Showing 135001 words to 138000 words out of 150033 words
Chapter 46 - Rabo Ya Rantse Book One Complete Hausa Novel
kike sabida yanayin lalurar dake tare dake"
Banza tayi masa sabida ta Lura Namiji ne Shi mai masifar Kishin Iyalin shi dama tasan banzar daya yi mata ɗazu nada nasaba da wankin daya ga tana yiwa tsohuwar.
"To in ban mata ba yaya za'ai kenan matar data yi mana karamci me zamu saka mata dashi?"
"Zan ke bawa almajirai suna yi mata Nima ai bance wani abu ba"
Ya faɗa lokacin da yake janyota saman Cinyar shi yana cusa kanshi a wuyanta.
Idanunshi a lumshe yace
"Baki gaya min abin da zan siyo Miki ba Nasan Kema kina jin yunwa"
Ta zame.
"Ka siyo mana gawayi dan yafi sauƙi akan gas Sannan ka siyo min tsakin masara in ka tambaya za'a nuna maka wajan masu awo suna saidawa"
Yana lasar Saman Kunnenta yace.
"Bana son ki wahalar min da kanki Ki bari Allah ze Hore mana Muna siyan gas Ɗin"
Ta girgiza kai.
"Nasan kawai ƙarfin haline irin naka Ni ba wani wahala da zan sha ka siyo in Allah ya hore maka"
Bai bata amsa ba sabida yadda yake tsotsar ramin Kunnenta yana hura mata iskar cikin bakin sa.
"Fatima na ina son ki kamar raina"
Ya faɗa a birkice yana Kwantar da ita a saman katifar ya Ɗora kanshi a saman Ƙirjinta Kusan Mintin su goma a haka kafin ya Haɗe bakin shi da nata wata irin tsotsa yake yiwa laɓɓanta kamar ze cire mata su.
Bata hana shi ba sabida ta fahimci a buƙace yake da ita a hankali ya Tura hannunshi Cikin rigarta.
Subuhanallah lamarin akwai Girma sirrin nasu ne na Masoyan Juna wata irin soyayya mai cike da tsabta da Nutsuwa yake Aika mata Farha tun tana basarwa itama ta ware iya abin da ta sani take yi masa wanda ya birkice har ya Kusan tona Musu asiri sabida sumbatun sa Sun shafe lokuta suna Bawa Junan su farin ciki da Nutsuwa kafin Ya zare Ta daga Jikinsa yana shafa sumar kitson kanta.
"Allah yayi Miki albarka zumata Kullum ƙara Birkitani Kike wai meye sirrin?"
Ta cusa kanta a kirjinshi tana wasa da gashin Kirjin sabida Tuni yayi fatali da sutturar su.
Ya kuma rufeta da zanin gadon yana shafa gadon bayanta.
"Yanzu ta yaya zaka Kuma wanka?"
Yaji tambayar tata cikin Kunnen shi.
"Kema ta yaya zaki wanka?"
Dariya tayi shima dariyar yayi a hankali ya Miƙe ya gyara jikinshi ya ɗauki Bokiti yabar ɗakin ga mamakinta kuwa se gashi bayan wasu Lokuta ya dawo kanshi a jiƙe da alamun wanka yayi Yana tsaye yana Goge kanshi Itama ta fita bayan ta dawo ya shirya ze fita dole ya ce taiwa Inno Girki ta miƙa mata Yayi mata sallama ya fita daga ɗakin sabida bai saba zaman Gida ba.
Lokacin da yabar Gida miƙar hanya yayi batare daya san ina zashi ba Kawai kuma dama ƙarfin hali ne irin nashi kuɗin sa gaba ɗaya yayi siyayya dashi Babban tashin hankalin sa gawayin da tsakin data buƙata bai da Kuɗin kuma baya son ya nuna mata gazawar shi sabida ya fahimci tana Ƙarfafa masa gwiwar shine akan Komai.
"Bawan Allah lafiya ka takani baka sani ba?"
Cewar wani mutum wanda ze wuce ta kusa da Aliyu Jikin Mutumin duk ya ɓaci da baƙin Mai alamar bakani ke ne.
"Dan Allah kayi haƙuri"
Aliyu ya faɗa yana ƙoƙarin wuce Mutumin.
"Bawan Allah dan Allah ko zaka gaya Min damuwar ka dan akwai tarin mamaki ga mutum kamar ka kana tafiya kana tunani har ka takani baka sani ba kuma dai gashi ras kake"
Aliyu ya juyo tare da cewa.
"Lafiya lau Alhamdulillahi Amman kai haƙuri"
"Dan girman Allah ka gaya min Ni naji ajikina kana da damuwa Kuma musulmi ɗan uwan Musulmi ne duk da akwai nagari akwai mugu"
Cewar Mutumin.
"To ni baƙo ne ina zaune a sabon garin rigasa na fito neman abin yi"
Dariya Mutumin yayi.
"Ban yarda ba ranka ya daɗe sabida bakai kama da kalar wahala ba"
Aliyu yaɗan ware ido
"Dama wahala akwai kalar ta Tab"
Mutumin yace.
"To koma dai da wasa kake Ni sunana Dini ina zaune a hayin rigasa Kaga waccan titin Ƙaton ginin da kake gani To tsohuwar tasha ce da aka dena Lodi da ita To se Muka mayar da wajan Gareji ana gyaran motoci sannan ana sauke ƙarfen gyaran Mota wanda Kullum Mota sama da ashirin na kawo ƙarfen daga lagos Indai zakai aikin sauke ƙarfan zan maka hanya duk da basa buƙatar ma'aikata Ni bakani ke ne gyaran Mota nake aciki Muna mutunci da masu kawo ƙarafan"
Aliyu yace.
"Da gaske malam Dini?"
Dini yayi dariya.
"In sha Allah ta yuwu inna taimake ka nima Allah yayi min abin da zato bai taɓa zato ba"
Aliyu ya cika da mamaki.
Jerawa sukai da Dini bayan Dini ya karɓo abincin daya siyo ƙaton gareji ne sosai Mutane nata kaiwa da kawowa Suka shiga wajan Ogan wanda Dini ya gabatar da Aliyu abin mamaki Ogan da Mutunci ya karɓi Aliyu dan har suna wasa da Juna yace masa aikin daga ƙarfe Bakwai na safe ne zuwa shiddan yamma kullum za'a baka Dubu Goma sannan Kuma kawai dan yaga Aliyu ne yaji yana ƙaunar shi amman ba da ban haka bama sun rufe ɗaukar ma'aikata akwai riga da wando masu tambari da sunan wajan ya ɗauko ya bawa Ali yace dasu ze ke zuwa.
Aliyu yaji komai kamar a mafarki yayita Godiya lallai Duniya babu tabbas yau Shine da aka ce za'a ke bawa dubu Goma yaji kamar an saka shi acikin aljanna wanda shi kafin faruwar hakan yana iya bawa Mutum kyautar Da se Mutum ya gigice da ita ma'aikatan sa nawa ne suke cin abinci a ƙasan sa
Bayan sun Rabu da ogan Godiya yayi tayiwa Dini har Dini yace godiyar ta isa haka Kayan a hannun shi ya tawo Gida gaba ɗaya mamaki da al'ajabin wannan alkairi daya haɗu dashi ya sanyaya masa Jikin sa
Kayan kawai ya aje ya fita masallacin sallar la'asar sabida Lokacin daya zo farha bata ɗakin Bayan ya dawo ya tarar da ita ta shigo.
Se ɗaga kayan daya zube a saman katifa take tana kallo.
Bayan yayi mata sallama yace.
"Ina kika shiga nazo bakya ɗaki Nifa bani son yawo"
Tayi Murmushi.
"Naje kaiwa Inno Shinkafar dana dafa mata ne tana ta Godiya"
Ya nemi guri ya zauna.
"Wannan kayan fa na Menene?"
Cewar farha cikin sigar tambayar shi........*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*RABO YA RANTSE 101*
kwanciya yayi a saman katifa ya tallafe kanshi da hannunshi yana kallon rufin ɗakin.
"Kana jina ina maka magana kai Min shuru shikenan"
Ta faɗa cikin rashin Jin daɗin yadda yake yi mata shuru wani bin idan tana yi masa magana.
"Fatimah nifa wani lokacin bana son yawan magana kaina har ciwo yake min in ana magana sosai Ki haƙuri Har na huta" ya faɗa a hankali Tashi tayi zata fita daga ɗakin ya Damƙo mata hannunta, "Ni ka cikani mai zan yi maka bayan na dameka da surutu"
Ta faɗa hawaye na zubo mata daga cikin idanunta.
"Subuhannallahi Why are you crying? Fatima, after I was with you, stop crying. I don't want you to be quiet" ya faɗa yana sa tafin hannunshi yana cire mata hawayen nata Kukan take sosai "Tausayin kaina nake" ta faɗa cikin kuka da sauri kuma a ruɗe yace "Kamar yaya tausayin kanki wani abun ke damun ki?" ta girgiza kanta "Idan banyi hira dakai ba da wa zanyi daga maka magana kace kanka na ciwo in ana magana" ta faɗa muryarta na shaƙewa ya marairaice tare da cewa "Bazan kuma faɗin haka ba Me kike so nace yanzu?" ta kalle shi da gaske yake gaya mata maganar Shi haka halittar shi take Mutum ne marar yawan son magana.
Ta ɗan matsa daga kusa dashi.
"A,a shikenan kawai a bar maganar" Yace "Fushi kikai dani ba kyau Saurin fushi" "Niba fushi nake dakai ba to mai kayi min"
Ya gyara zaman shi "Fita nayi Neman abun yi kinga kina da Juna biyu Dole akwai abubuwan Buƙata ga asibiti da zaki fara zuwa ina son In kaiki ganin Likita dan a duba Lafiyar Babynmu Kinsan abin da ya bani mamaki?" ta girgiza kai tana tsira masa idanunta.
Labarin dukkan yadda sukai da Dini da kuma Ogan tashar Ya bata ya ƙare da cewa "Gaskiya abin ya bani mamaki yadda Komai yake zuwa mana cikin sauƙi haka ɗan sauyin rayuwar Da muka samu kaɗan Ne"
Farha tayi Murmushi tace.
"Ai tunda ka ji ƙan Al'umma kai ma Allah zeji ƙanka sannan kuma Ka saka ɗumbin Mutane a farin ciki Ko kasan Allah yana son bawa ya saka bayin sa a farin ciki Ni dama naji ajikina Allah baze tozarta kaba"
Ya zuba mata ido.
"Allah yasa mudace"
Ya faɗa yana tashi lokacin ana kiran sallar magariba.
Ya shiga tattare hannun rigar shi.
"Bari nayi alwala"
Ta tashi da sauri ta ɗauki Buta ta cika masa da ruwa sannan ta komo ɗaki ta Ɗebi gishiri ta shiga bayin ta barbaɗa ta kora ruwa sannan takai masa Butar bayin
Ta dawo lokacin ze fito daga ɗakin.
"Na kai maka Butar Bayin"
"Nagode" ya faɗa yana fita daga ɗakin Ya Shiga bayin yayi abin da zeyi ya Nufi masallaci Da gaske bamai son maganar bane ta Lura haka yanayin sa yake se Dole yake mata magana doguwa.
Bayan tayo alwala tai sallah tayi azkar sabuwar Fitilar Batir daya zo da ita ɗazu Cikin kaya ta Buɗe ta kunna Ta fita waje da gas Ruwan Shayi ta ɗora masa tasan baya cin abincin mai nauyi da daddare kamar yadda yace mata Sauran indomie ɗin ɗazu Kuma ta ɗumama farar sauran Shinkafar data dafawa Inno ta ɗumama taci da ƙyar ta Kammala Komai ta shiga ɗaki Tayi sallar Isha'i bayan sallar Isha ya dawo tai masa sannu ta gabatar masa da tea ɗin da sauran Indomie Ɗin Tea ɗin ma kawai yasha yace ya Ƙoshi Fita tayi ɗakin shafa ta Miƙa mata Indomie tace ta bawa yara shafa taita Godiya har Mijin shafar ma seda ya Leƙo yace angode farha ta juya ɗaki Lokacin harya Cire kayan shi ma daga shi se Singlet da Gajeran wando yana kwance Ya lumshe idanun shi amman ba bacci yake ba Rage kayanta tayi itama ta raɓa Gefen shi Nan da nan bacci ya ɗebe su naji ya wanda basu sami damar yin shiba.
*KANO*
"Nidai ranka ya daɗe so nake ka bani ɗaurin bakin Mijina sabida dukkan abin da nake dan shi nake dan ya sami ƴan cin kanshi amman sam bai gano ba sannan Shi ma ƙanin Mijin nawa Ina son ai Masa Haɗaɗɗiyar Mallaka wadda zeji kaf Duniya ba wadda yake so sama da Jamila ta, Kaga in ya aure ta Dukkan Komai nashi ya dawo ƙasan Mu Inda hali shima a ɗaure masa bakin sa"
Sakina Kenan Gurfane a gaban tsohon Bokan ta wanda ta yarda shi bayan ta sami sabo wanda take waya dashi rannan da daddare ganin aikin sa bai mata yadda take soba yasa yau ta dawo wajan tsohonta nada wanda ta taɓa zuwa wajan sa amman bai taɓa mata aiki ba ta sauya waje se yau suka dawo ita da jamilar ta.
Ya janyo madubi ya zuba ƙasa akai ya fara zanawa yana bajewa.
"Mijin ki ze mallaku Zan baki baƙar laya wadda zaki sami sabuwar gawa wadda ba'ajima da Binnewa ba ki cusa a bakin ta yadda wannan gawa ta Mutu haka bakin sa ze Mutu Se yadda kikai dashi"
Ya ƙara baje wata ƙasar kana yace.
"Bana ganin Komai a tare da ƙanin Mijinki se haske Kwata kwata taurarin sa basa kawo bayani se haske kawai Gaskiya aikin sa yafi ƙarfina Ke Bama zan Ɓoye Miki ba Duk wanda yace Miki ze iya yi Miki aiki akan shi ƙarya yake Kuɗin ki kawai zeci bawai asiri bane baya kama shi a,a Wani irin Murɗaɗɗan Mutum ne mai taurin kai da kafiya uwa uba addini ya ratsa shi Da wuya aiki ya Huda shi nan Kusa A lissafin masana taurari ma za'a iya kai wa shekara hamsin ana masa asiri amman bai huda Jikin sa ba wannan shine gaskiyar Bincike na amman In kina Musu Kije wajan wani ki tambaya"
Sakina ta share zufa tare da cewa
"Ranka ya daɗe Nafi shekara biyar ina aiki akan sa da matar shi"
Da sauri ya ɗaga mata hannu yana zana ƙasar sa.
"Kin san kaf Bincike babu wanda yakai na ƙasa gani! To wallahi waɗanda kika kaiwa Kuɗin ki akan shi sun cuce ki dan babu wani abu naki a tare da wannan Mutumin matar shi Kuma ɓarewar Cikin Jikinta ya samo nasaba ne da yawan Bin malamai ita ma da suke Yi bata sani ba sheɗanun da suke turawa surukarta akan suyi aiki akanta sune suke Shiga Jikinta suna lalata mata Cikin da take samu yanzu haka mahaifarta ta fara saki In batai wasa ba ma Zata iya samun matsala"
Sakina tai wata zabura tare da gyara zama sosai
"Ban gane ba kai min yadda zan fahimta?"
Yace mata "Bani sunan matar Ƙanin Mijin naki" sakina ta gaya masa ya Cigaba da zana ƙasa yana gogewa har yakai Minti ashirin a haka.
Sannan yace.
"Na bincike ta tas Itama ai ba don Allah ta auri ƙanin mijin naki ba, mahaifiyarta bata ƙaunar surukarku sabida manufar ma ta tarwatsa farin cikin surukarku ta shiga ta fita ta haɗa auren ƴarta da ƙanin Mijinki Kullum faɗi tashin su akan Su kawar da surukarku suke sabida ana musu bincike ana gaya musu surukarku Ke Ɓarar da cikin ƴarta to basu sani ba sheɗanun da suke aiki dasu sune In suka raɓi Surukarku da ƙanin Mijinki In basu sami nasara ba sabida tsarkin dake tare da surukarku da ƙanin Mijinki to sesu Huce takaicin su ajikin ita matar ƙanin Mijin naki wadda a ƙasan mararta suke dira su lalata ɗan tayin Cikin Jikinta su sakar mata Jini ana ta aikin banza a asibiti ne amman ga ainihin inda matsalar take tattare yanzu haka mahaifarta ta fara gajiya ko wani lokaci zata iya fuskantar matsala"
Sakina tai Huci tare da cewa.
"Lallai dara taci Gida wato aljanun da suke aiki dasu don su Shiga Jikin Aliyu Ko Ammi in an turo su Jikin su Ammin basu sami Ƙofar shiga ba sabida tsarkin dasu ammin ke tare dashi wato se su Huce ajikin Mami su ɓarar da Cikinta su lalata shi kenan?"
Ya jinjina kai.
"Kinsan aisu sheɗanu haka suke sam basu da gwani zafin takaicin Raɓar da sukai Jiki mai tsarki Ƙonewar da sukai Shine suke Huce haushin ajikin Ita yarinyar"
"To sun jima suna Aiki da Sheɗanun Kenan?" cewar sakina.
"Ita dai surukarki tun farkon auren ne da suka Neme ta asirin ya Huda ta amman yanzu kam jikinta akwai tsarin addu'a duk abin da suke baya tasiri gaskiya Kuma ita a yanzu ma abin da yasa bata son ɗan nata yayi aure sabida sharrin matan zamanin nan ba don wata manufa ba sedai ana zaton wuta a maƙera seta Koma masaƙa labarin tane ya faɗo nan"
Ya faɗa yana dariya.
Sakina ta tsorata dasu mami ashe suma a tafe suke.
"To ni yanzu kace Ba abin da ze tasiri a jikin ƙanin Mijina to meye amfanin na ɗaure bakin Mijina kuma yaya batun auren shi da jamila?"
Ya cigaba da binciken sa.
ya ɗago tare da cewa.
"Idan kika ɗaure bakin Mijinki zaki sami Haɗin kanshi ta yadda zaki tarwatsa Komai na ƙanin Mijin naki sabida Ƙanin nashi ya bashi yarda sosai Mijin ne ze zama garkuwarki Duk dukiyar ƙanin Mijin taki dake wajan Mijin ki seku tattare ku hana shi In ma kika ɗaure bakin Mijin baki da buƙatar auren ƙanin Mijin naki da ƙanwarki Sakina nasan ki Muguwa ce Ke ita ƙanwar taki ai ba don Allah kike son ta auri ƙanin Mijin naki ba dan dai kawai Ta samo Muku dukiya ne" da sauri sakina tai masa Inkiya da hannunta murya can ƙasa tace "Rufa Min asiri ta tashi ta fita tana waya kar taji abin da kake faɗa ka ɓatan aiki"
Yayi Murmushi.
"To mubar batun auren su mu gama da wannan ɗaurin bakin"
Ta langwaɓar dakai..
"To yanzu ina zan sami gawa?"
Yayi dariya.
"Gaskiya da wannan don yanzu yawanci maƙabartu an saka Masu gadi sabida Irinku masu sakawa gawa laya da Kuma masu yankar sassan Jikin gawa shiyasa aka saka tsaro sosai"
Sakina tai jimmm.
"To ko biya zanyi a saka"
Ya girgiza kai "Gaskiya wannan aikin naki ne ba'a buƙatar hannun kowa"
Sakina tai Murmushi.
"Akan biyan buƙatata ba abin da ba zan iya yiba Sabida haka Nina san yadda zanyi Duk yadda zanyi danna sami gawa zanyi" adaidai nan kuma jamila ta gama wayar ta shigo ɗakin Lokacin sakina ta ɗauki jakarta ta Buɗe ta zuba masa Kuɗi a gaban shi sukai sallama suka yo Gida A gidan su suka kwana sabida dare yayi washe gari sakina ta sako yaranta gaba suka dawo gidan Ammi tun daga falon farko ta gano gidan babu lafiya jakarta ta aje tare da nufar ɗakin Ammi sabida Ko ina na gidan tsit hatta Kayan kallo suna kashe sallama tayi ta shiga ɗakin a hankali Ammi ta miƙe daga kwanciyar da tayi tana amsawa sakina sallamar tata.
Cikin ladabi sakina take gaishe da Ammi ta karyar da kanta tana cewa.
"Ammi waya ce ta gigita aka Min Jiya maman mu bata da lafiya, Shine Muka tafi ko sallama bamu yi Muku ba"
Ammi tace.
"Allah ya bata lafiya jikin girma ne se a hankali ai"
Shuru ɗakin yayi Lokacin sadiƙ ya shigo Cikin shirin fita kamfanin Aliyu dan ya gudanar da abin da ze dan cikin satinan yake son su wuce lagos sabida ya mayar da hankalin sa kan Kula da kamfanin Aliyu nacan.
Sadiƙ ya kalli Ammi cikin kulawa.
"Ammi har yanzu baki break fast ba dan Allah Ki barwa Allah Komai In sha Allahu Yana cikin Ƙoshin lafiya"
Kamar jira Ammi take seta fashe da kuka.
"Sadiƙ ta yaya hankalina ze kwanta tun Jiya nake Kiran Numbobin baba duka a kashe"
Sadiƙ yace.
"Kema ammi kina da maido da magana baya kin manta ya bawa Musa wayar tashi"
Ta share hawayenta "Ba Numbobin nasa da yawa ba ai wayar shi ba ɗaya bace ya Allah kasa Babana yana cikin Ƙoshin lafiya"
Sadiƙ ya kwantar da Murya yana bawa Ammi haƙuri har dai ta dena Kukan.
"Abban su baka ganni bane?"
Cewar sakina sadiƙ bai Ko dubi Inda take ba yasa kai zebar ɗakin
"Sadiƙ dawo Mahaifiyarta ce babu lafiya shine ta fita bata gaya maka ba kai mata alfarma mahaifi ya wuce wasa"
Cewar Ammi dan ita yanzu bata son ɓacin ran kowa tsoron Tafiyar Aliyu ma kaɗai bala'i ne a gareta.
Sadiƙ ya dawo jikinsa a