Showing 42001 words to 45000 words out of 124441 words
Babu laifi ya sakarmata fuska, Hajara da kanta ta fahimci bai gama hucewa ba, a karshe har kuka ta saka sosai tana ƙara neman afuwarsa har da cewa yanzu tana da aure kuma ta san darajar auren, ba za ta sake ta ƙara yin kuskuren baya ba. Jikin Malam ya yi sanyi, anan komai ya wuce har ya karɓi tulin ledojin da ta yo masa tsaraba. Ƙatuwar darduma sai turaruka masu tsada da ƙamshi, sai ko jallabiyoyi har biyar.
"Hajara, wannan sai ka ce don ni ki ka yi tafiyar? Duk a Saudiyar ki ka jido kayan nan? Kin ko tsaya ibada ko yawon kasuwa ki ka yi?"
Ya ƙarashe da ƴar dariyar mamaki yana ɗaga wani kwalbar turare mai matuƙar kyau da ɗaukar idanu wacce ya fiddo a ɗan gidansa.
Ita ma Hajara dariya ta yi.
"Malam ibada na yi mana. Ai daga can Dubai muka yada zango, sai da muka yi sati kafin mu taho. A Abuja ma mun yi kwanaki biyu."
Ya jinjina kai yana murmushi.
"Allah ya yi albarka to, nagode. Ina na Innarki?"
Ya furta yana dubanta, shiru ta yi ba ta ce uffan ba. Ya kula har lokacin Hajara ba ta karɓi Inna a matsayin Uwa ba.
"Autar Mama ki yaƙi zuciyarki, koda babu yawa, ki ɗan buɗewa Mairamu ita, ina da yaƙinin za ki ji daɗin mu'amala da ita irin ta Uwa da ƴaƴanta. Mairamu tana kaunarki, da ace kin san yadda ta dinga bibiyata da roƙo da lallami kan na yafe maki, haƙiƙa na sani da zuciyarki ta sanyaya. Rayuwar duka nawa take Autar Mama? Ki tambayi kanki, me Mairamu ta taɓa yi maki marar daɗi a rayuwa? Ko don ta auri mahaifinki? Toh kin fi kaunar gida ya mutu babu mace a cikinsa? Kin fi so na dinga yawon shigowa da abincin siye? Ko kuwa kin fi kaunar ganin na ƙare rayuwata babu aure? Ki zama mai tawakkali da yarda da kaddara Autar Mama."
Hajara hawaye ta ke fitarwa, kai ka rantse tsabar nadama ce ta sanya su zuba, sai dai kuma a nata ɓangaren ba na komai ba ne da ya wuce tunanin zaƙin soyayya har ya mantar da Malam da Mahaifiyarta. Wato dai Mairamu ta datse igiyar farin cikinta ta ko'ina, a wajen kuma kowa cikin zuri'arsu. Malam ɗin da take ganin koyaushe yana goyamata baya, yanzu wannan ɗin ma ta kau. Hum! Lallai Mairamu ta ɗauko ruwan dafa kanta, ita kuma za ta bi kowa da yadda ya so, idan sun sakankance da cewa ta ɗauki Mairamun tamkar uwa, sai ta nuna mata ba ta da wayo. Wannan tunani ya sa ta lanƙwasar da murya.
"Ka yi hakuri Malam, zan yi iyakar bakin ƙoƙarina na ga komai ya wuce a zuciyata. Allah ya gafartawa Mamana, ya sa aljanna makoma."
Ya yi murmushi sosai.
"Amin amin. Allah ya maki albarka. Haka ake son musulmin kirki ya kasance."
Ta yi murmushin da bai kai zuci ba tana wasa da zoben gwal ɗinta.
"Amin Malam."
Daga nan sai ta ga ya ƙara sakarmata fuska sosai ba kamar a farko ba. Ta ƙara fahimtar lallai ya ɗau sha'anin Mairamu da girma. A ranta ta yi ƙwafa kawai, tana tunanin kalar ƙuncin da za ta jefa ta ciki ta hanyar Sadiya.
Sai bayan sallar isha'i tukunna ta yi musu sallama don har abinci aka ci tare da ita. Inna ta yi mamakin yanda Hajara ta sakar mata fuska har da yi mata fatan alheri na kawo kuɗin auren Sadiya da za'a yi, ba dai ta nuna mamakin a fili ba, ta bar shi a matsayin wataƙila Malam ne ya yi mata nasiha. A ranta tana fatan Allah yasa ta sauya ɗin dagaske.
Sadiya kuwa ba ta ji ko ɗarr ba don wai Hajara ta yi tsaraba ga Husna ta ware ta. Dama ai ba ta sa a ka ba, ita ma ba ta kwaɗayin komai da zai fito daga hannunta. A wayar da Husna ta yi da Aminiyarta Shema'u ne ta ji ashe daga Saudiya har Dubai suka je, dalilin jimawarta kenan.
***
Hajara ce ke safa da marwa a tsakar falonta, maganganun Safiyya da ma Malam da ya tabbatar mata da kawo kuɗin Sadiya suka yi mata tsaye a rai. Ta dunƙule hannunta na dama ta kai wa na hagu duka. Huci ta furzar gami da girgiza kai, a fili ta ce.
"Na rantse Sadiya ba za ta yi aure ba. Ba asiri ba, ko tsafi ne sai na yi don ganin hakan bai kasance ba. Tabbas zan rama!"
Ta ƙarashe tana duban kanta a madubi, gaba ɗaya idanunta sun kaɗa tsabar ɓacin rai. Bacci kuwa ya ƙaurace mata a idanu, har ga shi nan ƙarfe ɗaya ta buga da mintuna na dare amma babu ko alamun hakan. Duk kuwa da cewar mijinta bai kai da shigowa gidan ba, hakan bai wani dame ta ba a yau ɗaya saboda a ganinta damuwar Sadiya ta yi auren wuri ya fi yi mata karan tsaye fiye da kai wa daren mijinta a waje.
"Kar ki kusa ki saka min idanu akan abin da ya ke sanya ni jimawa a waje. Idan ma wajen ƙadangarun barikin nake zuwa, ke ma ai a can muka haɗu. Don haka ki fidda idanunki harkokina, ni kuma zan sakarmaki bakin aljihuna, yadda ki ka dama haka za ki sha."
Wannan ne kalaman mijin nata Alh Nuhu a ranar farko da ta hau borin kishi don ya kai ƙarfe uku a waje bai shigo gidan ba.
Tunani ta shiga yi, wa za ta yi haɗin gwuiwa da shi don zuwa wajen ƴan tsibbu? Wacce ta faɗo mata a rai ne ya sanya ta ƙyaƙyacewa da dariya na samun mafita.
©Rufaida Umar
Tun sallamarta ya ɗauke kansa a fuskar wayar dake hannunsa ya na amsawa, kallonta yake yi sosai. Ta yi mishi kyau cikin doguwar riga na material kore mai ratsin fari. Ta yane kanta da farin mayafi. Suna haɗa idanu ta ɗan kauda nata kan tana murmushi a kunyace. Ƙarasawa ta yi ta zauna a can ƙarshen kujerar da yake kai sannan ta ce.
"Yaya Huzaif ina wuni. Ya su Abba da Mami da Anti, fatan duk suna nan kalau?"
Sauke ajiyar zuciya ya yi.
"Lafiya lau Bebi, dukkansu lafiya lau suke. Abba yana can yana ƙoƙarin ya ga komai ya tafi daidai a goben."
Ta yi murmushi ba ta ce uffan ba, a goben ne za'a tsaida lokacin bikinsu. Ta san zancen kenan.
"Bebi idan na tuna sati na sama zan koma sai na ji kamar na cewa Abba a ɗaura auren kawai mu tafi, ƙafarki ƙafata."
Ta ɗan tsuke baki.
"Don Allah ni dai a'a. Ai idan ka tafin za ka dawo ka same ni lafiya kalau."
"Dagaske? Ba za ki kula kowa ba?"
Ta ɗan dube shi yanda ta ji ya marairaice murya, fuskar ma gaba ɗaya ta koma kalar tausayi, sai ta ji ya ba ta tausayin ta kawar da kai.
"Bebi, please don Allah, roƙonki fa nake yi. Kar ki kula kowa idan ba na nan."
"To ni dama ai ba wanda nake kulawa kafin kai, ban ga dalilin da zai sa na kula wani bayan na same..."
Sai ta yi daurin jan mayafi ta ɗan rufe gefen fuskarta tana ƴar dariya. Shi ma dariyar ya ɗan yi cike da shauƙi, kalamanta sosai suka yi mishi daɗi. Ya sani sarai me take son faɗi, ya kuma san idan ya dage akan sai ta ƙarasa to fa za su wuni su kwana idan har Sadiya ce. Wannan dalili ne ya sa bai ja ba ya amsa zancenta.
"Na gode ƙwarai Bebina. Allah ya sa mu zamewa junanmu abin alfahari kuma mafi alheri."
Ta amsa da amin. Daidai sadda suka tsinkayi sallamar Husna, suka dubi ƙofar, ita ɗin a su take kallo da ƴar dariyar da ba za ka iya tantancewa ba ta ƙaraso tana ajiye tray dake hannunta. Sai fa a sannan Sadiya ta tuna ashe Inna ta ce ta tafar masa da ruwa da lemo mai sanyi, shaf ta mance.
Husna kuwa ta haɗiye zazzafan kishin da ta ji yana bijiro mata, ta shiga jan magana ta sigar zolaya tana duban Huzaif wanda ke ɗan mamakin ganinta don tun ƙulluwar alaƙa tsakaninsa da ƴar uwarta bai ƙara sanya ta a ido ba, hirar ma da suke ɗan yi a kafafen sadarwa ta janye mishi don ko wayarta ya kira don magana da Sadiya a baya, sai dai kawai ta miƙawa Sadiya wayar ba tare da ta yarda sun gaisa ba. Yana so ya fassara hakan da abubuwa da dama, amma kuma ya sani babu ma amfanin hakan, gwara komai ya cigaba da tafiya a ninke, buɗawar ba zai amfane ta da komai ba tunda ita ke kiɗa da rawarta.
"Yaya Huzaifa ina wuni, an zo lafiya?"
"Lafiya Alhamdulillah ƙanwarmu, kwana da yawa kin ɓuya."
Ba tare da ta kalle shi ko ta amsa zancensa ba ta yi murmushin yaƙe tana maida duba ga Sadiya.
"Ke kam soyayya ta yi daɗi ba ki kawo wa masoyin naki koda ruwan sha ba. To ai shikenan, ga shi nan Inna ta ce a kawo. Ki karasa ladanki."
Tana kai wa nan ta miƙe da zummar tafiya. Huzaif mamaki ya kusan kashe shi, duk a kalamanta bai ga inda ta tauna harshenta ba, ya yi mishi kama da kamar rashin kunya haka ko kuma wata manufa. Amma sai ya yi tunanin ƙila don saƙo da saƙo suke shi ya haddasa hakan.
"Ni da kaina zan zuba, ke za ki fara sha tunda ko babu komai dama nan gaba ci da shayarwarki ƙarƙashina za su dawo."
Karaf zancen na Huzaif ya dira a kunnen Husna da bai fi taki ɗaya ta bar falon ba, ta juyo ta dube su. Sadiya na kallonsa kaɗan, yayinda shi kuwa ya sauko gami da ɗan durƙuso ya buɗe jug na kunun aya ya shiga tsiyayawa a kofi. Babu wanda ya ƙara lura da wata halitta mai sunanta a wajen don haka a gaggauce ta karasa ficewa ta nufi ɗakinsu.
Inda Allah ya taimaka ma Inna na ɗakinta. Kuka ta fara ta jawo wayarta ta shiga neman layin Hajara. Tana ɗagawa a ruɗe ta shiga tambayarta abin da ke faruwa. Murya a shaƙe ta amsa.
"Anti anya zan iya cigaba da jurewa? Wani abin kamar da gayya ake yi don zuciyata ta sosu."
Ta ji sadda Hajara ta sauke ajiyar zuciya.
"Za ki iya Momina. Ai jinin da ke yawo a jikina shi ke yawo a jikinki. Ina da tabbacin ba za ki ɓatan shirina ba. Ke dai ki cigaba da haƙuri kina nuna komai ba komai ba. Gudun ma wani abin ya faru a yi wani zargi can. Kinga ki kwantar da hankalinki, na san gobe ma ba za ki iya yinin gidan ba, zan tambayar maki Malam ki shigo gidana kin ji ko?"
"Toh Anti."
"Yauwa Momina. Ki ƙara daurewa, ke za ki dara a gaba. Ke za ki zama Amaryar Huzaif kawai ki kwantar da hankalinki."
Duk da tana ji kawai Antinta ta faɗi don ta rarrashe ta ne, amma sai ta ji murmushi ya suɓuce mata. Ba su jima tare ba suka yi sallama don Hajara ta ce ta maida hankali ga karatu tunda ta sanar da ita sun fara gwajin aji a makaranta (Test).
***
Washegari da safe Sadiya ta tashi zuciyarta wasai idan ta tuna yau iyaye za su shiga maganarta da Yaya Huzaif. Haka suka yi shirin makaranta ita da Husna bayan sun gama kari. Falon Malam suka fara shiga kamar yanda suka saba suka gaishe shi, ya amsa lokaci guda yana karɓar kofin kunun gyaɗar da Inna ke miƙo mishi.
"Ke Autar Mama ta ce za ki je gidanta ko?"
Husna ta gyaɗa kai tana ɗan murmushin yaƙe tun bayan wayar soyayya da ta ji Sadiya sun yi da Huzaif a yau ta ji ranta ya sosu.
"Shikenan, idan kin dawo sai ko shirya ki wuce. Ta nemi alfarmar ki kwana biyu zuwa lahadi kya dawo don ba ta jin daɗi ne."
Cikin jin daɗi ta amsa da toh. Ita dai Sadiya kamar ya da Inna ba ta ce uffan ba, ita ma ba ta ce komai ba. Suka yi musu sallama suka fice bayan Malam ya ba su kuɗin mota da na kashewa.
"Ina fatan babu matsala? Na yanke hukunci ban sanar da ke ba."
Malam ya furta yana kallon Inna. Ta numfasa.
"Ko kaɗan, ai kana da ikon zartar da kowane irin hukunci kan yaranka, kai ne fa Babansu. Sai dai Hajara ba lafiya amma ba ka sanar da ni ba? Ai ko ban je dubiya ba zan kira a waya na ji ya jikinta."
Girgiza kai Malam ya yi, sanyin zuciya irin na Inna na ba sa mamaki.
"Ita ya dace ta kiraki matsayinki na Uwa gareta ta sanar da ke. Na yi mata faɗan hakan, sai na yi zaton ko ta kira ne. Amma ina mai baki hakuri."
Murmushi Inna ta yi.
"Shikenan, Allah ta ba ta lafiya ya sa kaffara."
"Amin. Anjima can babban gida za'a karɓi baƙin da misalin ƙarfe uku na rana da yardar Allah."
"Toh, Allah ya nuna mana. Ya sa albarka." Amsar da ta ba shi kenan. Shi ma ya bi da amin.
***
Sadiya na zaune a ɗakinsu da yammaci sai ga Zahra ta shigo tana mata guɗa a kai. Harararta ta yi da murmushi ɗauke saman fuskarta.
"Ka ga Amaryar Huzaif. Allah ya sanya alheri. Ai Mama ta cemin wai an saka nan da watanni goma. Kafin lokacin kuwa mun yi Candy abinmu. Toh ko auren wa za'a riga yi tsakanin ni da ke?"
Zahra ta ƙarashe da dariyar mugunta, Sadiya ta kai mata duka don ta san dalilin dariyar, wato dai ta gama cin alwashin karatu da tutiyar babu namijin da za ta kula sai ta zama likita, amma kuma ga shi so ya yi mata tarko ta faɗa. Zahra idan tsokanar ta tashi haka za ta yi ta jan ta.
"Ina ɗiyar tawa take?" Faɗin Maman Zahra dake shigowa kafin kuma ta yi sallama. Sadiya ta yi ƙasa da kanta tana gaishe ta a kunyace. Ƴar guɗa Maman Zahra ta yi wanda ya sa gaba ɗaya ta ɓoye kanta a kafaɗar Zahra tana murmushi. Fatan alheri ta yi mata ta fice. Haka ma wasu a cikin ƴan uwan Malam da suka zo yiwa Inna fatan alheri suka shigo dakin. Ranar kam Sadiya ta sha zolaya sosai.
***
Hajara ta fito daga ɗakinta cikin shiri, Husna dake saman teburin cin abinci tana ba ƴar aikinta mai suna Atine umarni ya sa ta murmushi. Ba ta ce komai na ta tsaya ta na kallon diramar da suke yi. Wai Atine ta dafa mata Indomie da gwangwanin kifi alhalin da sauran farfesun kayan cikin da ta gani ta ce a dafamata. Atine kuwa sai haƙuri take ba ta. Husna ta ja tsaki.
"Ni ba zan ci ba, ki ɗauke ki yi min yadda nake so."
Ta yi jifa da cokalin ta miƙe ta taho falon. Anan ne kuma ta ga Hajara, Atine da sauri ta yi kicin da farantin Indomie tana tsoron faɗan Uwar ɗakinta Hajara.
Kamo hannun Husna ta yi tana murmushi.
"Momina, ina fata da burin na ga kin samu rayuwar jin daɗi ta daula irin wannan ko fiye da hakan. Allah ya sa ki zama matar Huzaif."
Husna ta yi dariyar farin ciki gami a yin farr da idanu.
"Amin Antina. Fita za ki yi?"
"Eh, zan je wani wuri ba jimawa zan yi ba."
Ta gyaɗa mata kai da fatan dawowa lafiya. Husna ta bi gidan da kallo sadda Antinta ta shiga mota direbanta ya ja. Hasko ta take yi a irin wannan daular ita da Huzaif ɗinta.
***
Hajara da ƙawarta Waleeda ce zaune a gaban wani ƙasurgumin boka.
"Yanzu me kike so a yi?" Tambayar kenan da ya watso mata. Ta sauke ajiyar zuciya.
"Ina son komai a bi shi daki-daki, ba na so a yi ƙwaf ɗaya ne. So nake a fara haddasa rashin jituwa a tsakaninsu, ta yadda wasu lokutan zasu yi ta faɗa da juna, soyayyar dai ta dinga tafiyar hawainiya. A ƙarshe kuma idan lokacin da za'a raba tsakaninsu gaba ɗaya ya zo, zan yi magana."
Boka ya yi dariya.
"Ai wannan ba abin tashin hankali ba ne. Aiki ne ƙarami, aljani kawai za'a tura musu, kowanne ya dinga jin haushin ɗan uwansa.."
"A'a, so nake shi ya dinga jin haushinta, ba na son ita ɗin komai ya sauya a tare da ita dangane da mu'amalarsu "
"Na fahimta, a kan shi yaron zamu yi aiki kenan."
Hajara ta jinjina kai tana murmushi.
"Akan sa ne. Huzaif sunansa."
"An gama. Kar ki samu damuwa. Ku ba ni nan da sati komai za'a yi shi a ƙare."
Hajara ta dubi Waleeda suka yi murmushi kafin ta ɓalle bakin jakarta ta fiddo maƙudan kuɗaɗen da ba ta san adadinsu ba ta ajiye a gabansa. Daga haka suka tashi suka fice.
***
Shirye-shiryen soma jarrabawa kawai Sadiya ke yi, sai ya kasance ƙarfe huɗu take dawowa gidan domin koda an tashi sukan tsaya bitar da ake musu a makarantar.
Kamar koyaushe, yau ɗin ma tana falon Innarta tana karatun jarrabawa, wani al'amari ya faru tsakaninta da Huzaif da ya ɗaure mata kai. Layinta ya kira a yammacin daidai lokacin da ta ba Inna waya suna magana mai muhimmanci da Adda Ruƙayya wacce take kusan sa'ar Innar amma kuma sunan na Adda Ruƙayya ya bi ta tun suna yara. Sun ɗauki lokaci mai ɗan tsawo suna tattaunawa duk dai akan abin da ya shafi zuwa Gombe da zasu yi biki a zuri'arsu.
Sun shafe kusan mintuna goma sha biyar kafin daga bisani su yi sallama, Sadiya da ke a falon Inna ta baza litattafai tana karatu ta ji shigowar Inna da kuma wayar da ta ajiye mata ta fita. Ba ta ma ko dubi wayar ba don ita a yadda ta saka karatun a rai, gani take idan fa ba ta mayar da hankali ba toh ba za ta samu ta haye darussan da za su taimaka mata kai wa ga gaci ba, abin nufi, watarana a wayi gari ta soma karantar fannin Likita da ta ke muradi. Daidai da Jamb da aka zana kwanakin baya, Malam sam bai bari ta zana ba don yana kan ra'ayinsa na cewa matuƙar ba ta shiga ɗakin aurenta ba to fa ba za ta soma karatu ba. Idan ta tuna sanadin Anti Hajara ne mahaifin nata ya sauya ra'ayi takan ji ƙarin tsanarta a