Showing 30001 words to 33000 words out of 150033 words

Chapter 11 - Rabo Ya Rantse Book One Complete Hausa Novel

baccinta take sosai da alamun Kuma baccin yana mata daɗi dan da alama ko sallah bata yi ba.
Toilet ya buɗe ya taro ruwa a hannunshi yana zuwa daidai fuskarta ya yayyafa mata ruwan Firgit ta Miƙe tana sosa fuskar tata da alama Sanyin ruwan ya ratsa mata Jikinta.
Ya koma jikin Ƙofa yayi folding hannunshi fuskarshi a ɗaure ya dube ta.
"Why are you sleeping like this until it is time for prayer?"
Da sauri ta kalli saitin window, ah lallai yace baccin me take haka har lokacin sallah ya wuceta, Sai dai ta ɗan tsorata sanda taga inda take a kwance ita dai tasan a saman ɗan kwalinta ta kwanta to waye ya hawo da ita saman gado.
Ta juyo ta kalle shi ganin yadda ya ɗaure fuska Ya haɗe girar sama data ƙasa ya sanya tai maza ta sauko daga saman gadon shaf ta manta babu hijabi ajikinta ta wuce shi ta shige toilet alwala ta ɗauro harta fito yana nan tsaye aranta tace ko soja ya rufa maka baya kai dai baka gajiya da tsaiwa kamar yasan abin da take faɗi kenan azuciyarta sai jin muryarshi tayi yana cewa.
"Why are you looking at me or you are not praying?"
Ɗankwalin ta shinfiɗa a ƙasa ta tayar da sallah har ta idar yana tsaye ta jima tana addu'a kafin ta shafa ta juyo Ta kalle shi Tai ƙasa da kanta cikin rawar murya tace masa.
"Ina kwana"
Bai amsa ba ya cigaba da magana.
"Ina wayar da na baki ki saita alarm amman No Need ki dinga Missing jam'i bayan akwai masallaci acikin gidannan,Take care that I don't catch you again and don't pray early"
Ya faɗa mata hakan lokacin da yake ƙoƙarin Buɗe ƙofar ya fita.
"Amman dan Allah in ka fita ka sa azo ayi sauka a ɗakinnan"
Cikin mamaki ya juyo ya dube ta.
"Sauka kamar yaya I don't understand you"
Hawaye ta matso da yawa muryarta na rawa.
"Nidai na san a ƙasan ɗankwali na nayi sallah na kwanta amman dana tashi na ganni a gado"
Ta faɗa tana sakin kuka mai ƙarfi.
Dariya ta bashi amman bai yi yadda zata ga dariyar tashi ba.
"Toke mai yasa kika yi salla a ƙasan bayan akwai carpet a ɗakin?"
Shuru tayi masa tana cigaba da kukan ta da gaske dai tsoron ɗakin takeji.
"Shikenan dama nine na gayama aljanun ɗakin su dinga hawar dake saman gado in kinyi bacci har bakin masifa ma zasu dinga Yankewa"

Da sauri ta miƙe ta biyo shi tazo gab dashi kamar zata Rungume shi hawaye take.
"Dan Allah kayi hakuri ba zan kuma maka magana ba daga yau"
Duk yadda yake Ƙunshe dariyar sai da ta fito Ya ɗan yi dariyar kaɗan wadda ta ƙara haska zatin kyan shi.
"Tom naji jeki ki gyara kayanki ki jera su kije ki break ba zasu kuma ba"
Daga haka ya fita daga ɗakin Bakin gado ta koma ta zauna tsintar kanta tayi tana murmushi sabida yadda yayi mata magana yanzu cikin sigar son ya kwantar mata da hankali.


Lumshe ido tayi tunanin Ummanta da Missing ɗin ƴan gidansu ya kamata.
*WACECE FARHA* ?
*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*RABO YA RANTSE*

*20*


*A LOVE STORY 20*
Malam Abubar ɗan asalin ƙaramar Hukumar gwale dake kano ɗan cikin unguwar Mandawari mazaunin unguwar Ɗandago, Ɗa Na uku a wajan mahaifin shi Malam Abubakar tun asali sana'ar sai da Bilo yake da ita ya tara kuɗi yayi aure inda yake zaune da matar shi guda ɗaya indo Wanda yadda Allah ya hore masa a sana'ar tashi ta siyar da Bilo idan ya yi Sai ya ƙara aure ya auro Hafsatu dukkan su matan nashi Jera haihuwa suke Farko indo ta haifi Adama Sai Hafsatu ta haifi Samira haka suke ta haihuwar su kufi a kufi har sai da suka haifi ƴaƴa biyar biyar duka mata Ganin haka yasa Hankalin Abubakar ya tashi sabida yana masifar son ya haifi ɗa namiji Sai ya fara neman aure a nan cikin Ƙoƙi ya haɗu da Asiya yaje wajan Abokin shi Asiya itace ƙarama a gidansu yayinta duka matane iyayen su sun rasu tun suna ƙananu Riƙonta sai ya koma hannun yayarta.
Abubakar bai ƙasa a gwiwa ba wajan Neman auren asiya wadda a lokacin ba wata babba bace sabida tana da ƙaramin Jiki sosai Yayin ta da farko sunce ba zata su turata tai kishi da mata har Biyu ba sabida yarinya ce amman yadda Abubakar ya dage Haka suka bashi Asiya ya aura ya kawota gidan shi wanda Hafsa da Indo suka haɗe wa Asiya kai suda ƴaƴan su Faɗin irin Wahalar data sha agidan ba ɓata baki ne dan hatta wankin su dana ƴaƴan su ita take Musu a wannan Lokaci haka zalika Ranar girkinsu ita ke Musu girkin a wajan Mijinta kaɗai take samun sassauci dama kuma sai baya nan suke gana mata azabar.
Cikin haka mahaifin Abubakar ya rasu Dama mahaifiyar shi tuni ta jima da mutuwa ranar sadakar bakwai haka matan gidan sukai tafiyarsu Umman zage Babbar yayarsu Asiya tazo gidan kamar an jefo ta taga Asiya gurfane a gaban ƙatuwar tukunya tana faman hura wuta.

"Sallamau alaikum"

Umman zage tayi sallama.

Asiya ta ɗago ido fal hawaye da majinar hayaƙi.

"Umman zage ce agidan namu sannu da zuwa"

Asiya ta faɗa tana Goge fuskarta.

Ta miƙe tsaye ta shiga ɗaki ta ɗauko tabarma ta shinfiɗa wa Umman zage wadda ta tsaya ta zubawa ƴar uwarta ido cike da tausayawa.

"Umman zage ki zauna bara na kawo Miki ruwa"

Cewar Asiya tana nufar randa ta ɗebowa Umman zage ruwa mai sanyi ta kawo mata gabanta ta ajiye mata.

Umman zage bata ɗauki ruwan tasha ba ta dubi Asiya.

"Auta kinga yadda kika koma kuwa? gaba ɗaya kinyi baƙi kin sake ramewa anya kina jin daɗi acikin gidannan kuwa?"

Asiya ta ƙaƙalo Murmushin dole.

"Umman zage, Lafiya ƙalau kawai Baƙuntar zaman waje ɗaya ne"

Ta faɗa tana ɓoye damuwarta, dan kada ta ɗagawa ƴar uwarta hankali.

"Auta idan kin Ɓoye min damuwarki wa zaki gayawa Mahaifan mu sun Mutu sun bar Min ku har ku Huɗu nice babba acikin ku, Dan haka kada kiji shakkar gayan matsalar Ki Kinji Auta Ba zamu bari ki zauna cikin matsala ba"

Asiyah sai ta fashe da kuka.

"Wallahi Umman zage tun da nazo gidannan nike wa matan gidannan Komai hatta Wankin kashin ƴaƴansu, Yanzu ma sun tafi gidan gaisuwa Basu tafi dani ba sun bar Min girkin su kuma idan yazo faɗa zemin yace banje ba Kinsan shi mafaɗaci ne a wajan sa kaɗai nake samun sassauci"

Tunda ta soma magana Umman zage ta zuba mata Ido ita takaicin Asiya ma shiya fi Komai Ɓata mata ranta.

"Shi Mijin naku ya sani?"

Da sauri ta girgiza mata kanta Alamun bai sani ba.

Umman zage ta Ɗaga waya ta kira Abubakar bayan sun gaisa.

"Abubakar yaya ƙarin haƙuri?"

Daga nasa ɓangaren yace.

"Alhamdulillahi Babbar Yaya ya yaran namu?"

Umman zage tace lafiya lau.

"Dama ina gidan kane in kana kusa kazo in kuma Baka kusa nasan an maka rasuwa to zan rufo maka gidanka na tafi da Asiya Gidana in ka dawo ka biyo zamu yi magana"

Asiya ta zubawa Umman zage ido tana kallon ta dama tasan za'ai haka shiyasa tsayin watannin datai agidan tana fuskantar matsalaloli bata taɓa kai wa Umman zage Kukan taba sabida tasan halin ta macece wadda ba'a taka mata nata tana da zafi sosai.
Haka zalika sauran Yayin nata suke su Umman ɗorayi suma duk zafi gare su Ita kaɗai ce mai sanyi tana da haƙuri sosai.

Abubakar ya gigice.
"Lafiya Babbar Yaya? Ganinan base kun kai ga tafiya ba"
Daga haka Umman zage ta kashe wayar bala'i ta shiga surfawa ta inda ta shiga ba tanan take fita ba.

"Tirr da wannan sanyi naki ni akwai kishiyar data isa ta juyani wallahi ba'a haifeta ba baki gado muba kina kallona dai sai dana riƙeku har ku huɗu na aurar daku ai ina da kishiyoyin wa kika gani acikinsu tana muku daidai da kallon banza to zama samun guri tafiya rage tsaiwa"

Ita dai Asiya hankalinta duk a tashe yake na wayar da Umman zage tayi wa Abubakar sabida Tasan In Umma ta tafi ƙarshen abin akan ta zai ƙare, Jimawa kaɗan Yayi sallama ya shigo ya janyo kujera ya zauna Yana gaishe da umman zage.

"Babbar yaya ina yini?"

Ta dube shi

"Lafiya ƙalau, yaya daɗin haƙuri?"

Yace.

"Lafiya lau, Ya kuka je gida? angode Allah ya bada lada"

Umman zage tace.

"Amin"
A taƙaice.

"Dama nazo ne domin na kuma yi maka gaisuwa sai na tarar da Asiya ita kaɗai kaga waccan ƙatuwar tukunyar da take akan Murhu matan ka sun bar mata tai musu Girki fisabilillahi ina asiya ina waccan Tukunyar salon Ƙirjinta ya buɗe"

Abubakar ya haɗe rai a take anan

"To ƙararsu ta kawo Miki kenan? to ai girki ita ya kama tunda su ne masu ƴaƴa dole zasu je Wajan gaisuwa ita kuma tai musu abinci"

Ya faɗa yana hararar Asiyah wadda ta Sunkuyar da kanta a ƙasa.

"Duk ba wannan ba Asiya ta sanar dani irin zaman da take agidannan zamane na bawa da uban gidan shi ita ke wa matan ka wanki hatta girki ita ke Musu to Asiya dai zama dakai bai zame mata dole ba idan Babu hali ka sakar min abata na tafi da ita yanzu base anjima ba"...............


*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*RABO YA RANTSE*

*21*


*A LOVE STORY 21*
Jikin Abubakar ya ɗauki rawa cikin sauri ya dubi umman zage wadda harta Miƙe tsaye yace mata.

"Dan Allah dan Annabi kiyi haƙuri, Babbar yaya kin san ba zan taɓa cutar da Asiya ba"

Da sauri ta katse shi da cewa....

"Cuta ta nawa kuma Abubakar aini ka shani na warke yanzu fa agabana ka rufe ido kana cewa, Girki ita ya kama tunda ita ce marar ƴaƴa to kaga kenan kana goyon bayan Matanka ne"

Shima da sauri ya tashi kamar zai durƙusa mata.

"Wallahi Babbar yaya ba haka bane"

Ta ɗaga masa hannu.

"Haka ne mana Abubakar, Alhamdulillahi tunda kai da bakinka kace bata haihu ba kaga zatai daɗin samun wani Mijin da zarar ka sake ta"

Ya haɗe girar sama data ƙasa.

Muryarshi a kausashe ya dube ta.

"Nidai a mini afuwa idan hakan ta sake faruwa ki ɗauki dukkan hukuncin da kika ga dama, Asiya tana sona ina son Asiya, Na rantse da Allah akaf matana ita nafi so kuma itama ta sani rabani da asiyah kamar Yimin Illah ne"

Ya faɗa kamar zai kuka!

"Naji to amman da sake, Daga yanzu ka dinga saka idanu akan al'amuran gidanka idan ba haka ba gaskiya zaka zo watarana ka tarar na Ɗauke Asiyah dan ba bora bace"

Da sauri yace.

"Naji babbar yaya kuma na Amince, In sha Allah! Hakan kuma ba zata kuma faruwa ba Indai nine mai gidan zan tsawatar"

Daga haka Umman zage ta dubi Asiya wadda har Lokacin taƙi ɗagowa.

"To sakarai saiwa sala, Saura ki zauna tsoro suda ƴaƴansu su cigaba dayi miki izaya Wallahi na kuma zuwa na tarar dake A wannan yanayin tafiya zanyi dake ba soba nina ga laila majunun"

Har ƙofar Gida Asiya ta raka Umman zage Tana kuma jaddada mata akan ta Miƙe tsaye tana karɓar ƴancinta agidan Haka ta dawo Abubakar ya tare ta yana huci kamar zai kawo mata duka.

"Ke ashe baki da hankali da tunani ke sakarar ina ce, Waya gaya miki ana fallasa sirrin aure Kuma ni kin taɓa gaya min halin da kike ciki agidannan?'

Ya faɗa kamar zai mareta.

Jikin Asiyah yana rawa tace.

"A,a ban gaya maka Allah ya baka haƙuri"

Ya ƙara matsowa yana tattare hannun riga da gudu tayi ɗakinta ta rufo ƙofa Ya ƙaraso bakin Ƙofar yana cewa


"To na rantse da Allah kika kuma gayawa wani sirrin gidana sai ranki ya ɓaci marar hankali wadda bata san ciwon kanta ba"

Haka ya ƙaraci bambamin sa da cin mutuncin sa yabar Gidan Yana fita ta fito tana duba tukunyar shinkafar data ɗora Ƙauri ne ya cika hancinta shinkafar tayi Baƙi ta ƙone ƙurmus gashi babu wata dama Girkin Indo ne kuma mai girki ce take riƙe makullin ɗakin adana kayan abincin gidan.

"Wayyo Allah! yau na shiga uku a wajan matan gidannan umman zage dama baki zo ba"

Ta faɗa a fili tana fashewa da wani irin Kuka! har akai la'asar tana kuka gajiya tayi da kukan ta nufi banɗaki ta ɗauro alwala itama yunwar take ji amman tunanin tashin hankalin matan gidan har yafi mata yawa akan yunwar cikinta.

Haka ta wanzu acikin ɗaki har akai magariba tayi sallah ga gidan shuru ba kowa ga ba wuta duk tsoro ya cikata can wajan bayan sallar isha'i suka shigo da koke koken Ƴaƴansu gaban Asiya ya yanke ya faɗi ta kuma shigewa ƙuryar ɗakinta ta Ɓuya.

Hafsatu ce ta ƙaraso bakin ƙofa.
"Ina yarinyar gidannan ina abinci ƴaƴanmu suna ta kuka?"

Asiyah ta kuma ɓuya tana saro ido waje cikin hasala Hafsatu ta kuma ɗaga murya.

"Ke Hasiya su waye sa'annin ki kina ji muna miki magana zaki fito ko sena shigo?"

Cikin sauri Asiyah ta janyo mayafi ta fito waje har ƙasa ta zube tana cewa

"Sannun ku da dawowa"

A fusace indo tace mata.

"Mu ba wannan muke buƙata ba ina abinci? da yunwa muka shigo cikin gidannan"

Asiya ta soma ruwan hawaye

"Wallahi Ban sani ba ya ƙone sai dai na dafa muku wani"

Da sauri indo tace.

"Me kika ce? kina nufin shinkafar har kwano guda ta ƙone kina ubanki?"

Hafsatu ce ta rufe Asiyah da duka indo ta tayata Samira da adama dasuka ɗan fara tasawa suna dariya harda riƙe ciki.

Zuwa lokaci kaɗan Asiyah ta jigata ta fara haki tana wani irin Numfashi sai suka tsorata suka rabu da ita Suna hankaɗata ɗakinta yadda suka daketa haka suka barta kuma itama bata iya tashi ba sabida Jinin dake zuba ta ƙasanta.

Mararta na ƙullewa tana curewa waje ɗaya tuni sun manta da ita sun shiga hada hadar ɗora abincin dare sabo tunda wancan ta Ƙonar suna yi suna mita cikin haka Abubakar ya shigo gidan kai tsaye ɗakin asiyah ya nufa sai dai yaci karo da ita abakin Ƙofa tana nishi ya ɗagata yana cewa


"Asiyah mai ya same ki?"

Idanu ta lumshe kafin ta fara nuna masa mararta tana Nishin azaba.

Da ƙarfi ya furta.

"Indo zoki taimaka min mu fitar da ita a sami motar asibiti, da sauri kamar gaske tazo ta kama Asiya shikuma ya fita ya samo mota suka sakata aciki suka tafi asibiti Cikin hanzari Likitocin asibitin suna amshi Asiya suka ɗorata a gadon tura marasa lafiya suka shiga wani ɗaki da ita.

Abubakar ya kasa zaune ya kasa tsaye tsoron shi ɗaya shine kada asiyah ta rasu idan ta mutu shima kanshi yasan yayi asarar mace tagari sannan idan ta rasu ta wannan hanyar yasan Ƴan uwanta ba zasu barshi ba ya juyo ya kalli indo wadda tai tsuru kamar shege a rabon gado


"Ke indo mai ya same ta ne?"

Cike da bariki tace

"Muda muka shigo gidan a lokacin mukasan abin da ya same ta"

Ya girgiza kai ya cigaba da safa da marwa a wajan hannunshi a bayan shi yama rasa wani tunani ne zeyi a wannan lokaci Ko wanine ya shigo gidan ya doke ta ko faɗuwa tayi ta buge dan shi tunda ya gama bala'in sa daya bar gidan bai kuma shigowa ba sai yanzu.


Likitan ne ya fito daga ɗakin ya dubi Abubakar wanda ya kasa zaune ya kasa tsaye yace masa.

"Malam in ba damuwa ina son ganin ka a office ɗina"..............

*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*RABO YA RANTSE*

*22*


*A LOVE STORY 22*
Da sauri indo ta matso wajan shi ganin kamar ya damu sosai da kiran da likitan yayi mishi.
Dafashi tayi cikin kwantar da harshe wanda ta iya ta furta masa.

"Kawun su kada ka damu, Ba mamaki faɗuwa tayi, dammu ma da muka dawo daga Gidan rasuwa maganar duniya munyi wa yarinyar nan amman muka ji shuru shinkafar ma ta ƙone da alamun tun rana data ɗora bata duba taba"

Ya ɗago idanu jajir ya dube ta.

"Indo naga kamar Asiyah bata Numfashi indo inna rasa Asiyah nima tawa ta ƙare binta kawai zanyi sabida soyayyar da nake wa Asiyah"


Takaici ya kama indo ta fahimci kamar ya mance dawa yake tare yake yabon kishiyarta a gabanta Bata kuma ce masa komai ba ta koma saman benchi tayi zaman ta shikuma yabi bayan likitan zuwa Office ɗin nashi.

"Salamu Alaikum, Likita na ɓata maka lokaci kayi haƙuri fa"

Kawu ya faɗa yana zama a saman kujera likitan yana ta rubutu a saman farar takarda.

"Wassalam, kada ka damu, dama gashi maganine zaka siyo mata yanzu dai an samu cikin nata bai zube ba sai dai a kula da bata tsoro ko ɗaukar abu mai nauyi da sauransu"

Likitan ya faɗa yana miƙawa kawu farar takardar.
Kawu ya washe baki.

Yana cewa.

"Alhamdulillahi Asiyah ɗauke da cikina kai nagode wa Allah yau sai na raba sadaka Allah yasa namiji ne"

Likitan yabi shi da kallo yana mamakin wannan murna da Mutumin yake yi.

Kawu fita yayi pharmacy, yaje ya siyo magungunan kamar yadda Likitan ya rubuta masa sam baiji tsadar magungunan ba haka ya siyo harda allura ya kawo wa likitan.

Likitan ya amshi alluran ya nufi ɗakin da aka kwantar da Asiyah yayi mata ya dawo.

Da sauri kawu ya tare likitan.

"Likita yaya jikin Asiya ko zan iya ganin ta?"

Likitan yayi dariya! sabida yadda ya hango tsantsar ƙauna da kulawa a wajan Mijin nata.

"Mijin Asiyah jeka gano jikin ta koka barmu mu sarara"

Kawu har yana tuntuɓe wajan nufar ɗakin hangota yayi kwance samɓal a saman gado fuskarta tai fayau idanunta a rufe.
Ya ƙarasa gaban gadon ya zauna yana kamo hannunta.

"Sannu Hasiya Allah ya rabaki da cikin nan lafiya"

Haka ya zauna harta farfarɗo Yana ta zuba mata sannu Ita dai bata ce masa komai ba har Likitan ya dawo ya basu sallama suka tafi gida kawu sai faman riritata yake kamar ƙwai.

Suna zuwa gida ya tara matanshi da ƴaƴan shi yace kada a kuma saka Hasiya komai agidan yaja musu kunne Baƙin ciki kamar ya kashe su haka sukai ta gunguni sanin halin shi yasa Basu nuna ƙin amincewar su da sharuɗan nashi ba.

Haka rayuwar ta cigaba da tafiya daga ɓangaran Abubakar ( kawu ) kamar ya goya asiyah dan tsabar so da tattali sai dai idan ya fita ne matan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login