Showing 102001 words to 105000 words out of 150033 words

Chapter 35 - Rabo Ya Rantse Book One Complete Hausa Novel

alkairi da kuka bani auren yarinyar ku batare da kun duba ni ɗin waye ba, Kuma in sha Allah zan riƙe fatima da gaskiya da Amana"
Ya faɗa yana tashi wanda lokacin Umma ta fito da baƙar leda a hannunta Dambun nama ne acikin wata farar roba wanda Yaya nafisa tazo mata dashi rasa me zata bashi tayi shine ta fito dashi.
Yana ganin umma ta fito yayi murmushi umma ta kawar dakai Tare da cewa.
"To kazo mana babu zato ka ɗan wannan kayi guzuri babu yawa"
Ta miƙa masa Ledar sannan ta ɗan kalle shi.
"To Allah ya tsare hanya ya kiyaye hanya ya kuma karɓi ibada, Koda wanda zeje wajan farha?"
Cewar umma yaɗan yi jimm.
"Mama akwai saƙo ne?"
Shiga ɗaki umma tayi can ta fito da wata ledar daban.
"Maganinta ne Na ciwon ciki da take fama dashi, to ban san a wani hali yanzu take ciki ba nidai na amso mata shi to kuma har yanzu naji shuru bata zo ba" Umma ta faɗa idanunta yana kawo ruwa se kawu ya hau sababi.
"To Asiya in banda abinki Kukan me kuma zakiyi yaronnan dan fa ya kwantar mana da hankali yazo In marar gaskiya ne ta yaya zezo gidannan eye? kuma yace in ya dawo ze kawo mana ita mu ganta dan hankalinmu ya kwanta"
Lokacin hawayen Umma ya gama zubowa.
"Kayi haƙuri dan Allah,ga maganin nata ka tafar mata dashi ka bayar akai mata akwai duk yadda zatayi amfani dashi ajikin takarda ikram ta rubuta"
Aliyu kasa amsar ledar yayi masifar tausayi baiwar Allah'r ta bashi lallai soyayyar ɗa da mahaifi se Allah ya lura gaba ɗaya hankalin mahaifiyarta ba a kwance yake ba yaɗan sassauta Murya cikin rarrashi Lokacin ya durƙusa a gaban umma ya dafa ƙasa da hannayen shi.
"Mama ki kwantar da hankalin ki, Ina da mahaifiya mahaifin tun muna ƙanana ya rasu, Ina da ƙanne mata wallahi bazan cutar Miki da ƴarki ba naga har yanzu baki gama Yarda dani ba Ni ba macuci bane, amman In hankalin ki baya kwance zanje yanzu na kawo Miki ita inna dawo sena zo na tafi da ita"
Kawu ne ya katse Shi da sauri.
"Jimin maganar banza Haba Aliyu kai kamar ba namiji ba kamanta shirmen mata ne rabu da Asiya soyayyarta da Fatima tayi yawa ban taɓa ganin ɗanda Asiya take so har ta kasa kawaici akan sa kamar fatima ba Inka biye mata ba zaka tafi ba zaman rarrashin ta zakai tayi har Lokacin ka ya ƙure...........*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*

*A LOVE STORY 83*

Cewar kawu Umma ta share hawayen ta.
"A,a Aliyu wallahi na yarda dakai fa Kada ka dawo min da ita ni ai uwa ce Burina Naga ƴaƴana agidan mazajen su Suna zaune lafiya Allah ya Tsare ga maganin nata"
Ta miƙa masa yasa hannu ya amsa Kawu har wajan mota ya raka Aliyu se hira suke kamar sun saba Aliyu ya shiga mota kawu ya koma gida Bakin matan gidan muƙus ba wanda ya iya magana Umma ta Mayar da Ajiyar Zuciya Allah mai rahma da jinƙai yau dai ya fitar da ita daga Gorin Babarsu Hadiza wadda take caɓa mata magana kusan kullum akan auren farha to yau dai ga Mijin farha yazo Mijin kere sa'a kuma ya cika kowa da abin arziƙi dan kuɗin daya bawa Umma haka ya bawa ko wacce acikin su Ranar Umma ta saki ranta har yaya nafisa kafin ta tafi nata gidan tana tsokanar Umma Su kansu yaran gidan wuni sukai maganar Mijin farha ɗan gayu mai kyau mai Kuɗi ranar dai Abin se San barka shi kanshi kawu ya wuni cikin farin ciki Musamman na kawo ƙarshen zaman shi haka da Aliyu zeyi domin wannan shago daze Buɗe masa ba ƙaramin Daɗi kawu yaji ba.

Aliyu jingine kanshi yayi da Jikin seat ɗin kujera mahaifiyar fatima ta bashi tausayi jiyay ze cigaba da riƙe mata ƴarta Amana Muddin rai, Haka zalika mahaifin fatima ya kwanta masa arai sabida yadda ya nuna yarda a tare dashi har kunyar kanshi yaji lokacin da ya ga mahaifin fatima ya dage yana kare shi a wajan mahaifiyarta, yaja ajiyar zuciya yana cewa "Ya Allah ka tayani riƙon amanar waɗanda suka bani yarda" Musa dake driving yace "Oga kana magana ne?" Aliyu yayi Murmushi tare da cewa "A,a" ya faɗa sanda yake Zazzage maganin da Umma ta bashi zaro idanu yayi Lokacin da yake karanta maganin maganine na ciwon mara na gargajiya shine Umma ta karanta tace na ciwon cikine Murmushin gefen baki yayi tare da aje maganin yana wani Lumshe ido yana tunanin ai ya kawo mata ƙarshen ciwon mararta tunda sun zama abu ɗaya dama yawanci ƴammata na fama da ciwon mara ne saboda rashin aure ƙarfe uku daidai suka ƙarasa airport tuni su sadik sun tsufa a wajan sallama sukai da Juna adaidai Lokacin Jirginsu Aliyu ya ɗaga ƙasa mai tsarki sedai fatan Allah ya dawo dashi lafiya.

Washe gari da Ammi da sadiƙ da sakina da ƴaƴan sadik safna sajeeda Mami suma nasu Jirgin ya ɗaga bayan su hajjo sun bar Gidan kowa ya tafi kafin su dawo dama shima Bashir Ranar da Aliyu ya tafi shima yabi jirgin abuja na ƙarfe shidda gaba ɗaya Gidan Ammi se ma'aikata maza dan babu kowa.


Zaman farha agidan Salma se son barka sabida zama suke na mutunta juna da alkunya a tsakaninsu Salma tana girmama farha abin har Kunya yake bawa farha dan hatta abinci Salma bata yarda farha taje dinning har ɗaki take kawo mata kuma ta hana ta aikin Komai ita ke yi mata Abin na damun farha Yau kwananta goma agidan wanda ya kama azumi kwanan shi goma Salma tayi mata awon Cikin a dubarance ta karɓi Fitsarin Farha ba tare data bari ta gano komai ba kuma Alhamdulillahi abin da Aliyu ke zargi ya tabbata dan Ciki ne ɗauke ajikin farha har na wata ɗaya da Sati uku wata Biyu ba sati ɗaya kenan tun daga nan kulawar da salma ke bawa farha ta Kuma ninkuwa Kuma Alhamdulillahi Farha tana ta samun lafiya matsalarta kwaɗayi da bacci amman bayan nan yanzu ko amai ba sosai take yi ba Ga wata ƙiba data ke yi kamar bata azumin ga shi ta ɗashe ta koma fara tas kallo ɗaya mai hankali ze mata ya tabbatar tana da shigar yaron ciki wanda ita sam bata san dashi ba kusan koda yaushe ta kwanta inta danna cikinta taji yayi tauri se tace Tsutsar ciki ce seta tashi ta ɗauko ayaba tai ta ci kamar yadda ya gaya mata sabida gaba ɗaya ta manta da wata al'adarta sam batai tunanin Misssing watan data yi.
Kayanta ma sun mata kaɗan basa shigarta yanzu sabida yadda Ƙirjinta ke rinjayarta se kayan da Musa ya kawo mata take sakawa Take harkokinta Daga ɗakinta zuwa falo Tare dasu Dady dasu ka manne mata dan Ko bacci ma tare suke yi.

Salma Farha na bata tausayi sosai haka zalika Aliyu gaba ɗaya tausayi suke bata tunda ya gaya mata halin da suke ciki shida yarinyar taji tsananin tausayin su ya kamata ita kaɗai take juya abin aranta Ta rasa wa zata gayawa Taji daɗi Dan shi kansa Mijinta ya lura bata da kuzari yayi nacin ta gaya masa meke damunta tace azumun da take yine kaɗai da kuma yanayin aikin ta dama shi mijin ta bamai sa ido bane koda yaga farha sau ɗaya bai tambayi salma wacece ba tunda yasan ba zata kawo masa wadda bata da alaƙa da ita ba daman ita ma farha ba fita take ba tun da suka haɗu sau ɗaya basu sake haɗuwa ba.

Kimanin kwanaki ashirin da fara azumi rabon farha da Aliyu tun wayar da yayi mata ranar daze tafi abun na damunta sosai na yadda bai taɓa kiranta ko a wayar ƙanwar shi yace a bata ba, wani bin inta kwanta haka zatai tayin kuka har bacci ya ɗauke ta a hankali ta shiga tsananin damuwar rashin Mijinta wanda bata san tana son shi da yawa ba seda sukai nisa da juna Komai dai gashi nan a gidan salma amman baya burgeta har taji tafi son zaman gidan Ammi duk da wiyar da take ci amman ai da sauƙi tunda tana tare da Mijinta Kome tace tana so se salma ta samo mata fara ma da take so Har ta isheta sabida Kullum in salma ta dawo daga aiki seta siyo mata Tsabar yadda ta saka damuwa aranta yasa daga tasha ruwa zazzaɓi yake rufeta haka Zata ƙudundune taita rawar sanyi se cikin dare yake lafa mata sannan ga abin da yake tsorata ta shine Motsin da cikin ta keyi mata Haka zata dafe cikin tana jin yana motsi taita hawaye seta ci ayaba Guda goma arana tana fatan Allah yay gaggawa fitar da tsutsar da take damunta acikinta.

Yau azumi kwana ki ashirin da biyar Salma ce ta shigo ɗakin farha kasancewar week end ce ranar babu aiki ta zauna a bakin gado farha kuma tana kwance Cikin bargo yanzun ma kukan ta gama bayan tayi sallar azahar ta kwanta bacci.
"Aunty fatima bacci kike yi ne dama zaki bani size ɗin kayan kine sabida zan miƙa mana ɗinkin sallah" cewar salma farha ta miƙe zaune sabida bata da nauyin bacci.
Salma ta kalleta tace mata "Subuhanallahi Aunty fatima kuka! kuma kukan me kika yi haka fuskarki duk ta tashi haka kodai kina Missing ɗan uwana ne?"
Salma ta faɗa tana Juyawa Kusa da farha suna fuskantar Juna farha cusa kanta tayi a cinyoyinta tana Ɓoye fuska sabida maganar salma ta bata kunya "Dan Allah ki sanar dani Ko kina Missing ɗan uwa ne?" ga mamakin salma se taga farha ta girgiza kai se kuma ta fashe da kuka Mai ƙarfi tana yarfe hannunta.........
*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*A LOVE STORY 84*

"Subuhanallahi abin har ya kai haka Aunty fatima kuka kike yi meke damun ki me nake yi miki zama dani ne bakya so ko wani ke takura miki agidan nan?" salma ta faɗa duk a ruɗe farha kasa magana tayi kuka take yi sosai wanda hakan ya ƙara tsorata salma Sabida ko jiya da sukai waya da Aliyu seda ya ƙara jaddada mata cewa ta dinga kula da fatima sosai saɓani suke dashi duk sanda ya kira salma Ita kuma bacci take idan yace a bata wayar salma seta ce masa ba'a son mace idan tana da ciki ake tashinta daga bacci wannan tasa tun yana cewa ma a bata in ya kira har yama dena sedai kawai ya kira salma su gaisa ya tambayi lafiyar matar sa ya kashe wayar tunda ya yarda da salma ɗari bisa ɗari yasan ba zata cutar masa da fatima ba shiyasa Ya saki hankalin shi bai damu ba.

Goge hawayen daya wanke fuskar farha salma take da hannunta jikinta duk yayi sanyi muryarta a raunane ta kuma cewa "Kinƙi min magana fatima dan Allah ki gaya min in da wani abun da yake damun ki, ɗan uwana ya damƙa min ke amana in na bari wani abun ya same ki naci amanar zumuncin Allah Ko baki da lafiya ne duk kin min shuru?" salma ta faɗa kamar zata yi kuka girgiza kai farha tayi tare da sauka daga saman gadon taje banɗaki ta wanko fuska ta dawo ta tarar da salma ta zabga tagumi daga nesa da salma ta zauna muryarta har lokacin bata saki ba tace "Aunty salama wani gagarumin abu ne yake damuna" salma ta ɗago a saɓule tace mata "To fa wani abu ne Aunty fatima wanda har ya sakaki wannan kuka haka wanda ya ɗaga mini hankalina?" farha ta sunkuyar da kanta ƙasa sabon kuka ne yake tawo mata cikin kukan tace "Nina san ƙarshena ne yazo ƙila mutuwa zanyi ma" salma tai saurin matsawa kusa da ita tare da cewa "Subuhanallahi Aunty fatima baki da lafiya meke damunki amman baki gaya min ba?" ta faɗa tana kama hannayen farha, Farha ta kuma fashewa da kuka! kafin tace "Ni kaɗai nasan abin da yake damuna na rasa jin daɗin bakina kullum yawu yayi ta taruwa naita bacci kuma kome naci bana jin daɗin sa ban sani ba ko ƙarshe nane yazo shiyasa Allah ya zaren ɗanɗanon komai" salma ta kusan hantsilawa sabida dariyar data zo mata batare data shirya taba da ƙyar salma ta saita kanta tana sauraran Farha wadda take ta faman kuka can kuma ta cigaba da cewa "Aunty salma bazan ɓoye miki ba tabbas akwai abin da yake ajiye acikinnan nawa babban tashin hankalina Allah yasa Ba wata masifar bace Dana gaya masa kwanaki yace min tsutsar ciki ce sabida da farko tauri cikina yake min wajan ƙasan marata shine yace mini na dinga cin ayaba tsutsar ciki ce To yanzu fa abun ya gagara yakai maƙura dan motsi sosai nake ji acikina har dafe wajan nake bari ki gani" da sauri salma ta dafe hannun farha wadda take Ƙoƙarin ɗaga mata rigarta duk yadda salma taso danne dariyarta ta kasa tashi tayi ta fita falo ta kwanta a saman Kujera tai dariya ta godewa Allah har cikinta seda ya kusan ƙullewa wato Yaya Aliyu abin da yace wa ƴar mutane kenan ya ɗorata a keken ɓera wai tsutsar ciki gareta.
Wato shi wayo ga mutum halittace wasu ƴammatan suna da wayo da ganewa In wata ce da sauri zata fahimci Halin da take ciki, amman ita wannan sam bata gano kome ke damunta ba yadda mijinta ya ɗorata haka ta tafi, to ta yaya bata gane tai Missing mp ɗinta ba cewar salma a zuciyarta Koda yake in kana cin Damuwa bama ka gane kanka wataƙil tsananin damuwar gidan Ammi da yarinyar ke ciki ce ta hana ta gano Kana lamarin ta salma tashi tayi tare da komawa ɗakin ta tarar da farha zaune ta rafka tagumi.
Zama tayi wata dariyar tana ƙara tawo mata tana danneta "Aunty fatima karki damu babu wata matsala acikin ki ina zaton Kina da ulcer ne kin san ita ulcer Sihiri gareta Yadda takewa Mutum acikin sa seya rantse Ma ciki gare shi" farha ta share hawayenta "Wallahi Aunty salma abin yana damuna sosai, nace to kada naje ko wata gagarumar matsalar ce a tare dani abun yana damuna sosai ban dai gaya miki bane ni naketa fama" salma ta dinga kwantar mata da hankali ta nuna mata wannan motsinfa ba mamaki ulcer ce ke damunta Seda salma ta karɓi size ɗin Farha na kayanta sannan ta miƙe tsaye "bari naje na kai mana ɗinkin kafin ashara ruwa zan dawo in sha Allah" farha taɗan kalleta "Amman Aunty salama sefa an ɗan ƙaran rigata dan waccan tai min kaɗan dama tare muka je aka gwadani kawai dama na jima ban fita ba duk ƙafafuna kumbura suke sabida zaman waje ɗaya" salma taɗan zaro ido "Rufa min asirin faɗan Mijinki ni na isa na fitar dake waje so kike ya dawo ƙasar yau kenan?" farha tayi dariya "Tab ta yaya dan kawai na fita se ya wani dawo wama ze gaya masa babu wanda ya san na fita ai" salma tayi wata dariyar tana cewa "Nidai rufa mini babu ruwana nafi son mu rabu lafiya da mijinki Dan yadda ya kafan sharuɗa akanki Ba zan tsallake ba ina fatan Allah yasa yadda ya kawoki lafiya yazo ya ɗaukeki lafiya" farha ta kalli salma "Yawwa dan Allah Aunty salma shine yace Miki ni matar shi ce?" salma taɗan fito da ido tana murmushi "Tunda ke wancan karon kin Ɓoye mini ai shi ya gaya min be ɓoye mini komai ba" farha tayi ƙasa da kanta "Amman ke ya gaya miki To amman mai yasa be gayawa su Ammi ba? ko lokacin daya kaini gidan cewa yayi kada na bari kowa yasan ni matar sace wannan ne yasa ban gaya Miki ba koda nazo gidannan kwanaki sanda kika ɗauko ni, sabida ya min gargaɗi akan kada na Nuna ko alamar muna da alaƙa dashi Wannan abun yana Ɗaga min hankali dan Allah Aunty salma rayuwar aure zata tabbata a ɓoye ne?"
Salma ta girgiza kai cikin damuwa tace "gaskiya maganar Ɓoye auren ku ma bazata yuwu ba sabida na tabbata kema ai a wajan mahaifan ki yaje ya amso auren ki to sabida me shi ze Dinga Ɓoyewa nasa iyayen ke matar shice bayan auren ku ba haramun bane wannan ba Hujja bace In ma don Kada hankalin Ammi ya tashi yake yin hakan ni a ganina gwara ma tun yanzu ta sani kafin Lokaci ya ƙure naso na bashi shawara amman kuma Bamu sami lokacin hakan ba sabida sanda ya kawo ki sauri yake tayi"*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*

*A LOVE STORY 85*

Hankalin farha a ɗan tashe tace "Nima abin da na gani kenan Wallahi Aunty salma in da nasan akwai matsala acikin gidan su da bazan gigin kawo kaina ba na lura shi baya son ko kaɗan asan ni matar sace ke kanki nasha mamakin da naji ya gaya miki ni matar sace shiyasa in kika lura zaki ga koda kike tsokana ta da matar ɗan uwa na ɗan sha jinin Jikina"
Tausayi farha ta bawa salma.
"Ni kam ya gaya min kome hatta sanadin auren ku ya gaya mini Kuma ni kin mini ina son auren ku Kuma ina muku fatan zaman lafiya mai ɗorewa" farha tace "to anty salma har yaushe ne ze faɗawa mahaifiyar shi gaskiya toko hayar iyaye yayi ma aka ɗaura mana auren nifa duk bana hayyacina so nake ya dawo ayi wadda za'ai ma gwara in ba dama nai takai na Kafin zama yayi nisa" salma tayi murmushi tare da cewa "Yaya Ali baze taɓa hayar iyaye ba ƙannen mahaifin mu ya tura gidanku aka amso mai auren ki, Kuma abin da baki sani ba shine Wallahi yana son ki in da baya son ki da baze dinga damuwa da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login