Showing 9001 words to 12000 words out of 150033 words
Chapter 4 - Rabo Ya Rantse Book One Complete Hausa Novel
karya ɗin ba zaki tafi?"
Tai murmushi mai ƙayatarwa.
"Umma sai na dawo zan karya ɗin"
Acikin kuɗin da Salim ya bata jiya umma ta ɗauki dubu ɗaya ta bata tana mata fatan alkairi.
Ta fita tsakar gidansu batare data kalli matan gidan dake hada hadar ɗumaman tuwo da dama koko ba.
"Manyan ma'aikata sai ina?"
Cewar Babarsu Hadiza cikin sigar zolaya.
Farha data sa kanta a soro ta ɗaga murya sosai tace mata.
"Gidan nasara da sa'a na nufa in Allah Ya yarda"
Daga haka tafita daga gidan titi taje ta sami abin hawa sai da ta biya ta ɗauki shema'u sannan suka wuce.
Suna tafe suna hira inda shema'u take bata labarin da ya gali ya bata jiya na cewa ashe Gidan rediyon na wannan mutumin ne anan ya galin su ya fara aiki kafin ya bari wai kuma in dai zaka samo wa md rahoto tofa zai ta ƙara maka albashi.
Farha tai zuru kafin tace.
"Ya Allah kasa mudai muna da rabo"
Haka suka ƙarasa bakin gate ɗin bayan sun sallami mai Adaidata sahun daya ɗauko su, Suka shiga cikin gidan Rediyon zaman jiran Md ɗin sukai har wajan takwas da rabi kafin ya ƙaraso.
Da far'a ya dube su.
"A,a su fatima ne da wuri haka, Ah lallai ba zamu dinga samun matsala daku ba ku biyoni ciki"
Suka miƙe suka shiga office ɗinsa.
Zama sukai a saman kujerun office ɗin shima ya zauna sannan suka soma gaishe dashi.
Ya dube su Yana ɗaga takardun su.
"To Alhamdulillahi duk abin da nake buƙata a tare daku na samu, sai dokar gidan rediyon nan da zan faɗa muku, Bana son fashi sannan labarai na hausa da turanci ko wanne ya faɗo kanku zaku iyayi"
Duk suka bashi nutsuwar su sannan ya ɗora.
"Ni dai fatana duk inda labari yake mai daɗi wanda zai ja hankalin jama'a ina maraba dashi ku kawo mana Mu watsa tashar mu ta sami karɓuwa, Albashin ku dubu ashirin ne a wata, sannan babu taka maiman lokacin tashi ya danganta da yadda duty yazo muku wanda ake kafewa a waje kowa ya duba lokacin shi"
Farha a wannan karon ma sai da ta zube ƙasa tai masa godiya ya umarce su dasu tashi ya rakasu su zaga wajan da yakamata haka suka bishi ya nuna musu ko ina hatta ɗakin yaɗa labarai da sauran su Ma'aitan tashar basu da yawa abin har ya bawa su farha mamaki, Haka suka gaggaisa da sauran ma'aikatan sannan ya baro su anan domin suga yadda ake gudanar da aikin.
Ranar su Farha basu tashi ba sai wajan la'asar kuma ba komai sukai ba kawai ganin yadda ake labarai ne da yadda ake ɗauka da yadda ake yaɗawa Wanda kafin kace me Farha harda daɗa ganewa sosai.
A gajiye liƙis ta shiga gida wanda tana zuwa ɗakin umma ta zube Fa'iza sai dariya take mata wadda tazo gidan ta wuni Da ƙyar Farha ta miƙe tayo wanka taci abinci dama sunyi sallar su acan Da gayya ta fita tsakar gida ta leƙa ko wani ɗaki ta shaida musu ta sami aiki Sai dariyar yaƙe suke mata Haka ita dai ta koma ɗaki tana bawa su umma labari.
**********
Sadiƙ bayan ya shirya Ya nufi Ɗakin Ammi har ƙasa ya tsugunna ya gaishe da ita sannan yace mata zai je ya Dubo Mami sai ya wuce lagos dan jirgin sha biyun rana yake son yabi Ammi tayi masa fatan alkairi sukai sallama ya shiga mota drivern gidan ya kaishi asibitin da aka kwantar da Mami.
Da sallama ya shiga Ɗakin da mami take Hajiya Tajira maman mami ta saki fuska sosai tana cewa.
"Wa nake gani a cikin asibitinnan kamar Abubakar sannu da zuwa"
Sadiƙ ya zube har ƙasa yana gaida maman mami kafin ya tashi ya zauna kujerar da take kallon Mami wadda take zaune ta miƙe ƙafa tana shan tea fuskarta fayau duk ta rame.
"Sannu Mami yaya jikin ashe haka Allah ya aiko?"
Sadiƙ ya faɗa cikin jajantawa.
Mami tai ƙasa da kanta tana kallon Ƙarfen gado bata ce komai ba.
"Kiyi haƙuri kada ki sanya tunanin komai aranki In sha Allahu zaki sami wani ingantacce"
Maman mami ta karɓe zancen cikin kwantar da murya.
"Haka ne fa Abubakar nima haka nake ta gaya mata, Amman daga ita har Alin sun ɗaga wa kansu hankali musamman ma shi daya ce ya ƙagu yaga magajin shi"
Sadiƙ ya cije leɓe yana murmushi yasan wannan faɗi ne Ba yadda za'ai Aliyu ya faɗi haka amman sabida kada ya ƙaryata ta yasa yace.
"Dama ai haihuwa ita ce ribar aure Mama muma fatan da muke Allah ya bashi ɗan kanshi"
Daga haka ya miƙe ya zaro 20k daga aljihun sa ya direwa Mami yayi mata fatan Allah ya bata lafiya ya fita yana ƙoƙarin Fita daga ward ɗin su Sajeeda suka shigo hannun su ɗauke da ƙaton Basket na Kayan Break fast ya dube su.
"Ku yanzu dan sakarci kun san zaku zo amman baku bari mun tawo tare ba?"
Dariya sukai a tare suka gaishe dashi sannan yayi musu sallama driver ya nufi airport dashi dan yayi jiran jirgin daze bi bai bari maganar Maman mami ta sami gurbi a zuciyar shiba sabida yasan mata basa rabo da kace nace shiyasa ya kawar da maganar bayan yayi wa ɗan uwan shi zato mai kyau.
Su Safna sun gaisa da Maman mami sannan sukaiwa mami sannu suka dire mata Basket ɗin sabida sauri suke suna da lecture suka bar ɗakin Mami ta bisu da harara tana jan tsaki.
"Wallahi Mama na tsani sadiƙ ɗinnan inna ganshi kamar na shaƙe shi sabida a duniya ba maganar wanda Aliyu yake ji sama data sadiƙ komai nashi ya ɗora shi akai"
Hajiya tajira tace.
"Ina sane ai na yaɓa masa magana kuma nasan ya fahimta kedai sha kurumin ki wallahi ba zamu barsu haka ba dole ma mu raba wannan alaƙar"
Mami ta kuma jan tsaki.
"Suma waɗannan ƴan iskan yaran sai iyayi da girman kan tsiya wancan satin fa wayoyi ya sai musu masu uban tsada sannan yace wai ana fara visar umarar azumi zasu tafi Wallahi mama saura kaɗan na faɗi sabida takaici kuma bara na koma nima sai an tafi dasu Hassana"
Haka suka lalace a wajan suna ƙulla sharrin su kafin Likita tazo taga jikin mami jim kaɗan tazo ta basu sallama da yake da driver nan da nan sukai Gida a maimakon ya wuce da ita gidanta sai Hajiya tajira tace su wuce Fagge inta ƙara jin ƙwari sai ta koma Basu bi takan Aliyu ba Bare a tambayi izininshi.
******
Ranar Farha ta wuni ta kwana cikin farin ciki kuma washe gari babu sanya ta fita wajan aikin ta Alhamdulillahi ta sami wani daga cikin ma'aikatan yana ƙara nuna mata komai Taji daɗin Wajan aikin nata Haka ta cigaba da Fita aikin wanda tuni ta goge har tana ƙoƙarin shiga ɗakin watsa labarai Babban Burin Farha ya cika a sati ɗayan datai a Garkuwa Radio Duk inda ka zaga Muryarta ce raurau ke fita cikin labaran Yammaci wanda duk wanda ya kunna Radiyo ya kamo tashar garkuwa zaici Karo da Muryar Fatimah Ɗandago dan sam batai amfani da Abubakar ɗin ba Dole tasa Salim ya ƙara ɗaga mata ƙafar kawo kuɗin sabida da kanta tace yaje ya bawa kawu haƙuri ta roƙe shi daya bari tai kamar wata guda da fara aikin sai ai maganar auren nasu kuma Salim bai musa ba sabida yana sonta haka yaje wajan kawu da batun wanda kawu yay faɗa amman ya ce daga wannan lokacin baze kuma ƙarawa ba damma daga wajan salim ɗinne aka sami tsaikon.
Cikin rufin asiri farha take aikin ta sabida bama kowa ne yasan ita ce fatima ɗandago ba sabida yawanci da farha aka santa Wani bin haka zataji kawu na sauraron labaranta taita dariya tana jin farin ciki sam bata da matsala a wajan aikin ta kuɗin mota kuwa wannan dubu biyar ɗin umma tace ta aje ta dinga ɗauka tana fita aikin Abu ɗaya ne ta kula a wajan aikin shine Md babu ruwan shi da ingancin labari shidai kawai a kawo masa ya ɗora a kafarshi dan Rediyon shi tai farin jini sam ba ruwan shi sabida Allah ya bashi jarabar son kuɗin tsiya sabida yasan In dai Radion shi tai suna da talla ma kaɗai zai iya biyan ma'aikatan shi.
Tana jin ƴan uwanta ma'aikata na ƙorafi da wannan matsala don zata iya jawo wa gidan rediyon barazana Ita dai da yake Allah bai sa taci karo da wata matsala ba yasa ta saki ranta Shema'u tana sashin labaran wasanni na safe ita kuma tana sashen watsa labarai na yamma wannan tasa sam bama sa haɗuwa da shema'u sabida lokacin da shema'u zata tashi ita kuma lokacin take zuwa Daga gidansu ma bata da lokacin kowa kullum tana ɗaki tana Rubuce rubucenta na labarin da aka bata wanda zata watsa shiyasa wani bin ma sai kaji Ana cigiyarta acikin gidan.
*ABUJA*
*09022260850*
*RABO YA RANTSE...!!*🌹
*NA*
*AUTAR MANYA*
ADABI WRITTER'S ASSOCIATION
*008*
Ya lumshe idanunshi yana shafa kwantacciyar sumar da take saman kanshi kwance yake a katafaran gadon dake cikin hotel ɗin IBETO tunda yazo garin Abuja bai sami zama ba zirga zirga yake akan ƙoƙarin ganin Motocin daya yi order daga kwatano sun shigo kamfanin shi.
Wayar shi dake gefen shi ce take ringing ya lalubo ta da dogon hannunshi mai cike da gargasa ya ɗago idanunshi yana duba screen ɗin wayar AMMI sunan dake ta yawo a saman screen ɗin wayar tashi sai da ya bari ta katse sannan ya kirata.
"Assalamu alaikum Ammi ya kuke?"
Daga Ɓangaran Ammi ta ce masa.
"Lafiya lau, Nace Mami fa tana gidan su ashe da aka bata sallama can suka wuce kai ma Babana mai yasa baka leƙa sanda zaka wuce Abujan ba"
Zazzafar iska ya fesar.
"Ammi kinsan Sadiƙ yazo so mun ɗan jima dashi ne na ƙure lokacina"
Ammi tace.
"To naji yakamata Ka dawo sabida ka samu ka leƙata ta dawo ɗakinta"
Kansa a ƙasa yace.
"Dama gobe Nake son na dawo sabida ƙungiyar matasan gwale da suka gayyacen wasan ƙwallon ƙafar su, Amman shi Bashir zai zauna ne har sai anyi clearing ɗin komai"
Daga ɓangaran Ammi fatan alkairi tare da addu'ar nasara tayi masa Ya lumshe idanun shi bayan sunyi sallama da Ammi wata iskar ya kuma fesarwa.
Ya lalubi Numbern Mami.
Tana zaune a ɗaki tana shan farfesun kan rago taji wayarta tana ringing My One and only sunan data masa saved dashi kenan shike yawo a saman screen ɗin wayarta ta kalli Ƴan biyu ƙannenta suka miƙe suka bar ɗakin Da sallama ta ɗaga wayar Muryarta a narke.
Dakakkiyar muryar shi mai cike da taushi ita ta karaɗe cikin kunnenta.
"Mamy waye ya baki izinin tafiya gida?"
Ya tahume ta.
Inda inda ta soma yi tana kame kame.
"Dama Mama ce tace na biyota sabida jikina ba ƙwari"
Aliyu yaji ranshi ya ɓaci da wannan shashancin da mami tayi.
"To ki koma gida"
Daga haka ya katse wayar shi ya cillata can saman gado ya miƙe ya nufi toilet ruwa ya sakarma kanshi kafin ya ɗauro tawul ya fito gaban dressing Mirrow yana goge Ruwan dake ɗigowa daga jikinshi.
Ya shirya cikin ƙananun Kaya Wando Nevy blue mai santsi sai riga Polo kalar wandon ya feshe jikinshi da haɗaɗɗan turare Ya ɗauki wayar shi ya fita daga ɗakin
Kai tsaye Katafaran kamfanin shi dake kan titin Ibrahim Badamasi Babangida dake garki area 11 ya nufa sukai magana da managern shi sannan ya dawo ɗakin Yau gaba ɗaya jin shi yake wani irin kasala da Buƙata Sun taru sun masa katutu shi namiji ne mai lafiya Ya fahimci yawan takurar da yakewa Mami ne yake sanya cikin dake jikinta samin matsala tun sanda Likita yayi masa bayanin nan yaji hankalin shi ya tashi Sabida shi indai zai ci zai sha tofa ba ze taɓa ganin Matarshi ya kauda idanu ba Babban abin daya ɗaga masa hankali shine yadda Likita ya bashi shawara akan cewa inda hali ya ƙara aure sabida Mami ta dinga samun sassauci daga yawan buƙatarshi Wannan bayani da likita yayi mashi tunda yakai Mami asibiti shike damun shi a tsarin shi Babu neman matan banza dan ba'a haɗa arziƙi da zina sannan kuma shi bai da ra'ayin ƙara aure to wama zai aura Dama Najuwa yaso ita kuma da Ammi taƙi Ya haƙura tuni tai aurenta Mami kuwa zaɓin Ammi ce.
Tsaki yaja lokacin daya miƙe tsaye ya shiga Toilet ya ɗauro alwalar sallar magariba anan ɗakin yayi sallah Ya jima a zaune har akai Kiran sallar isha'i Ya tashi ya gabatar yana idarwa yayi waya a kawo masa Black tea Ba'afi Minti Biyu ba yaji kwonking Ya miƙe ya amso tea ɗin wanda yake ta tururi Ya zauna saman stool yana sha Bayan ya kammala ya cire kayan jikin shi ya kwanta ba jimawa bacci yayi awon gaba dashi.
Da sassafe yayi shirin komawa kano wanda kai tsaye daga airport Gidan mai girma gwamna Driver ya wuce dashi sabida meeting ɗin da aka kirashi na gaggawa akan kawo ƙarshen zaman banza ga matasa wanda gwamnati zata bada tsarin Jari na musamman domin a taimakawa matasan.
*****
Wannan satin aka dawo da Farha tsarin labaran safe kuma cikin Hukuncin Allah an haɗesu da shema'u wanda daga farha har shema'u sunyi murna da wannan abu sai dai yadda Md ya buƙaci su soma fita Kasuwanni da titina dan ɗauko rahoto abin baiwa Farha daɗi ba dan Yau sai ƙafarsu ce ta kawosu sabida Sunje ɗauko Rahoton faɗan daba anan warure wani ɗan daba daya Biyosu da zabira ƙafar kowace ta kaita gida Daran ranar Farha ta kasa bacci tai ta juyin gajiya ga ƙafarta tai tsami.
Umman farha data gama jin labaran ƙarfe Goman dare Wanda Mai bawa Gwamna shawara a Ɓangaran Matasa *Aliyu Audu Madaki* ya sami ganawa da gwamna a yau domin bada jari na musamman ga matasan dan kawo ƙarshen zaman banzan su wanda yace shi kanshi yana buƙatar matasan da suka kammala secondry Guda Hamsin N.c.e zuwa degree guda ɗari gaba ɗaya Ɗari da Hamsin da suzo Kamfanin shi Mai suna *MADAKI MOTORS AND SERVICES* dake kan titin lawan danbazau don a tantance su ya basu aiki a kamfanin don ya tallafa musu wajan rage zaman banza.
Kabbarar Umma ce tasa Farha ta buɗe idanunta da suka ƙanƙance sabida Gajiyar gudu.
"Umma danna mini ƙafata"
Farha ta faɗa tana hamma.
"Ke rabu dani ina jin abin alkairi ya Allah kasa wannan alkairi yazo mana gidannan Su Halifa su sami aikin kamfanin nan tunda har gyaran motoci naji ance ana yi wannan bawan Allah Ubangiji ya biya shi da gidan aljanna"
Farha da bata fahimci Komai ba tace.
"Umma keda wa haka kike ta Kabbara?"
Umma tai murmushi.
"Wallahi farha inda haka za'a sami masu kuɗi masu taimako irin wannan mai bawa gwamna shawara akan matasa da an sami ci gaba sosai naji ance shima matashi ne kuma da kuɗin sa gwamna ya ganshi dan yadda yake taimakon matasa da Kula dasu ne ma ya jawo hankalin gwamna ya haɗa tafiya dashi wanda aka ce da ƙyar ma ya yarda ya karɓi SA ɗin"
Farha bata fahimci komai ba taja Mayafin rufarta bata farka ba sai asubah tana yin sallah tai wanka ta soma shiri Ƙarfe bakwai tabar Gida Har tausayi take bawa umma a sati Biyun datai har ta ƙara ramewa ta koma ƴar firit Kullum takance Umma burina naga Kin daina wahala daga na ɗauki albashi zan baki Ki sai komai na buƙatarki.
Tare da shema'u suka ƙarasa Cikin Gidan rediyon Suna gaisawa da sauran ma'aikata Md ya aiko Kiransu.
Cikin ladabi suka gaishe dashi yana zaune, Yana cike takardu.
Ya dubi Farha.
"Fatima wani labarin Kika ji mai Fusgar hankali acikin wannan satin?"
Farha tai jimm can sai batun Data ji umma nayi jiya ya faɗo mata.
"Yallaɓai Naji Dai Maganar SA na gwamna a ɓangaran matasa wanda zai basu tallafi na Musamman wai ko a kamfanin shi Oho dai"
Md ya ɗaga waya ya kira ɗaya daga cikin Abokan aikin su farha.
Da sauri Taj ya ƙaraso suka gaisa da Md.
"Kaji abin da yake ta Yaɗuwa a gari shine batun bada aiki na kamfanin SA na gwamna a ɓangaran matasa nima naji wannan labari kuma naso daga tashar mu ya soma fita dan hakan zai calling attention ɗin jama'a zuwa tashar mu tunda hakan bai samu ba Taj ina son Mu nemo Wani labarin akan shi wanda zai Jawo hankalin Mutane zuwa tashar mu nidai suna nake so kamar yadda kuka sani"
Office ɗin yayi shuru Farha da shema'u na raba ido Taj yace.
"Gaskiya yallaɓai nidai a sanina Yadda naji ana Faɗin alkairin Madaki zai wuya ka sami wata matsala daga ɓangaranshi kuma idan har ka lalubota ƙarshe abin akanka zai ƙare dan Babban mutum ne a garin nan Kaje Ƙofar na'isa zuwa galadanci zuwa gwangwazo zuwa gudundi Mandawari gidan sarki kaga yadda matasa suke Yinsa kaga taɓa irin waɗannan akwai Bala'i"
Md yayi dariya.
"Nifa taj baka fahimta ni babu wata matsala data taɓa haɗani dashi, Hasalima a pasta kaɗai nake ganin shi kawai yadda yanzu zancen shi ya cika gari nake son na samo Koma meye da sunan shi dan nasan tashata zatai farin jini kaga daga nan zan soma amsar manyan advert a wajan mutane"
Tajjuddeen yayi shuru.
"Eh to yallaɓai yana da Special Issue amman wannan na familyn sane Naji ance bai taɓa haihuwa ba duk cikin da matarshi ta samu zubewa yake"
Jikin Md har rawa yake wajan cewa.
"Serious taj? wajan wa kaji?"
Taj yay murmushi.
"Ah Kasan Babban mutum ne shi to dole wani bin koda yana son Sirri hakan baze yuwu ba dole maganar shi ta dinga fita more especially daya soma siyasa"
Md yace
"Haka jeka taj zan nemaka"
Md ya dubi su farha bayan fitar Taj.
"Yawwa ina son ku juya wannan labarin nashi ya koma cewar Tsafi yake da duk Cikin da matar shi take samu domin yayi kuɗi"
Zufa ce ta soma karyowa daga Jikin farha da Shema'u.............
*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*RABO YA RANTSE...!!*🌹
*NA*
*AUTAR MANYA*
ADABI WRITTER'S ASSOCIATION
*009*
Duk da uban raɓar na'urar A'c data ke kaɗawa a office ɗin, Hakan bai hana Gumi wanke musu Jikin suba.
Shema'u ta kalli Farha wadda take ta faman ƙifta ido kamar zata fasa ihu.
Maganar Md