Showing 33001 words to 36000 words out of 150033 words

Chapter 12 - Rabo Ya Rantse Book One Complete Hausa Novel

gidan suke ƙuntata mata musamman Indo dan tafi Hafsa Iya kirsa da Iya wuri Cikin Asiyah tuni ya fito yana ta girma abinda take so shi take ci.

Ga wani irin buɗe da Allah yayi wa Kawu dan sosai Allah ya wadata shi har gyaran gida yayi musu wanda hakan ya kuma ƙuntata zuciyar matan gidan.

Asiya tana gab da zata haihu ƴar wajan Indo sadiya ta rasu Kuka kamar Indo zata haɗiyi zuciya A daddafe akai sadakar bakwai ranar Allah yasa Asiya ta fara naƙuda wadda Umman zage tazo ta kaita asibiti zuwa dare ta haifo ƴar ta mai kyau jajir kamar mahaifinta sak.

Kawu daya je asibitin ya ɗaga jinjira a maimakon yayi takaici ba namiji ya samu ba sai yahau murna nan da nan yaji son yarinyar ya shiga zuciyar sa.

"Hali dubu komai naki dubu ne Allah ya raya ki Halimatussadiya"

Cewar kawu yayi mata huɗu ba da sunan marigayiya ƴar wajan indo fafur da aka sallame su Umman zage taƙi kai asiyah gidanta haka ta tafi da ita zage domin tace Asiya ina zata iya wankan jaririya kawu badan yaso ba yabar ta haka akai suna yarinya taci Suna Halima Kamar yadda ubanta ya raɗa mata cigaba sukai da wanka har na tsahon kwana arba'in kafin ta zagaya gidan ƴan uwa bayan tayi arba'in ɗin kana ta dawo ɗakin ta in ka kalli Asiya da Sadiya sai ka ƙara kallo sabida kyan da sukai da ƙiba.

Ta ɗan sami sassauci agidan sabida yadda Indo take son sadiya Dan bama ta iya cewa sadiya sai dai tace sadiyata sabida sunan ƴarta da kawu ya sanyawa sadiya.

A hankali sadiya ta Cigaba da girma yarinya mai wayo da dubara koda yaushe tana tare da uwarta dan bata yarda da kowa agidan cikin haka suma su indo suka sami juna biyu Lokacin kuma ana shirin Bikin Adama da samira lokacin yaran sun gama primary Kawu ya ce aurar dasu zeyi iyayen nata kuka akan ƙanƙantar ƴaƴan haka kawu ya samo musu mazaje ƴaƴan abokan shi akai bikin su adama tana agadasawa ita kuma samira tana mandawari.

Ba jimawa su indo suka haihu indo ce ta fara haihuwa sai hafsatu duka maza suka haifa sai dai yadda kawu yay murnar haihuwar sadiya bai murnar haihuwar ƴaƴa mazan ba Ƴaƴa sunci suna Nura da Salmanu haka rayuwar ta cigaba da tafiya.

Sadiya irin mai jikin girman nan ce dan saida ta kere ƴaƴan su Indo a girma kuma tun tana ƙarama mai kishin mahaifiyarta ce ko kaɗan bata kwaso sanyin Asiya ba ( umma ) sam sadiya mafaɗaciya ce Dan ko abu za'aiwa uwarta to sai dai in tana makaranta amman agaban ta ba wanda ya isa ya taka mata uwarta bayan sadiya umma ta haifi Nafisa ba jimawa ta haifi fa'iza daga lokacin kawu kuma a sannan arziƙin yayi ƙasa gidan Bilon shi ma ya ɗaga ya siyar sai buga buga kawai yake.

Lokacin umma ta sami ƴanci dan sadiya ta zama budurwa babu uban daya isa ya taɓa musu uwarsu dan ko kawu ne ya ma umma faɗa to sadiya kwana take kuka kuma ba zata ci abinci ba ga kawu yana masifar son sadiya A hankali Aka fahimci yarinyar aljanu ne suka taɓata dan data soma zama budurwa sosai Nan da nan suke bugeta wanda hakan yana ɗagawa su kawu hankali dan in abun ya tashi babu sauƙi.

Ganin halin da suke ciki ne sadiya ta dubi umman su Lokacin tana ɗauke da tsohon ciki tace mata.......
*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*RABO YA RANTSE*

*23*


*A LOVE STORY 23*
"Umma ya kamata ki fara yi mini awara ina fitar miki da ita titi danni gaskiya zamannan ya isheni haka"

Umma ta kalli sadiya da tausayawa duka lokacin shekarun ta bama su yawa bane damma dai mai gaɓɓan girma ce.

"Haba sadiya ta yaya kamar ki zanyi wa awara ki bari ƙarfin ki yakai"

Sadiya ta dubi umma.
"Umma kinga su matan gidannan ƴaƴan su suna taimaka musu ke kuma kullum sai dai kita wankau ga sanyi ni dai dan Allah ki min zan saida miki"

Sanin halin nacin sadiya yasa umma ta amsa mata da to daran sadiya bata bar umma ta sake ba haka ta addaba mata sai da ta bata kuɗin wake rabin kwano washegari sadiya ce ta kai markaɗe umma ta dafa mata awarar.

Ta fita can titi tana soyawa da yamma duk wanda yaga sadiya sai yayi sha'awar awarar sabida ƴar mai kyau da ita ga ta tsaf ba ƙazanta kafin magariba awara ta ƙare se kuɗin ta cas babu abun da ya ɓata Sai dai sukai sati suna awarar Kuma cikin hukuncin Allah kullum sai ta ƙare ganin haka yasa Umma ta ƙara ta koma ta kwano ɗaya da wannan ribar awarar suke ci suke sha randa kawu ya kawo su haɗa.

Ganin wannan sai hankalin indo ya tashi sai ta farawa sahura ƴarta lokacin ita ce kusan sa'ar sadiya sai ta fara mata awarar itama dan gasa


Dan tsokana sai sahura take zuwa kusa da sadiya tana soyawa.

Ranar da sahura ta fara zuwa sadiya bata mata magana ba sai da aka tashi sannan tace.

"Sahura ina baki shawara daki Koma wancan ɓangaran wannan ɓangaran nawa ne in kunne yaji jiki ya tsira"

Sahura tasan Halin sadiya kamar yunwar cikinta.
Tana zuwa gida ta gayawa Uwarta indo ta fito tana cin mutunci akan ba uban daya isa ya hanasu yin awara kuma awara yanzu suka fara.

Sadiya ta fito aguje ta rarumo Muciya tabiyo indo a ranar sun ga masifa dan Indo bata kwana agidan ba Sabida tsoron sadiya umma Aljanun sadiya na damun ta sabida mayar da yarinyar suke kamar wata juju.

Washegari indo ta dawo kawu ya kirasu yace bai amince su cigaba da awarar ba sabida haka ya soke yi sadiya ta kada baki tace masa.

"Kai yanzu kawu idan ka hanamu yin awara kana da abin da zaka bamu su suna da ƴaƴa maza Ita kuma uwarmu bata da kowa sai mu yunwa inta kama su fa'iza tsakar dare umma kuka take nidai gaskiya baze yuwu na dinga ganin ɗigar hawayen uwata ba sabida haka sai na fitar da awara ko umma bazata yi min ba zan amso jari wajan umman zage nayi"

Amaimakon kawu ya hau masifa sai yahau cewa.
"Haba dubu tawa kimin fatan na samu na wadata ku mana, Nima kaina bana son halin nan da kuke ciki"

Duk yadda kawu yaso tabari taƙi awara ta cigaba da fita da ita kuma Allah yasa mata nasibi wannan awara sai da ta koma ta kwano biyar Baƙin ciki kamar ya kashe Su indo gasu su komai suka taɓa narke wa yake.

Haka umma ta haifi Fatima wadda taci sunan mahaifiyar Umma wadda suke ce mata ( farha ) duk ƴaƴan umma dana sauran matan farare ne tas amman ikon Allah farha baƙa ce ƴar ƙarama Tunda aka haifi farha Sadiya ita ke rainon farha sabida ƙanƙantar yarinyar sadiya ke fita da ita wajan suyar awara ta goye ta kamar ƴar tsana sadiya kewa farha wanka ta wanke mata kayan ta Umma na jinjina yadda sadiya take son Farha yarinyar akwai wayo Bata yadda da kowa daga umma sai sadiya Cikin haka Farha bata fi shekara Biyar ba kawu yace wa Umma zai aurar da sadiya ga ɗan yayan shi Umma kuka sadiya kuka amman kawu ya rufe ido sadiya tana gama primary Kawu ya aurar da ita duka ƴaƴan yayin shi ya bawa sadiya da sahura Raziƙa kuma ɗan maƙotan su a tare ya aurar dasu su uku.

Nafisa ta rage da fa'iza da farha nafisa sokuwa mai sanyin hali irin na umma shiyasa komai na umma ya koma baya dama sadiya ce gadarar ta Dan nafisa ko an bata awarar ƙarshe ta saki baki maza su kwashe su gudu haka umma ta haƙura dayin awarar ta zubawa sarautar Allah ido sai dai wani abu ɗaya farha halin sadiya gareta Zafi da faɗa masifa kamar me ga ƙanƙanta amman akwai zafin zuciya da ƙarfin hali dan bata ragawa duk wanda yayi mata suma su indo sun haifi ƴaƴa mata bayan farha Indo ta haifi Hadiza Hafsatu ta haifi Ruƙayya sai ƙannen su farha faɗan tsiya kuma kayan su baya taɓuwa Tunda aka sanya farha a makarantar primary lokacin ana shirin bikin Nafisa farha ta mayar da kai ga karatu tana zuwa boko da islamiyya daga ta dawo kuma tayi ɗaki taita bitar karatun ta kaf gidan farha tafi kowa son karatu cikin haka akai Bikin Nafisa lokacin tuni Yaya Sadiya ta haifi mai sunan Umma

Bayan bikin sadiya da nafisa Umma ta haifi Ikram Dole umma ta koma da sana'arta ta wankau sabida ita farha tace ba zata soya awara ba gaskiya ita karatu zatai sai dai kuma duk wankin da za'a kawowa umma zata zauna suyi tare ta ninke takai gidajen waɗanda suka kawo wankin fa'iza son jikin tsiya bata komai sai ci da bacci shiyasa suke faɗa da farha sosai akan wannan lalacin.

Cikin haka wani hamisu ɗan maƙotan su sana'ar Bugu yake na shadodi yace yana son fa'iza Hamisu shike sangarta fa'iza in ƙwai ne haka zai kawo mata taci tai naƙ kayan toshi kuwa kowa zuwa yake kallon na fa'iza sosai Hamisu yake kula da Fa'iza wadda itama kawu ya haɗa su da sauran ƴaƴan su Babarsu Hadiza ya aurar dasu su Uku Gidan ya rage Farha ce Babba a mata sai Yayin ta maza Guda Uku Halifa Nura Salmanu sai ƙanne da suka taso su ruƙayya dan sunfi farha tsayi da jiki in ka kalleta sai ka rantse sune Gaba da ita.

Farha ta gama secondry kawu ya kirata ɗakin sa.


*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*RABO YA RANTSE*

*24*


*A LOVE STORY 24*

Farha ta ƙarasa gaban kawu yana ɗaki yana sauraran labarai a radio.

"Kawu naji ance kana kirana gani"

Kawu ya dube ta bayan ya aje radio ɗin dake hannun shi.

"Na ganki fatima, Dama akwai wani abokina da ɗan sa ya ganki yace yana son ki Salim yaro ne mai kirki da sanin darajar mutane, Yana kasuwanci a kantin kwari dama na barki ne kin gama secondry sabida naga kina son karatu kuma zamani ya canza ƴan uwana da abokaina suna min faɗa akan aurar da ƴan uwanki danai da wuri"

Farha nan da nan ta haɗe girar sama data ƙasa murya a shaƙe tace wa kawu.

"Nidai kawu amin afuwa gaskiya bazan yi aure ba sai na Cigaba da karatu har na kai matakin  dana zama ƴar jarida"

Kawu ya dube ta.

"To baki isa ba daga ke har Hasiya ƙarya kuke aure zaki naji kuma da na gabana"

Farha ta sanya masa kuka wiwi tana masa magiya.

"Kawu kada ka min haka tun asali ina son karatu na kaf ƴaƴanka baka bar kowa yayi makaranta ba dan Allah ka barni nayi"

Kawu ya dube ta ranshi a ɓace.

"Ita bokon Dole ce na barku kun sami na alkur'ani ko a wajan Allah bani da laifi dan haka na soke batun wata cigaba aure zaki salim zaizo ku daidaita"
Da gudu ta tashi tayi ɗakin su Umma tana masifar son farha sabida sunan mahaifiyarta ne in taga farha cikin damuwa ita ma shiga damuwar take nan da nan umma ta ruɗe tana tambayar farha menene farha na kuka tana shaidawa umma.

Bayan umma ta gama sauraran farha tace.
"Sha kurumin ki wallahi ba mai miki aure yanzu har sai burin ki ya cika kedai bari  na saka Najib ɗan umman zage ya cigiya miki f.c.e tunda takardun ki sun yi kyau"
Daran ranar farha ta kwana da farin ciki.
Wanda umma sai da suka kai ruwa rana da kawu sannan ya bar Farha ta cigaba da karatun.

Lokacin da salim ya fara zuwa wajan farha tana zaune ranar Alhamis babu makarantar dare.

Ikram ta sheƙo aguje.

"Yaya kinyi baƙo akan lifan"

A ƙufule farha ta mako mata mafici.
"Dalla malama gafara ki bani waje baƙon ubanki"
Umma dake Cikin uwar ɗaki tana ninke kayan wanki tace.

"Ni wannan zafin rai naki farha shike bani tsoro ita meye laifin ta ai jakada baya laifi"

Farha ta turo baki gaba ta danno shi.
"Nifa umma ina ga baƙon kawu ne gaskiya ina tsoron fita"

Umma ta ɗaga murya cikin ƙosawa da gardamar farha tace mata.

"In ba zaki fita ba ki gaya masa nidai ba ruwana nagaji kullum maganar baban ki ina ɗaure miki gindi to wallahi babu ruwana gwara ma ki tashi ki fita kije kiji damai yazo"

Farha tana gunguni ta miƙe ta yayi bi hijabi a saman ƙyaure ta ɗora akan ta tafita.

"Farha zonan"

Harta kai bakin ƙofa taji kiran umma da sauri ta ƙarasa wajan umma ta tsaya har lokacin tsinin bakin ta bai koma ba.

"Shafa hoda mana fuskarki sai maiƙo take yi"
Badan taso ba ta shafa powder ta fesa turare dama ita bata san kwalliya haka Allah yayita.

Ta fita ta same shi ɗan gajere ne baƙi kakkaura yana zaune a saman lifan ɗinshi daga nesa ta tsaya ta turo masa bakin ta gaba.

"Gani"
Ta faɗa tana kawar da kanta Salim ya sauko ya ƙaraso gabanta ƙaƙƙarfan ƙamshin turaren shi ya bugi hancin ta.
"Assalamu alaiki ya sanyin zuciyata mandirin ƙalbina tauraruwa a birnin dake zuciyata"
Takaici ya kama farha a ranta tana cewa ji wani ƙauyanci amman bata nuna mai ba sai ta amsa mai sallamar.

"Da farko sunana salim ɗa na farko wajan mahaifan sa muna nan tsallaken ku Babana abokin mahaifin kine na gama ginin gidana a mai dule, Ni da gaske nazo da maganar aure Ina kasuwanci a kantin kwari ina sai da atamfofi da Kayan mata"

Farha ta kau da kanta dan ƙamshin turaren Salim ya soma bugar mata da kanta.

"Naji amman ni gaskiya ba yanzu zanyi aure ba in zaka jira ka jira in ba zaka jiraba ka tafi, Ni kam makaranta zanyi har sai kuma na sami aiki sannan zanyi aure"

Ta faɗa tana harare harare.
Salim ya saki murmushi mai ƙayatarwa.
Yana mata kallon ƙuruciya, Aranshi yana Yaba wautar ta.

"Naji na amince in zaki ga ƙarshen biro da takarda ni zan jiraki farha ina mugun sonki tunda na ganki wallahi na kasa sukuni ji nake kamar ina wata duniya daban ta masoya ki taimakeni Farha kada ki juyawa soyayyata baya ina sonki kamar raina a shirya nake dana fuskanci kowani ƙalubale akan son ki"

Farha ta saki baki babba dashi ya dage yana ta zuba mata kalamin soyayya ita har kunya ya bata haka dai ya tafi bai sami amsa a wajan farha ba.

Acikin satin salim ya dami farha da naci ga lokacin ta soma F.C.E Inda ta sami departement ɗin da take so wato Mass comminucation a matakin farko na diploma gaba ɗaya farha ta ƙara mayar da hankalinta akan Karatunta sam bata da lokacin kowa sai na karatu ƙawarta ɗaya shema'u ƴar ƙofar nasarawa Dp ɗinsu guda da shema'u farha nada mugun ƙoƙari yawanci ƴan ajinsu bakwaini suke ce mata sabida tsabar ƙanƙantarta.

Soyayyarsu da salim kuma tayi ƙarfi sosai dan salim irin mutanan nan ne masu naci ya nacewa farha, Hidima yake mata yana kashe mata kuɗi sosai dan yawanci Kuɗin da take kashewa na makaranta salim ke bata tun umma na faɗa harta haƙura kawu mutum ne mai zafi shiyasa ma Farha bata fiye amsar abin salim ba haka Farha ta cigaba da makarantar ta koda yaushe salim idan yace ze turo sai tace ya ƙara mata lokaci.

Farha tana da masifaffan ciwon mara wanda umma ke amsar mata magani dan idan ya tasar mata Har suma take Farha bata da haƙuri ga rashin kunya wani bin salim ma inta Botsare masa da ƙyar yake shawo kanshi Umma tayi namijin Ƙoƙari sosai akan farha dan ita ke biya mata kuɗin makaranta duk wata buga buga umma tayi akan farha ta sami ilimi, Sabida yadda umma take son farha sosai Babban farin cikin farha ta sami aikin jarida idan ta gama makaranta.

Zaman gidansu farha ya cigaba da wanzuwa kamar yadda yake sabida Hidimar da kawu ya barwa matansa yasa ake cewa gidan.

Gidan cida kai sabida yawan su kuma wasu suce ƴan gidan yawa.

Faɗa acikinsu kamar me yanzu da ƴaƴan umma suka taso sam matan gidan bamai takata sai dai fa ta ciki na ciki ne kawai gashi kowa yafi son ɗansa yayi gaba yafi na wani Ƴaƴan gidan nada haɗin kai a waje dan basa taɓuwa amman agida kamar kaji sabida masifa gashi kowa uwarsa ya sani.

Cikin wannan ƙadamin farha ta sami aiki a gidan RADIDON GARKUWA bayan ta gama karatun ta, Ta hanyar yayan shema'u Wanda wannan aiki ne dalilin tarwatsa dukkan Burin farha data ci na ta sami aiki dan taga matan gidansu na shan wahala ta sami aiki dan ta dinga taimakon mahaifiyarta sabida wani bin kwana zasu yi basu ciba Ikram taita kuka Sai dai kana taka Allah yana nashi adaidai sanda ta sami aikin ƙaddarar Auren Aliyu ta tarwatsa mata dukkan waɗannan Burika nata ko yaya rayuwar farha zata kasance?

*WANENE ALIYU*.........

*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*RABO YA RANTSE*

*25*

*A LOVE STORY 25*

Marigayi Sale madaki Shine Kakan Aliyu wanda ya haifi Mahaifin shi Allah ya jiƙan shi da rahma Alhaji Abdu Madaki.
Sale madaki haifaffan jahar kano ne anan cikin Galadanci gidan iyayen shi yake mahaifin sale mutum ne mai dukiyar gaske sana'ar saida fata yake shiyasa mutane ke masa laƙani da Madakin fata Kuma sale kaɗai Allah ya bashi aduniya Bayan Rasuwar Dukkan mahaifan sale sai sale ya gyara ƙaton gidan mahaifan nashi yayi aure ya auro matarshi salamatu ƴar nan kusa da gidan su Suna zaman su lafiya da salamatu inda ya cigaba da sana'ar saida fata ya gaji mahaifin shi.

Shuru shuru tunda sukai aure salamatu bata haihu ba tuni abin ya dameta amman shi sale ya dangana yana bata haƙuri koda yaushe akan cewa Haihuwa lokaci ce haka suka shafe shekaru Biyar da aure Amman salamatu ko ɓatan wata bata taɓa yi ba Ganin haka yasan ya ƙanin mahaifin sale yazo har gida ya same shi lokacin sale bai fita kasuwa ba.

"Nazo ne akan maganar matar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login