Showing 123001 words to 126000 words out of 150033 words

Chapter 42 - Rabo Ya Rantse Book One Complete Hausa Novel

kuma na Kira salma tazo yanzunnan ta zubar da Cikinnan Tunda nasan ba asibitin da suke zubda Ciki sabida Doka ce"!!


Jada baya Aliyu ya dinga yi yana girgiza kansa.
"Ammi ina son matata babu dalilin da zesa na saketa Kuma Allah ma baya son saki duk da ba haram bane! Sannan Ammi in kika zubar mata da Ciki Wallahi Nima rasa ni zaki dan In kina ƙaunata To Kiso Cikin Jikin fatima nina ɗauka Murnar Cikin Jikinta zata Goge Dukkan wani ɓacin ranki au ashe ba haka bane........

"Dakata baba ni bana son wannan yarinyar ba kuma nason na haɗa zuri'a daga tsatsonta sabida haka koka bi zaɓi na Ko ɓacin rai ya Biyo baya wallahi"

Ammi ta faɗa cikin hargowa.

Farha ta dinga shafa Cikinta tana Kuka Jitai Tana masifar son abin da ke Cikin nata.

Aliyu a hankali ya Miƙe yabar falon yana tafe yana haɗa hanya Ammi ta janyo wayarta ta shiga Kiran salma ta bata Umarni akan tazo Cikin gaggawa Falon Shuru yayi ammi ta bar wajan Su safna Suka Nufi ɗakin su sadiƙ ya Juya ya fita mami da dafe bango Ta bar falon sabida har Lokacin mafarki take.

Falon yayi tsit se Sautin Kukan farha a hankali ya tako ya ƙaraso gabanta.
"Taso"
Ya faɗa babu walwala tashi tayi shikuma ya ɗauki Kayanta Suka fita daga falon Harabar Gidan tsit sabida Lokacin ana sallar la'asar Cikin wata Mota suka shiga da kanshi yaja Motar Har zuwa Bakin titi kafin ya ɗauko wayar shi ya kira Musa zaman Jiran Musa sukai wanda kusan Minti talatin yazo.

Aliyu ya Koma baya kusa da farha Musa yaja Motar tafiya sukai harta kusan awa se gasu a wata babbar tashar Motoci Kaduna Shine abin da kwandastan motar yake faɗa

Aliyu yace Musa ya Tsaya suka fita ya fito da kayan shi da nata Babbar Wayar shi Ya miƙawa Musa tare da cewa.
"Ka aje Min a wajan ka Wannan Kuma takardar ka kaiwa Ammi"
Daga haka ya kama farha Suka Shiga Cikin Motar dama Mutum Biyu ne suka rage yabar Musa a tsaye kamar an dasa shi yama rasa me zeyi sabida bai san Komai akai ba.
Da sanyin Jiki Musa yaja Motar zuwa gidan Aliyu kuma kamar yadda ya faɗa kai tsaye Musa sashin Ammi ya Nufa Lokacin salma ta ƙaraso duk hankalinta a tashe Kusan a tare ma suka shiga sashin ita da Musa Lokacin da suka shiga falon sadiƙ da Bashir suna tsaye se Ammi Dasu safna daga gani kamar magana suke sallama sukai suka shiga falon Musa ya rissuna ya miƙawa Ammi doguwar takardar da Aliyu ya bashi tare da cewa.
"Ammi gashi Inji yallaɓai yanzunan na kaishi tasha"
Har rige rigen Miƙa hannu sadiƙ da Bashir sukai wajan amsar takardar Jikin sadiƙ rawa yake a fili yake karanta saƙon da takardar ta Ƙunsa mai ɗauke da Rubutun Aliyu ajiki.

_Ammi ki yafe Min ko zamu gana ko ba zamu gana ba Ammi na zaɓi na nesanta kaina dake sabida matakin da Kika ɗauka akaina duk ba zan Iya ba Domin Ko a addini haka haramun ne saki halak ne amman Allah baya so Bare Ni fatima batai Min laifin da zan sake taba sannan Kuma in na yarda Kika zubar mata da ciki kamar nai Kisan kai ne bare ma Ni ina son cikina Tunda matata ce ta sunna amman In kina Musu Kije ki tambayi su kawu Ko Musa ma yasan Komai akai Ammi na Tafi duk Inda Allah ya nufa na zauna nai rayuwa na raini Cikin fatima na zauna da ita kamar yadda itama ta yarda dani ta zauna dani ta rabu da iyayenta akaina Na bar Muku komai nawa Ku riƙe Ni fatima da Cikinta sun fimin dukiya da Duk Jin daɗin rayuwa ina fatan Dukiyar dana bar Muku zata baku farin ciki kwatankwacin wanda Nake baku na barki lafiya Daga ɗanki Aliyu Kuma ina roƙon gafarar Ki in nai Miki ba daidai ba_ ....................
Autar manya ce marubuciyar......
*ƁOYAYYAR ƘAUNA*
*BA SON TA NAKE BA*
*ƊAN MAJALISSA*
*MURADIN ZUCIYA*
*ASHE ZUMA*
*TAURARO*
*KOBA SO*
*RABON WANI*
*FITAR RABO*
*DA IZZATA*
*BAƘON LAMARI*
*AUREN BARE*
*H A S K E*
*RABO YA RANTSE*

*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*A LOVE STORY 95*

"Innalillahi wa'innah ilaihirraju'un" Ita ce kalmar da sadiƙ yake ta ambata acikin bakin sa kuma da sauri haka zalika a bayyane yake furta kalmar gaba ɗaya Gumi ya jiƙa wa sadiƙ Rigar dake Jikinsa ga wani Wanda yake Kuma biyowa daga goshin sa zuwa fuskar shi Ita ko salma ƙafafunta kasa ɗaukarta sukai Seta zube a wajan tana ambatar Sunan Allah wani irin ɗaukewa numfashin Ammi yayi na wucin gadi wanda seda Bashir ya riƙota dan gaba ɗaya tai suman tsaye ko motsi ta kasa yi Babu abun da kake ji a cikin falon se sautin Fitar Kukan su Safna.

"Ammi kin cuce mu kin cuci kanki wannan wani irin son zuciya ne me Aliyu yayi miki haka? Ammi aduk cikin mu babu mai yi miki biyayyar da yake Miki Yau gashi kin wayi gari babu shi ko tausaya mai baki ba na halin da ya shiga Jiya ke idanunki sun rufe son zuciyarki kaɗai kike hangowa yau gashi kin buɗi idanu babu Aliyu Ya bar miki gidan da komai nashi Seki zuba ruwa a ƙasa ki sha sabida Murna"

Sadiƙ ne yayi wannan furuci cikin Fushi ya juya zebar falon Musa ya riƙo hannayen shi cikin ladabi Musa yace.
"Ranka ya daɗe a sassauta kalma mahaifiya ce in rai ya ɓaci hankali ke Nemo shi kuma kada ka fita dan Allah muyi zaman neman mafita Ba fushi ba ni ban san abin da yake faruwa ba wallahi da bazan bar yallaɓai yay tafiyar nan ba Kuma ko wayar shi bai tafi da ita ba ka ganta a hannuna"

Ammi ta zabura tana furta.
"Na shiga uku ni Aminatu na banu ina zan ganka Baba wallahi dukkan abin da na gaya maka ba har raina ba tsananin ɓacin ran auren da kai ne batare daka gaya Min ba amman in akwai abin da nafi so a duniya shine ɗan ka Baba"

Bashir ne yayi magana cikin haushi.
"In kina son shi mai yasa Kika kasa karɓar ƙaddarar shi mai yasa har kika furta zaki zubar masa da cikin matar shi har kika kira yaya salama haba Ammi duk Ɓoye ɓoyen da yaya Yayi sabida wa yayi?"

Kuka ammi take tana cewa.
"Ko giya na sha bazan iya zubar da Cikin taba ku fahimceni kurari nake masa har Kiran salama dana yi Kuma koda na shiga ɗaki bayan nayi wa salama waya wallahi Kuka nake Na farin cikin wannan ƙaruwa da Muka samu sannan na Jinjina girman rabo Lallai In RABO YA RANTSE se meshi kuma duk inda mai rabon yake se ya same shi har ga Allah naso mami ce ta sami ƙaruwa da baba amman ni Musulma ce nasan ƙaddara kuma nasan Cewa dukkan abin da Allah yayi ya tsara ya ƙaddara ba makawa seya tabbata wannan yarinya ita ce mai rabon Haihuwa da Aliyu......."

"Amman ammi kika tozarta ta kika wulaƙantata tun a hanya kike aibata ta Nai kukan rashin sani wallahi in da nasan matar yaya ce ba zan taɓa cin zarafin taba dan yaya yayi mana a rayuwa komai muka samu shine sila komai muka zama shine tsani ko kashi ya kawo mana wallahi zamu yaɓa ajikin mu sedai kash rashin sani ya kaimu ga yiwa baiwar Allah cin kashi agidannan raini cin zarafi Kaicon Mu"
Cewar safna tana wani irin kuka duk yadda Ammi taso fahimtar da yaran nata sun kasa fahimtar ta kowa ya ɗora laifin akanta a wannan Lokacin ta kuma tabbatar da cewa kan ƴaƴanta a haɗe yake dan ko wanne acikin su kamar ze haɗiyi zuciya ya Mutu Salma da tunda tazo batai magana ba ita tace.
"Nice shedar cewa matar sa ce dan bai Ɓoye Mini komai ba koda Kuka tafi umara agidana ta zauna Babu kalar wahalar da bata sha a laulayi kuma koda yaushe hankalin sa yana kan matar shi dana zauna nai nazari sena gano cewa wannan aure nasu haɗin Allah ne wallahi nina san duk ranar da ammi tai ƙoƙarin raba shi da wannan yarinya akwai matsala dan mace akewa dole ba namiji ba, Ammi mai yasa idanunki suka rufe kika kasa karɓar ƙaddarar da Allah ya ƙaddarata cikin halak! yau da ace miki ya sami Ɗa ta hanyar zina da wannan yarinya ba farin ciki bane ace ta hanyar aure aka samu ba Ammi duk ɓoye Ɓoyen da yayi na auren shi gudun ɓacin ranki ne ni yasha gaya min cewa salama bana son ammi tasan nai aure sabida bata so salama har fargabar ranar da ammi zata san na ƙara aure nake kuma se Allah ya bashi yarinyar arziƙi wadda take son shi tsakani da Allah wadda take taya shi yi Miki biyayya dan wallahi yadda yake masifar son yarinyar nan wllahi idan irin ƴammatan wannan zamani ce da tuni Ta rabaku da tuni Ta bayyana ita wacece a gurin sa ƙarƙari base dai ki faɗan ki gama ba amman da yake tana da tarbiya ta kwantar da kai ta nuna ita ƴar aikin ce kamar yadda yace tana binki ammi tana bin ƴaƴanki ammi amman ammi seda kika jawo Aliyu yayi nisa dake Kuma ko nice abin da yayi hakan zanyi dan babu irin biyayyar da bai Miki ba wannan son zuciyarki ne Kika so ki aiwatar masa shi kuma haƙurin sa ya ƙare Kinga yanzu ya ɗauke matarsa sun Gudu batare da ya gaya miki kalma marar daɗi ba zeje yayi rayuwar shi ba tare damu ba ze zauna a tsakanin ƴaƴan shi da matar shi Ko zamu gana ko ba zamu gana ba Allahu masanin gaibu"

Da kuka salma takai ƙarshen maganar kafin bashir yace.
"Ammi ke mahaifiyar muce wallahi ammi baki kyauta ba Kuma ina son kawai ki karɓi laifin ki Kuma kiyi nadama wallahi ammi naso yarinyar nan kamar zan Mutu kuma yaya ya gano ina son ta amman bai taɓa nunan cewa Matar sa bace Kuma bai yarda ya sami matsala dani akanta ba seya dinga Nisantani da garinnan wannan Ne silar daya Ce sena zauna a abuja dana dawo yace na tafi lagos da kaina na zauna nai karatun Ɓoyayyar alaƙar dake tsakanin wannan yarinyar da yaya tun daga nan Kuma na fara yakice ta araina domin wata Fuskar tafi gaban mari Kuma ana barin halak dan Kunya cewar bahaushe, maganar gaskiya ammi nadama da gyara abin da ya ɓaci zaki bawai Kita maganar cewa kina so ko bakya so ba domin duk wannan ya wuce Sedai Mu san abin yi wani mataki zamu ɗauka akan wannan matsala ni babban tashin hankalina ma shine kada ƴan Cikin gida suji wannan labari"

Bashir ya faɗa yana share hawayen sa Ammi a raunane tace "Naji bashir wallahi nai nadama ni kaɗai nasan me nake Ji acikin zuciyata Sajeeda bani ruwa bani ruwa na sha" Ta faɗa cikin kuka tana Jan Numfashi da ƙyar sadiƙ ya Miƙo mata ruwan tasha Musa ya gyara Murya shima duk ya karaya Muryarshi ta sauya kamar zeyi Kukan Cikin Sanyin Murya yace.

"Wato ita ƙaddara haka take tana faruwa ne ga bawa batare daya shirya mata ba Kuma batare daya san zuwan taba Da aure da Mutuwa da sauran dukkan jarabawar da Allah ze saukar wa bawan sa yana saukar wane kai tsaye batare da bawa yasan Lokacin faruwar hakan ba sedai kawai yaji shi acikin wannan yanayin to kamar haka ne ta faru a tsakanin auren Aliyu da fatima Nine sheda Kuma dukkan wanda ze bada shaidar wannan aure bayan Nine seko waliyan sa shaƙiƙan sa dangin mahaifin sa dan bana zaton ko mai Gida sadiƙ ya gayawa sabida yadda abun yazo a ƙurarren Lokaci nine na bincika masa komai na wannan yarinya Kuma nine nasan komai daya danganci ita yarinyar tunda niya ɗora akan Bincikar wacece ita wanda Alhamdulillahi ta fito a cikin zuri'a mai kyawun tushe da asali duk da bama su wadata bane iyayenta amman mahaifinta Mutum ne kaifi ɗaya mai gaskiya da riƙon amana ina fatan Allah yasa Ko bayan bayyanar su ne kada waɗannan Maganganu da kalubalen da wannan yarinya ta shiga agidannan yaje Kunnen mahaifinta dan tabbas ze iya raba auren su dan ba ason ranshi ma akai auren nan ba hasalima ita akwai wanda take so akwai wanda aka tsaida maganar auren su dashi To wannan Rabon shine yay ɗawainiya dasu dukkan su har Allah ya tsara auren Nasu Fatima ƴar jarida ce Dan ataƙaice ma daga kanta mahaifinta ya soma barin ƴaƴan shi mata su cigaba da karatun Boko domin dukkan yayinta daga sun taso yake aurar dasu don mahaifinta Mutum ne mai yawan zuri'a sun haura su Ashirin ƴaƴan babanta Kuma duk yadda kuke Ji da haɗin kai wallahi sun fiku dan ina mai rantsuwa da Allah inda sun san halin da take ciki agidannan da tuni maganar rabuwar Aliyu da ita ta tabbata Tuni har anyi an gama.................
Sabida mahaifinta babu ruwan shi da Kuɗin suruki in kuna jin ana maganar dattijo to wannan Mutumin dattijo ne na asali mutum ne mai dattako da Gudun duniya kaifi ɗaya mai magana ɗaya! In zaku tuna kwanakin baya akwai wani ƙazafi da akaiwa Aliyu a gidan wata radio! to wannan labari ita fatima ita ce ta jagoranci yaɗa shi sabida yadda mai gidan radi'on yayi mata Kurarin ze koreta in bata yaɗa labarin ba ita Kuma lokacin ana gabda sanya ranar Bikinta tana Buƙatar abin da zatai don hidimar Bikinta sannan mafi ƙarfin yaɗa labarin akwai rashin sanin Illar hakan a hukunce da kuma doka kasancewar ta farin Shiga a wannan harkar Bayan labarin ya bazu Aliyu ya sakani na nemo masa shugaban wannan tasha wanda har takai su gayin shari'a sedai abin da ya bani mamaki Daya ce na nemo masa yarinyar datai labarin amaimakon yaje mata da sigar Ɗaukar doka akanta a,a se yaje mata da sigar Soyayya nidai a yadda yace Min ze aure ta ne dan ya Ƙuntata mata kamar yadda tai jagoranci wajan ɓata masa suna acikin al'umma sedai Shi Allah yadda kake zaton shi ya wuce nan Allah bai ƙaddara hakan ba seya ƙaddara soyayyar gaske azuciyar Aliyu akan wannan yarinya wadda Lokacin da yaje mata akwai ɗan abokin mahaifinta wanda yake sonta yake mata hidima wanda akai magana da mahaifinta da nasa akan Ze kawo mata Kuɗin aure sedai zuwan Aliyu wajanta ya tarwatsa wannan magana yarinyar ta kafe ita se dai Aliyu Abin da ze baku mamaki yadda bata san Ko shi waye ba amman ta kafe tace ita shi zata aura wanda hakan ne ya fusata mahaifinta har yace wa Aliyu koya turo ya ɗaura Musu aure koya bada ita sadaka wannan tasa a daren Aliyu ya je ga ƙannen mahaifin sa washe gari suka amsar mai auren fatima a wajan mahaifinta wanda Ni ma ina cikin shedun wannan ɗaurin aure nasu Kuma nina ɗauko ta daga gidan su na kawo ta nan bayan Mun Ƙulla cewa Nace ƙanwata ce zatai Miki aiki mata da Miji se Allah kinga ashe har ta samu Ciki ba tare da wani ya sani ba sabida haka Ammi haƙuri zaki ki ɗauki wannan ƙaddara dan mai kyau ce Da Allah yasa akai auren sannan aka samu Cikin Inda a waje aka same shifa ita Kuma wadda kike son ta haihu da ɗan naki Allah bai yarda ta haihu dashi ba har yanzu Kinga rabon fatima ne a gaba kafin na matar tasa sannan maganar da Kike wai abin da Kike tsoro kada ya auro matar da zata rabaku kinga fatima ta ciri tuta kenan tunda har ta iya zaman watanni agidannan tana Miki biyayya dan ba da ban wannan matsala ba da Babu abin da ze faru a tsakaninku da ita Sabida haka wannan ma Izna ce ga wasu iyayen masu takura da sa ido akan sha'anin ƴaƴan su kin ga gashi nan yayi auren Ba tare da sanin ki ba Kuma kina tare da Ita a gida ɗaya har ta sami Ciki duk Allah ya rufe Miki ido ni a ganina ko wannan ma ta ishi ki bar bayin Allah'n nan su sami ƴancin kansu ki rabu dasu dan da ai bayan ranki gwara ayi kina raye ina fatan waɗannan maganganu nawa basu ɓata Miki rai ba kuma zaki saka su acikin Kundin nazari ki ƙara fahimtar cewa idan Allah ya baka babu mai hanaka in Allah ya hanaka babu mai baka Kuma Koda Allah yasa sun dawo gare mu ki gyara laifukan ki ta hanyar so tattali da kyautata wa fatima wannan shine abin da zaki dan ki wanke kanki a wajan Aliyu"

Musa yakai maganar Cikin Nutsuwa Falon tsit yayi kowa ya cika da wannan abun mamaki na auren Aliyu da fatima lallai RABO YA RANTSE se meshi wannan rabo shine silar auren su wanda Allah ya rufe idanun duk wani wanda ze kawo musu cikas akan auren su har seda rabon ya shiga sannan Allah ya bayyana da kansa...


Sautin kukan Ammi ne ya cika falon.

Autar manya ce marubuciyar......
*ƁOYAYYAR ƘAUNA*
*BA SON TA NAKE BA*
*ƊAN MAJALISSA*
*MURADIN ZUCIYA*
*ASHE ZUMA*
*TAURARO*
*KOBA SO*
*RABON WANI*
*FITAR RABO*
*DA IZZATA*
*BAƘON LAMARI*
*AUREN BARE*
*H A S K E*
*ZUMA A BAKI*
*BAƘAR FATA*
*RABO YA RANTSE*
*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*A LOVE STORY 96*
Rabo Ya Rantse
Arewabooks autarmanya

"Sadiƙ bani ruwa mai sanyi na sha Bashir ƙaro Mini ƙarfin Ac innalillahi wa'innah ilaihirraju'un Ya Allah ka farkar dani daga Baccin da nake yi Ni Amina na shiga Uku Mai yakai ni ga shiga Hurumin Ubangiji gashi nan tun kafin aje ko ina ya nunan niba komai bace"
Ammi ta faɗa lokacin sadiƙ ya kuma kawo mata ruwan Bashir ya ƙaro mata ƙarfin Ac Amman gaba ɗaya Jikinta zufa yake Se rawa hannun data riƙe Gorar ruwan yake seda ta shanye ruwan tas sannan ta sunkuyar da kanta a ƙasa ta Kuma fashewa da kuka!
"Tabbas Hurumin Ubangiji na shiga domin Shine ya haɗa waɗannan yara kuma shine yay Nufin bawa auren su kariya Kuma shine yay Nufin sanya Rabon haihuwa a tsakanin su Amman ni da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login