Showing 45001 words to 48000 words out of 150033 words

Chapter 16 - Rabo Ya Rantse Book One Complete Hausa Novel

yanzu manufata da auren Aliyu shine naga na haihu dashi Komai nashi dashi kanshi ya dawo ƙarƙashin Ikona"
Tajira taja tsaki.
"Ki shaƙe ɗan iska ya sheƙa akwai hanyoyin ɗaukar rai kala kala ya mutu ga maza nan sai wanda kike so kawai Ki kashe shi waze ɗauka kece tunda daga ƙarshe Ki ƙalawa uwar sa kice ita ta kashe shi dan tana baƙin Cikin ya haifi ƴaƴa Su gaje shi, Shikenan fa a baki tuminin takabar ki Kizo mu fantama tunda Dai Boka ya tabbatar ba wani aiki daze ratsa Aliyu Itama Aminar da yaya aikin yaci kanta har ta gigice akai auren naku"
Mami tabi Mahaifiyarta da kallo.
"Mama nidai addu'a zaki min na haihu da Aliyu shine burina Amman bana fatan na ɗauki rayuwar shi wallahi Ina son shi!"
Zagi uwar tahau yi wa mami kafin ta Miƙe tabar mata ɗakin.
"Wallahi mama ba zan iya kashe Mijina akan abin duniya ba Ni burina ya haihu dani na mallake shi yanda ita kanta uwar tashi sai tai shekara bata sanya shi acikin idanunta ba"
Ta faɗa a bayyane kamar wani na Jinta.
Ranar da tunani kala kala Mami ta kwanta bacci rabi na Maman tane ada mamanta tana goyon bayan ra'ayin ta sai dai tun Jiya data je wajan Bokan su ya basu tabbacin ba zasu sami Aliyu yadda suke soba shine Tunanin Mamanta ya karkata ga shawarar da Bokan ya basu akan kawai su kashe Aliyu Ko banza Mami zata ci Tuminin takaba ita Kuma Mami ta turje akan abarta inta koma tasan zata kuma samun wani Cikin wanda take sarai ze zauna ajikinta.

Da Asubah Farha ta Miƙe taje tayo awala tai sallah ta koma baccinta Har wajan 10 tana bacci kafin Safna tazo ta Buga mata Ƙofa............*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*RABO YA RANTSE*

*32*


*A LOVE STORY 32*

Idanunta fal bacci ta taso gaban ƙofar muryarta sanyi ƙalau wadda ta ɗan dashe irin ta masu bacci tace.
"Waye" a zaton ta shine sabida ƙofar akwai key har lokacin bata zare ba tun jiyan data ma ƙofar key da zata kwan ta bacci.
Ga mamakin ta sai taji muryar ɗaya daga cikin ƴan matan tace mata.
"Ubanki na ƙauye ne taso Ki buɗan daƙiƙiyar banza"
Tashin hankali ƙafar Farha rawa ta soma yi wani irin Ɓacin rai ya ziyarci Zuciyarta.
"Sai dai ubanki na birni ya taso ya buɗe miki jaka dabba wadda bata san darajar ɗan adam ba to nafiki zama ƴar hau"
Ta faɗa a zuciye idanunta har sauya kala yayi.
Ihu Safna ta saka tana dukan ƙofar da ƙarfi tana ɗurawa Farha zagi Ta uwa ta uba tana shan alwashin idan ta buɗe ƙofar sai ta La'anta ta.
A fusace Farha ta buɗe Ƙofar wadda Safna ta janyo Farha Falon su ta watsata a center ɗin falon safna ƙatuwa ce farha ƴar ƙarama rufe Farha tayi da duka wanda Ihun Farha shiya janyo Hankalin Ammi da Hajjo dake Kitchen tana haɗa break fast Sajeeda ma dake ɗaki aguje ta fito Falon wanda yayi daidai da lokacin da Safna ta haye ruwan Cikin Farha tana jibga kamar ta sami jaka.
"Ke Safna kashe ta zakiyi baki da hankali" cewar Ammi tana ƙoƙarin Riƙo safna wadda ta naɗe hannun riga tana dukan Farha.
A zuciye ta miƙe tana tsuma.
"Ammi wai yarinyar nan daga naje kiranta ta wanken Toilet zan wanka shine ta hau zagin Babana me na mata"
Ta faɗa tana wawuro Farha wadda har Fuskarta wajan idanunta ya fashe Sajeeda ita ma kukan kura tayi ta janyo farha tana duka haka suka rufu akan ta duk yadda Ammi take Musu magana basu ji ba Ammi Fushi tayi taja gefe tana cewa idan sun kashe Ƴar mutane hukuma zata ɗaure su a banza Hajjo kuwa kuka take tana a kawo musu ɗauki.

Cikin sauri ya ƙaraso Falon Ammi sanye yake cikin wani azababban lallausan Yadin Tissue mai azabar kyau wanda kyansa ya nuna tsadar sa sai ƙamshin Mayen turaren shi mai kama hanci yake Yana tafe yana duba agogon Fata fari tas dake hannun shi sabida so yake yaje Daura A yau ɗin ya dawo dan ganawa da wani babban ɗan siyasa wanda yake siyan motocin sa.

Abin da Aliyu ya gani shine ya sanya shi ƙarasawa Cikin falon da sauri Idanunshi ne ya hango masa aika aikar da ƙannen shi ke shirin yi wanda sam su idanun su ya rufe basu san da shigowar shi falon ba.
Direct wajan Wayar jikin Tv ya nufa ya ɗano ta irin mai kaurin nan daga safna har sajeeda har ammi da hajjo basu ji takun shi ko maganar shiba sai saukar wayar kawai suka ji yana laftawa su safna ajiki waɗanda sukai saurin sauka daga saman Farha suna Ƙoƙarin guduwa Haɗe su yayi ya gwara kawunan su waje ɗaya nan da nan Goshin su ya fashe abin ka da fararen fata kafin ya saka ƙafa ya kwarfe su faɗuwa sukai ya shiga tafka musu Wayar wadda duk sai da ya fitar Musu da jini ajikin su.
Tun Ammi na kallon Abun a wasa har ta zo gaban shi tana masa magana amman bai saurare ta ba sai da ya tabbata ko hannu basa iya ɗagawa sannan ya cillar da wayar Sai nace tunda mai gani yake ganin idanun Aliyu bai taɓa ganin Yanayi irin na yanzu ba idanun shi har wani ruwa ya tara sabida jaa ita kanta Ammi Baya tayi sai Huci yake Jikin sa yana tsuma.
"Ammi inda ban zo ba kina kallo zasu kashe Musu ƴa nawa take zasu rufu su Biyu akanta suna dukan ta uban me tai musu"
Ya faɗa yana Zaro ido waje.
Sajeeda data miƙe aguje tai ɗaki ta ɗaga Murya tana cewa.
"Ko kai kaji abin da tai haka zakai mata babanmu ta zaga yaya"
Aguje yabi ta wadda yake cewa.
"Ta zagi uban naku ubanku yafi nata daraja ne"
Kamar yasan abin da ya haɗa su ganin yana neman ya cimmata yasa Ammi ta ɗaga Murya.
"Baba kada ka kuma dukan min ita abin ya isa haka ai ba jakai bane akan wannan jarababbiyar yarinyar yau kake wa ƴan uwanka wannan dukan kamar bare to na gaji Wallahi kawai Musa yazo ya tafi da ita dan bazan aje masifa agidana ba"
Bai ko saurari Ammi ba ya ƙaraso gaban Farha wadda take kwance kamar gawa ya ɗagata cak yayi ɗakinta da ita daga Ammi har safna data sha duka da Hajjo sakin baki sukai da hanci suna kallon ikon Allah.

Shikuma yana zuwa tsakiyar ɗakin ya direta sai Lokacin ta sami damar kuka dukan shi take a ƙirji tana wani irin kuka!
Muryarta a shaƙe take ce masa.
"Daka bari ai sun kashe ni mai yasa zaka Duke su ba jaka baiwa ka siyo musu ba ai da ka bari kawai sun kasheni ba zaka tabbatar Min da baka ƙaunata ba har se ka sa sun kashe ni ka kaiwa Iyayena gawata"
Takaicin ta ya kamata Aliyu bai san sanda ya wanke ta da tagwayen maruka har Biyu ba zaman ƴan bori tayi a tsakiyar ɗakin ta saka wani irin Kuka ya juya zai fita daga ɗakin da wani irin Sauri ta miƙe aguje tabi bayan shi ta ɗane bayan shi ta cakume shi gam tana kuka.

"wallahi yau sai ka kasheni nasan nai maka laifi dana yaɗa labarin ka ba akan gaskiya mai yasa ba zaka kaini Kotu ba to in ba zaka kaini kotu ba ka kasheni ai kai mai Kuɗine in ka kashe ni ka kashe banza ba mai maka magana amman ni nagaji da wannan ƙaddararran auren naka gwara kawai anyi ta ƙare"

Juyo da ita yayi gaban sa ya saka hannu ya riƙota cak ya ɗorata a saman Ƙirjinsa ya kaita kan gado ya aje ya sunkuyo daidai Fuskarta har tana Juyo kamshin cikin bakin sa.

"Shiii why are you raising your attention on something that is impossible?"
Ya miƙe tsaye tare da zube hannayen shi acikin aljihun wandon shi.
"Ba abin da ze faru acikin dukkan da kika lissafo kawai abin da na sani kece zaki ci baƙar azaba a wajan su in kika cigaba da rashin Kunya in kin mani na jure su ba zasu jure ba"

Ya faɗa hankalin shi a kwance a wannan Lokacin ya sami Nutsuwa ba kamar lokacin da ya shigo falon ɗazu ba.
Murya cikin kuka tace.
"Allah ya isa tsakani na dakai ko wuta tana cin kabarin ka bazan yafe maka ba"
Ya riƙe baki cikin mamakin furucin ta.
"Baki da ɗa'a fatima baki da tarbiya bada ban ina tuna wasu abubawa ba dana miki abin da zaki Dena min wannan tsiwar amman ba damuwa ai ga basawan Ammi nan sun ishe ki haka zasu yita dukan ki kamar Allah ya aiko su"
Kuka ta kuma fashewa dashi.
"Zan so suyita dukana daga nan har suyi sanadin ajalina"
Yayi Murmushi mai sauti.
"Mu gidannan bama kisa amman akwai horo ga marar Kunya irin ki Kuma daga yau bani kuma tare miki tunda nima Kin riga da kin rainani bakya ganin darajata a matsayina na"
Bai ƙarasa ba kuma kome ya tuna Oho ya lalubo wayar shi dake Ringing acikin aljihun shi.
"Hello Musa Okey ka bani Minti Biyu gani nan ok" ya katse Kiran.
Ya ɗan dube ta.
"Ki sami ruwan ɗumi ki gasa fuskar ki baki ga yadda ta ƙara Miki Muni ba"
Ya faɗa yana Wani ɗan iskan Murmushi.
Pillow ta ɗauka ta cillo masa ya cafe yana dariya ya fita yabar ɗakin................*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*A LOVE STORY 33*

Yana fita daga ɗakin nata ya gyara fuskarshi daga dariyar da yake ta koma a ɗaure tamkar bai taɓa dariya ba har Lokacin su Ammi suna falon bai ko kalli saitin kowa ba ya wuce yana ƙoƙarin fita daga falon Ammi ta kira sunan shi a hasale.
"Baba baka ganni a falon bane?"
Cak ya tsaya duk yadda yaso daidaita yanayin sa abun yaci tira a yadda fuskar shi take ya ƙaraso wajan Ammi ɗin ya sami Kujera mai kallon wadda take akanta ya zauna yana duba agogon hannun shi har Lokacin Bai saki fuskar shi ba wanda hakan da yayi ya ƙara jefa Ammi cikin shakku.

"Ita ɗin Meye haɗin ka da ita da zaka ɗagata Ku shiga ɗaki harka jima a ɗakin nata Me kuke yi?"
Wara ido yayi Wanda hakan ya ƙara haska zatin kyan da Allah yayi mishi.
"Ban fahimci me kike nufi ba Ammi I don't understand what you mean by this statement kimin yadda zan fahimta?"
Ya faɗa yana kuma duba agogon shi ya matsu yabar Falon sauri yake.
"Naga kamar sauri kake ka tashi ka tafi"
Ko motsi ya kasayi sabida dama can in Ammi tana fushi baya iya kataɓus yanzun ma wannan yanayin ya ji a tare dashi.
"Please Ammi Kada na fita kina fushi dani"
Ya faɗa Yana ƙoƙarin ƙaƙalo Murmushi amman ya kasa dan har yanzu maƙogwaron shi a bushe yake tamkar wanda aka gasa da wuta.
"Nidai kawai ka kira Musa yazo ya ɗauke waccan jarabar Tunda kake baka taɓa ma ƴan uwan ka irin dukan daka Musu akan wannan yarinya ba Haka kawai ban san abin da ze faru nan gaba ba sabida haka tun wuri gwara tasan inda dare yayi mata"
Ya zuba mata ido harta kammala maganarta kwantar da murya yayi sosai.
"Ammi sai kawai abar Su, akanta suna dukan ta itama fa mutum ce kamar su meye bambancin su? ƙila ma tafisu Muƙami a wajan Allah wallahi akan wannan yarinyar sai muga ba daidai ba wajan Allah, Gaskiya Ammi bani da idanun dazan tari musa akan yazo ya ɗauki ƴar ƙanin mahaifinsa a gaban mahaifiyata ta kasa riƙeta bawan Allah'n da ƙila ma ya girmeni amman Hidima yake min ba dare ba rana Girmamani yake tare da dukkan wani abu nawa Musa yana min abin da kuɗina ba zasu mini ba I can assure you of that'
Har yakai aya a bayanin sa tana kallon shi dama tasan za'ai haka wani irin kafaffan ɗa Allah ya bata tun yana ƙarami haka yake idan yace Eh hakan ne idan yace a,a da wuya a sauke shi akan wannan tsarin.

Ta ɗaga murya sosai.
"To naji bayanin ka ai kai Ko ɗan jarida bai kaika tsari da tambayar tsiya ba To kajini da kyau bazan lamunci iskancin ta agidannan ba wallahi ta ƙara misayar yawu dasu Safna sai na koreta da kaina ba tare da Neman shawarar kaba baze yuwu yara da gidansu azo a takurasu ba kuma kai ma daga yau kada na kuma ganin daidai da magana ta ƙara haɗaku nan ga Hajjo nan da muka shafe shekaru ai banga kana Janta kamar yadda kake wa yarinyar can ba mai kama da sauro"

Ta faɗa tana wani irin huci.
"Ammi halittar Allah ce dai ba kyau ka haɗa mutum da dabba Don in aka barka kai ba zaka yi dukkan su ba, Amun afuwa tunasarwa ce"
Daga haka ya miƙe yabar mata falon batare daya Yi mata sallama ba.

Ammi tagumi ta zabga kafin ta fara magana da hajjo dake jere abin karyawa a dining.
"Hajjo kinga baba ko An ya zan iya barin yarinyar nan agidannan tunda nake da Baba bai taɓa Yin ja in ja akaina ba sai akan waccan matsiyaciyar mai kama da Tsinken sakace Ina da sake"
Ta faɗa tana Miƙewa tsaye da sauri Hajjo ta ƙaraso.
"Haba hajiya Amina ina tunanin ki ze tafi duk abin da Ɗana ya gaya miki gaskiya ne Kada kije ki faɗa Fushin Allah sanadin yarinyar nan faɗa ne sunyi shi da su Safana sabida haka Ki rabu dasu shi kuma kin san Ɗana yana da tausayi Ta yuwu tausayi yarinyar ta bashi amman ki kwantar da hankalin ki"
Ammi har Lokacin se huci take.
"To ita dasu ɗaya ne gidan uban ta ne da gadon ta acikin gidan Haka kawai bare yazo yafi ɗan gida"
( Hhh hajiya Ammi gidan Mijinta ne kece baki da masaniyar hakan )
Hajjo ta kuma yin ƙasa da murya.
"Ina fa ba gidan uban ta bane wane Mutum da aikin Aljan ai wani kaya sai amale ke ɗauka Allah ya huci zuciyar uwar ɗakina ki mata afuwa mai zuciya da sisin gwal uwar sadiƙ da Aliyu ga bashir a gefe Allah dai ya jiƙan Alhaji da gafara ya raya su salma"
Ammi bata iya furta komai ba ta wuce ɗaki a ranar ba wanda ya kuma fitowa falo sabida ammi a ƙule take an taɓa ƴaƴan gwal tana ɗakin su Safna na cinyarta sajeeda na kafaɗarta ta gama gasa Musu Jikin su sai kuka suke duk Fuska da Jikin nasu ya haye yayi sumtum ita kam Safna data fi Jigata zuwa azahar zazzaɓi ya rufeta har rawar Ɗari take hankalin Ammi daya kuma tashi rasa yadda zatayi da safna tai daga ƙarshe wayar salma ta kira tana sheda mata A gigice salma ta hawo Mota daga asibitin data ke aiki kasancewar ta Nurse Ce ta tawo gidan bayan ta shaidawa Mijinta halin da ake ciki ta cikin waya.

Zuwan salma ne yasa Ammi taɗan sami Nutsuwa Allurai salma ta rubuta da ƙarin ruwa ta bai wa driver yaje pharmacy ya siyo musu.
Minti kaɗan ya kawo ta haɗa alluran cikin ruwa ta ƙara wa safna wadda zuwa Lokacin har baccin azaba ya kwasheta itama sajeeda maganin ciwon Jiki ta samu tasha ta kwanta Salma ta dubi Ammi wadda har tayi wujiga wujiga dan fargaba tace mata.
"Ammi wai meke faruwa ne agidan naki da alama ba normal zazzaɓi bane kamar akwai shatin duka ajikin ƴaƴan naki Allah yasa ba Bashir bane ya sauke gajiyar shi ajikin su?"
Ammi da ta kuma haɗe rai tamau ita ta dubi salma tare da cewa........
*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*

*A LOVE STORY 34*

"Ai inda Bashir ne ya dake su da ba zakiji wayata ba, sabida ina bashir ze iya musu wannan azababban dukan"
Salma tasha jinin jikinta can kuma tace.
"Ammi Allah yasa ba rashin kunyar tasu suka ma wani a waje ba dan wallahi ba kowa ne ze iya jure halin ƴaƴan kiba Shiyasa kullum faɗan da nake musu kenan wannan tasa yanzu suka min ƙaura suka dena zuwa in da nake don basa son gaskiya"
Ammi tayo kan salma tana cewa.
"Kin fara wa'azin naki ko me shegen iyayi da manyan ce kamar wata uwata to ɗan uwanki ne ya saka waya ya zane su kamar jakai haka ya Mayar min da ƴaƴana wallahi ba dan cikin su ɗaya ba sena maka shi a kotu"
Salma ta kama haɓa kullum Abin Ammi ƙara gaba yake akan su safna su kaɗai ne matsalar Ammin su.
"Ammi akan Su safna zaki maka Yaya Ali a kotu? dan nasan Ya Sadiƙ baya kano tunda kika ce ɗan uwana nina san da Ya Ali kike Ammi meye yayi zafi Ammi Kin san baze dake su There is no reason ba"
Salma takai maganar cikin sanyin halin ta wanda kowa yasan ta da hakan sam bata ɗauki duniya da zafi ba.
"To bari kiji wata matsiyaciyar ƴa musa ya kawon yau kwana biyu wai marainiyace ƴar ƙanin mahaifin sa tunda yarinyar nan tazo gidannan shikenan Ya shiga takura wa ƙannen shi akan ta dan kawai safna zata shiga toilet taje tana buga mata ƙofa akan ta Miƙe ta wanke mata Shine tahau zagin mahaifin safna kin san safna da zuciya koni yaya nake da ita shine fa suka hau kokawa Sajeeda ta fita tana taya safna Wallahi Salama baki yadda ya Dinga dukan ƴaƴan nan ba kalli fa jikin su duk shatin tabon Duka"
Ta faɗa a ƙufule.
Salma taja ajiyar zuciya.
"Ammi Idan na fahimceki Musa P.a ɗin yaya shine ya kawo Maki Ƴar uwarshi amman kamar aiki zata ke Miki Ammi akwai gyara anan shin Kin bibiyi kowa acikin su kin gano me laifin ammi ɗa fa na kowa ne su yanzu su safna ba zasu iya wanke Toilet ba har se me aiki tazo ta wanke Musu kafin su shiga fisabilillahi Ammi wani ɗa namijin ne ze yarda da haka wallahi ni yanzu baban su Dady kafin ya tashi na kammala komai idan ze tafi Office da abincin sa yake tafiya kuma kinga dai ina aiki wani bin har Night duty nake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login