Showing 21001 words to 24000 words out of 124441 words
mota baƙa wuluk mai bakaken gilasai ta faka a gabansu, suka buɗe suka shiga. Anan ne Hajara ta cire hijabinta ta shiga kwalliya a fuskarta. Ko mayafi ba ta yafa ba. Koda ta kammala shirinta, shiru ta yi tana duban waje, tana ji ƙirjinta na faduwa don yau ta rantse koda ace budurcinta zai tafi, to fa ta shiryawa hakan, a ganinta tunda aure ya gagare ta, ai komai ma yanzun za ta iya aikata shi. Tsanar Inna na ƙara ninkuwa a zuciyarta, ta sani ita ce silar jefa ta wannan mummunan tafarkin, da ace ta bar ta ta yi aure da hakan duk bai faru ba. Watakila da yaranta biyu. Mace da namijin da zasu ci sunan iyayenta mafi soyuwa a ranta. Ta tuno da Sadiya, ƙwafa ta yi. Ta rantse sai ta tarwatsa rayuwar Sadiya ko ta wace hanya ce yanda Innarta ta tarwatsa nata. Sai da Azeema ta taɓa ta tana magana kafin ta yi firgigit ta dawo hayyacinta. Ita da Blessing da Waleeda kadai ne masu aikin jinya a asibiti, Azeema kawar Waleeda ce mai zaman kanta. Asalinta ma ƴar Kaduna ce ta zo ta kama haya a Kano saboda iyayenta sun yafe ta adalilin barikin da take yi na gaske iyakar karfinta da jiki. Wannan ta sanya suka hade kawunansu suna cin karensu babu babbaka. Nusaiba kuwa wacce ta samu aiki a babban asibitin gwamnatin da ke can wajen garin Kano ya yi sanadin ja baya da alaƙarsu sai ko ta waya. Kusan koyaushe sai Nusaiba ta kira ko ta taɓo ta a chat su yi hirar rayuwa. Ita ma har lokacin ba ta yi aure ba, abin da ta ga dama take yi.
Dama kullum huɗubarsu ga Hajara bai wuce ta saki jiki ta bada kai bori ya hau ba. Ita da ta san dukkan wata hanya ta tsarin iyali ai ba za ta taɓa daukar ciki ba. Kuma koda aure ne ya tashi sun ci alwashin yi mata ɗinkin da babu wani ɗa namiji da zai gane ta taɓa bariki.
Ba ta taba ji a ranta za ta dauki huɗubarsu ba sai a yanzun da ta ke jin haushin auren ma tunda ba a yarda ta yi sa ba. Har suka isa jefi-jefi take tsoma musu bakinta a hirarsu.
***
"Ba wani aiki ne mai wahala ba a wajenku ma'aikatan abin, muna buƙatar mabiyar jariri, wato mahaifar da ke tahowa tare da jarirai har guda biyar. Idan har ku ka yi mana wannan ƙoƙarin muka samu, muka kuma yi nasara kwalliya ta biya kuɗin sabulu har muka hau wannan kujerar mulkin, toh muna rantse muku sai kun zaɓi nawa ku ke da buƙata a wajenmu."
Gaba ɗaya kusan a gigice suke kallon kallo tsakaninsu, babu kamar Hajara wacce ta ji kamar ta saki fitsari a wando. Aikin tsafi da asiri? Kuma wai ita ake buƙatar saka hannunta ciki?
Ta dubi Alhazan su uku, Alhaji Nasiru, Garzali da Nuhu. Miƙewa ta yi tana girgiza kanta da ja baya har tana tuntuɓe da ɗan kamfen Waleedah da ke yashe a tsakar falon.
"A'a, a'a, babu ni a cikin wannan tafiyar. Ba zan yi ba. Zan sadaukar muku da jikina ku cigaba da yanda ku ka so, ba kuma zan tona asirinku ba. Sai dai na rantse ba za'a yi wannan harkar tsafin da ni Hajara ba!"
Daga haka ta shiga tattara kayayyakinta ta shirya tsaf, kallonta kawai suke yi babu kamar Alh Nuhu wamda ya ji hankalinsa ya yi mugun tashi, shi ne ya fara saninta a ɗiya mace, kuma shi yanda yake ji ma a ƙoƙon ransa aurenta zai yi ba zai bari ta kuɓuce masa ba don ta yi masa ɗari bisa ɗari. Miƙewa ya yi ya riko hannunta dake faman rawa, kai duka jikinta ma rawar yake yi, ta tsaya tana dubansa.
"Kar ki yi mana haka Hajara. Mun ji, mun ji ba za ki tsoma hannunki a cikin harkar nan ba. Amma ina za ki je yanzu a daren nan? Don Allah ki yi hakuri ki zauna mu kwana a nan, gobe sai ki tafi."
Hankali a tashe ta dinga girgiza kai, gaba daya ta ruɗe ta fisge hannunta, daƙyar ta yarda da batun Alh Nuhun wanda ya tsawatarwa su Alh Nasiru masu yi mata bambamin cewa ba ta isa ta fita ba tare da ta aminta da batunsu ba ko kuma su dauki mataki a kanta. Ɗaki ya ja ta ya rufe daga shi sai ita, nan ya dinga yi mata alƙawarin ba zai bari a cutar da ita ta ko'ina ba. Ita kuwa ban da uban kuma babu abin da take yi. Anan ne fa ya rantse mata shi da aure ma yake sonta. Ta dakatar da shi ta ce sam ba ta son batu na aure. Ya dai ji ta, ya kuma yi shiru amma ba don ya kyale batun auren ba. Haka ya lallaɓa har ya maimaita abin da ya yi ɗin a farkon zuwansu masaukin nasu, a karshe ya cikamata asusun banki da zunzurutun kudade har miliyan biyu, wannan ba karamin gigita Hajara suka yi ba.
"Wallahi aurenki nake son yi Hajjo. Ki yi tunani ki ban damar da zan gabatar da kaina. Na rantse maki za ki ji dadi fiye da tunaninki a zamantakewarmu. Sai kin zama cikin mata abin kwatance. Na ji labarin yanda ake fasa aurenki a bakin Waleeda, kuma hakan bai karyan zuciya ba. Ni zan aureki mu sha sha'aninmu son rai. Wancan maganar kuma da aka yi, ki bar ta a inda ki ka ji ta. Ni zan yi maganinta. Ba za'a kara sanyaki ciki ba."
A sanyaye ta gyaɗa kai alamar ta ji ta amince amma kuma ba wai don ta yi na'am da batu na auren ba. Sai dai tunda uwarta ta haife ta ba ta taɓa ganin zunzurutun kudade haka a bankinta ba. Gaba daya ya gama kashe mata jiki, wannan rayuwa ta daula da take kwadayi ta soma hasko ta cikinsa a gidan Alh Nuhu. Sai dai tana tsoron kar shi ma sai magana ta kankama a fasa. Karshe ta ce ya bata lokaci za ta yi tunani. Yace ya bada.
***
A can kuwa bayan sun keɓe su uku, Alh Nasiru rai a ɓace ya ce.
"Ka san kuwa barin yarinyar nan ba zai yiwu ba ko? Wai Nuhu mai kake so ka ce? Wato a kyale ta bayan ta san wannan sirrin namu? Yan uwanta ba su yi mana taurin kai ba saboda sun san me ke musu ciwo sai ita?"
Alh Nuhu ya yi dariya.
"Kar fa ku samu damuwa, ni zan yi wa abin tufka. Aurenta zan yi. Hakan ne za mu samu damar toshe bakinta. Wai mu da muke da Boka Gagare? Har za ku yi tunanin tonuwar asirinmu? Idan har aka rufe mata baki ta ina za ta fesar? Kuma magana ta gaskiya ni dai ta yimin, aurenta kuma zan yi."
Suka kyakyace da dariya gami da cafkewa. Sai a lokacin hankulansu ya kwanta.
"Ya za ka yi da Haj Nuriyya?" Tambayar da Alh Garzali ya jefamasa kenan.
Alh Nuhu ya shafi sanƙon dake tsakiyar kansa.
"Ai ba kanta farau ba, wannan baƙin kishin dole ta yakice shi tunda a gidan ubanta ma huɗu na gani kafin na auro ta. Kuma ni ba ni da ra'ayin haɗa mata biyu a gida ɗaya. Ita dai ta cigaba da zamanta a Lagos, wannan Amaryar ta Abuja ce."
Suka kara darawa. Ba wai nufinsa a Abuja zasu zauna ba, sai dai wata sara da maza ke yi na kiran gidan Uwargida da Lagos, na Amarya kuwa Abuja.
Da wannan suka karƙare magana bayan Alh Nuhu sun ba shi tabbacin amincewar su Blessing saboda gaba ɗaya sun ruɗar da su da kyautar dubu ɗari biyar da aka yiwa kowaccensu da sunan somin taɓi. Azeema kuwa da ba a asibiti take aiki ba ta ce ita za ta shiga wajensu a asibitin ta karɓa ta fito da su ta ajiye a hannunta.
***
©Rufaida Umar
https://chat.whatsapp.com/FQc8pWPPMQe2IE1dUoteD1
*Hajjaju kindade kina Neman inda Zaki dinga sarin kayayyaki domin kisiyar kisamu riba?😄😃... Sha kurumin ki yar uwa Maza kishiga wannan group din Mai albarka domin samun kaya masu inganci d kuma rahusa*💃💃💃
*Muna kawo kaya daga china, Lagos d kuma sauran wurare. Muna saida bags, shoes, jewery, kayan yara, sleeping dress da kuma sauransu. Kayayya kinmu a gida suke d kinsiya xa'a Miki delivery sharp sharp*🥰💃
SANNNAN GA MASU SON FARA BUSINESS BASUDA JARI ZAKU IYA REPOSTING KAYANMU KU DORA RIBARKU AKAI WATO DROPSHIPPING😍 muyi ma customers dinku delivery cikin sauki acikin Leda gari yayi zafi*🤣
*Muna aika kaya ko'ina cikin aminci d Amana*
*** *** ***
*Kazar Kwanci...*
Sadiya ke duba sakamakon jarrabawar Husna cike da takaici ganin wannan karon ma ba abin kirki ta yi ba a makaranta. Ta rasa son wasa irin na Husna, koda dai, tun sadda ta samu waya ba ta da aiki sai buga wasanni sai ko kallace-kallacen fina-finan India fassarar Hausa. Da dai sauransu.
Hannu aka saka aka fisge takardar har tana ɗan ɓantarewa. Hakan ya sanya Sadiya ɗaga kai ta dubi mai shi. Husna ce ta yi mata tsaye a kai cikin shigar riga wacce ta ɗan kamata mai tsawo har gwuiwa sai ko dogon wandon da ake wa laƙabi da fensir. Sai faman huci take yi da jefa mata wani kallo na rashin mutunci kafin ta ce.
"Kin ga ba na son irin wannan halin Sadiya! Ina ruwanki da kayana da za ki taɓa min? Aikin banza kawai, don kin ga kin ɗara kowa a ajinku da maki mai kyau shi ne ni kuma za ki buɗe min nawa sakamakon? Mtsw."
Ta karashe da jan dogon tsaki, idanunta har kumbura suka yi tsabar kukan da ta ci na wannan rashin hazaƙa da ta nuna don hatta da Antinta Hajara sai da ta ce ba ta kyauta mata ba ganin yanda take tsaye wajen koyar da ita karatu amma ta watsa mata ƙasa a ido.
"So ki ke yi ƴan uba su yi mana dariya Momina, gaskiya idan wata shekarar ba ki yi abin da ya dace ba zamu yi baram-baram da ke. Idan ba kya so a ji kanmu toh ki maida hankali."
Abin da ta ce mata kenan, Malam kansa ya yi faɗa kuma yace muddin ba ta maida hankali ba to fa zai haramta mata riƙe waya. Duka wadannan batutuwa ne suka taru suka baƙanta ranta har ta sha kuka mai isarta. Dama daga Inna har Sadiya babu wacce ta kalleta hakan yasa ta zuciya ta fice a gidan ta shiga makwafta tunda uwarta Hajara ba ta gidan. Sadiya kuwa da aka hana ta ganin sakamakon Husnar, ta shigo dakin ta hange shi saman gado inda ta yi jifa da shi ta ɗauka tana karantawa, haka ta shigo ta iske ta.
Sadiya ba ta ce mata uffan ba ta miƙe ta fice a ɗakin, idan da sabo zuwa yanzu ta fara sabawa da wannan rainin na Husna gareta. Ita kuwa Husna bin ta da harara ta yi kawai tana turo baki ta nemi gefen gadon ta zauna. Wayar ta dauka ta cigaba da dannawa, a ganinta ma sai me idan ta maimaita ajin? Ai ba kanta farau ba a makarantar. Da wannan ta yi watsi da dukkan wani tunani, sai kuma take jin babu dadi ga yadda ta yiwa Sadiyar, hakan duk sai ya hana ta sukuni. Amma da ta tuno maganganin da Anti Hajara ta fadamata sai ta ja tsaki ta watsar.
"Yanzu za ki ga hatta da Malam kowa zai maida hankali ga Sadiya, ji dai yanda yake ta yaba kokarin da ta yi har yana misalta hakan da shi a lokacin da yake sakandire. Hum, Momina idan Sadiya ta fi ki kyau a fuska da sura, kar ki sake ta fi ki a kwakwalwa, ki dage sosai. Ni na san yanzu murna take da farin ciki jin babu ya ita a gidannan."
Abin da ta ce mata kenan wanda yasa babu damar ta ga Sadiya ta yi ko murmushi sai ta tsargu ranta ya baci ta ji kawai da ita take.
***
BAYAN WATANNI BIYU...
Hajara ta gama tabbatarwa ba ta dauke da juna biyu, hakan na nufin tsarin iyalin da ta yi kafin wata mu'amala ta haɗa su da Alh Nuhu ya karɓe ta. Zuciyarta kuwa zuwa lokacin babu wani sauran fili da soyayyar Alh Nuhu bai ginu ba. Ko a cikin labari ta kasa labartawa wani ko wata mummunan aikin da ƴan siyasan nan suka sanya su. Ta kuma ga tabbacin cewa Waleeda sun yi aikin saboda yanda suke facaka da kuɗaɗe. Babu kamar Waleeda wacce har gida ta siya na kanta. Tana cikin manyan celebrities da suke tashe a duniyar soshal midiya a sannan.
"Kar ki yarda ki yi wasa da damar da ki ka samu Hajjaju, ki ba da kai kawai bori ya hau. Na rantse maki ba ke kaɗai ba, mu kanmu da muka raɓe ki sai mun lashi wannan zumar da za ki tsunduma a cikin ƙoƙonta. Ni na san ba za ki watsar da mu ba duk sadda duniyarki ta yi faɗi."
Abin da Waleeda ta ce mata kenan a farko farko sadda ta ƙi sakin jiki ta amshi tayin auren da Alh Nuhu ya yi mata. Yanzun kuwa ta yi amanna da shi. Alh Nuhu ya je ya ga Malam da Kawun su Hajara a can babban gida tare da magabatansa har da dukkyar aure. Abinka ma da manya, a ranar waliyyansa suka bukaci a daura aure biki ya biyo baya. Malam da Abba farko ba su yi na'am ba, amma koda aka tuntuɓi Hajara ta amince da hakan, nan take Abba ya yi wa Hajara walicci aka ɗaura aure sannan aka tsaida sati uku a zummar za'a yi biki da kai Amarya.
Duk wannan buduri da ake yi Inna ko a neman auren ba ta da masaniyar komai. Tun a na saura sati da zuwan dangin Alh Nuhu, Malam da ma yayyun Hajara maza duka sun sani idan ka ɗauke Zakari wanda ya je Daura a ranar tare da matarsa Hadiyya, bikin Yayan Hadiyyar ake. Anti Hafsatu kuwa koda wasa Hajara ba ta sanar da ita ba, ta ma roƙi sauran yayyunta maza akan kar su faɗamata saboda tabbas idan ta ji to kamar Innar ta ji ne. Jin Innar tana nufin rushewar auren nata. A cewarta, Malam bai ji dadin zancen ba, koda ya nuna ba haka ba Hajara ta shiga kuka da sheshsheƙa tana zantukan da tasan dole su karya zuciyarsa musamman tunda suka shafi Asma'u. Wannan dalili yasa ya karɓi roƙonta ya kuma yi alfarmar yin shiru da bakin nasa sai bayan an ɗaure kamar yanda ta buƙata kafin a sanar da Inna.
"Ba hakan na nufin na yarda da zaton da ki ke yi a kan Mairamu ba ne Autar Mama, sai dai saboda kin roƙi hakan, na kuma karɓa zan rufe yanda ki ka bukata. Ina so dai ki san cewa babu mai yi sai Allahn da ya ƙage mu. Komai na faruwa bisa yanda ya tsara shi. Ku kyautata zato ga Mairamu, mutuniyar kirki ce mai sonku da zuciya ɗaya."
Kalaman na Malam sun shiga ta dama sun fice ta hagu don ba su yi tasiri a zuciyar Hajara ba, su Hashim da Baba Habu da Mustafa kuwa, kowa da yanda ya kalli zancen. A bangaren Hashim, kawai daɗin zama ne ya sanya Malam din goyon bayan matarsa, Baba Habu kuwa ko oho, Mairamu ko tana sonsu ko ba ta yi a ganinsa damuwarta ce. Shi kuwa Mustafa dama can ba ya kaunarta, to don me zantukan Malam za su karya zuciyarsa alhalin bai ga shaida a ƙas ba? Kusan dai dukkansu maganganun Hajara sun fi tasiri a zuƙatansu, sun fi yarda da cewa mai yiwuwa mugun hali irin na kishiyar Uwa ce ya yi tasiri a kan Inna Mairamu ta ke hana uwarsu aure. Amma fa babu wanda ya damu akan ta kaunace su ko a'a.
Ba su ne suka ƙara gasƙata cewa fasa auren Hajarar daga Innar ba ce ba, sai da suka ga an daura auren ƙanwartasu lami lafiya ba tare da sanin Innar ba kuma hakan ya yiwu.
"Biri ya yi kama da mutum, shiyasa ni fa sam hankalina bai kwanta da shiru-shirun matar can ba. Ashe dai zagon ƙasa ta ke yi."
Faɗin Baba Habu yana girgiza kai cike da takaici da jin ɓacin rai game da lamarin Inna Mairamu.
"Ai dama da walakin goro a miya, ba zai yiwu ace hakanan ba tare da wani kwakkwaran dalili ba a na fasa auren Hajara. Na yi shiru ne dai ban furta ba. Amma ai na jima ina zarginta." Faɗin Mustafa kenan.
Hashim ya yi murmushi.
"Sai dai kuma ai Dukan Ruwa ba zai hana gwarje amo ba. Duk dai abin da Inna ta ƙi afkuwarsa yanzu ya riga ya faru. Hajara da rai da lafiyarta za ta shiga ɗakin aurenta da yardar Allah. Kar a ce mata komai please, akwai ranar ƙin dillanci tunda dai ita ma ta haifa."
Gaba daya suka jinjina kai suna gasƙata zancen Hashim, tabbas ta haifa kuma za ta gani a kan nata.
***
Idanu waje ta ke duban status din da Hajara ta ɗora. Dagaske an ɗaura aurenta? To yaushe? Ya aka yi aka ɓoye neman ba ta da labari?
"Kut! Ni Hajara za ta ci amana! Duk yanda nake bibiyarta da kyawawan kalamai, har ta yi aure ba ta shaida min ba?" Faɗin Nusaiba a fili ƙarara, tana jin wani zugi da tsananin baƙin ciki mai kama da hassada a ranta.
"Me kike so ki ce? Ba aminiyarki ba ce?" Faɗin Maman Boy cike da mamaki bayan ta ajiye biron hannunta saman tebur bayan ta kammala rubutawa wata mata kwanan wata da ya dace ta dawo don yin wata allurar na tsarin iyali, ko takardar ba ta kai ga miƙawa matar ba tsabar abin na Nusaiba ya ɗaure mata kai. Matar dai na tsaye tana kallonsu.
Nusaiba kuwa wacce sai a lokacin ta ankara da suɓul da bakan da ta yi sai ta wayance da cizon yatsa tana duban Matar dake tsaye.
"Ki sallami mata tana jiranki." Abin da kawai ta iya cewa kenan