Showing 1 words to 3000 words out of 124441 words

Chapter 1 - Kazar Kwanci Hausa Novel Complete

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GJCgZzbBrsV8mesM7Zwyzf


*KAZAR KWANCI...*

©Rufaida Umar

*Free pages*


*PAID BOOK*


_*Haɗakar fiƙrah littattafai uku ne na marubuta👇🏽*_
Rufaida Umar
👉🏽KAZAR KWANCI.
Fareeda Abdallah
👉🏽RANAR NAKA.
Jeeddah Lawals
👉🏽NADIA
_Labarai ne guda uku da marubutan suka yi haɗakar Fiƙrah domin daɗaɗa zukatan masu karatu😍 Domin samun damar karanta labaran duka uku za a biya N1500 ta wannan asusun bankin👉🏽_
5407827015
FCMB
Farida Abdullahi
_Idan kuma guda ɗaya ake so a karanta daga cikin ukun za a biya N700, guda biyu kuma N1200, sai a tura screenshort na shaidar an biya ta ɗaya daga cikin waɗannan lambobi_
+2349034973645
+2347039080978
+2349030312094
*Masu buƙatar a tallata musu hajojinsu a ɗaya ko biyu ko duka littattafan sai su tuntuɓi wannan lambar 👉🏽 +2347039080978, Sai kun zo😍*


*1)*


" Mairamu! Mairamu!!"

Matar dake zaune saman kujera ƴar tsugunno dafe da kumatu yayinda ɗaya hannun ke riƙe da buta ta yi firgigit ta farka daga kogin tunanin da ta lula har ba ta san da wanzuwar mutum ba sai jin kiran da ta yi a can cikin kanta. Ta dube shi sai kuma ta yi saurin ajiye butar ta miƙe tana ɗan ɗingisa ƙafarta da ta yi tsami dalilin jimawar da ta yi a zaune ta miƙa hannu domin karɓar ledar da ya shigo da ita tana fadin.

"Sannu da zuwa Malam, yanzu ka ke tafe?"

Wanda ta kira da Malam cike da damuwa ya girgiza kai, madadin ya miƙa mata ledar sai ya riƙe ya soma magana a tausashe.

"Tun yaushe na shigo nake ta sallama ba ki amsamin ba, anya kuwa Mairamu rayuwa za ta tafi a haka? Ki rufamin asiri naji da damuwa ɗaya kar ki haifarmana da wata ki kwanta ciwo."

Kanta a ƙasa ta share kwallar da ya zubo mata.

"Toh Malam. In sha Allahu zan kiyaye."

Daga haka ta sa hannu ta karɓi ledar ta kai masa ɗaki sannan ta koma ta zubo ruwa a kwanon tasa ta ajiye mishi a saman ɗan teburin dake falonsa. Shi kuwa koda ya shigo falon kai tsaye ɗakinsa ya shiga ya faɗa banɗaki, kafin ya fito ta koma tsakar gidan ta yi alwala don tuni an soma kiraye-kirayen sallar Magriba. Shi din ma yana fitowa daga dakin ya nufi hanyar fita zuwa masallaci sai ya dakata ta hanyar juyowa ya kalle ta.

"Ki kira Hafsatu ki ce maza ta sa a maido yaran nan gida."

Ta dube shi tamkar za ta yi magana sai kuma ta hadiye ta amsa da toh. Koda ya fita sai da ta gabatar da sallah ta ɗan yi addu'o'inta da ta saba kafin ta dauki waya ta yiwa Hafsatu flashing. Ko mintuna uku ba su cika ba ta biyo bayan kiran. Sai da suka gaisa ta ce.

"Babanku yace ki sa a kawo yaran nan gida."

Daga can Hafsatu ta amsa.

"Inna ba za'a bari zuwa gobe ba sai na kawo su da kaina? Yanayin Hajara fa har yanzu babu sauki sai ta wuni ba ci ba sha sai aikin kuka."

Inna Mairamu ta numfasa, ta sani dole Hajara ta shiga damuwa tsantsa ta yadda zai wahala lokaci guda ace komai ya wuce a wajenta. Ace har sau hudu ana neman aurenka a fasa? Sati biyu kenan da yi amma har lokacin ba a bar gulma da kuma zunɗensu a unguwa ba. Wasu su ce asiri ne kishiyar uwarta (Inna Mairamu) ta yi mata shi ne dalilin da yasa hakan ke faruwa don ba ita ta haife ta ba. Yayinda wasu ke Allah wadai da masu halin munana zato ga Inna Mairamu da suka yiwa shaidar arziki.

"Hello, Inna kina jina?"

Sai a lokacin ta dawo hayyacinta.

"Ina jinki Hafsatu, hakanan za ta dawo gidan tunda Babanku ya yi umarnin. Zan dai roƙi alfamar ya bari zuwa goben ki taho da su."

"Shikenan Inna, Allah ya nuna mana."

Inna ta amsa da amin kafin su yi sallama, kaf yaran Malam a mata babu wata da ta ɗauke ta tamkar uwa irin Hafsatu. Ita ce babbar ɗiyarsa a mata idan ka cire manyan samarin yaransa su huɗu wadanda su ma a gidan ta tarar da su. Gaba daya yaran Malam su tara ne cif, biyu ne kaɗai yaranta. Hashimu, Sadik (wanda suke kira da Baba Habu), Mustafa, Zakari, Hafsatu, Safiyya da Hajara gaba ɗaya mahaifiyarsu ɗaya sannan mahaifiyarsu ta kasance yar uwar Malam, wannan yasa dangin Malam da dangin mahaifiyartasu a dunkule suke wuri guda, sai bayan rasuwarta ne Malam ya auri Inna Mairamu, dangin Malam kaɗan a cikinsu ne ke sonta, hakanan yaran Malam din, Hafsatu ce kusan tasu ta zo ɗaya sai ko Zakari ɗan baruwansa, amma sauran komai Inna Mairamu ta yi ba ta taɓa wanke kanta a wajensu.
Haka ta dinga hakurin zama har ta haifi yaranta biyu duka mata.

https://chat.whatsapp.com/GJCgZzbBrsV8mesM7Zwyzf


*PAID BOOK*

*KAZAR KWANCI*


*Free pages*

_*Haɗakar fiƙrah littattafai uku ne na marubuta👇🏽*_
Rufaida Umar
👉🏽KAZAR KWANCI.
Fareeda Abdallah
👉🏽RANAR NAKA.
Jeeddah Lawals
👉🏽NADIA
_Labarai ne guda uku da marubutan suka yi haɗakar Fiƙrah domin daɗaɗa zukatan masu karatu😍 Domin samun damar karanta labaran duka uku za a biya N1500 ta wannan asusun bankin👉🏽_
5407827015
FCMB
Farida Abdullahi
_Idan kuma guda ɗaya ake so a karanta daga cikin ukun za a biya N700, guda biyu kuma N1200, sai a tura screenshort na shaidar an biya ta ɗaya daga cikin waɗannan lambobi_
+2349034973645
+2347039080978
+2349030312094
*Masu buƙatar a tallata musu hajojinsu a ɗaya ko biyu ko duka littattafan sai su tuntuɓi wannan lambar 👉🏽 +2347039080978, Sai kun zo😍*

02

Malam ba shi da ra'ayin hana yara karatu, shi ɗinma tsohon Malamin makarantar gwamnati ne da a yanzu ya yi ritaya ya buɗa shago babba na siyar da litattafan makaranta iri-iri a kasuwar sabon gari. A yaransa mata Hafsatu da Safiyya duka koyarwa suke yi sai ko Hajara da ta fi su basira da son karatun wacce tun tana ƙanƙanuwa take da ra'ayin zama Likita.
Lokacin da mahaifiyarsu ta rasu tana aji na uku a ƙaramar sakandire.
Bayan auren Malam da Inna Mairamu kuwa, fitsara iri-iri ta ke yi mata.
A wasu lokutan Malam bai fiye tsawatarwa Hajara ba saboda a cewarsa tausayi take ba shi don ba karamin shagwabar da ita Mahaifiyarta ta yi ba sai gashinan lokaci ɗaya mutuwa ta yi mata yankan kauna. Komai take so yana kokarin yi mata, Inna Mairamu ma duk iyaka kokarin da take na kyautata mata Hajara ba ta gani, asalima komai ta yi mata sai tace ai dama dukiyar mahaifinta ne ita ba ta da kudin da za ta kyautata mata da shi tunda ba ta aikin komai kuma ko boko ba ta je ba asalima tun a can Nanny ce a makarantar da Malam ya koyar a baya kafin ya yi ritaya kuma ya zo ya aure ta. Abin yakan yiwa Inna Mairamu ciwo matuƙa amma hakanan take dannewa. Mace ce marar son hayaniya ko kadan, dama can an santa da hakuri, rasuwar mijinta na farko ne ya sanya ta zawarci da kananan shekaru saboda auren wuri aka yi mata. Ba ta taɓa haihuwa da tsohon mijinta ba sai bayan da ta auri Malam. Tashin farko ta haifi ɗiya mace, ta kuma roƙi alfamar Malam akan ya sanya sunan mahaifiyarta wacce ta ke tsananin so kuma ta rasu ta bar ta tun tana ƴar shekaru goma. Malam ya yi mata wannan karar ya sanyawa ɗiyar suna Sadiya. Ta ji dadi kwarai, wanda hakan ba ƙaramin baƙanta ran su Hajara ya yi ba don sun ci burin ace sunan mahaifiyarsu ya mayar, ta tsani Sadiya tsana ba kaɗan ba. Inna ta shanye abubuwa da yawa akan Sadiya. Sai ya kasance masu so da kaunar Sadiya a yaran Malam, Zakari ne kawai sai ko Hafsatu. Su Mustafa dama babu abin da ya yi musu zafi da Innar don sai ta dau dogon lokaci ba ta sanya su a idanu ba. Idan sun so ganin mahaifinsu, kodai su shiga dakinsa ta kofar waje, ko kuma su bishi can kasuwa. Safiyya kuwa duk radda ta zo gidan sai ta yadawa Inna baƙaƙen maganganu ita da Hajara sannan take tafiya. Sadiya tana da shekara uku a duniya, Inna ta ƙara haihuwar ɗiya mace wacce ta ci sunan mahaifiyar su Hajara, Asma'u suke kiranta da Husna.
Darajar wannan sunan yasa yaran suke ɗan tattalin Husnar ba sa nuna mata ƙyama. Hakanan Hajara, duk iskancin da take yi ga Inna Mairamu da Sadiya ba ta yinsa ga Husna, sai ya kasance ita da ɗiyarta ko tsawatar mata ta yi akan wata ɓarnar da ta aikata sai Hajara ta ji haushi har ma ta sanar da Malam wai saboda an saka sunan mahaifiyarta ne yasa Inna Mairamu ta tsani Husna take cin zalinta.
Akan Husna, Inna Mairamu ta sha yin faɗa da Malam domin shima irin kaunar da yake yiwa tsohuwar matarsa sai ya tattara shi ya ɗora akan Husna, komai take so haka yake yi mata ga yayyunta wadanda su ma suka shagwaɓa ta amma fa ba sa ga maciji da uwarta.
https://chat.whatsapp.com/GJCgZzbBrsV8mesM7Zwyzf



*KAZAR KWANCI...*

*PAID BOOK*

03

*Free pages*

_*Haɗakar fiƙrah littattafai uku ne na marubuta👇🏽*_
Rufaida Umar
👉🏽KAZAR KWANCI.
Fareeda Abdallah
👉🏽RANAR NAKA.
Jeeddah Lawals
👉🏽NADIA
_Labarai ne guda uku da marubutan suka yi haɗakar Fiƙrah domin daɗaɗa zukatan masu karatu😍 Domin samun damar karanta labaran duka uku za a biya N1500 ta wannan asusun bankin👉🏽_
5407827015
FCMB
Farida Abdullahi
_Idan kuma guda ɗaya ake so a karanta daga cikin ukun za a biya N700, guda biyu kuma N1200, sai a tura screenshort na shaidar an biya ta ɗaya daga cikin waɗannan lambobi_
+2349034973645
+2347039080978
+2349030312094
*Masu buƙatar a tallata musu hajojinsu a ɗaya ko biyu ko duka littattafan sai su tuntuɓi wannan lambar 👉🏽 +2347039080978, Sai kun zo😍*


***

Inda dai ta gode Allah, dalilin kaunar da Husna ke nunawa ga yayarta a wasu lokutan yasa Sadiya sai ta ci albarkacinta a wajen Hajara ta ke ɗan ragwanta mata. Ta ce duk abinda Mominta (sunan da take kiran Husna da shi) take so, toh fa nan duniya itama tana sonsa. Amma ganin irin farin jini da Sadiya ke da shi wajen jama'a ya sanya ta ji tana ba ta haushi.
Mazan kuwa gaba dayansu sun yi aure kowanne na zaune da iyalinsa a unguwanni daban-daban. Asirinsu a rufe, babu dai wani mai arzikin a zo a gani sai dai ta ko'ina sai sam barka. Safiyya da Hafsatu ne dai suke auren masu kudin, mijin Safiyya, Barrister ne mai zaman kansa hakanan Hafsatu wanda mijinta ya kasance ɗan siyasa kuma Chairman na ƙaramar hukuma. Bai hana ta koyarwa ba amma daga baya sai ya gina mata makaranta mai kyau da tsari inda da safe ake boko, da yamma kuma ake Arabi.
Sadda Hajara ta kammala karatunta ta soma aiki a wani ƙaramin asibiti, Sadiya duka-duka shekarunta takwas a duniya ita kuwa Husna shekararta biyar. Hajara takan yi shigar da take so na matsastsun kaya ta yafa siririn gyale ta fita babu dama Inna Mairamu ta yi magana sai ta taso mata da hayaniya. Wani lokacin kuma idan ta soma yi mata fitsarar tana ganin Husna ta soma hawaye sai ta yi kwafa ta daina ta ce wai ta ci albarkacin Mommynta. A karshe Hajara sai ta soma hurewa Husna kunne tana nuna mata ai Inna Mairamu ta tsane su ne saboda uwarta ta mutu ba ita ce ta haifesu ba. A hankali yarinyar ta soma jin haushin takurar da Inna Mairamu ke nunawa Hajara, yayarta mai sonta, duk abinda ta ce tana so shi take siya ta kawo mata. Koda ta soma aiki albashinta na farko akan Husna ya ƙare, ba ta damu da Sadiya ba sai idan ta ga Husna ta nuna rashin jin dadin ba ta yiwa Sadiyar tsaraba ba sannan take yi mata, tana yi tana wurga mata kallon tsana. Babu abin da yasa ta ƙara tsanar Sadiya sai ganin da ta yi ta fi Husna kyau nesa ba kusa ba. Fara ce tas mai hanci da manyan idanu, har da dimple.

Takan cewa Husna, "Ke ba ki da wayo, Sadiya ta fiki kyau ki daina wasa da ita. Irinsu ne za kiga kowa ya fi so ya fi kauna, ke kuma sai ki ga mutane ba sa sonki."

Husna takan yi watsi da zancen abinka da yarinta, ita ba ta fahimtar ma komai, amma ta sani Sadiya ta fi ta farin jini a wajen jama'a, ba ta da wayon gane komai. Ita baƙa ce don mahaifinsu ta biyo kuma ba ta da hanci kamar na Sadiya, kusan kamanninsu daya da Husna da suka biyo mahaifinsu. Dangi ne da ba su da kyawun fuska na a zo a gani sai ko ilimi da suke tunƙaho da shi. Hakanan halittar sura daidai misali.

Inna Mairamu kuwa mace ce mai kyawun halitta kasancewarta ruwa biyu, mahaifinta asalinsa ɗan Nijar ne haifaffen Diffa kuma bafulani yayinda mahaifiyarta ta kasance bahaushiya ƴar Kano.

Dangin Malam har watsa mata habaici suke yi wai idan dai kyawu na siyan zuciyar ɗa namiji toh bai siye na Malam ba, domin har gobe ba ta maye gurbin Asma'u a zuciyarsa ba. Don Asma'u ta rayu da Malam tun ba shi da aikin yi, soyayya ce tun ta ƙuruciya. Takan yi murmushi ba ta cewa uffan, zai wahala su ce wani abin ta maida musu martani face murmushi. A zuciyarta kuwa ta yi ta kiran sunayen Allah don samun sassauci daga bacin rai da suka ɗarsa mata.

A haka rayuwar ta dinga tafiya, samarin sai su yi zuwa nawa gidan ba ta sani ba, wani lokacin daga can waje suke shiga ɗakin baƙi na Malam su gaisa da shi su fice, idan sun shigo toh fa Husna suke son gani babu mai bi ta Sadiya. Zakari kuwa babu abin da ya yi masa zafi, haka zai shiga ya sha hira da Inna Mairamu har da dariya.

Kudaden da Hajara ke samu kusan kaso hamsin a ciki, akan Husna yake ƙarewa, ita a lallai sai yarinyar ta zama ƴar gayun da za ta ketare Sadiya a komai koda nan gaba. Kayan Husna kuwa kusan rabinsu Hajara ce ta yi mata, Sadiya takan ci albarkacinta. Amma da ta lura yarinyar tana fin Husna kyau a kayan sai ta koma siya mata wanda bai kai na Husnar daraja ba. Inna Mairamu tana shiga damuwa sosai ganin irin bambancin da Hajara ke haddasawa tsakanin yaranta, har ta kai Husna soma jin tsanar Sadiyar itama, wannan dalili yasa ta zaunar da yarannata su biyu ta ja musu kunne da nunamusu duk abu daya ne su. Ashe Hajara na ji, ta kuwa saka kuka da Malam ya zo ta sanar da shi wai Inna Mairamu ta kama su Husna tana musu iyaka da ita da sauran yayyunta, tana zuga su akan su din ita ce ta haife su, su kuna ƴan uba ne a wajensu. Abin mamaki koda Malam ya nemi ba'asi a bakin Husna sai ta ce eh hakane. Sadiya kuma ta ce ba haka Innar ta ce ba, Malam sosai ransa ya ɓaci, ya yiwa Inna tas, ya ce babu wanda ya isa ya raba masa kan yara. Har da cewa shi yasan da ace Asma'u na raye ba za ta taɓa bambanta yaranta da na Innar ba.
https://chat.whatsapp.com/GJCgZzbBrsV8mesM7Zwyzf



*KAZAR KWANCI...*


*PAID BOOK*

*Free pages*

*04*

_*Haɗakar fiƙrah littattafai uku ne na marubuta👇🏽*_
Rufaida Umar
👉🏽KAZAR KWANCI.
Fareeda Abdallah
👉🏽RANAR NAKA.
Jeeddah Lawals
👉🏽NADIA
_Labarai ne guda uku da marubutan suka yi haɗakar Fiƙrah domin daɗaɗa zukatan masu karatu😍 Domin samun damar karanta labaran duka uku za a biya N1500 ta wannan asusun bankin👉🏽_
5407827015
FCMB
Farida Abdullahi
_Idan kuma guda ɗaya ake so a karanta daga cikin ukun za a biya N700, guda biyu kuma N1200, sai a tura screenshort na shaidar an biya ta ɗaya daga cikin waɗannan lambobi_
+2349034973645
+2347039080978
+2349030312094
*Masu buƙatar a tallata musu hajojinsu a ɗaya ko biyu ko duka littattafan sai su tuntuɓi wannan lambar 👉🏽 +2347039080978, Sai kun zo😍*

***

Ranar Inna ta zubda hawayen bakin ciki, ta kuma ba shi hakuri. Daga nan ta zuba idanu kawai sai ta koma kai wa Allah kukanta.

Sanadin fasa auren Hajara da ake yi ya janyowa Inna baƙin jini a wurin yaran mijinnata da ma danginsu da makwafta. Wannan shi ne ainahin damuwar da Inna Mairamu ke ciki, jikinta ya yi sanyi, ta sani Allah kaɗai zai fidda ta daga zargin jama'a.

Tana nan zaune tana ɗan jan carbi tana tunane-tunane har Malam ya dawo daga masallaci. Ta sanar da shi alfarmar da Hafsatu ta roƙa ya amsa da toh.

Washegari da safe bayan Malam ya kammala kari ya fita babu jimawa wurin ƙarfe sha ɗaya Inna Mairamu na maida kayan wanke-wanken da ta yi kicin sai ga sallamar su. Sadiya ce a gaba, ta karasa da sauri ta rungume uwarta gami da sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi, ita kaɗai ta san a kwanakin nan irin musgunawar da Hajara ta yiwa rayuwarta a gidan Anti Hafsatu kai kace ita ce silar da aka fasa auren nan. Ba don ma Anti Hafsatun na kwaɓar Hajara ba da ba ta san ina abin zai tsaya ba. Koda za su taho daga ta taka ƙafar Husna ba tare da ta kula ba Hajara ta kwashe ta da wani wawan mari a fuska har sai da suka kusan faɗa da Anti Hafsatu. Haka suka shiga motar kowanne ransa babu dadi har suka ƙaraso gidan.

Inna Mairamu ta ɗago Sadiya daga jikinta tana ɗan murmushin yaƙe duk kuwa da shatin yatsun da ta gani kwance gefen fuskarta. Abinka da farar fata har wurin ya yi ja ga idanunta su ma kana yin kallo ɗaya za ka fahimci ta ci kuka.

"Ke kuma sai ka ce wacce ta shekara ba ta nan? Ni matsa can ki bani wuri."

Kafin ta yi magana sai ga Husna ta shigo babu ko sallama tana turo baki, hannunta riƙe da jakar kayanta.

"Ke Sadiya wa kika mayar ƴar aikinki? Wallahi ki koma ki shigo da jakar ki don ni ba baiwarki bace."

Sadiya itama ta juyo ranta a ɓace, wannan raini da Husna ta yi mata yana baƙanta ranta ainun. Ta sani dai ba laifin kowa ba ne face Hajara, ita ce ta jaza mata. Ta dubi Inna, Inna ta yi mata alamar kar ta ce komai wannan yasa ta yin ƙwafa kawai, sanadin Husnar ta sha mari wajen Hajara. Matar da take tsananin shakka tun tana ƙarama sai dai zuwa yanzu ta rage jin tsoron ba kamar a baya ba. Kawai dai ba ta iya maida mata martanin zantukan da take yi musamman ga mahaifiyarta. Tana wannan tunanin sai ga Hajara ta shigo wannan ya sa ta haɗiye abin da ta yi niyyar faɗi.

"Momina, wuce ki ajiye jakar mana. Ke karɓi ki miƙa mata ciki."

Ta furta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login