Showing 132001 words to 135000 words out of 150033 words

Chapter 45 - Rabo Ya Rantse Book One Complete Hausa Novel

Firfita take masa tana kaɗe masa sauro wanda ta hana sauron Hawa Jikin Aliyu sabida Yadda take kaɗewa da Wannan kwalin dake hannunta......... *Masu Application ɗin arewa books se kuje kuyi serching autarmanya ko kuma ku danna blue link ɗin dake  ƙasa, marasa arewa kuma zasu iya siya sena saka su a paid grp ɗina  Paidbook 500 naira in to 0078174806 sterling bank evidance of payment 09022260850*

*A LOVE STORY 99*
Rabo Ya Rantse
Arewabooks autarmanya

Duk da ita ma baccin ne a idanunta ga shi duk ta gaji dan ko ina na jikinta ciwo yake yi mata ga nauyin Aliyu dan ji take kamar cinyoyinta zasu rabe gida biyu amman haka nan ta daure ta cigaba da kore masa sauron tana kuma kaɗa masa iskar kwalin wadda take bada gudunmawar Bashi iska shiko baccin sa yake sosai harda Munshari Jiyo da kanshi yayi daidai saitin cikinta yana Saka hannu ya zagaye ƙugunta ya cigaba dayin baccin sa hankali kwance.
Ta jingina da jikin bangon ɗakin Danshin Jikin bangon na Ratsa saman kanta ga ɗan tashin gansa kuka wanda ya hautsina mata yanayin ta wani irin yawu ke tarar mata ga zuciyarta na tashi Tuni yawun ya cika bakinta Numfashinta yana fita sama sama hawaye ke zubo mata Ta ƙudura azuciyarta ba zata yafe wa Ammi ba kuma ba zata taɓa ganin farin Ammi ba sabida ita ce tikitin jefasu acikin wannan hali mai tayi wa Ammi Tunda take bata taɓa ganin Mutumin daya tsaneta ƙiriƙiri kamar Ammi ba ko sunan Ammi a wannan Lokaci Farha bata ƙaunar taji Tun tana hawaye har Kukan nata ya tsananta amman da yake Aliyu baccin nashi mai nauyi ne sam bai Jita ba baƙar Leda ta ɗauko ta zuba Miyan bakinta sabida Tana gudun idan ta zame shi ta fita zubarwa ze farka Ta Buɗe Ƙofar ɗakin ta jefa Ledar ta rufo Ƙofar A hankali ta komar da kanta ta cigaba da kukan da take yi.

Wani bacci ne mai daɗi ya sureta amman duk da haka kwalin yana hannunta a haka aka kira sallar asubahi Duk da Baccin sa mai nauyi ne amman ana kiran sallah ya Juya Yaji ƙafafunsa a ƙasa ga uban sauron daya cika masa ƙafa se Cizon Shi yake Juyawar da zeyi Cinnaka ya gantsara mai cizo a ƙafar shi.
Tsananin mamaki ne ya kama Aliyu Sanda ya ɗaga kanshi yaji shi a jikin farha a saman cinyarta ya zuba mata ido wato a haka suka kwana ya kalli hannunta kwali ne take masa Firfita dashi wani tausayin ta da sonta ne ya ƙara kamashi wanda Ko zafin cizon Cinnakan ma bai sami tasiri a jikinsa ba ya tashi ya janyota Jikinsa wani irin tarin Cincirindon sauraye ne a saman kanta har wajan Fuskarta tsoro da tashin hankaline ya kama shi sabida yasan matsalar sauro ga mace mai Juna biyu ya kwantar da ita saman tabarmar ya saka zaninta ya rufe mata har fuskarta sannan ya Miƙe ya fita daga ɗakin alwala yayi gidan Shuru shidai da sauri ya buɗe Ƙofar ya fita Wani masallaci ya hango daga can ƙasan layin ya ƙarasa seda yayi raka'atul fijir kafin a tayar da sallar sannan yayi zaman Jiran a tada sallah bayan sun idar da sallar zama yayi Yana lazumi har wajan shiddan safe yayi addu'oi sosai sannan ya fito daga masallacin dan Shine ma ya rufe masallacin ya tawo Gidan Abin mamaki Lokacin daya shiga Gidan A lokacin yaga ɗan hayar Gidan yana jan ruwa zeyi alwala Babu wani sakin Fuska Aliyu ya masa sannu! sannan ya shiga ɗaki Ba kuma komai yasa haka ba shine yadda Aliyu keda taka tsantsan Baka shigewa jikin mutum tashi ɗaya har se kasan waye shi.

Tana zaune ta idar da sallah ya kama haɓa cikin mamaki.
"Yaushe kika tashi fatima?"
Ya faɗa yana ƙoƙarin zama a kusa da ita.
"Ina kwana"
Yaji muryarta.
"Lafiya lau yaya kwanan baƙon waje?"
Tace masa "Alhamdulillahi"
Yayi Murmushi.
"Amman mai yasa kika kasa bacci jiya kikai ta min Firfita bayan ke ma kin gaji?"
Ta ɗanyi Murmushin yaƙe dan ba ƙaramin ciwo Jikinta yake mata ba amman tasan ta gaya masa hankalin shine ze tashi.
"Nina saba da wannan rayuwar kaikuma baka saba ita ba"
Yaɗan dube ta da rashin fahimtar zancen nata.
"Kimin yadda zan gane"
"Nina na taso gidan talakawa mana na saba kwana cikin sauro da zafi kaikuma ka taso kana da Kuɗi ka saba kwanan Ac da Fanka kaga inna barka a haka zaka cutu duk da nasan yanzun ma dauriya kake"

Ya ɗan kalleta cikin wani yanayi.
"Fatima ki faɗi gaskiya nasan dai duk rashin gidanku ba zaki taɓa kwana a irin wannan ɗakin ba Ko talauci ma da rashi ai mataki mataki ne Wani yafi wani kamar yadda Kuɗin ma yake mataki mataki wani yafi wani"

"Haka ne kam dama ita duniya makaranta ce in kana ganin babunka to baka dubi wani bane kai se kaga kana cikin aljanna Nima dai nasan Mu talakawa ne amman wallahi ɗakunan su Umma babu gansa Kuka Kuma akwai ledar tsakar ɗaki"
Shi dariya ma ta bashi Wato yaro yaro ne.

"Shiyasa aka ce in kana kallon na ƙasa dakai Kullum zakai ta yiwa Allah Godiya Kinga wannan Kwana ɗayan danai anan gidan na ƙara Godewa Allah Kuma na ƙara Jinjina ni'imar daya mani sannan na ƙara Jin tsoron shi Koda yaushe Kana samun Kuɗi kana cin mai kyau ka sha mai kyau ka tashi a mai kyau ashe wani ma wajan baccin ya gagare shi yanzu dai duba saman ɗakin nan In damuna ce ba zamu Iya bacci ba barina gida wata makaranta ce Allah ya kawo ni"
Ya faɗa yana Jingina da Bangon ɗakin hannu yasa yana cire mata Hijabin tare da cewa.
"To yanzu me zaki Break dashi?"
Ya faɗa sanda ya cire mata Hijabin gaba ɗaya ya tsira mata ido yanayin Kallon yana saukar mata da kasala.
Ta lumshe ido.
"Ko mu kwanta?"
Ya faɗa Muryar shi har sarƙewa take ta gano Nufin shi.
"A,a"
"To me zaki ci na siyo miki?"
"Kai kana da tabbacin tsabtar wanda zaka siyo min a wajan sa nifa Allah ya bani tsirfa wallahi bana son abincin waje"
Yayi Murmushi.
"To Gimbiya duk yadda kika ce"
Ya faɗa yana zira hannunshi a saman rigarta.
Ta Buge hannunshi.
"Dan Allah ni ka rabu dani ba zan iya komai ba yanzu duk Jikina danƙo"
Ya Tashi tsaye.
"To bari na fita yanzu zan dawo"
"Ina ka sani da zaka fita?"
Yayi murmushi tare da cewa.
"To se nai ta zama ma tambayi ai baya ɓata"
Se ta miƙe tana saka hijabinta.
"Nidai Muje tare wallahi bazan je a sace kaba kai baka san ko ina ba gwara ma kome ye ya same mu tare"
Dariya ta bashi.
"Dan Allah Ki koma babu wani abu daze same ni haba kada ki mayar dani mace fa se kace wani ɗan ƙauye"
Ta ɓata rai.
"Zaka fita amman ka bari anjima sabida kaga yanzu safiya ce Koni ce fara ai na haƙura da cin abincin har anjima"
"Inna zauna me zaki bani nifa wallahi a matiƙar Buƙatarki nake to na nuna Buƙatata kince a,a to zaman me zanyi"
Ta kalle shi.
"Kai yanzu har ka sami Nutsuwar buƙatata?"
Yayi mata wani kallon ƙasan idanu.
"Ƙarshen Nutsuwa ma tunda ina tare dake Ko a titi Muka kwana zan sami Nutsuwa bare Muna gida a ɗaki to meye saura?"
Ta koma ta zauna Shima zaman yayi amman ya cire rigar Jikinsa shima zafin na damun sa sosai Gaba ɗaya Kirjinsa Kwantaccen Gashine har ya zagaye Nippy ɗinshi ta kawar dakai sabida bata taɓa ganin shi kamar a wannan yanayin ba.
Ya matso wajan ta ya shiga cire mata hijabin.
"Ki dena min haka babu abun da zan Miki Please"
Ya faɗa yana Cire mata hijabin da rigar Jikinta wadda tun ta lace ɗin data sako ne a gidan salama kai tashin hankali beyi ba sam.
Ta kare Ƙirjinta da hannayenta "Dan Allah ka rabu dani"
Ya janyota ya matseta a ƙirjinsa har Zuciyoyinsu suna Jin bugun junan su.
"Ba abin da zan Miki amman ki barni naji ɗumin Jikin ki" ya faɗa yana sakar mata Hucin Numfashin sa Luff tayi ajikinsa ƙamshin dake manne a fatar shi yana ziyartar hancin ta.

"Jikana baka tashi bane?"
Suka ji Bugun ƙofar Inno tana Kiran Jikanta.
A wahalce ya saki farha yana saka rigar shi Muryar shi wadda ta shaƙe ya ɗan ɗaga.
"Mun tashi Baba Bari na fito"
"To fito ga koko na siyo Muku da Ƙosai maza ku karya Dan gudun wannan shu"umar Cutar kwalsa take ko me"
Farha me zatai In ba dariya ba Kuma dariyar harda Biyu na farko Ulcer inno zata ce na biyu kuma yadda ta hango Ba ze raga mata ba Inno tazo ta katse masa hanzari wannan abu yayi mata Onga rigarta ta mayar tana dariya shikuma ya fita waje.

Suka gaisa da Inno tana miƙo masa kwanan kokon da Ƙosan.
"Ban ji daɗi ba kada ki kuma siyo mana abin karyawa dan Allah"
Ya faɗa.
"To ka amshi wannan dai na riga na amso muku"
Ya amsa yana Godiya Girma da tausayin Tsohuwar yana ninkuwa a zuciyar shi.
"Amman jikana kai ƙwara ne ko naga jan naka kamar na ƙosai"
Duk yadda yaso kamewa seda ya dara.
Yayi ƙasa da Murya.
"Keda kika ce Ni ɗan yayanki ne so kike asirinki ya tonu ko me?"
Seta kama baki tana dukan bakin ta.
"Shegen baki Ungozomar bata gasa shi sosai ba, to ai abunne jikana ban taɓa ganin mutum mai kyan kaba anya bakai jiɓi da waɗanda muke gani a talabijin ba kuwa?"
"Inno maganin ciwon kai To bari na fita inna dawo zan baki amsa"
Ya faɗa yana Komawa ɗakin sabida bai saba yawan magana ba Aliyu irin Mutanan nan ne marasa magana haka halittar shi take Ko magana aka cika yi fita yake sabida ciwon kai yana shiga farha tasa dariya.

"Jan ƙosai"
Ta faɗa tana dariya tare da amsar Kwanon ƙosan haɗiyar yawu tayi.
"Kai wannan ƙosai yaji albasa"
Ya kalleta.
"Zaki ci kenan?"
"Harda gudu ma"
Hmmmm
"Keda kika ce bakya cin abincin siyarwa kuma yaya zaki ci wannan Ki bari na fita nazo da abin da zaki ci"

Tai saurin Buɗe kwananon ta ɗauki Ƙosan ɗaya takai bakinta.
"Ko a masai ake tsoma wannan dai se naci"
Shagala tayi da cin ƙosan da shan Kokon wanda ya zame yabar mata ɗakin Fita yayi Cikin Ikon Allah bai sami duhun kai wajan shiga cikin garin sosai ba.

Farha ta duba taga baya wajan wato wayo yayi mata "Allah ya kiyaye hanya" ta faɗa tana cin ƙosan wanda yayi mata daɗi bayan ta kammala ta fita har ɗakin Inno wadda take zaune tana jin Radio.
"A,a jikata Kin fito kenan?"
Farha ta zauna.
"Ina kwana Dafatan kin tashi lafiya yaya hidima damu Allah ya saka da alkairi dama kwanukan na kawo Miki"
Inno ta washe bakinta mai giɓi.
"Kai babu komai ai komai yiwa kai ne Jikata ke Kuma baƙa Ƙirin Ma sha Allah kalar hausawa"
Farha me zatai in ba dariya ba.
"Haba inno Nima ai Jar ce kamar Ƙosai"
Dariya sukai daga ita har Inno tashi ɗaya Jinin farha dana Inno yayi Mugun haɗuwa.
"Inno bari na gyara Miki ɗakinnan naki naga ko ina tarkace dama haka ɗakin Tsofi yake ina abun shara?"
Inno ta washe baki tana cewa.
"To jikine duk babu ƙarfi ga shi bani da mataimaki se Allah haka dai nake karkaɗe makwancin nawa na kwanta kafin Mutuwa tazo Shiyasa haihuwa tayi a rayuwa inda ina da ɗan kaina ai da ban zauna ɗakina babu shara ba"
Tausayin Inno ya kama farha.
Tsintsiya farha ta ɗauka ta shiga sharar ɗakin ta gama ta ninke mata kayanta masu dauɗar ta fitar dasu waje haɗe da kwanukan wanke wanke Har tsakar Gidan farha ta share sannan ta shiga ɗakin su nan ma sharewa tayi ta haɗe Musu kayan su Gefe Guda.
Soson Buhu da ruwa ta ɗauka ta shiga ɗakin dashi ta dinga wanko gansa Kukar data cika ɗakin ta gama ta Wanke tsakar ɗakin ta Koro ruwan tsakar gida ta haɗa ta wanke tas Sannan ta amso omo wajan Inno ta mata wanke wanke

Wankin Inno ta soma yi a bakin Rijiya Inno kuma tana zaune a bakin Ƙofa duk daɗi ya isheta se Hirar su suke.

Shafa ce ta fito da yarinyar ta a hannu tana ganin farha ta saki Fuska tana ce mata.
"A,a ina kwana yaya kwanan baƙunta kuma......?  *Masu Application ɗin arewa books se kuje kuyi serching autarmanya ko kuma ku danna blue link ɗin dake  ƙasa, marasa arewa kuma zasu iya siya sena saka su a paid grp ɗina  Paidbook 500 naira in to 0078174806 sterling bank evidance of payment 09022260850*
*A LOVE STORY 100*
Cikin sakin fuska farha tace wa shafa.
"Alhamdulillahi nagode"
Ta cigaba dayin wankin ta shafa ta zauna a kusa da inno suna Cigaba da hirar su Lokacin Mijin shafa ya fito kallo ɗaya farha tayi masa bata Ko gaishe dashi ba ta sunkuyar da kanta tana cigaba dayin wankin ta.

"Inno waɗan nan ne ƴaƴan naki?"
Cewar Mijin shafa Inno tace

"Ita ce surukar mu ɗan nawa ya fita"
Cikin haka Aliyu yayi sallama a gidan yara ne Guda Biyu ke biye da bayan shi da kaya niƙi Niƙi sukai ta shigo wa dasu har Suka gama ya sallame su shikuma ya dinga shigar da kayan ɗakin su Inno se sannu take masa shafa da Mijinta Kuma suka koma ɗaki dan gaba ɗaya Mijin shafa jiyay Aliyu na bashi tsoro yana shakkar sa ga wani kwarjini daya yi masa.

"Ki aje wankin haka kije wajan Mijin ki babu daɗi ya dawo Kina zaune naga Ko sannu da zuwa baki masa ba"

Farha tayi dariya tare da cewa.
"Rabu dashi Inno gwara na tashi gaba ɗaya Inna je ba lallai ya bari na fito ba Kinga da kaya ya shigo"
Inno tayi dariya tana cewa.

"Haka ne kuma Allah dai ya saka Miki da aljanna" farha ta cigaba da wankin wanda har akai sallar azahar tana yi Lokacin ya fito daga ɗakin ya tafi masallaci tana yi masa adawo lafiya yayi mata banza Gabanta ya faɗi ko ba'a faɗi ba tasan laifi tayi masa shiyasa yayi mata shuru a sanyaye ta ƙarasa wankin ta shanya Lokacin shafa ta Fito zata Ɗora Girkin rana.

"Dan Allah In kin sauke zan ɗorawa Mijina ruwan wanka"
Inji farha tana kallon shafa wadda take haɗa gawayi a kurfoti.
"Lah zo ki ɗora in kin sauke sena ɗora girkin ai ba yunwa muke jiba"
Cewar shafa farha ta cika da mamakin shafa Mace mai Kirki mai rawar Jikin son taga ta kyautatawa wanda ke tare da ita.

"Bara na ara Miki tukunyata naga kamar baku zo da kayan aiki ba"
Shafa ta ɗauko ƙatuwar Tukunya lokacin wutar ta haɗu gawayin yayi rushi sosai Shafar ce ta cika Tukunyar da ruwa har baki ta ɗora farha nata Godiya.
"Wallahi babu Komai ai zaman tare ya wuce wasa"
Mijin shafa ne ya kirata Sabida haka farha seta Koma tayi alwala ta Miƙawa Inno sauran sabulun wankin ta Nufi ɗakin su.

Mamaki tayi sabida ya shinfiɗa sabuwar Ledar tsakar ɗaki wadda ta haska ɗakin sosai ga kuma katifa madaidaiciya wadda zata ɗauke su Harda sabon zanin gado daman kayan data ga yaran na shigo dasu Gidan yawan su ya bata mamaki Gefe ɗaya ya aje babban Buhun shinkafa da galan Ɗin mai da ƙaramin gas da Katan ɗin indomie se tukunya Guda Biyu da Plate da Spoon da dai sauran kayan Kitchen ɗaiɗaiku se ƙaton bawon wanki da Bokitin wanka da Buta babba da ƙarama da Net wanda ya kafa a saman katifar tasu Ɗakin se ƙamshin turaren room frashner yake kayan su ma ya jere su sunyi kyau duk da bai fito dasu waje ba.

Dardumar data ga ni a Can Lokon ɗakin a shinfiɗe ta ɗauko ta shinfiɗa ta tayar da sallah bayan ta idar ta zauna tana addu'a Lokacin ya shigo ɗakin sallama ciki ciki kamar ammasa Dole yayi.

Ya sami gefen katifa ya zauna ya wani rafka tagumi kamar mara lafiya.
"Sannu da zuwa bari na ɗora maka abinci amman kafin nan bari na wanke maka banɗaki se kayi wanka"
Ta faɗa tana kallon sabuwar tsintsiyar daya jere a bayan Ƙofa da sabon abin zuba shara da abin kwashe sharar Duka a bayan Ƙofa.

Yayi mata shuru.
"Yallaɓai magana nake Inna maka laifi kayi haƙuri nidai"

Ta faɗa tana ɗaukar Bokitin ta fita da tsintsiyar ƙaton Omo daya siyo ta farke ta tsiyaya ta zuba Ruwa ta wanke masa bayin tas ta Juyo masa ruwan wankan ta sirka masa takai masa bayin.
"Na gama ko zaki ɗora Abincin"
Ta leƙa ɗakin shafa amman bata shiga ba shafa tace "To gani nan"
Ta shiga ɗakin har Lokacin yana zaune.
Ta ɗauko sabon kwandon wankan daya zo dashi ta koma takai masa Bayin.
Ta kuma dawowa.
"Na gama Kaje kayi wankan"
Ya tashi a saɓule ya fita ya shiga banɗakin Kafin ya fito harta Fito masa da kayan daze saka Ta ɗauki gas Ɗin ta fitar dashi bakin Ƙofa Ta ɗauko Tukunya ƴar ƙarama ta zuba ruwa ta ɗora masa Indomie.
Tana zaune a bakin Ƙofar ya fito daga wankan Ya shiga ɗaki Lokacin data gama dahuwar ta juye masa a plate sannan ta Ɗora masa Baƙin shayi.

Ta kammala Komai ta Shigar da gas ɗin bakin ƙofa sannan ta shiga wanka ta fito ɗaure da zani da Hijabi yana zaune Amman ya shirya ya sauya kaya.
Ta shafa mai sama sama ta sanya Doguwar riga marar nauyi Bata saka ɗankwali da Hijabi ba ta zauna a gaban sa ta Janyo plate Ɗin

"Ga abincin nasan baka karya ba amman ka fara shan baƙin shayin"

"Kin zuba wa Mutanan Gidan?"
Ya tambayeta.
Kunyace ta kamata.
"Ni ban zuba Musu ba"
Ya ɗan zaro mata ido.
"Amman ke kika ari tukunyar su Kika ɗora ruwan wanka bazakiji Kunyar Ki girki ki hanasu ba To Ki ɗora musu wani Musamman Tsohuwar nan Koki ɗiba Musu Ɗanye ki basu"

Ta zumɓuro mai baki.
"Kai fa ka saba kyauta Amman ka tuna yanzu rayuwar ta canza dole mu tattala inya ƙare waze bamu?"

Yayi Murmushi.
"Allah ne ze bamu kamar yadda ya bamu wannan sannan ka bayar baya hana ka ƙi samu sema Allah ya buɗa maka ni gaskiya ban saba rayuwar baƙin hali ba shiyasa naji hakan wani Iri"
Aiko seya ƙular da farha nan da nan tahau fushi.
"Nike nan nina saba da rayuwar baƙin hali kake Nufi Kome?"
Dariya yayi tare da ɗaukar tea spoon yana Juya tea ɗin yana kurɓa

Har ya gama sha ƙunci take Ya ja plate yana cin Indomie.

"Lahhha dama haka kika iya Girki ma sha Allah Alhamdulillahi nayi farin ciki"
Ya faɗa yana cin Indomie ɗin hannu baka hannu ƙwarya kaɗan ya rage ya na Hamdala ga Allah gefe farha taja dan ita bata ma bata sha'awa ba Indomie ɗin.
"Ke me zaki ci yanzu sannan Kuma Nidai Ki dena wankin da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login