Showing 87001 words to 90000 words out of 150033 words
Chapter 30 - Rabo Ya Rantse Book One Complete Hausa Novel
"Bana gida, kuna lafiya ko? dama na kiraka ne danna gaya maka ka kwantar da hankalin ka Baba akan kome zaka gani daga wajena Ina ɗaukarku a matsayin mahaifa dan Allah ku saki ranku fatima tana cikin Ƙoshin lafiya kuma zata zo gare ku Very soon cikin farin ciki" Kawu yahau share ƙwalla har Muryar shi tana rawa lokacin da yake cewa "Nagode Nagode Ali Allah yayi maka albarka ada ina ta ɗar ɗar amman jin kamilalliyar Muryarka yasa naji nutsuwa Kuma muna ta ganin saƙo yau ma kayan abinci sun Kuma sauka wasu kan wasu harda na maƙota mun gode ƙwarai" Aliyu yaji Nauyin godiyar kawu seya basar da amsa godiyar yace "Ina mama kuma mu gaisa?"kawu yace bari ya miƙa mata Umma tana ɗaki ta zabga tagumi duk abin duniya ya dameta ita fa kada suje ko kuɗin kan yarsu ake kawo Musu da sunan Kayan abincin kawu yayi sallama ɗakin yana cewa "Ungo Hasiya kuyi magana da Mijin Fatima" umma ta saki ajiyar zuciya ta amshi wayar tun kafin tai sallama Aliyu ya rigata yana kuma haɗawa da gaisuwa cikin ladabi.
Cikin jin nauyi umma take amsa gaisuwar kuma daga jin muryarshi tasan Ba ƙaramin yaro bane dan babu baragada ko shirme a nutse yake gaishe da ita.
"Umma Aliyu ne Mijin fatima na kira ne Mu gaisa kafin nazo Muku da ita dan Allah ki kwantar da hankalin ki wallahi Fatima tana cikin Ƙoshin lafiya kuma komai kika ga na aiko da zummar na kyautatawa mahaifana Nayi muku bada wata manufa ba dan ku kamar iyayena kuke"
Umma ta saki fuska tace.
"Babu komai na Gamsu Kuma in sha Allah zan dena wasi wasi a game dakai nidai ina roƙon ka daka dinga haƙuri da halin Farha yarinya ce mai tsiwa Se an haɗa da haƙuri watarana se labari sannan Muna son zamu turo ƴan uwanta don suga inda take kaga ba abin da akai mata na aure daga cikin abin da ya shafi ɓangaran mahaifa dan haka ina son ƴan uwanta suzo nan su ganta"
Aliyu ya Lumshe ido ya buɗe tare da cewa.
"In Sha Allah Mama Fatima ce zata fara zuwa ta gaishe daku,sannan maganar wani abun ɓangaran iyaye kada ki damu komai zan mata ai haƙƙina ne ina son zanje umara nan da ƴan kwanaki Se bayan sallah inna dawo zamu zo daga nan ma suma zan ɗauke su sesu gano inda take"
Umma cikin Nutsuwa tace
"To angode Allah yayi maka albarka Munga abin arziƙi Allah yasa kafi haka Allah ya raya maka zuri'a"
Cikin alkunya yake amsa addu'ar da umma keyi Masa, Bayan kawu ya amshi wayar Aliyu ya ƙara Kwantar masa da hankali kuma sosai kawu ya sami Nutsuwa da hakan sukai sallama.
Aliyu ya aje wayar ba tare daya kira Ammi ba dan har gabanshi faɗuwa yake inya tuno gida dan yasan Ammi nacan na jiran shi seda ya cewa musa ya tsaya yayi masa siyayyar kayan lashe lashe dana marmari Musa ya fita yaje ya siyo ya dawo mota suka ƙaraso gida A harabar Gidan Musa ya bawa Aliyu keyn motar suka yi sallama da juna seda Aliyu ya tsaya a masallacin Gidanshi yayi sallar Isha'i wadda ake ta kira kafin ya ƙarasa Part Ɗinsa siyayyar ya raba Biyu ɗaya ya bari a mota ɗayar ya shiga da ita ciki.
Da sallama acikin bakin shi ya shiga Ƙaton falon nashi mami tana zaune a falo tana kallo taci gayu cikin Cgreen material ɗinkin Riga da skirt tasha kwalliya a fuska Jikinta yana tashin ƙamshi da sauri ta ƙaraso wajan shi ta amshi Ledojin dake hannun shi takai dining ta aje tana mai sannu da zuwa
Ya raɓe ta ya haura saman shi mami tabi bayan shi Lokacin data shiga Bedroom ɗinshi yana tsaye yana Cire kayan shi ta ƙaraso gabanshi ta taimaka masa ya cire rigar Jikinshi ta Cire mai agogon dake hannunshi Ta Shiga Bathroom ta haɗa masa Ruwan wanka hatta towel daze tsane Jikinsa seda mami ta aje masa sannan ta fita daga ɗakin
Ƙasa ta sauka ta haɗa masa abinci a dining komai tayi readyn sa sannan ta koma Lokacin ya fito daga wankan yana tsane Jikinsa da ƙaramin towel Mami ta buɗe closet ɗinsa ta ciro masa Jallabiya Brown colour tare da Boxer da singlet ta feshe turare ajikin kayan ta miƙa masa tana tsaye ya saka kayan ta kwashe towel Ɗin daya cire da wanda ya goge Jiki ta kai washing machine ta Gyara masa gadon sa sabida zanin gadon yaɗan yamutse.
"Mamy Allah yayi miki albarka Allah ya Shirya min ke"
Ya faɗa cikin jin daɗin Hidimar data ke masa Don mami mace ce harda ƙari bada ban ya kamata da laifin daya ke binciken ta dashi ba da se yace ko kawo masa ƙararta akai baze yarda ba zece sharri akai mata sabida Halinta na zahiri data nuna masa na Juriya da kirki da kunya.
Gaban mami yaɗan faɗi dan har Lokacin ɗari ɗari take dashi.
"Yaya me nayi kuma da zaka ce Allah ya shirya ni?"
Ya saki wani malalacin murmushi mai sauti.
"Nima kice Allah ya shirya ni zan ce Amin" Ya faɗa yana Lakatar Kumatunta dariya tayi tare da kama hannun shi ta langwaɓar da kanta
"Yaya muje Abincin yana jiran ka"
Ya shafi saman cikin sa.
"Kamar kin san ina jin yunwa"
Yabi ta suka sauka seda Ma suka kai dining sannan yace ta je ta ɗauko mai wayar shi a saman gado ta koma ta ɗauko masa ya amsa ya saka a aljihun jallabiyar shi Sakwara da Miyar ganye wadda taji naman sa irin yankan manya manyan nan ta zuba masa ta tura mai.
Ya yatsina fuska yayi.
"Kin san ban son abinci mai nauyi da daddare kuma ina son sakwara amman dan mugunta baki da da rana ba se dare" Dariya mami tayi tace "To ina ma ka zauna da ranar in da zaka zauna ai da kaga Sakwara" ta faɗa tana dariya ya janyo silver ɗin data zubo masa ruwan wanke hannu ya wanke yayi Bisimillah ya soma ci ƴar kaɗan yaci yace ta haɗo masa Coffee miƙewa tayi ta koma Kitchen ta haɗo masa yasha ya Miƙe ya kalleta.
"Zan je wajan Ammi bana son dare yayi rabo na da ita tun safe"
Dariya mami tayi tana cewa.
"Ai yaya baka taɓa Burgeni ba se yau"
Ya wani zaro mata ido wanda ya ƙara hasko kyansa yace mata.
"Yanzu duk Ƙoƙarin da nake danna Mantar dake komai bana burgeki se yau?"
Mami dariya take sosai har tana Rufe baki kafin tace "Kai yaya kana da fassara marar ƴanci bafa anan wajan ba Ina nufin yadda kayi wa sakina akan Farhan gobe ai ba zata Kuma dukan ƴar mutane ba"
Shima Murmushin yayi tare da cewa
"Okey na gane, to mamy ai abin da sakina tayi bai dace ba, bari naje kada Ammi tayi bacci"
Yayi saurin kawar da maganar sabida baya bawa mami fuskar Kawo masa maganar ƴan uwan shi.
Duk da itama ɗin ƴar uwarshi ce amman kowa ɓangaran shi daban.
"To ka gaida ita nikam yaya Zan kwanta a ɗakina dan Ina Fashin sallah zan sha magani kafin kazo ma inaga nayi bacci"
Ya wani kama ƙugu ya zuba mata ido.
"Kina nufi me kenan ba zaki zo ɗakina ba kome?"
Da gudu tabar wajan tana cewa.
"Bye yaya seda safe"
Sabida tasan nacin sa ko tana Mp ɗin ma seta sha matsa a wajan sa dan seta gwammace kiɗa da karatu..........*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*A LOVE STORY 70*
Seda yaga shigarta cikin bedroom ɗinta sannan ya saki ajiyar zuciya mai ƙarfi ya Fita daga Falon bayan ya kashe hasken Falon ya rufo Ƙofar Ko ina haske ne a harabar Gidan ga securities kota ina wani irin daɗi yaji da Mamy ta kawo masa reason ɗinta na ba zata kwana a ɗakin shiba sabida dama a yadda ya tsara ya raba yau ma kwanan Fatima ne sabida Lokacin daze tafiya a ɗakin Mamy yake Yanzu kuma daya dawo Jiya ya kwana a ɗakin Fatima yau ma anan ze kwana Gobe kuma mamy da Jibi dama ya rasa yadda zeyi da Mamy se kuma Allah ya kawo masa mafita Seda ya biya mota ya ɗauko abin da ya sai mata ya shiga falon Ammi a dining ya aje ledojin ya ƙarasa cikin falo Bashir ne kaɗai a falon yana danna waya Aliyu ya kalle shi ya wuce Ɗakin Ammi yana tafiya yaji gaisuwar da Bashir ke masa ya amsa Tare da shiga ɗakin Ammi Ya tarar da ita a zaune a ƙaramin falon ta Tv kunne tana kallon Sunna Tv ya zauna daga nesa da ita yana gaishe ta.
"Ba gajiya baba yaya Isa da kai?"
Ya ji ta faɗa Ya ɗago batare daya gano me take Nufi ba Ammi ta kuma maimaita masa"Nace yaya isa da kanka baka ga Kirana bane Ko har ka kai matakin da zan Kiraka ka ƙi ɗaga wa Baba?" Aliyu ya matso gaban Ammi da sauri ya kama Ƙafafun ta Jikinsa duk rawa yake dajin furucin Ammi "Ammi kada ki kuma faɗin haka Allah kada ya kaini matsayin da zan Kauce umarnin ki Ammi duk abin da kika ce nayi zanyi muddin bai kauce umarnin Allah ba"
Ammi ta yi dariyar takaici "An ya kuwa Baba nakai matsayin nan tunda inda nakai ba zan ce kayi abu ba kaƙi yi" da sauri yace "Ammi me kika ce nayi bam miki ba Ammina?" ya faɗa duk hankalin shi a tashe "Cewa nayi ka ce wa Musa yazo ya ɗauki ƙanwar shi dan annoba ce agidannan Tunda nake dakai ban taɓa jin kayi Musayar yawu da matar Sadiƙ ba se akan ta haka kwanakin baya ka kusan kashe ƙannen ka akanta, sannan Shima Bashir naga take taken sa to sabida haka Nidai ba zan sami kwanciyar Hankali ba har se ka ɗauke yarinyar nan daga gidannan In ba haka ba Nida kaina zan sa a samo Min Numbern musa na Gaya masa" ALIYU ya yarfe zufar data ke Karyo masa duk da sanyin Ac'n dake falon Ya kalli Ammi wanda inda ta lura zata hango Tashin hankalin daya shiga amman da yake hankalinta ba anan yake ba sam bata lura ba "Shikenan Ammi in dai matsalar Wannan yarinyar ce kada ki damu, Amman kimin alfarma zuwa bayan sallah kafin nan zanyi mata ɗan alkairi wanda Musa zeji daɗi batare daya San kece kika ce a koreta ba" Ammi ta ɗaga masa hannu "Kada ka raina min hankali Me Yasa ba zaka mata alkairin yanzu ba se bayan sallah kafin nan ta gama min illah a gidana kawai ka sallame ta yau Gobe ta kama hanyarta" Aliyu yaji Gabansa ya faɗi aiko Fatima bata da Cikinsa baze iya korarta ba bare Kuma yanzu da take ɗauke da Gudan Jininsa rabin rayuwarsa Cikin daya Saka rai da shi.
"Ammi ki haƙuri" tayo masa kaa "kai bazan saurare kaba Ai bama kai Musa ya kawowa ba ni ya kawowa dan haka tafiya zatai ba zata zauna min ba" Aliyu yaji ranshi ya ɓaci Mai yasa yawanci Ammi tafi takura shine fiye da kowa "To Ammi duk yadda Kikai daidai ne Allah ya taimaka" daga haka ya Miƙe ya juya zebar ɗakin tasan sarai haushi yaji seta sanyaya Murya "Shikenan amman ana sallace sallah zata bar min gidana" Muryar shi can ƙasa yace "Duk yadda kika ce Ammi"
Yabar mata ɗakin Yana fita falon Jamila ta fito daga ɗakin da suka sauka dan har Lokacin ba'a gyara part ɗin sadik ba sanye take da riga da wando na pakistan kanta ba ɗankwali Zata shiga Kitchen ta tsaya ya ƙaraso zeyi hanyar dining ta sha gaban shi tana wani kaɗa mai Jiki tai ƙasa da murya.
"Aliyu kasan dan kai na sauka a gidannan amman kana ta share ni" Takaici yazo masa wuya wannan wace Irin mace ce marar kamun kai Tun kwanakin baya da sakina tace masa Ga jamila ya aura ko Allah ze sa A dace ta haihu dan su Irin haihuwa ne Buɗar bakin sa ya bawa sakina amsa da cewa Ai mami ma ba Juya bace Allah ne bai tsayar ba Dan Shi gaba ɗaya jamila bata cikin tsarin matan da yake so kwata kwata dan wayewar ta tayi yawa idanunta a buɗe yake shikuma sam baya son macen da idanunta yake Buɗe, bayan nan ma totaly Jamila batai masa ba.
"Idan danni kike zaune anan, Gidan lallai zaki dawwama aciki dan abin da kike Bibiya ba zaki samu ba Idan kika kuma shiga harkata kuma" ya matse yatsun sa suka bada sautin ƙas! ƙas! ya juya zebar wajan ta kamo Gefen Rigarshi tai raurau da ido zatai Kuka ya ɗora hannunshi ajikin rigar tashi ze Cire hannunta adaidai nan farha ta fito yunwa take Ji Kanta har juyawa yake dan azabar yunwa sabida tun da ta Kulle kanta sallah ke tada ita sam bata Leƙo falon ba rabon ta da abinci tun wainar safe idanun farha ne suka sauka akan Shi suna tsaye shida wannan Budurwar Goge idonta take dan ta tabbata abin da ta gani Gizo ne Ko Gaskiya sedai Idanunta ya nuna mata gaskiya adaidai nan Aliyu ya zare hannun Jamila daga rigarshi ya Juya yayi hanyar dining da Gudu ita Kuma jamilar ta Juya ɗaki tana dira ƙafa kamar ƙaramar yarinya se hakan ya Bada style kamar Masoyan da suka rabu cikin shauƙin ƙauna Farha jitai tana neman faɗuwa wani Irin Kishi mai zafi ne ya taso mata rasa Yadda zatai tayi domin Yunwar ma jitai ta daina Jinta Juyawa tayi ta koma ɗaki wanda adaidai nan kuma Aliyu ya ɗago dan yaji ƙarar Rufe Ƙofa Ɗaukar Ledojin da ya mata siyayya yayi ya Nufi hanyar ɗakin nata wanda adaidai nan ita kuma ta Jingina da Jikin ƙofa ta ɓare baki tana Kuka kamar Wadda aka cewa Umma ta rasu..............*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*A LOVE STORY 71*
Aliyu Ya Murɗa handle ɗin ƙofar yaji ta a rufe Ya laluba aljihun jallabiyar shi ya ɗauko key sedai koda ya zira shi jikin ƙofar yaji da alamun wani key ɗin ajiki A hankali ya Jingina da jikin ƙofar ya ɗan kara Fuskar shi yana jiyo sautin kukan ta Danna ƙofar yake a hankali yayi magana wadda yake da tabbacin zata jita.
"Fatima ki buɗe min ƙofar wai mene ne hakan?"
Shuru yaji taƙi magana still kukan take yi bata daina yin shiba, Cikin hargowa yace "Wallahi in baki buɗe ba zan sa a ɓalla ƙofar wannan wani irin rainin wayo ne zaki rufe mini ƙofa" Cikin tsiwa tace "Ni bazan buɗe maka ƙofar ba sabida bana buƙatar ganin ka a ɗakina" Murmushi yayi tare da cewa "Please Fatima dan Allah ki buɗe min" turo bakinta tayi gaba tare da Buɗe mai ƙofar da sauri ya tura ya shiga ya maido ta ya rufe tana Ƙoƙarin juyawa da zafi zafi ya janyota jikinsa ya haɗa ta da ƙirjinsa Ƙamshin mayen turaren shi na Labbra ya doki hancin ta wani irin kashe mata jiki ƙamshin yayi har tana neman faɗuwa ƙasa ƙara kamata yayi sosai ya saki ledojin hannunshi ya Turata Jikin bango ya danne mata Ƙirjinta da ƙarfin nasa ƙirjin Ya kawo fuskar shi dab da tata ya tsare ta da girman Idanunshi Lumshe idanunta tayi dan ko kaɗan ba zata jure wannan Kallon da yake hukunta ta dashi ba Hura mata iskar cikin bakin sa yake mai ɗauke da ƙamshin Mint a hankali hawaye ya soma fitowa daga cikin idanunta Bai hanata Kukan ba Zubewa tai a jikinsa tasa hannu ta kamo Ƙugunshi wanda ta kasa ritsawa sabida Yadda yayi mata girma Shikuma ya saka Hannu yana shafa gadon bayanta tsawon Minti goma suna a haka kafin ya ɗagota a hankali ya raɗa mata.
"Be quiet and tell me what made you cry, but this cry of yours is too much Fatima" turo masa mitsitsin bakin ta tayi gaba wanda yasa Haƙorin shi yaɗan cije ƙasan lips ɗin nata Kuka ta saka tana dira ƙafafunta ɗagata yayi cak ya nufi gado da ita ya ɗora ta akai tare da sunkuyo wa daidai Fuskarta "Nasan dalilin kukan naki yanzu zan Miki maganin shi" juya mai baya tayi Shikuma yaje ya ɗauko Ledojin daya yar a bakin ƙofa Ya hawo saman gadon ya ajesu Sannan ya miƙe Tsaye tare da cire jallabiyar Jikinshi Rintse idanu tayi sabida yadda Ƙirarshi ta bayyana acikin singlet da boxern daya rage ajikin sa lallai maza ba kunya cewarta cikin zuciyarta Bata tsorata ba seda ya kuma hawowa gadon ya juyo da fuskarta tana facing tashi Fuskar hannu yasa ya shiga buɗe Ledojin ƙamshin kazar data sha gashin Inji ta doki hancin ta Lumshe ido tayi nan da nan yawun bakin ta ya shiga tsinkewa Ya fito da Soyayyan dankali Wanda akai masa ƴar miyar ƙwai a saman shi se tsire wanda yaji Ƙuli da su Cabbage Haka ya dinga jere mata dukkan kayan ƙwalam ɗin daya siyo mata a gabanta.
"To Gimbiya kici wanda kike so a gado sena ɗauke idan kin gama ci"
Ya faɗa da Murmushi a saman fuskar shi Maƙe kafaɗa tayi tare da turo baki.
"Ummmm ni bazan ciba"
Seta hau masa kuka Yaɗan matsota kaɗan ta kafe shi da ido ko ina na jikinshi gashine kwance hatta cinyarshi wadda take fara ƙar kamar ka taɓa Jini ya fito acikin ta.
"Sabida me ba zaki ciba Pls fati kada ki Hukuntani da rashin Cin abincinnan dan Allah"
Haɗe rai tayi tare da cewa.
"Idan naci damuwar kace, Ba yanzu na ganka da waccan Guzumar ba wallahi an dai Ji kunya"
Ya ɗan ɗage gira se kuma yayi dariya wadda tai masa kyau kafin yace.
"To ina ruwanki niba Mijin mace Huɗu bane, Kika sani ko amarya zan Miki"
Ya faɗa cikin sigar wasa dan yanayin nata ya saka shi acikin Nishaɗi.
"Allah ya kiyaye kayiwa mami dai amman bani ba"
Har Lokacin dariya yake "Ai ke akaiwa mamy Ita kuma ke za'a yiwa"
Juya masa ƙeya tayi tare da cewa.
"Kama sani Wallahi idan ka aureta sena gudu kuma bama gida zanyi ba dan kar ma kaje a maido ni"
Tana faɗa tayi Rub da ciki ta