Showing 81001 words to 84000 words out of 150033 words
Chapter 28 - Rabo Ya Rantse Book One Complete Hausa Novel
shi bai manta ba"
Kuka take sosai dan ya ƙular da ita da wannan maganar daya gaya mata gwara ya saka bulala ya zaneta.
"Nima Allah ze kawon mafita Kuma wallahi bazan zama abar tausayi ba, dama ko baka gaya min baka sona ba ai na sani haka rannan kace kada naci muku abinci baka san abin yana cimin rai ba ko" Aliyu dariya ta bashi Yadda take acting se yaji duk ta kawar masa da takaicin data ƙunsa masa.
"Eh mana amman dai kin dena cin abincin ko? kin siyo garin kwaki kin mana yajin abincinmu" Pillow ta ɗauka ta kwaɗa masa ya cafe yana haɗawa da hannunta ya janyo ta saman cinyarsa se Kuka take yahau shafa gadon bayanta.
"Shiii to kukan ya isa yanzu gaya min me yake sakaki amai, ki daina min rashin Kunya ni ba sa'an ki bane in ba haka ba Magana ɗaya tak da zan miki zata saka ki kuka ba adadi"
Ya faɗa cikin yin ƙasa da Murya yana laluban zip ɗin rigarta Da dubara Aliyu ya cire mata rigar Jikinta.
"Subuhanallahi Ya Allah........!
Ya faɗa muryar shi a shaƙe Lokacin daya ci karo da cikakken ƙirjinta wanda ya cika ya batse har tsone masa idanu yake.
Ya lumshe ido tare da Buɗewa ya ƙura musu ido babu ko ƙiftawa tabbas yaga sauyi a tare da yarinyar Cikin rashin controling ɗin kanshi ya kwantar da ita yana ɗora fuskar shi a tsakiyarsu yana goga mata sajen shi mai haɗe da gemu a wajan Lumshe ido tayi tana shafa kanshi bata taɓa jin daɗin abin da yake mata ba se yau ɗago kanshi yayi wanda da sauri ta janyo kan nashi ta ƙara mayar wa kamar zata fashe da kuka matso da kan nashi yayi daidai saitin bakinta ya haɗe da nashi ya shiga sarrafa dukkan inda yaci karo wani Irin nishaɗi Aliyu ya tsinci kanshi aciki sakamakon haɗin kan da Farha ta bashi abin da bai taɓa samu daga gareta ba tunda yake zuwar mata da lalurarshi se yau ada har kuka take tana Raki amman yau tsit kake ji kuma sun jima suna Tare seda kowannen su ya sami Nutsuwa ya ɗagata duk Jikinta ya saki ya kaita Bathroom da ƙyar tai wanka sabida bacci Shikam zama yayi tare da zabga tagumi bayan ya tsarkake Jikinsa yana kallon yadda take ta baccinta hankali kwance.
Wajan 11 na dare ya gaji da zaman ya miƙe ze tafi Farha ta riƙo hannunshi tana Murzawa Ta kwaɓe Fuska tana kallon shi.
"Cika ni zan tafi dare yayi ba anan zan kwana ba"
Kukan dake taso mata ta danne, dan ƙari take so sedai kunya ta hana ta tai magana kada ya rainata.
"Zan ci wainar fulawa mai mangyaɗa da tumatur da albasa da yajin tafarnuwa"
Ta faɗa tana Lumshe ido ya zuba mata ido na ɗan Lokaci kafin yace.
"Tashin hankali da wannan daren fatima ki bari da safe se Hajja tayi miki amman ni ina zan sami waina"
Aikuwa ta haɗe rai ta soma hawaye tare da sakin hannun shi ta juya masa baya.
Fita yayi daga ɗakin batare daya yi mata magana ba alamunta suna masa yanayi da na masu juna Biyu idan har ya canka daidai dan haka mami ke masa tsurfa kala kala idan tana da ciki shikuma yayi ta Biye mata dan haihuwar yake so.
Hannu ya ɗaga adaidai Ƙofar daze Fita daga falon Ammi yana addu'ar Allah yasa Abin da yake zargi ne kuma Allah yasa rabon sa ne ya inganta masa da wani irin ƙarfin gwiwa ya nufi parking space dan ya samo mata abin da take Muradi ɗin.......
Yana fita farha ta kwanta a saman gado tana kuka wiwi tasan baze samo mata wainar ba kuma ita idan bata ciba ba zaman lafiya Numfashin ta har wani Ɗaukewa yake ta rasa mai yasa a kwanakin nan duk abin da ta ƙwallafa rai akan shi idan bata samu ba se taji kamar zata Mutu, Kuka take tasan ai kawai Morar jikinta yake ba son ta yake ba bare ya damu da abin da take so Kukan da tayi ne ya haddasa mata zazzafan ciwon kai mai zafi wanda kafin kace Me ta dinga karkarwar sanyi zazzaɓi ne mai zafin gaske ya rufeta zuwa wani Lokacin Idanunta ya Lumshe ta shiga jan Numfashi da ƙyar Jita ke kamar Kwananta ze ƙare...............*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*A LOVE STORY 65*
Cikin wata baƙar ferari488 ya shiga mai azababban kyau ya kunnata ya tada ita ya nufi bakin gate da sauri yake danna horn masu gadi suka tawo aguje suka buɗe masa ƙaton gate ɗin ya saita kan motar ya fita zagaye yake a saman titin Ƙofar na'isa to shi ina zega masu siyar da waina har wajan 12 na dare yana saman kwalta gaba ɗaya jiyay hankalin sa ya tashi bashi da sauran Nutsuwa idan bai samo mata abin da take so ɗin ba a tal'udu ya tsaya wajan wasu ƴan daudu ya siya mata soyayyar awara daya ga suna soyawa ya tambaye su ko suna saida waina suka ce ta ƙare daya ke da face mask a fuskar shi wadda dama yana da ledarta acikin ko wace mota tashi shiyasa ba wanda ya gane shi seda ya karɓi awarar ya koma mota sannan ya lura ashe shirt ɗin sa ma daya ɗauka a ƙofar Toilet ya saka sanda ze fito a baibai ya sakata dan tsabar yadda ta ɗaga mai hankali Driving yake yawanci Sahu ya ɗauke damma cikin gari ne suna hirar dare Cikin yakasai ya shiga kai tsaye gidan Umma Suwaiba ƙanwar Babanshi wadda Mijinta ya rasu yabar ta da marayun ƴaƴa mata da maza wanda mazan Aliyu ne ya ɗauke su aiki a kamfanin sa matan kuma ya aurar mata da uku saura biyu ƴammata a gabanta.
A ƙofar gidan Umma suwaiba yayi parking ya fito samarin ƴaƴanta suna ƙofar gida da abokansu suna hira irin ta matasa Daga ƙofar gidan kuma an ɗan karo ƙofar Aliyu ya wuce su ya Shiga gidan bakin sa da sallama Hasken ƙwan solar daya sa aka haɗa musu ya haske tsakar Gidan Falon ya shiga ya zauna Umma suwaiba dake zaune a saman darduma da carbi a hannunta ta Zubawa Aliyu ido bayan ya zare face mask ɗin taɗan saki Fuska.
Ya zamo daga kujerar daya zauna.
"Umma ina yini"
Cikin mamaki take amsa gaisuwar wadda bayan ita yaja baki yayi Shuru yana matsa hannun shi domin ya rasa ta inda ze fara maganar ma.
Umma suwaiba ta dube shi hankalinta a ɗan tashe.
"Aliyu lafiya kuwa da wannan dare ko dai wani abunne mai ya faru a cikin gidan?"
Ta faɗa aɗan gigice, ya shafa kai yana Duba wayar shi sha biyu da kwata har tayi.
"Umma yaran ma sunyi bacci bara naje kawai" da sauri ta katse shi "Kamar yaya lafiya?" cike da jin nauyin ta yace.
"Wai waina aka taso ni nema Umma wainar fulawa da man gyaɗa da tumatur da albasa da yajin tafarnuwa da wannan daren" washe baki umma suwaiba tayi tare da ɗaga hannunta sama.
"Alhamdulillahi Ya Allah ka tausayawa wannan bawa naka Ya Allah kasa wannan rabo tabbatacce ne, Bari na soya mata Allah sarki mami Allah ya raba lafiya kasan mai juna Biyu idan tana son abu in bata samu ba babu zaman lafiya" Shidai bai ce komai ya sunkuyar da kanshi ƙasa gaba ɗaya jinsa yake kamar bashi ba yanzu ya ƙara tabbatar da zargin sa na Yarinyar can ta sami cikin sane amman duk da haka ze ɗauketa suje asibiti Ya lumshe ido lallai Allah Shine tabbataccen sarki a ɗan zaman su wanda baifi na sati Biyu ba har Rabon ciki ya Shiga tsakanin Su wato Rabon haihuwa dashi ne ya haɗa su Rabon haihuwa dashi ne yakai ta aikin jarida Rabon haihuwa dashi ne yasa ta Bijirewa Iyayenta da masoyinta ta zaɓe shi Lallai Rabo dangin Ajali ne Idan Ya Rantse se me shi lallai RABO YA RANTSE! A tsakanin shi da fatima Jiyay yana masifar ƙaunar abin da ke cikinta wata irin murna da farin ciki yake ji jiya ke kamar akan ta ya soma ganin cikin shi yana son duk abin da ke cikin nata wani irin tausayin yarinyar yaji ƴar ƙarama da ita tana ɗauke da cikinsa ta rabu da kowa nata sabida shi gaba ɗaya Jikinsa sanyi yayi har Umma suwaiba ta kawo masa wainar bai gama dawowa daidai ba, komai daya ce ta haɗa a saman wainar yayi mata godiya ya ɗauki kular da wainar ke ciki Umma suwaiba har soro ta bishi tana faman yi masa addu'a da fatan alkairi ya fita se lokacin Ƴaƴan Umma suwaiba suka gane shi aikuwa suka taso suna gaishe dashi sukai sallama ya shiga mota se Gida Lokacin ƙarfe ɗaya ta kusa yana shiga gida ɗaya nayi Ya kashe Motar ya ɗauki Ledar takeaway ɗin awarar da kular wainar ya shiga sashin Ammi ya buɗe ƙofar falon da key ɗin Jiki tunda an gyara ƙofar falon duhu dum ɗum ya lalubi Ƙofar ɗakin nata ya buɗe ya shiga ciki har Lokacin da haske a ɗakin Da alamun bata kashe ƙwan ba ya aje kayan hannunsa ya ƙarasa bakin gadon ya zauna ya Sanya hannunsa ya ɗagota Jiyay jikinta kamar gaushin wuta se faman Nishi take.
hankalin shi a tashe ya shiga cewa.
"Fatima ke fatima yaya zaki min haka gafa wainar nan na samo Miki tashi kici"
Lumshe ido tayi tare da ɗora kanta a kafaɗar shi tana jan Numfashi tana hawaye.
Muryarta a hankali take masa magana
"Ni kabani wainar naci yunwa nake ji"
Ɗagata yayi ya saukar da ita ƙasan carpet ya ajeta ya ɗauko wainar da awarar hannun shi har rawa yake ya shiga Buɗe wainar sedai tana jin ƙamshin ta se ta miƙe aguje amai taita sheƙawa a banɗaki ya taimaka mata ya gyarata ta fito tana dafa bango.
"Ka fitar min da ita bana son ƙamshinta"
Aiki ja ya faɗa a ranshi lallai ciki a gaishe shi duk wahalar da yasha kafin ya samo wainar nan amman ance ba'a ci ya fita da ita.
Ya karya muryar shi.
"Haba fatima nasha wahala kafin na samo dan Allah kici ko kaɗan ce"
Ta zauna ajikin gado tai sama da kanta kafin ta saka hannu tana toshe hanci"Ni bana so nace ka fita da ita in ba zaka fitar ba ni sena bar maka ɗakin" da sauri ya rufe wainar ya aje saman madubi "To yanzu me zaki ci?" se faman nishi take daga gani ƙarfinta ya ƙare sabida aman da take ta faman yi awarar ya tura mata gabanta cikin tsoro yana addu'ar Allah yasa taci ga mamakin sa se yaga ta saki fuska ta kalle shi "Dama ita nake so kuma yanzu" bai ce mata komai ba ya zuba mata ido duk ta sauya masa, taja awarar tana ci hannu baka hannu ƙwarya kamar wani ze ƙwace mata duk yawan awarar seda ta cinyeta tsaf tayi hamdala "zan sha ruwa" ta faɗa tana lumshe ido ya tashi yaje fridge a falo ya ɗauko mata ruwan tana kallon ruwan ta taɓe baki "Ba lemo?" yaɗan kalleta "Wanne kike so Gimbiya?" ya faɗa yana kallonta "Coca cola nake so" da sauri yaje ya ɗauko mata irin babbar nan, ya kawo mata Ruwan ta buɗe ta ɗauki Cup ɗin Kusa da ita ta buɗe coc ɗin ta zuba a cup ta ƙara ruwa ta shanye daga haka se bacci a wajan ta dinga bacci Ya tattare komai data bari ya gyara wajan Ruwa ya taro a bawo da ɗan towel ya ɗagata ya mayar saman gado ya cire mata kayan jikinta ya shiga goge mata Jikin nata da ruwan sabida zafin da Jikinta ya ɗauka ruf da ciki tayi a saman cinyar shi ta saka hannu ta zagaye Ƙugunshi kanta yana daidai cikinsa ta cigaba da baccinta Da dubara ya sauke bawon da towel ɗin ya jingina da jikin bango har asubahi Aliyu bai rintsa ba yana zaune ita kuma tana jikinsa baccinta take hankali kwance..............*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*A LOVE STORY 66*
Rasa yadda zeyi ya zareta daga jikin sa yayi sabida baya son yayi Missing Jam'i a hankali kamar mai tsoron kada ta farka ya ɗagata ya ɗora kanta saman Pillow ya kwantar da Jikinta a saman gadon ya sanya ƙaton Devut ya rufe mata Jikinta dashi ya yunƙura ze tashi ta riƙo hannunsa ya leƙa fuskarta Idanunta a lumshe yake sedai ta ɗan turo bakin ta gaba Ya ɗanyi Murmushi wato acikin Baccin ma se anyi tsiwa
Ya zame hannunta daga cikin nasa Ya sauka daga saman gadon ga mamakin sa se yaga ta tashi zaune ta ɗan kalle shi.
"Ina zaka tafi Kuma ni wallahi bazan zauna ni kaɗai acikin ɗakinnan ba ga sanyi ga tsoro"
Ya bita da kallo kafin yaɗan langwaɓe kanshi muryarshi Very cool, yace mata.
"Sallah zan je nayi Kimin afuwa"
Daga haka da sauri ya buɗe Ƙofar ɗakin nata ya fita Cikin sauri ya Ƙarasa masallaci a bakin masallaci Yayi alwala ya shiga ciki Lokacin ana ƙoƙarin tada sallah ya bi jam'i bayan sun idar ya jima yana zaune baya tunanin ya koma wajanta saboda yana son fita Office yasan idan ya koma kuma wata rigimar ce sabuwa sedai kuma ya shiga tunanin abin da zata ci Jikinsa ba ƙwari ga rashin bacci ga gajiya haka ya ƙarasa part Ɗinsa ba kowa a falon da alamun Mami bata tashi ba Saman shi ya wuce yana shiga ɗakin sa ya faɗa wanka ya fito Jallabiya kaɗai ya saka ya ɗan fesa turare sama sama ya kwanta ba jimawa wani bacci mai daɗi ya kwashe shi..
Jikin mami yana wani irin mazari ta shiga ɗakin ta tare da danno Ƙofa ta sanya Key ta shiga Kiran mamanta Tajira tana zaune tare da wata ƙawarta taga kiran Mami ta ɗaga tana cewa
"Yaya aka yi kike ta jera min kira da wannan Lokacin?"
Mami ta share zufar data karyo mata cikin sauri tace.
"Mama ba kanta fa akwai matsala"
Da sauri tajira tace.
"Matsalar me kuma sarkin ƙorafi ba dai za ki barni na huta ba"
Mami ta ji gabanta ya faɗi haka dai ta danne ta soma cewa.
"Wallahi mama aiki ya sami tangarɗa dan Aliyu yaci abincin Ammi yau ni bamma san yadda zan ba kaina gaba ɗaya ya ɗaure"
Zumbur Tajira ta miƙe tare da shiga cikin ɗakinta.
"Me kika ce mami wannan wace irin banzar magana ce maganin da muka tsallake tsaunika sahara Burji muka karɓo shine zaki ce Aliyu yaci dan ubanki asarar Kuɗina nayi kenan kome?"
Kuka mami tasa ta soma cewa
"Wallahi mama nayi iya yina akan kada yaci amman shi seda yaci Ni babban tashin hankalina ma kada Aliyu ya mutu koya sami matsala"
Tajira ta kwashe da dariya.
"Ah lallai laila majnun! tattabara uwar soyayya ai ba zaki gane barno gabas take ba har se ya danƙaro Miki kishiya ni ina ruwana da wani Aliyu yaci Allah yasa ma gaba ɗaya su Mutu gayyar tsiya mu huta"
Mami tai saurin cewa
"A,a mama Ammin dai ta Mutu amman ban da Mijina yanzu Mama meye mafita?"
Tajira tace "Ai cigaba da danƙarawa matsiyaciya dan dai kuskure ɗaya nasan baze hanata sheƙawa barzahu ba kada ma ki damu shima inda rabon ajali yaci can gasu gada"
Mami bata ji daɗin furucin mahaifiyarta ba ita tana son Mijinta kuma tana son su rayu tare saɓanin mahaifiyarta da kawai daula da dukiyar take hange ba komai ba sallama sukai mami ta kashe wayar anan tai kwanciyarta tana saƙa wasiƙar jaki har dare ya raba ta kasa bacci Kuma ta kasa tinkarar ɗakin Aliyu sabida shakkar sa take tunda yace mata idan yaci ze Mutu shikenan taji tana shakkar Tunkararsa a taƙaice anan ta kwana wanda se asubah bacci ya ɗauketa ba ita ce ta farkaba se bakwai na safe tai sallah ta Kuma komawa Baccin nata.
Da ƙyar Farha ta tashi taje toilet alwala ta ɗauro a zaune ma tayi sallah sabida yanzu kuma ƙafafunta ke mata wani irin ciwo jita ke kamar ana sara mata su wainar jiya daya aje a saman madubi ta ɗauka a haka ta dinga cusawa tana ci duk da tayi yami amman ita tai mata daɗi tana gama ci ta koma gado se Bacci Hajja data zo aikin safe ta leƙo ɗakin ganin Farha na bacci ne yasa bata tashe taba ta shiga kitchen ta soma haɗa musu abin karyawa wajan ƙarfe goma sakina ta fito falon lokacin hajja tana tsaka da jera kayan kari a dining suka gaisa da sakina wadda ta zauna a saman Kujera sakina ta ɗan dubi hajja tana cewa.
"Dan Allah Hajja ina wannan yarinyar ta jiya?" Hajja tai Jimm kafin tace "Oh fati tana ɗaki bacci take dan Jiya tasha aiki"
Sakina ta ɗan kalli Hajja se kuma tayi shuru can kuma tace "Taso min ita tayiwa yarana wanka zamu fita ne Nida Jamila zamu je gidanmu" Da Hajja har zata yi magana se kuma ta fasa ta kama hanyar Ƙofar ɗakin Farha da ƙyar Hajja ta farkar da ita daga baccin sabida baccine mai nauyi "Tashi fati zaki wa ƴaƴan sadiƙ wanka inji Hajiya sakina tana jiranki a falo" Idanu jajir Farha ta miƙe Jiri ke ɗibarta Wanka tayi sama sama ta fito Doguwar rigar material ta saka tare da yafa ɗan ƙaramin Mayafi a saman kanta wanda ya tsaya iya wuyanta Doguwar rigar ta karɓi surar Jikinta domin daga ƙirjinta ta kamata daga ƙasa ne ta buɗe ta ɗan fesa turare kaɗan ta fita falon tunda ta fito sakina ta zuba mata ido haka kawai aranta take jin yarinyar batai mata ba ita dai Farha a gaban sakina ta tsugunna tana gaishe ta a yatsine tace.
"ki shiga bedroom ɗin da muka kwana ki gyara mana shi ki wanke mana toilet sannan kiwa yarana wanka"
Daga haka sakina ta tashi tabar Farha a wajan
Cije baki farha tayi domin yadda ƙafafunta ke ciwo ba zata iya sunkuyon wankin banɗaki ba sedai babu damar ta musa cibi ya zama ƙari haka ta miƙe tayi hanyar ɗakin da sakinar ta umarce ta a bakin ƙofar ma seda ta ɗan tsaya tana cije