akai kamar ya saɓawa ƙa'ida Dan saki halak ne amman Allah baya so Kuma baki Mini Komai ba sannan Tace a zubar da Cikin sunna har na wata Uku nan ma Kinga ta saɓawa ƙa'ida Ko?"
Ya faɗa a raunane wannan shine karon farko da taga raunin Aliyu.
Bai jira amsarta ba......
"Fatima kada ki ƙara cewa na sake ki kada ki ƙara cewa zaki zubar da cikin Jikin ki in dai ba so kike ki rasa ni ba a yanzu kece garkuwa ta bani da kowa se ke seko Cikin dake Jikin ki"
Ya faɗa cikin sanyin Murya wani irin tausayi Aliyu ya bawa farha wata irin soyayyar shi ce ke ƙara Huda Sassan Jikinta bata taɓa sanin tana mugun son shi bama se a wannan Lokacin.
_Dama shi yasa ka auri macen da take son ka sabida ana zaton ita ce zata iya rayuwa dakai acikin ko wani yanayi haka zalika baka gane wake son ka se kana cikin Ciwo ko halin rashin madafa anan zaka gane wake son ka da gaskiya amman in kana da rai kana da lafiya kana da kuɗi to masoyanka basa ƙarewa_

Ta kwantar da kanta a saman kafaɗunsa Hawaye yana zubo mata daga cikin Idanunta.
"Ka taɓa jin wata rana lokacin ina gida kafin ka aure ni na gaya maka ko a bukkar daji kake rayuwa namin daji na zagaye dakai ni zan iya zama dakai? tom ka saka aranka Ni ba zan taɓa juya maka baya ba Allah ya sani Ina son ka cikin ko wani hali amman dan Allah kai ma kada ka saka damuwa aranka kaga baka da lafiya nima kaine garkuwata In ka shiga wani hali rasani zakai, Dole ka daure Ita dama ƴa mace ai Inda mijinta yake nan zata Bishi ka dena wannan Ƙuncin bana so na ganka cikin wannan yanayi kaji"
Ta faɗa tana ɗaga kanta tasa hannunta tana wasa da Ƙasumbar data taru a fuskar shi

Jinginar da kansa yayi ajikin bango ya Lumshe idanunshi Nutsuwa na shigar masa Jikinsa sabida kwanciyar hankalinta yafi Komai yi masa daɗi da basa Nutsuwa dama duk tunanin rabi akan ta ne a wannan Lokacin

Tashi tayi ta gyara musu tabarmar  ta ɗauko mayafinta ta shinfiɗa Musu akai sedai babu Pillow ma.
"Kazo ka kwanta naga duk ka gaji"
Ya tashi.
"A,a bari na fita Ko sallah bamu yi bafa Sannan na samo Miki abin da zaki ci"
Ta kalli yadda gari yayi shuru duhu ya sauka.
"Kana jin yunwa nasan"
Ya girgiza kai.
"Bana jin yunwa fatima Kin san abincin dare bai dame niba"
"To in danni ce kada ka fita Nima bana Jin yunwa kada ka fita baka san yaya yanayin unguwar yake ba kaje ka gamu da macuta"
Ya kalleta da wani irin yanayi.
"Baki ci abinci ba Kuma bake kaɗai bace"
"Wallahi bana jin yunwa Ko tuwon da waccan matar ta ce zata kawo na tashi zan amso dan karta ga Mun wulaƙantata ne"
Ya ja ajiyar zuciya.
Ta miƙe.
"Muje muyo alwala"
Suka fita a bakin Ƙofar Inno suka ɗauki Buta gidan tsit kowa yayi bacci Shine yayi Bisimillah yajan yo ruwan a rijiya ya cika musu Butar Seda ya rakata Bayi tayi Fitsari yana tsaye akanta ta gama tayo alwala Suka fito Seda ta shiga ɗaki sannan Yayi abin da ze yi sannan ya Komo wajanta zanin ta cire a tabarmar Sukai sallah Sannan ta mayar da zanin

Ya tashi ya koma saman tabarmar ya jinginar da kanshi bacci ne yake Kama shi sama sama.
Kafin ta yunƙura ta Miƙe tai abin da zatai ta dawo wajan shi har bacci mai nauyi ya ɗauke Shi Zama tayi a kusa dashi Ta kwantar da kanshi a saman cinyarta Ta ɗauko wani kwali dake Gefenta tashiga yi masa firfita Duk da tana Jin Baccin amman haka ta hana Idanunta bacci Aliyu yana kwance a cinyarta se

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login