Showing 78001 words to 81000 words out of 150033 words
Chapter 27 - Rabo Ya Rantse Book One Complete Hausa Novel
sema ya gani ya bada tukwici"
Ta faɗa tana juyawa wajan Ludayin Mami tana dariyar jin daɗi da sauri tai wuf ta zuba magani a ruwan Miyar da farha ta Ɗora Farha sam bata lura ba ta miƙa wa mami ludayin ta Cigaba da haɗa miyar tata Mami ta fita da Ludayin da babu abin da zatai dashi dama dan ta zuba magani a miyar ne tayi wa Farha dubara
Farha da ɗayan Gas ɗin ta ɗorawa Aliyu tea ɗin Ta raba hankalinta Biyu can tana miya nan tana kula da tea bayan ya tafaso ta zuba a flaks ta aje Miyar na tafasa Ƙamshin daddawa dasu citta na tasowa Farha taji zuciyarta na tashi sabida bata san ƙamshin ɗankwali ta saka ta Toshe hancinta haka ta kammala Miyar ta haɗa takai Falo haɗe da sauran kayan abincin ta gyara dining Ɗin tas ta ɗauko turaren wuta ta kunna.
Ammi ita kanta a ranar seda ta yaba da yadda Farha tayi Ƙoƙarin haɗa komai aikuwa se sannu take mata Ammin ma taci gayu Su safna ma haka.
Ita dai farha data samu ta shiga ɗaki kwanciya tayi a saman gado nan da nan bacci ya ɗauketa............*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*A LOVE STORY 62*
Yana saukowa daga step ɗin jirgin yana lumshe idanun shi sabida shaƙar Iskar Jahar sa Abar alfaharin sa da yake yi kano kenan ta dabo ci gari koda me kazo an fika mai mata mai matasa mai malamai mai masoya Manzon Allah ( s.a.w ) mai dala tushen birni mai gwauron dutse mai masauratar da take da tarin tarihi kano jalla babbar hausa kano tumbin giwa!
Da sauri musa ya ƙaraso gaban sa bayan ya bar harabar da jirgin ya sauke su Musa ya amshi ƴar ƙaramar Jakar dake rataye a kafaɗun sa Haka suka nufi inda Musa yayi parking Ɗin Mota yana jiran shi wata haɗaɗɗiyar Black mercedes benz s class, Musa ya buɗe masa Back seat ya shiga ya zauna gaba ɗaya ya gaji tunda yabar lokoja ya tafi lagos bai zauna ba zirga zirga suke shida Bashir wanda jin sadik zezo arewa yasa wa Aliyu kuka akan ko kwana ɗaya ne ya barshi yazo yayi shima tausayin Bashir yaji shiyasa ya bar shi suka tawo tare sedai shi Aliyu ko acikin Jirgi yana Vip section sabida haka jirgin su na landing ya sauko batare daya tsaya jiran su Bashir ba dan su Driver ne yake jiran su.
Sadik da Yaran shi da sakina da jamila ƙanwarta da bashir driver ne ya ɗauko su a wata Farar BMW suma Musa yana tafe yana bawa Aliyu labarin yadda Shari'ar Md ta kaya Shidai ya dafe kai bai cewa Musa komai ba suna isa gida part ɗinshi ya shiga Mami ta tare shi tana masa sannu ya hau sama ya shiga wanka ya ɗauro alwalar sallar magariba a ɗaki ma yayi sallar sannan ya sauka ƙasa dan yunwa yake ji Jeans baƙi ne a jikinsa se farar Polo shirt se ƙamshin turare yake mai sanyin Ƙamshi ya ƙarasa gaban dining ya zauna yana kiran mami.
Ta ƙaraso tana rankwaɓo wa jikin shi.
"Yaya gani nayi sallah ne"
Ya ɗan kalleta kaɗan tayi kyau ba laifi.
"Ina abincina?"
Tai murmushi.
"Ammi tasa an haɗa a part ɗin ta acan zamu yi dinner"
Bece komai ba yayi sama da kanshi ya jingina jikin Kujerar da yake kanta yunwa yake ji ba kaɗan ba can ya kuma cewa.
"Ko ɗan ruwan shayi ma babu?"
Mami tace "Eh duk suna can"
Ƙaramin tsaki kurum yaja ya fito da wayar shi ya shiga danne danne seda yayi sallar Isha'i sannan suka jera part ɗin Ammi shida Mami.
Su sadiƙ a part ɗin Ammi suka sauka extra room ɗin dake Kusa dana su ammi Sakina ta saka kayanta shi kuma Sadiƙ ya aje nasa a part ɗin Bashir sabida su ba'a gyara musu part Ɗinsu ba akwai datti sosai Kuma duk aikinne yayi yawa sedai ko zuwa Gobe wanka sukai tare dayin sallah Nan fa suka baje a falo ammi nata tsokanar su Minal ƴaƴan sadik waɗanda suke jin yarabanci don maganar suma bata fita sosai saboda zaman Cikin yare, Intisar ce ma mai magana da hausa amman Minal da Hidaya se turanci se yarabanci nan da nan sun koma kamar ƙabilu.
Zuwan Aliyu da Mami ne yasa Bashir dasu safna suka ɗan shiga Nutsuwar su da dariyar da suke yi dan Sun san Gogan ba wasa Jamila ƙanwar sakina wadda ita kebin ta wadda sakina keson ta haɗa ta da Aliyu shi kuma yaƙi yarda se kallon Aliyu take kamar ta lashe shi lura da kallon da jamila kewa Aliyu ne yasa Mami taƙi sakin fuska tai kicin kicin da ranta ta koma bayan Mijinta ta zauna yaɗan kalli sadik da ke bawa Ammi labari.
"Oga nifa nazo yin dinner ne sabida yunwa nake ji" batare daya jira amsar sadik ba ya gaishe da Ammi wadda ta miƙe tana cewa su sakina.
"Ku taso muje muci abinci seku yi sallar isha'i"
Duk suka tashi ban da Jamila data zauna tana sunne kai ammi ta kalleta da kulawa.
"Jamila taso mana kema ai kin zama ƴar gida" sakina tayi dariya tana cewa.
"Ai Ammi ita haka take, yau fa kwanan ta biyu a lagos taje min hutu shine na tawo nan da ita"
Ammi tayi dariya tana cewa.
"Aiko ta kyauta"
Shikam Aliyu har ya ƙarasa dining ya shiga buɗe warmers ɗin da aka jere duk ba abin da yayi masa se tuwon daya gani marar yawa ya zuba a plate ya ɗauki spoon da sauri Mami ta riƙe Cokalin da Aliyu ze kai cikin bakin sa jikinta har rawa yake wajan ce masa "Yaya kada kaci dan Allah"
Ya aje cokalin ya tsareta da ido Lokacin kowa ya zauna a saman dining kuma kowa ya shiga zuba abin da ze kai cikin sa.
"Sabida me kar naci? idan naci mutuwa zanyi kome?"
Gaban mami ya faɗi ta shiga sosa kanta.
"A,a yaya dama Ammi nasa Farhan taiwa kasan ita bata son girke girken mu na zamani"
Aliyu yayi wani Basaraken Murmushi ya ɗauki cokalin ya cigaba dacin tuwon hankalin sa kwance Ammi kam dariya tayi tana cewa "Ai kema da se kisa ai da yawa Kin san yadda Mijin ki yake son tuwo" Mami sam bata ji mai ammi take faɗa ba ta shiga tashin hankali ko abincin ma ta kasa zubawa taci.
Falon ya ɗauki shuru kowa yana faman cin abinci se ƙarar cokula da Plate ke tashi.
Aliyu ya ɗan kalli mami ya cigaba da cin tuwon shi.
"Ina tea ɗin?"
Sosa kai tayi tare da ɗaga Murya sosai.
"Farhan kawo tea"
Aliyu yabi ta kallo yana tuna wace Farhan ɗin da take ta faman faɗi dan shi ya manta sunan farha farhan dan shi Fatima yake ce mata.
Lokacin Farha ta miƙe daga baccin tana sallah seda ta idar ta fito waje sabida jin Yadda Aunty mami keta ƙwala mata kira.
Gaba ɗaya se ta shiga damuwa sabida yadda taga mutane da yawa a falon kowa kuma ya zuba mata ido sum sum ta wuce Kitchen ta haɗo kayan tea ɗin a tray ta kawo gaban mami ta aje ta Lura da yadda wannan matashin ya tsaida Cin abincin sa tun bayan data fito se kallonta yake kamar maye, Sannan wannan baƙar Budurwar ma kallon ta take, a ɗarare ta shiga gaishe dasu sakina.
Sakina ba sakin fuska ta amsa jamila ma haka Bashir kuwa bai amsa ba se jarababban kallon da yake bin ta dashi Sadik ne ya amsa yana cewa.
"Hajiya Ammi tamu ina kika samo ƴar budurwa haka?"
Ammi murmushi tayi bata ce komai ba sabida abinci take bawa hidaya ƙaramar ƴar sadik.
Sakina ce ta ɗago a gadarance.
"Ke da Allah ɗauki yarinyar can Ki mata wanka" ta nuna intisar Farha ta juya zata ɗauki yarinyar Aliyu daya daskare a zaune yana binta da kallo na mamakin yadda ta kalli kowa ta gaishe dashi amman shi ta kasa koda kallon shine bare ya sami arziƙin gaisuwar ma.
Da sauri yace.
"A,a Sakina Ita wannan ƙanwar taki taiwa Intisar wanka mana, bakya ganin ita aiki take" batare daya kalli sakinar ba yayi maganar da sauri kuma ya cigaba da cin tuwon shi...............*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*A LOVE STORY 63*
Cikin son ta cusa masa haushi tace.
"Lah bari nayi mata wankan, meye aikina in ba yiwa kowa na gidannan Hidima ba ai bani da wani hutu se Hidimta Muku" daga haka ta ɗauki Intisar cak tayi hanyar ɗakin ta da ita Bashir da yaji ta burge shi data gwale Aliyu dama cike yake da haushin yadda Aliyu ke hana yarinyar tai wani abun sannan kuma yana nuna kamar shike iko da ita.
Da ɗan nishaɗi Bashir ya ɗaga Murya bayan ya kora ruwa.
"Hy baby zo mana ki zuba min Lemo a cup" cak ta tsaya tana nanata sunan daya gaya mata Anya ta je kuwa murmushi ta saki ta aje Intisar ta juya gaban Bashir se kallonta yake ta tsiyaya masa Lemon ta miƙa masa tana wani Irin murmushi ta koma ta ɗauki Inti ta shigar da ita ɗakinta ta cire mata kaya ta haɗa ruwa tayi mata wanka sam ta mance yaushe rabon ta da sabulun wanka se yau sabida ita idan zata yi wanka sedai ta ɗauko omo tayi dashi sabida bata son ƙamshin sabulun tana toshe hanci tana wa Inti wankan tana kwa gamawa ta soma sheƙa amai wanda yarinyar ta gudu daga toilet Ɗin ta fita falo ko kaya babu ajikinta.
Lokacin sun kammala cin abincin Shi kaɗai ke dining yana shan bakin shayi.
"Ke Intisar ina kayan naki?" cewar Jamila wadda ta Miƙe zata shiga ɗakin da suka sauka yarinyar tai kalar kuka tana cewa.
"Nanny ɗin amai take tayi a bathroom ɗin shine na fito" Jamila ta kamata suka wuce ɗaki Mami zama tayi a falo duk jikinta a sanyaye har lokacin a tsure take sabida Aliyu yaci wannan tuwo da sauri kuma ta miƙe ta nufi sashin su don ta kira maman ta a waya su san matakin ɗauka.
Bashir wata irin tafiya yake yana ɗaga lemon data zuba mai yana sha ji yake kamar bakin ta yake tsotsa dan jaraba Aliyu ya fuskanci Abin da tai masa yayi wa Bashir daɗi Se kawai ya raka Bashir da idanu har yabar falon domin Aliyu ya gama gano Bashir me yake nufi da yarinyar wannan tasa ya nesan tashi da gida amman yanzun ma ze ɗauki mataki akan Bashir Ɗin daga cikin falo sakina ma ɗaki ta wuce dan ta gaji sosai hutu take buƙata Falon daga sadik se Ammi dasu safna suna ta faman Hira shiko Aliyu be shiga cikin suba kuma bai tafi ba waya yake tayi da mutane daban daban duk da yaji zafin yadda ta yarfa shi ta gwasale shi a gaban ƙannen shi da matar shi amman sabida tsabar Muskilanci bai ko nuna a Fuskar shiba.
Sadiƙ hamma yayi tare dayi wa su Ammi sallama ya ƙaraso wajan Aliyu sukai sallama ya wuce makwancin sa su safna ma wuce wa sukai bedroom ɗinsu ganin haka Ammi ta dube shi.
"Wai kai me kake jira anan ne kowa ya kwanta kai ba hira ba kai ba tafiya ba?" Ya shafa kanshi bai ce mata komai ba ta miƙe ta kama hanyar Bedroom ɗinta tabar shi a wajan.
Ya sauke ajiyar zuciya ya miƙe ya nufi ɗakin marar kunyar can, kamar yadda ya raɗa mata yaja handle ɗin ƙofar ta buɗe ya shiga ya zira key a jikin ƙofar ya kunna hasken ɗakin sabida ta kashe hasken tun sanda ta fito daga toilet bayan ta gama aman ta kashe ƙwan ta kwanta duk da tana tsananin jin yunwa ga yawun ta se tsinkewa yake, amman bata sha'awar shinkafa ko taliya yau ɗinnan wainar fulawa take son taci mai man gyaɗa da albasa da tumatur da yajin tafarnuwa har ƙamshin wainar take ji a hancin ta wannan dalilin ne yasa ta ɗora hannu a saman cikinta tana kuka wiwi dan sosai take muradin cin wainar kuma bata son ƙamshin suyar tafi son kawai ta ganta a gabanta tana ci cikin haka hasken daya kunna ya gauraye ɗakin ta ɗago ta zauna tana kallon shi ya wani haɗe fuska kamar bai taɓa yin dariya ba.
"Ke baki da kunya ko? baki da mutunci baki san darajar aure na da yake kanki ba har Bashir yana ce Miki Baby kina amsawa kin mayar da kanki kamar baki san me kike ba me sakina ta fiki dashi da zata wani daka Miki tsawa! ki mata abu har Kiyi, sannan ince ba zaki ba ki gwale ni bayan rashin gaisuwa dana kasa samu a wajan ki, so kada ki ga na haɗa Ƙirji dake wallahi I will surprise you if you refuse to follow what I told you"
Har ya gama masifar bata ko kalli inda yake ba ita ta kanta take se faman sakin Numfashi take yi Shurun data yi masa ne ya ƙara fusata shi idan da abin da yafi tsana a duniya bai wuce Yayi magana ai masa banza ba bai wuce yayi faɗa a ƙi bashi haƙuri ba aiko yayi mata kaa cikin hargowa yana daka mata tsawa!
"I talked to you but you kept quiet, you made me crazy or something?"
Ya faɗa yana zuba mata girman idanunshi waɗanda sukai jajir Se tace tunda take bata taɓa ganin Yanayin nan a tare dashi ba rintse idanu tayi Jikinta yahau rawa Bakinta mai cike da yawu ta ɗaga tana cewa
"To ni me kake so nace maka, nayi magana kace nayi maka rashin kunya kome?" Seta saka kuka ta cigaba da cewa "Ni ka rabu dani ka barni haka nina san me yake damuna zaka wani zo kana min Ihu akaina dame zanji da gajiyar aikin gidanku koda Abin da yake damuna kashe kaina zanyi idan ban musu aikin ba, ba jaka ka kawo ba? ai ni jaka ce mai muku hidima kaine kace nida fita sedai naje gidan zoo wajan dabbobi ƴan uwana to meye danna yiwa matar yayan ka Biyayya nayi wa ƙanin ka duk fa acikin aikin dana zo yi muku ne ni baiwa ce daka siyo duk inda kuka kaɗani nan zanyi sabida haka ni kada ka kuma zuwa kana Min wannan ihun idan ba haka zan faɗi tsakanina dakai kowa ma ya sani idan yaso ka sake ni na huta da wannan ƙaddararran auren naka wanda bashi da Ƴanci"
Da gudu ta ƙarasa maganar sabida Aman daya tawo mata tun kafin takai ga shiga banɗakin ma Aman ya gama wanke tsakar Ɗakin a bakin Ƙofar bankaɗin ta tsugunna tare da dafa ciki tana sheƙa Aman yana tsaye yana mamakin furucin ta lallai ta shahara a rashin Kunya shine har yana magana tana mayar masa, Farha ta gama aman ta wanke wajan ta wanke bakinta ta taso zata Zo ta gyara inda ta ɓata ɗin a ɗakin santsin aman ya kwasheta luuu ta tafi zata faɗi da wani Irin sauri ya taro ta, ta faɗo masa saman Ƙirjinsa Allah ya taimaka bata kai ga faɗuwa a ƙasan ba.................*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*A LOVE STORY 64*
Idanu ta rintse ƙirjinta na dukan dum!dum! sabida gaba ɗaya ta bayar data faɗi ma ta gama sedai data tsinci kanta ajikin sa ya tallafe ƙugunta da hannun shi seta hau sakin ajiyar zuciya mai ƙarfi da sauri ta kuma soma zamewa ajikinshi sabida sabon Aman daya kuma tawo mata amman fafur yaƙi sakinta Lumshe ido tayi tana girgiza masa kanta alamun ya saketa dan ba zata iya magana da baki ba sakamakon yawun daya cika mata Bakinta tana magana zubowa zeyi bata da zaɓi face soma sheƙa masa Aman a jikinsa harta gama bai sake ta ba Mayar da Numfashi take tana dambe da Numfashin ta wanda yake Fita da sauri da sauri.
"Sannu" ya faɗa yana ɗagata cak ya kaita Toilet da hannunsa ya dinga ɗauraye mata Jikinta ya ɗagata cak ya kaita kan gado ya ajeta da kansa ya shiga gyara ɗakin seda ya goge aman duk da yana da masifar ƙyamƙyami amman ikon Allah shiya gyara ɗakin ya tube Rigar sa ya wanke ya shanyata ajikin Ƙofar toilet dan ta ɓaci yayi saura daga shi se dogon wandon Jeans ɗinsa da singlet.
Ya ƙaraso gabanta ya tsugunna ya kamo hannunta duk da yaji zafin abin da tai masa Musamman ƙaddararran auren sa data Furta wannan kalma tai mai zafi ba kaɗan ba amman hakan bai hana shi Jin tausayin halin data ke Ciki ba a yanzun
"Da ina da ina ke maki ciwo sannan kuma shi wannan Aman yau she kika fara?" ya faɗa yana kallonta da kulawa.
"Ni ba inda ke min ciwo amai kuma ban san adadin Lokacin dana fara ba ina ga maleria ke damuna daman haka take min ko a gida"
Bai magana ba ya tashi ya dawo kusa da ita ya zauna.
"Fatima" yaja sunan a hankali.
"Ummh" tace batare data kalle shiba.
"Nifa ba sa'an ki bane bai dace ki dinga min magana yadda kika ga dama ba danna Miki faɗa shine zaki ce da aure na ƙaddara, Yes ƙaddara ne kamar yadda kika faɗa ai daman komai kika ga ya sami bawa ƙaddarar shice sannan idan kika ce zaki fallasa aure na dake Ba damuwata bace Ke nake tausayi dan ba zaki iya rayuwa babu niba danna tabbata daga ranar da Ammi ta sani to seta rabamu shiyasa nake lallaɓawa har Allah ya kawo mana mafita, amman in kika tona shi kece a ruwa ni ina da matata"
Ya faɗa hankalin shi kwance kuka! farha ta fashe masa dashi.
"Nima ba abar tausayi bace tunda idan naje Gida salim ze dawo na aure shi"
Aliyu ya saki Murmushin Na miki illah.
"Ke mai yasa wani bin baki da hankali ne wani mahaukacinne ze aure ki a yanzu to nima jahadi nayi ai dana aure ki Idan ma zaki nutsu ki Nutsu ba wani salim daze aure ki ai ɗan halak ne shi idan kin manta rashin albarkar da kika masa