Showing 126001 words to 129000 words out of 150033 words
Chapter 43 - Rabo Ya Rantse Book One Complete Hausa Novel
ƙarfina da tasiri na a matsayina na Uwa naso na jijjige auren sedai Allah ya nunan Auren nashi ne ba nawa Ba haƙiƙa bani da ƙarfi bani da wayo ko dubara ya Allah ka yafen Nayi laifi Kuma zan gyara dukkan Kura kurai na"
Ammi ta faɗa Bashir yayi saurin cewa.
"Zuwa yaushe zaki gyara Ammi bayan kin bar kari tun ranar tubani Kin riga kin sa har ya tsallake ya tafi wanda bamu san wace duniyar ya tafi ba sannan Kin jefa zargin ba shi muke soba dukiyar shi muke so tunda gashi nan har yana furta yabar mana dukiyar shi Matar sa da ƴaƴan sa sun fiye masa dukiyar daya tara Ammi Tun asali wannan tunanin ya dace Ki soma kafin ki zartar da Hukunci Amman se idanun ki suka rufe wa ganin daidai da aiki dashi gashi yanzu Kin rasa ɗa ɗaya tamkar da dubu dan wallahi Yaya Aliyu ɗane guda ɗaya tak! a gareki amman abin da yake Miki zaki tara ƴaƴa dubu basuyi miki ba Duk wata fankama da Muke da bazar wa Muke in ba tasa ba tun kafin yakai haka ya hana hawayen mu ya zuba ƙasa da sunan na maraici Yake taimakon mu Ammi bazan manta ba In Yaya yaga ranki ya ɓaci Kuka yake Miki Baya barin wajan da kike har se Yaga kin sami Nutsuwa Kin dena Fushi dashi ai kamata yayi Daga Lokacin daya Nuna yarinyar nan matar shice zaki zubar da makaman yaƙin ki kija ta ajiki Ki rungume ta ki nuna mata ƙauna da soyayya da Kulawa Lokacin ne zesan Shima yana da uwa mai farin cikin samun Ƙaruwar shi gaskiya Ammi baki kyauta ba amman inna miki ba daidai ba a magana ta Ki yafe Min dan ke uwa ce a gare ni"
Bashir ya faɗa yana share hawayen shi!
"Ban ji haushin kaba Bashir Don Dukkan maganganun ka gaskiya ne Kuma suna bisa kan tsari na gaskiya sedai nayi Kuskure kuma babu wanda baya kuskure naso ace mami ce ta soma haihuwa da Baba ada sabida ina zaton Duk wadda ze auro ba zata Min Biyayya kamar ƴar da ƴar uwata ta haifa ba sedai tashin farko na gane ita ma waccan yarinyar mai Biyayyar ce don babu wadda zatai abin da tayi Mini Naci mata Mutuncin Ƴaƴana suyi mata amman Ko a fuska bata taɓa Nuna tana da alaƙa da Baba ba Ya Allah nasan nayi laifi Ina neman yafiya da gafarar ka sannan ya Allah ka kare Min Baba da matar shi aduk inda ya sami kan shi aduk inda ya ke Kada kasa hawaye da kukan da nake akan shi su zame masa masifa danni Uwa ce Kuma babu daɗi hawayen uwa akan ɗanta Ni nasan Baba ze dawo gare ni yayi ƙaurar zuci ne kawai amman kaf duniya baba bai haɗa soyayyata data kowa ba In ka cire Allah da Annabi ( s.a.w ) Baba bai da sama dani seko mahaifin sa Ko wannan matar tashi wallahi ba fina tai a wajan saba Bai kuma fi son ta akaina ba Kawai ɓacin rai ne tare da ɗaukin Cikin Jikinta amman Nina san Baba soyayyarshi ɗaya ce tana gare Ni sedai hurumi da matakin Soyayyar matar shi da ɗan shima daban aran shi"
Ammi takai maganar.
"Ammi ki dena wannan kukan ya isa haka addu'a zamu tsanan ta akan Allah ya dawo mana dashi sannan kada ki saka damuwa aran ki Kinga kema lafiya bata wadace kiba"
Cewar salama Ammi ta kuma Goge hawayen daya ƙi dena zubo mata tare da cewa.
"Salama kuka ai ya zama Dole wato ajiya faɗuwar da Baba yayi wallahi bana Ko Tantama akan Abun da nai wa yarinyar ne ɓacin rai yasa ya yanke Jiki ya faɗi salama ke baki san halin da muka shiga ba Baba fa a asibiti ya kwana Numfashin sa ya ɗauke Jinin sa yahau zuciyar shi ta Bugu Amman mai yasa ban duba halin da yake ciki ba nai sanadin ɓacin ran shi ya tafi da ciwo Ga matar tashi naga ƙaramar yarinya ce Tsorona da fargaba na kada ciwon nan ya kuma kada shi a gurin da ba Kowa nasa Ga matar sa ba wata wayayya bace ba Innalillahi wa'innah Ilaihirraju'un"
Ammi ta faɗa hankalin ta a tashe dan se yanzu ma wannan tunanin yazo mata a zuciyar ta.
Salma ta kaɗu da jin wannan furuci na Ammi dan bata da labarin ciwon Aliyu.
"Musa zaka ƙara tsayawa kai da fata fiye da yadda kake ada zamu ƙara haɓɓaka Dukiyar Aliyu da ƙarfin ikon Allah zamu tabbatar da ribar da ze samu yanzu tafi wadda yake samu Ada! sannan zamu toshe dukkan wata hanya da mutane zasu San baya tare damu Zamu Je gidan mai girma gwamna da kanmu tare da Bada Uzirin Saƙo daga Aliyu cewa yaɗan ɗauki Hutu Ya tafi London Dan ya Huta acan wanda In mukai haka ina ganin zamu toshe Duk wata hanya da mutane zasu san abun da yake faruwa sabida Sunan shi ya riga yayi fice muddin Muka bar maganar nan ta fita akwai matsala Bashir bana son naji wannan magana ta fita ka kula ko Cikin Gidan su Baba bana son kowa yaji mu kuma zamuyi addu'a zamu saka ayi masa Akan Allah ya Juyo mana da hankalin sa Gida dan Aliyu shine garkuwar Mu Kuma in sha Allah zamu tsare masa martabar sa da Mutuncin sa yadda ya tafi yabar Dukiyar shi haka ze dawo ya sameta Zamu tabbatar da ƙarfin Zumunci Zamu tabbatar damu zumuncin Mu ba irin na wannan zamani bane daga yau dukkan abincin da Komai da ake a wannan Gida da Kuɗin Aliyu nina soke za'a dinga fitarwa daga aljihunmu nida Bashir har sanda Allah ze Bayyana mana shi ba zamu taɓa mai kwandalar shiba Bashir zaka zauna A Abuja Musa Kana kano Ni kuma Ina lagos zamu tsaya da ƙarfin Ikon Allah"
Sadiƙ yakai maganar Cike da ƙarfin gwiwa dana zuciya Sajeeda tace.
"To Amman yaya sadiƙ kasan fa Yaya Aliyu ba iya gidannan yake ciyarwa ba harda Cikin Gida da sauran Al'umma da yake bawa taimako sannan yanayin yadda Aunty Mami ta fita baka tunanin zata gayawa mahaifiyarta baka tunanin maganar zata fita?"
Sadiƙ ya kalli sajeeda.
Kafin yayi magana Musa yay saurin cewa.
"Nima nasan wasu gidajen da yake kaiwa kayan abinci daga ciki harda Gidan surukan shi Ni na ɗauki wannan nauyi nima da aljihuna zan ke tura Musu da kayan abinci kyauta kamar yadda yake basu batare dana bari sun san halin da ake Ciki ba Dan Ni kam yanzu Alhamdulillahi Nima ina da Kuɗin dazan Iya tsayawa da ƙafata dan Mai gida Aliyu Bangon sukari ne dukkan wanda ya raɓe shi seya sha zaƙi dan bayan albashina yana Min kyauta wadda take sani nai ƙaramin suma wadda Nima da Ita nake Riƙe iyalina nake ɗaukar Nauyin Ƴan uwana Alhamdulillahi Nima na ɗauke wannan nauyi"
Bashir yace.
"Tun da bani da nauyi Akaina ni zan ke aikawa da cikin Gida kayan abincin kamar yadda yake basu in sha Allah" Ammi tace.
"Ni kuma musa a gayawa masu gadi duk sanda wani yazo Neman taimako a kirani zan Fito na bayar Sannan acewa ma'aikatan Gidannan tafiya ce ta kama shi zuwa London sabida kar suga Ya shafe Lokuta baya nan duk da yana tafiye tafiye amman wannan bamu san ranar dawowar shiba se Allah"
Salma ta numfasa tare da cewa.
"Ni kuma zan ɗauke nauyin biyan ma'aikata albashi In sha Allah tare da Hidimar makarantar su Sajeeda kafin Allah ya bayyana shi Allah ya rufa mana asiri ya ƙara mana zumunci"
Sadiƙ da bai ce komai ba shine yayi magana.
"Sajeeda maganar Mami ki barta yanzu bama tada Nutsuwar Yaɗa maganar ga wani sabida ɗayan Biyu ne Ko dai tana cikin damuwar Mijinta Ko tana cikin damuwar Kishiyar dayay mata Koda ta gayawa mahaifiyarta ma Ba zasu so maganar ta fita ba mafita zasu Nema Ko sakina data dawo Zan kaɗata zuwa Jibi Muyi lagos bama zan bata damar sake wata Fitar ba In sha Allah ina tabbatar Miki da se asirin maganar nan ya rufu babu mai Jinta a waje sannan Ku tuna da wani abu kada kuga Mun ɗauke dukkan Hidimar da Aliyu yake ku ɗauka cewa yanzu Muma mun taka da ƙafarmu zamuyi abin da yake yi to fa ku tuna gaba ɗaya da bazar sa muke rawa Domin dukkan kuɗin da zamuyi amfani dasu Daga wajan sa zasu Fito dan albashin mu da dukiyar da muke da Ita duk a tare dashi Muka samu Ilimin da Muke aiki dashi Shine ya ɗauki nauyin sa Haka kema salma Albashin da Kike ɗauka da kasuwancin da Kike Dukkan su da bazar Aliyu Kike rawa dan shine ya tsaya Miki akai dan haka addu'a zamu cigaba dayi masa Allah ya bayyana mana shi Cikin Ƙoshin lafiya"
Sadiƙ yakai maganar Cikin Nutsuwa
"Haƙiƙa Kun cika ƴaƴan Halak Allah ya saka Muku da alkairi Allah ya ƙara haɗa kanku Allah ya bayyana Mini ɗan uwan ku"
Ammi ta faɗa Lokacin ana kiran magariba Kowa ya tashi ya Nufi masallaci Su Kuma sallah sukai agidan Har akai Isha'i salma tana tare da Ammi tana kwantar mata da hankalinta.
Musa ne ya shigo falon bayan sallar isha'i dan har Lokacin bai tafi ba Yazo dan yayi wa Ammi sallama.
Ammi ta dubi Musa.
"Musa in ban takura maka ba dan Allah ka kaini Gidan surukan Baba nida salama Tunda bata zo da Mota ba In mun dawo ka ajeni seka wuce da ita Gidan ta"
Musa yace.
"To babu damuwa"
A ladabce.
Ammi ta shirya bayan ta Zuzzuba kayan arziƙi acikin ƙatuwar Leda Salama ta ɗauka suka Fita sajeeda ta yafa mayafin abaya akan ta tabi bayan su safna wayar da suke da Kamal sam bata san fitar su Ammi ba.
Harabar Gidan suka Nufa suka shiga Cikin mota Musa yaja Motar suka fita kai tsaye Gidan su farha suka Tafi a bakin layin Musa yayi parking shine yayi wa su Ammi jagora har Ƙofar Gidan sannan ya koma Mota ya zauna Jiran su Fito su Koma gida.
Gate ɗin suka tura suka shiga gidan ko ina hasken farin ƙwan sola ya haske Gidan, Suka shiga Ƙofar Babban falo wanda ilahirin Mutan gidan ke zaune wasu na kallo wasu na cin abinci Salma tai sallama Babar su Hadiza ta amsa tana cewa.
"Maraba lale Ku shigo mana Ku zauna"
Duk su Ruƙayya suka zubowa su Ammi ido suna kallon ƴan gayu akan Kujera su Ammi suka zauna suna gaisawa da Babar su Ruƙayya da Babarsu Hadiza.
Shuru ne ya biyo baya kafin salma tace.
"Yawwa dan Allah Munzo wajan Maman Farhan ne Ko tana nan?"
Da sauri Babar su Hadiza tace.
"Eh tana ciki Bata fiya fitowa waje bane"
Su Ammi basu saurare taba suka Miƙe Babar su Ruƙayya tai Musu jagoranci har zuwa ɗakin Umma.
A ƙaramin falon Umma wanda yasha ƴan madaidai tan Kujeru daidai shi tare da ƙaramar TV'n jikin Bango su Ammi suka zauna Ikram dake zaune tana Cin Tuwo jin sallama da zaman Mutane a falon Yasa ta ɗago tana kallon su.
Kafin tace musu.
"Sannun ku da zuwa ina yinin ku"
Ammi ta zubawa Ikram idanu.
"Lafiya lau ƴammata Ina mamanki?"
Cewar Ammi har Lokacin tana kallon Ikram Kyan yarinyar yana fusgarta wato ita matar Baba Ita ce baƙa a gidan tunda ta lura duk ƴan matan falon farko farare ne masu Jiki kyawawa ma sha Allah.
Ashe ba Ammi ce kaɗai ta shiga mamakin ba har su salma da suka saki baki Tun farkon Shigowar su suna kallon kyan ƴaƴan Gidan So Ma sha Allah!
Ikram ta miƙe ta shiga ɗaki domin Kiran Umma dan Babar su Ruƙayya tun da ta rako su Ammi ta fita daga ɗakin don ta basu Guri.
Ikram ta shiga cikin ɗakin Umma wadda take zaune a saman darduma hannun ta ɗauke da carbi mai Dubu tana jan shi...........Autar manya ce marubuciyar......
*ƁOYAYYAR ƘAUNA*
*BA SON TA NAKE BA*
*ƊAN MAJALISSA*
*MURADIN ZUCIYA*
*ASHE ZUMA*
*TAURARO*
*KOBA SO*
*RABON WANI*
*FITAR RABO*
*DA IZZATA*
*BAƘON LAMARI*
*AUREN BARE*
*H A S K E*
*ZUMA A BAKI*
*BAƘAR FATA*
*RABO YA RANTSE*
*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
AUTAR MANYA
Arewabooks autarmanya
*A LOVE STORY 97*
Rabo ya rantse
A gefen gado ta zauna tana jiran Umma ta shafa zaman Kusan Minti Goma tayi kafin Umma ta ƙarasa lazumin ta shafa tana kallon Ikram.
"Har kin gama cin tuwon kenan amman dai ba bacci zaki ba Ko kin san akwai Guga a gaban ki gaba ɗaya kayan ki babu guga"
Ikram tace.
"Ehh umma ba kwanciya zanyi ba baƙi Kikai suna falo suna Jiran ki"
Umma tahau salati tare da cewa.
"Amman anyi sakaran yarinya salon suce na wulaƙanta su shine baki gaya Mini ba su waye?"
Ikram tai dariya tare da cewa.
"Wallahi ban san suba Nima Umma kina lazumi se kawai na katse Miki Kefa kika hanamu Yi miki surutu In kina lazumin Ki"
Umma ta naɗe abin sallah tare da kama hanyar Fita tana ƙara yiwa Ikram faɗa akan mai yasa bata gaya mata ba Har ta ƙarasa fita falon da far'arta da komai.
"Ah maraban ku lale marhaba sannun ku Da zuwa dan Allah Kuyi haƙuri Wai Ikram data tarar ina lazumi shine bata gaya Mini nai baƙi ba"
Ammi da far'arta itama tace.
"Ai ta kyauta sosai Koni bana bari sumin magana In Ina lazumi sabida ɓata nake yi"
Umma tai dariya tana fita daga falon Babban falo taje ta Buɗe Fridge ta ɗauko Ruwa da lemo ta zubo a tray ta Nufo ƙaramin falon sabida yanzu Alhamdulillahi Tunda Aliyu ya Buɗewa kawu ƙaton shago wanda yake sayar da kayan masarufi Shikenan Suka ƙara wadata dan babu abin da kawu baya dire Musu gana Aliyu duk ƙarshen wata gana su Halifa duka shiyasa gidan sedai Godiyar Allah.
Umma da sallama ta shigo falon ta aje Musu ruwa da Lemon sannan ta Kuma fita ta ɗebo Cincin a plate ta kawo Musu.
Zama tayi a ƙasan carpet tare da cewa.
"Ikram zoki kawo Musu tuwo Ki duba sama ɗakin su Halifa Ki ɗauko Babban Fulas ɗin tuwon yana can ɗazu aka kai Musu" da yake ranar Girkin Umma ne.
Ammi data saki baki tana kallon karamcin matar tun kafin tasan daga ina suke su waye su Ammi take haba haba dasu Se wata Kunya ta kama Ammi yanzu wannan mata mai Kirki da mutunta ɗan adam ita ce ta haifi ƴar da ɗanta ya aura Amman ta kasa Riƙe Ƴar da daraja Lallai Aliyu ya auro ƴar Mutunci dan ba tarin Dukiya ake bi a aure ba ka auro ƴar Daraja ƴar Gidan Girma da tarbiya shine kayi aure.
Kafin kace me Ikram ta fita se gata da kwanukan tuwo da Miya ta aje Musu Umma tace.
"To dan Allah Kuci mana Duk da ban sheda kuba Amman ai baƙo daraja gare shi"
Saboda Umma ba wayewa tai da Aliyu ba shiyasa bata gane suba Amman in da tasan shi sosai data kalli salma taga Aliyu don suna kama sosai Haka zalika Ammi to da yake bawai kallon shi Umma tai ba shiyasa sam bata gane su Ammi ba.
Sajeeda ta ɗauki ruwa salama ta ɗauki Lemo Ammi kam bata ɗauki Komai ba se Murmushi take kawai tana Hamdala a zuciyarta.
"To Nidai sunana Hajiya Amina amman ana ce Min Ammi mahaifiyar Aliyu Mijin fatima dama Mun zone domin Mu sada zumunci waɗannan Duka ƙannen shine su basa nan sun ɗanyi ƴar tafiya"
Ammi ta faɗa Cikin Nutsuwa Se Umma ta Kuma washe baki Cikin farin ciki tana cewa.
"Kai Ma sha Allah abu yayi daɗi sannunku sannunku mungode Mungode Allah yasa ka muku da alkairi Muna ta ganin hidima daga wajan Aliyu Amman Farha ce har yau bata zoba"
Umma ta ƙarasa faɗa Cikin rauni.
"Kallo ɗaya ammi tai mata tasan Tabbas rashin ɗiyarta yana susar ranta"
Ammi ta dafa kafaɗar Umma.
"Ki haƙuri Maman fatima ƴarki tayi dacen Miji ba danni na haifi abuna ba a,a wannan magana ce ta gaskiya nake Yi Miki ita Ki Godewa Allah Surukin ki ɗan albarkana ne Kinji Ki kwantar da hankalin naji duk yadda auren su ya kasance wanda Maƙasudin auren nasu zazzafan rabo Ne don yanzu haka fatiman ki nada ciki har na wata Uku"
Umma setai ƙasa da kanta sega hawaye nan Ammi bata hanata Kukan ba dan daga Umma har Ikram Kuka suka saka wiwi Umma har tana ajiyar zuciya kafin Salma ta soma rarrashin Umma.
Cikin haka kawu ya ɗaga labule yana cewa.
"Asiya zo mana ga kaji nan na kawo ki gyara su Gobe Musha dabge a gidannan Asiya kina ina......"maganar kawu ta tsaya sanda yaga baƙi a zaune a falon Ga kuma Umma tana share hawaye a ruɗe yake magana.
"Asiya Ke Ikram Kukan me kuke wani abun akai Muku?"
Duk ya faɗa a ruɗe Su Ammi ne suka katse masa tambayar wajan gaishe dashi A mutunce suka gaisa da kawu kafin Umma tace Muryarta a shaƙe.
"Surukar mu ce tazo Babar Mijin Farha"
Se kawu ya zauna ana sabunta gaisuwa.
Ammi na dariya tace.
"Wai fa daga Munce mata Fatima nada Ciki shine take wannan Kukan"
Kawu ya fara tafa hannu yana cewa.
"Ai halin Asiya se ita wallahi Koda yaushe haka nake fama da ita taƙi kwantar da hankalin ta akan auren nan na fatima Kuma na gaya mata dama wani alkairin baya samuwa seda ƙalubale ni kaina na shiga damuwar data kaini ga kwanciyar asibiti bayan dana bawa Ali fatima batare dana san ko shi waye bane sabida zuciyar danai na bijire Min datai akan umarnina na wanda na bata tace Ita Ali take so to daga ƙarshe daya zo nan Ya gaishe ni wallahi se naji na yarda dashi Amman Asiya ita taƙi sakin hankalinta Kullum tunani Kullum Kuka sabida jarabar son da ta ɗauka ta Ɗorawa Fatima kamar ita kaɗai ta haifa a duniya"
Ammi dariya ta saki Sajeeda da Salma ƙasa sukai da kansu Suna dariyar Dramar Kawu lallai mahaifan fatima ba ƙaramin Son ta suke Yi ba.
Ammi ce tace.
"Lallai dole na bawa Fatima kyauta wato akan Babana tai yaƙi ba ɗan kaɗan ba lallai fatima ƴar soce yadda Mamanta ke son ta Nima haka nake Son Baba kaf yarana yafi damuwa dani baya son damuwa ta Allah de yayi Musu albarka bai ɗayan su"
Se kuma aka shiga hira yadda Kawu yake hira da Ammi kai kace sun jima da sanin Junan su, Dan Ammi batai wata alkunya ba sosai ta sake suna hirar su da kawu kafin Umma tasa Ikram ta Kira matan