Showing 90001 words to 93000 words out of 124441 words
san me yake nufi da ta maida mishi nasa ba, amma ta gama sanin bai wuce layu da magungunan da ya damƙa mata ba na sabon aikin da ta karɓowa Husna. Da ma dai dukkan wasu taimakon da ya taɓa bayarwa.
Sauke ajiyar zuciya ta yi jin an ƙwanƙwasa gilashin motar kasancewar a rufe suke kuma na waje ba ya ganin na ciki. (Tinted glass).
Ɗago kai ta yi ta kalla, Yayansu Mustafa ne tsaye. Baƙin gilashinta ta ciro a jaka ta rufe ƙwayoyin idanunta waɗanda tuni sun kaɗa jawur kamar wacce ta ci kuka. Fitowa ta yi ta rufe motar tana gaida shi bayan ta ƙaƙalo murmushin yaƙe. Ya amsa fuskarsa a sake.
"Lafiya kalau Autar Mama. Waya ki ke ne? Tun ɗazu kin kasa fitowa."
"Eh waya na amsa. Bari na shiga ciki."
"To ba laifi. Ki je ai har an kawo kayan ma, mata sun soma kallo." Ya furta yana komawa can inda Yayansu Hashim da kuma babban wan su Huzaif suke tsaye suna hira.
Ita kuwa tafiya ta ke yi tana jin amsa-kuwwar maganar Mustafa a kwanyarta, a zuciyar kuwa tamkar an soka mata mashi take ji.
Yawun bakin Hajara sai da ya kafe na ɗan wucin gadi, duk da bai kai yawan akwatunanta ba, na Sadiya saiti biyu ne sai ko wani akwatin madaidaici da aka yi na Uwa da Uba. A gefe kuma ƙaton make-up kit ne kalar ruwan hoda. Manyan suturunta kuwa babu ƙasa da dubu goma, sai ko bangaren kananan kaya da sauran tarkace. Komai nata ka ɗaga an san na daban ne. Guɗa kuwa da mata ke yi a wurin ya sa Hajara ji kamar su na mata ihu a tsakar kanta. Ta daure iyakar dauriya ta na yaƙe, ƙarshe ta ɓige da karɓar Sadik a hannun Husna wanda ke tsala ihun kuka ta fita tsakar gidan da shi. Gwaggo Atine tana ganinta ta bi bayanta ta fito. Koda ta karaso ta fara da yamutsa fuska da tsaki.
"Aikin ɓurr, ai wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa, yo me..."
"Za ki bar nan ko sai na buge bakinki?"
Abin da Hajara ta faɗi kenan murya a kausashe tana watsawa Gwaggo Atine wani banzar harara. Gwaggo Atine ta saki baki sai kuma ta riƙe bakin ta bar wajen, girma ne ya riga da ya gama zubewa. Ta rantse rainin da Hajara ta mata ya haura na baya. A bayan ma ta fi ɗan ganin ƙimarta tunda gaisuwa kan gifta tsakaninsu, yanzu kuwa ai sauran mutuncin ya zube ƙasa warwas. Ta yi gaba tana jin uban tsakin da Hajara ta ja mata, sai da zuciyarta ta yi babu dadi amma kuma ya za ta yi da abin da ya fi ƙarfin wuta?
Hajara kuwa ga kukan Sadik ga kuma shewar da ta ƙi ƙarewa, abu goma da ashirin dai.
"Husna! Husna!!"
Yanayin yadda ta ke ƙwala kiran Husnar ka san a zafafe ta ke. Jin Husna ba ta ma san ana yi ba ya sa a matuƙar fusace ta ƙarasa cikin falon.
"Husna! Wai wane irin iskanci ne yaronki na faman ihu ba za ki dauke shi ki rarrashe shi ba?! Lefen baƙonki ne da za ki dinga rawar ƙafa wajen gani?"
Ba ta kula ma da shirun wucin gadi da ya falon ya yi ba, idanunta sun rufe. Mamaki ne tsantsa a saman fuskokin jama'ar da ke falon ciki kuwa har da Husna don ita baki sake ma ta ke duban Hajara kafin a tsorace ta kai hannu ta karɓi Sadik ta fice daga falon idanunta cike taf da ruwan hawaye. Abin sabo ya zame mata, tun tasowarta, tsawon shekarun da suka rayu tare, ba ta san wannan ɓangare na Hajarar ba a kanta sai yanzu, ta dai sha ganin tana gwadawa Sadiya amma kuma ita bayan shagwaɓawa da rarrashi babu abin da ta sani a wajenta.
"Hajara, lafiyarki? Yau kuma abin kan ƴar lelenki ya faɗa?"
Anti Hafsatu ta furta.
Ganin manyan an fara ca akan abin da ta yi ne ya sa ta fice daga falon, tana jin wata na ƙusƙus wai baƙin ciki ne ƙila tunda ba ƴar ɗakinta ba aka kawowa.
Ta so ta juya ta ga mai shi amma kuma ta fasa ga wani uban guɗa da wata ta saki har da faɗin.
"Sadiya ta yi goshi! Amarya a gidan Audullahi, Allah dai ya kaimu a shafa fatiha!"
Aka ɗauka da amin gaba ɗaya.
Ta iske Husna zaune a saman kujera tana shayar da Sadik tana zubar hawaye, nan ta shiga rarrashi da fadin ba da niyya ta yi ba.
"Wani magana marar dadi ne Alhaji ke ya fada min ta waya, shi ne ki ka ga duk na ruɗe. Amma ki yi hakuri kin san ba halina ba ne ba ko? Na taɓa yi maki?"
Ta girgiza kai tana share fuskarta.
"Toh ki yi min uzuri. Kin ji?"
Ta yi murmushi tana gyaɗa kai. Can kuma ta gano kuskuren da ta tafka a falon, hakan ya sa ta koma ta ware kamar ba ita ba. Waɗanda farko ma suka yi mata fassara duk suka ɗan ware gami da yi mata uzuri, wasu kuwa kallonta kawai suke amma gani suke har yanzu kamar da ƙiyayyar Inna a ranta.
***
Biki na ƙaratowa, ana ci gaba da shirye-shirye. Ta ɓangaren gidan su Hamma. Tuni baƙi ƴan uwan Nene da na Baffa sun soma zuwa daga Gombe ciki har da wasu a ƴan gidan Mai Martaba. Nene sosai suka yi musu tarba. Baffa har ma'aikata ya ƙaro waɗanda za su dinga girki saboda baƙi.
An yi fentin gidan gaba ɗaya, Nene har sauya mata kayan falo da ɗakuna ya yi. Nudrat gaba ɗaya ba ta zama, ita ce wajen Sadiya, ita ce karɓo ɗinkuna, can kuma a tsince ta a kasuwa. Haka ta ke faman zagaye. Idan ta tuno auren wa da waye sai ta ji zuciyarta na ƙara sanyi, tana alfahari da wannan auren sosai.
Hamma AbdulMajid kuwa, gaba ɗaya ya koma wani shiru-shiru fiye da baya. Abokan wasa ma idan suka sako shi gaba sai dai ya yi murmushi. Ko a ranar yau da ya dawo gidan don ƙara kimtsawa sakamakon Airport da zai je tarbar Maina da wasu a cikin ƴan uwansu da suka taho daga Gombe. Nene ta kula har wata rama ya yi da ya durƙusa yana gaishe da Gwaggonninsa don haka ta miƙe ta bi shi a baya.
"Wai lafiyarka kuwa? Meke damunka kwanakin nan. Hatta da abincin kirki ba ka ci, duk sadda ka shigo gidan a ƙoshe ka ke. Da safe kuwa kana gaggawa ka ke ficewa. Akwai wata matsalar ne?"
Ya hau susar ƙeya yana murmushin yaƙe.
"Babu komai Nene. Kawai dai yanayin zirga-zirgar kula da komai ne."
Ta sauke ajiyar zuciya tana kallonsa sosai. Jikinta yana ba ta akwai wata a ƙasa, sauyin ya yi yawa. Ba haka nan ba. Amma kuma sai ta bi shi da toh. Shi ko lura da ya yi kamar zancen bai shige ta ba ya sa shi saurin ɗauko batun zuwan Maina. Nan da nan kuma ta saki fuskarta.
"Wato haka ka yi niyyar wucewa ba ka faɗi ba balle a soma shirin tarbarsu? Tare da Mai Martaban ne?"
Girgiza kai Hamma ya yi har sannan ya na ta kokarin sakin fuska yadda ya dace.
"Aa, tare da su Lamiɗo ne. Mai Martaba sai safiyar ɗaurin aure zai shigo."
"Allah ya kawo su lafiya. Sai ka hanzarta toh. Bari na yi magana a fara shirin abinci."
Kamar ya ce babu buƙatar hakan tunda ya sani Maina a Hotel za su sauka amma kuma ya amsa da toh ya wuce bayan Nene ta bar wurin.
***
Fuskarsa cike da walwala a sa'ilin da ya fara hangen Maina, a gefensa Lamiɗo ɗa ga ƙanin Baffa. Sai Giɗaɗo ɗan wajen Fulani Amaryar Mai Martaba. Sai ko mafi kusa da Maina wanda bayan shi AbdulMajid din, Maina ba shi da amini sama da shi, wato Umar da suke kira Sadauki.
Ga su nan dai su huɗu ne suke tafe, amma kuma yanayin shiga da tafiyar ƙasaitar kaɗai sun isa su bambance maka waye shi. Babu gajere a cikinsu amma kuma kaf ya fi su tsayi da jiki ƙira ta maza ababen so a wajen mata. Fari ne tas har wani ja ja yake yi, idan ko magana ake na baiwar kyawun fuska, to fa Allah zubawa Maina shi.
Hamma da ke tsaye gaban motarsa fuskar ɗauke da murmushi ya ke dubansu su din ma shi suke kallo idan ka ɗauke Maina da ya maida hankali ga abin da ya ke tun kallon farko da ya mishi bai kara ba. Shi ma AbdulMajid bai yi karambanin cewa uffan ba saboda sanin Maina ɗin waya yake yi. Suka janye zuwa gefe suka bar shi inda ya kama murfin motar ya buɗe ya shiga ya zauna yana ci gaba da zuba ruwan turanci kamar ɗan mango park. Ƙa'idarsa ce waya a handsfree, wani irin mugun sabo ya yi da hakan wanda duk masu rayuwa da shi sun sani. Sabo ne da Mai Martaba sam ba ya son shi da ita, har daina amsar kowace waya ya yi idan yana tare da shi.
Can kuwa Hamma da su Giɗaɗo aka hau caccafkewa.
"Ango! Ango!! Shegen kaya! Fargabar auren ce ta ramar da kai? Tun ba ka fara awo ba?"
Faɗin Ishaq da suke kira Lamiɗo yana ƙarewa AbdulMajid ɗin kallo. Shi kuwa ƴar harararsa ya yi aka yi dariya.
"Kai ma ashe ka kula, ni ma na ga ya yi wani haske kamar shi ma ya fara shafa lallen Amaren, amma ka rame. Sai dai tun da mun iso kafin nan zuwa ɗaurin aure za mu san yadda zamu yi ka murmure."
Khamees ya ƙarashe cike da zolaya. Suka kwashe da dariya.
"Kwa yi kwa gama ƴan iska. Ni har akwai auren da zai jefa ni firgici?"
"Eh ai fa mun gani sadda ka maƙalewa waccan aljanar, yanzu da yake ka ƙwace daga bakin kura komai ma ka faɗi."
Ya ji zancen sosai ya shige shi, bai dubi Giɗaɗo bai maganar ba ya yi wa ma'aikacin da ke tsaye kusa da su jaye da ƙaton keken da aka ɗora akwatunansu nuni da motar.
"Ƙarasa a saka, boot ɗin a buɗe yake."
A ladabce ya yi gaba.
"Mu ma fa ba nan zamu kwana ba, don Allah ku dinga yi wa Maina faɗa. Ni fa na tsani a cika mana kunnuwa da hayaniyar da babu mu a ciki. Why on earth ace sai mutum ya saka waya a handsfree idan zai yi ta?"
Dawud (Giɗaɗo) ya furta yana ɗan shan mur.
"Ai kai ma ka na da baki, sai ka faɗa masa ko zai ji." Khamees ya furta da ƴar dariyarsa.
Hon ɗin da suka ji ne ya ba su tabbacin su yake jira. Nan suka taka bayan AbdulMajid ya sallami ma'aikacin ya rufe boot dinsa, yana zaune gefen direba.
"Manyan ƙasa, barka da isowa."
Maina ba tare da ya kalle shi ba hankalinsa na ga kallon gaban motar ya ɗan murmusa.
"Abdul Ango, fatan mun same ku lafiya?"
Hamma ya jinjina kai.
"Alhamdulillah."
Khamees ya ce,
"Ba ka kula da ramar da mutumin ya yi ba?"
Ya ɗago lumsassun idanunsa ya ɗan dubi Hamma wanda hasken fitilun titin fita daga tashar jirgin sama ya haska fuskarsa, sai ya kauda kai yana ɗan ɗaga kafaɗa.
"Wani abu ne? Bai wuce na rashin hutu."
"Hakane." Khamees ya amsa a taƙaice su Lamiɗo na mishi dariya.
Shi kuwa Hamma wata ƴar guntuwar ajiyar zuciya ya sauke. Shi kaɗai ya san meke cin ransa. Yana jin wayarsa na faman ruri a gefen aljihun rigarsa amma bai ko yi yunƙurin fiddowa ba sanin da ya yi tatsuniyar gizo ba ta wuce na ƙoƙi.
***
A kwanakin da aka kwashe a na yi wa Sadiya gyara, idan ka gan ta kai ka rantse wata ɗiyar shahararren mai arziƙin ce. Fatarta ta goge ta yi tas tamkar ka taɓa jini ya fito, har wani sheƙi take yi ga santsi da laushi da fatar ta yi. Sosai matar da ke mata gyaran ta ba da himma a aikinta.
A gefe ma ga su Adda Ruƙayya na mata nasu irin kalar gyaran na jiki. Kamar wancan karon, wannan karon ma Abba ne ya rantse shi zai yi komai na kayan ɗakin Sadiya. Kusan ma waɗanda ya yi a yanzun sun ninka na farko a tsada har sai da Malam ya so ya bari ko wani abin ya yi amma Abba ya ce sam. Ƙarshe ma har faɗa Abban ya yi akan don me zai yi kokarin taka masa burki a abin da zai yi ga ɗiyarsa.
Duka waɗannan sha'anin da kowa ke yi, a ɓangaren Sadiya ita kaɗai ta san meke cin zuciyarta. Damuwa ce tsantsa da rashin sukuni na irin bagararwar da Hamma ke mata. Babu waya balle saƙon rubutu. Idan ma ta kira ko ya ɗaga bada haƙuri ne zai biyo baya da fadin zai kira ta yana wani abun. Ƙirjinta koyaushe cikin bugun tara-tara yake yi. Hankalinta kuwa idan ya yi dubu to fa a matuƙar tashe yake.
A na gobe za'a sanya ta a lalle ta kasa haƙuri sadda Nudrat ta zo gidan kawo mata kayan fulanin da za ta saka ran kamu har da komai na kwalliyarsu. Ta dube ta bayan ɗakin ya yi saura su biyu kawai a ciki ta ce.
"Ni kam Hammanki abubuwa ne suka yi mishi yawa haka? Ko ba shi da lafiya ne? Na ga mun jima ba waya ba chatting. Allah ya sa lafiya ya ke."
Ta ƙarashe tana jin hawaye na cicciko mata amma ta haɗiye su gudun nuna rauninta a gaban Nudrat.
Nudrat ta ji Sadiyar ta mata fami da abin da ke mata ƙaiƙaiyi a zuciya, amma kuma ba ta son ƙarasa karya mata nata zuciyar don haka ta yi ɗan yaƙe.
"Kai lafiyarsa kalau sai dai ko hidimar. Kin san Maina sun zo, ko ban faɗi ba kin san yadda ya ɗaukake shi. Ni na san abin da ya hana ki jin sa kenan."
Nudrat ta faɗi ba don tana da tabbacin Sadiya ta yarda da kalamanta ba ko a'a, ta faɗi ne don rasa abin da za ta ce ba kuma wai saboda kare ɗan uwanta ba, a'a, kawai don Sadiya ta ji sanyi a ranta. Ta kuma ji ƙarfin ci gaba da shirin bikinta.
A gefen Sadiya murmushi da gyaɗa kai ta yi lokaci guda. Ta ji, amma ba ji irin na yarda ba, ji irin na a tafi a hakan kawai don ƙarfafawa Nudrat gwuiwar ta gasƙata kalamanta ɗin. Amma tana ji a jikinta ko mene ne ƙila ya sauya ra'ayi ne, ƙila ya gane ba ita ta cancanci zama matarsa ba. Ta san irin hakan, amma kuma ba ta so ta ci gaba da gasƙata gaskiyar. Inama wannan karon gaskiyar ta ƙaryata tunaninta, sai dai zai wahala kasantuwar hakan. Riƙo hannunta da Nudrat ta yi ne ya sa ta kalle ta.
"Kar ki saka komai a ranki. In sha Allah jibi war haka mun miƙa ki ɗakin aurenki da Hamma."
Murmushin ta yi karo na biyu wannan karon har fararen haƙoranta na bayyana.
"Allah ya nuna mana toh."
Nudrat ta amsa da amin. Daga bisani ta yi mata sallama ta fice. Sadiya ta ji zubowar hawayen da ta ke riƙewa.
'Ya Allah, ka tabbatar min da alkhairi.' Ta furta a zuciya kafin ta sa hannu ta ɗauke ruwan hawayen.
***
Washegari aka sanya Amarya a lalle. Suƙa yi shi a zamanance a farfajiyar gidan Abba da ya sha ado. Ga mai hotuna nan. Sadiya ta sha atamfarta cote d'voire babbar. Ta yi kyau shar abin ta. Ga mai hoto da aka kira ya dinga ɗaukarsu. Mami sai nan nan take da Amarya don ji take inama tun farko ita Huzaif ya aura. Nadama tsantsa take yi. Ga Hajara kuwa kallon kowa ɗai-ɗai take sai dai a matuƙar firgice take.
Ko yau Asubancin zuwa gidan Boka ta yi don jin yadda aka haihu a ragaya. Yo akan wane dalili a na gafara Sa kuma ba ta ga ƙaho ba? Har yaushe? Abu na ƙara tafiya, amma kuma babu wata alama ta nasara.
Har aka kammala taron ba ta shiga hoto ko ɗaya ba. Koda aka tashi ta kula da Zahra wacce ta ja hannun Amarya Sadiya suka zagaya can wurin garden na gidan Abba suna ƙusƙus. Gaba ɗaya sai hankalinta kacokam ya koma garesu don haka a gaggauce ta miƙe daga inda suke zaune ita da su Waleedah ƙawayenta ta bi sahu. Ta ja burki daga nesa da su tana jin murya Zahra na rarrashin Sadiya da faɗin.
"Don Allah ki saki ranki, hawayen ne bana so Sadiya. Me kike so jama'ar gidan nan su hankalta da shi? Kar ki manta fa gidan tsohon saurayinki ne ko me za'a ce ba zai sauya wa tuwo zani ba. Ki saka a rai ba wai fasa auren ne ya sa Hamma ba ya nemanki ba, da hakan ne ai ko yan uwansa ba za'a ga ƙyallinsu ba a yau. Kalli yadda suke kaunarki, ni ina ji a jikina ko mene ne bayan auren za ku magance shi. Please ki rage damuwarnan. Ni bana son ganinki haka. Kin ji?"
Iyakar nan ta ji, sai ta juya ta tafi tana jin zuciyarta kamar ta yi tsalle ta fito tsabar farin ciki da jin daɗi. Har wata dariya ta yi na murna.
'Shege Boka.' Ta yi furucin a zuciyarta gami da ƙara ƙyaƙyacewa da dariya. Da ta ƙarasa ga su Waleedah har sai da suka kasa haƙuri suka tambayi ko wani albishirin aka yi mata. Ta yi farr da idanu tana doka uban murmushi.
"Albishirin da aka yi min ai ya wuce zatonku. Ku dai a yi sha'ani kawai."
Daga haka ta share su ta maida duba ga Sadiya da Zahra da suka taho wurin jama'ar da wani murmushin da ta riga ta gane na dole ne a saman fuskar Sadiyar sai ta ji kamar ta yi tsalle da juyi. Har wata ajiyar zuciya ta sauke tana kissima irin kyautar bajintar da za ta yi ga Boka idan haƙanta ya cimma ruwa.
***
Hamma AbdulMajid kuwa babban abin da ya ke cin zuciyarsa a yanzun bai wuce samu da rashin da yake gani ƙiri-ƙiri na shirin afkar masa ba. Kullum soyayyar Fareeda ke ƙara ninkuwa fiye da baya a ransa. Musamman yanzun da take hana shi sukuni da rikici da koke-koke tana