Showing 117001 words to 120000 words out of 124441 words

Chapter 40 - Kazar Kwanci Hausa Novel Complete

ta tattara kwanukan da komai cikin kwandon.

A gefen Maina kuwa, wayar yake yi amma kuma hankalinsa na gare ta, shi kansa sai ya ji zuciyarsa ta sanyaya. Ko babu komai ya saka rai cikin farin ciki. Duk sadda zai kalle ta, ko tana ɗaure fuska ko kuwa yanayinta ya yi kama da mai ɗauke da tsantsar damuwa. Wannan ne karon farko da ya ga walwalarta, duk kuma akan ya yi mata zancen makaranta. Har ta fice ta kuma dawowa bai ajiye wayar da yake kai ba, ita kuwa tana son ta ce masa sai da safe gudun kar ta yi laifi ya ce an fasa karatun, amma kuma ganin wayar ba ta ƙare ba ce kawai sai ta fice.

Koda ta shige ɗakinta bayan rufe ko'ina da kashe kayan wuta, wani juyi ta shiga yi tana ƙara hamdala ƙafin ƙarshe ta zauna saman ɗan kujera mai kamar gado dake gefe guda a ɗakin tana murmusawa. Ba don dare ya yi ba ai da ta kira Innarta da Anti Hafsatu ta ba su wannan albishir ɗin. Ta soma yarda Maina na da kirki, kamar dai ba yadda ta zace shi ba a farko. Ta kula kuma kamar shan ƙamshi da magana ƙasa-ƙasa ɗabi'arsa ce. Yana yi ne tamkar ba ya son yi. Wannan daren dai haka ta kwana zuciyarta wasai sai tunani da begen maganganun Maina, musamman da ya ce zai zauna da ita matsayin 'yar uwa. Ita ba ta ga wani aibu a hakan ba.

***
Washegari kamar koyaushe a ka kawo musu abin kari. Har ta yi wankanta ta yi shiri cikin wani material mai baƙi da adon light green ɗin fulawoyi Maina bai sauko ba. Ƙarshe ma sai da ta gaji da jira ga yunwa da ke nuƙurƙusarta har ta yi zaman haɗawa kanta shayi don lokacin sha ɗaya saura. Zamanta kuwa ba jimawa sai ta ji motsin saukowarsa, kallonsa kawai ta ke ya yi wani irin kyau cikin shigar ƙananan kaya marasa nauyi. Ya ƙaraso ya ja kujera ya zauna. Sadiya ta ɗan russuna ta gaida shi. Ya amsa kafin da mamaki ya ce.

"Me kike ba ki yi breakfast ba har yanzu?"

Ta ɗan tsuke baki cike da ɗan jin kunya, haka kawai to sai ta ce shi ta ke jira alhalin babu dalilin jiran nasa?

"Ban ji yunwa ba ne sai yanzun."

"Ok." Abin da ya furta kenan. Kamar jiya ta haɗa masa komai sannan ita ma ta yi nata haɗin ta zauna a ɗarare ta shiga karyawa. Jifa-jifa sukan haɗa idanu ba ta gayya ba kuma lokaci guda su ɗauke kai. Ya riga ta tashi a wannan karon saboda yana da aikin da zai yi, meeting za su yi ta Zoom da wasu ƴan ƙasar waje duk a kan kamfaninsu na can. Har ya soma tafiya ya tsaya ya ɗan juyo.

"Idan da hali ki jinkirta gyaran ɓangarena zuwa nan da ƙarfe ɗaya. Akwai aikin da zan yi mai muhimmanci ne."

"Toh. Allah ya ba da nasara."

Addu'arta ya sa ya juyo gaba ɗayansa har gangar jikin yana murmushi ya lumshe idanu kadan ya bude a kanta ya ce.

"Ke ba kya rowar addu'a?"

Ta yi murmushin ita ma da ɗan mamaki ta ce.

"Rowar addu'a? Dama akwai masu yi?"

Sai ya ɗan taɓe baki gami da ɗaga kafaɗa kaɗan amma kuma ya rasa amsar bayarwa don haka ya ce.

"Ƙila."

Daga nan kuma ya juya ya koma saman, ta bi shi da kallo tana dariya kaɗan. Ban da Maina to wa yake rowar addu'a, ita kam ba ta taɓa ji ba. Ta dai lura cewa kenan yana jin daɗin addu'arta kuma sai ta ji za ta ƙara daɗa ƙaimi wajen yi mishi a fili da ɓoye.

"Ɗan ƙauye ya yi agogo." Furucin da ya fito daga bakin babbar baiwar Fulani kenan wato Sailuba sa'ilin da ta shigo falon Sadiya ta iske ta zaune tana shan haɗin fruitsalad a gefenta Bintu ce zaune ta maida hankali ga kallon shirin daɗin kowa a talabijin, sai ko Karima da ta buɗe musu ƙofar. 


Sau ɗaya Sailuba ta taɓa shigowa sadda Gimbiya Saudatu ta zo amma hakan bai sa Sadiya ta gane ta ba, koda dai bai wuce na mamakin irin kallon banza da haɗe-haɗe ran da ta dinga yi mata ba a wancan shigowar kai ka ce ta fi ta matsayi a gidan. Wannan karon Sailuba tafe take da wata budurwa mai sanye da kayan da ta zuwa yanzun ta gane uniform din bayin gidan ne. Kamar ba su da sukunin sanya suturar da suka so sai ranakun juma'a. A yadda ta ji daga bakin su Karima da Bintu, har ranakun bukukuwa a gidan da kuma shagalin sallah suna iya sanya suturarsu kamar kowa. 


"Sannu da zuwa." Cewar Sadiya tana mayar da cokali mai yatsun da ke a hannunta cikin bowl din da yake ajiye saman teburin gabanta. 


Sailuba sai da ta ɗan yamutse fuska kafin ta gaishe da Sadiya kamar ba ta so. 


"Barkanki da rana, an wuni lafiya? Dama mai girma Fulani ce ta turo ni."


Abin da ta furta kai tsaye kenan ba ta ko ba da dama ga Sadiya ta amsa gaisuwar ba. Bintu da Karima suka ɗan kalli juna da mamakin Sailuba, koda dai ba yau suka san ita ɗin ba ta da kirki ba, su kansu a farkon zuwansu masarautar daga wadda aka ba da kyautarsu sun sha wahala a hannunta matsayinta na manyan bayi da suka jima a gidan kuma iyayensu da ma yara da jikoki duka suna nan. 


Sadiya jin an ambaci surukarta sai ta ƙara maida hankali sosai ga Sailubar bayan ta dubi ƴar budurwar da ba ta fi shekarun Husnarsu ba.


"Kyautar baiwa ta baki, tana da tabbacin ba za ki ƙi kyautarta ba. Sunanta Jidda. Idan ma babu gurbin wani abu da za ta yi maki, to bisa umarnin Fulani ta ce a maida ɗaya da cikin Karima da Bintu can ita kuma ta maye gurbin ɗaya."


Abin ya yi wa Sadiya wani irin girma a kai, ta ji gaba ɗaya ranta babu daɗi. Wannan ai sai dai kai tsaye ya zama umarnin ba wai kyauta ba. Ta ɗan dubi Bintu da Karima waɗanda kansu ke ƙasa, jikinta ya yi sanyi. Ta fara sabo da su, suna da daɗin zama. Ga kuma ilimin da suka fara  ba ta na yadda lamuran masarautar ke gudana. Ta ji za ta karɓi Jidda saboda kiran da Sailuba ta yi mata da umarnin Fulani, amma ba don ta san taƙamaiman abin da za ta dinga yi ba. Ɓangaren mijinta ne dai har abada idan da rai da lafiya ba ta ga abin da zai sa ta ba da fuskar wata ta gyara ba. 


"A cewa Fulani na karɓi kyautarta da girmamawa. Na kuma ji daɗi. Allah ya ƙara girma." Ta faɗi tana ɗan murmushi. Sailuba da har a sannan ranta a haɗe yake ta amsa. 


"Zan isar da godiyarki. Na bar ku lafiya."


Daga haka ta miƙe daga zaune da ta yi a saman kafet ta fice tana barin Jidda a nan zaune. Ita kuwa Sadiya ta kai duba ga  tafkeken agogon dake bangon ɗakin. Saura mintuna kaɗan ɗaya ta buga, wato dai Maina ya kusa kammala meeting ɗin da ya ke yi. Ta dubi Jidda, baƙa ce ga wasu billaye a gefen kuncinta duka biyun. 


"Jidda."


Ba tare da ta kalle ta ba ta ɗan ƙara ranƙwafa kai.


"Na'am ranki ya daɗe."


Girgiza kai Sadiya ta yi. 


"Anti za ki dinga ce min kin ji ko? Ɗago ki kalle ni." Ta ɗago kai ta dube ta.


"Ina fatan zamu yi zaman amana da ke?"


Ta yi saurin maida kanta ƙasa ƙirjinta na lugude tana tuna babban maƙasudin kawo ta aiki a gidan. Amma a fili ta daure ta gyaɗa kai ta ce. 


"Da yardar Allah ba za ki same ni me cin amanarki ba Anti. Zan zauna da ke zuciya ɗaya."


Tana murmushi ta amsa da Allahu ya sa. Nan kuma ta gabatar mata da Karima da Bintu matsayin masu taimaka mata da wasu aikace-aikacen. Ta ce dai ta dinga taimaka musu da wasu ayyukan. Daga haka kuma ta miƙe a ɗan gaggauce ganin har ƙarfe ɗaya ta buga da mintuna, kamar jiya, haka ta yau ma ta ɗauki kayan abincinsa niƙi-niƙi har Karima na taimaka mata da zuge kofar gilashin hawa benen. Jidda ta bi ta da kallo.


Ba ya falon amma kuma ga takardu a saman kujeru da tebur da tarkacen wayoyinsa da ma laptop. Ga dukkan alamu ma bai jima da shiga ɗakin ba. Ta ajiye tray ɗin a gefe, tana so ta tattara amma kuma sai take tunanin ko dai bai kammala da su ba, kawai sai ta nemi wuri ta zauna tana jira ya fito ta ji ko yanzu zai ci abinci. 


Ba ta jima zaune ba sai ga shi. A farko kasancewar bai san da mutum ba sai da ya ɗan firgita amma kuma iyaka zuci ne bai nuna a fuskarsa ba. 


"Barka da rana." Ta yi furucin cike da girmamawa. Bai amsa ba sai da ya shigo falon ya nemi wuri ya zauna yana ɗan kwantar da kai jikin kujera don ji ya yi duk ya gaji ga yunwa.


"Barkanki dai. Me na samu?"


Ya ƙarashe yana kai duba ga inda ta ajiye kayan abincin ɗin da ya hango. Daga yanayinsa ka san yunwa ya ke ji. Ta kuwa miƙe tana dubansa. 


"Ina iya tattara takardun nan?"


Kansa kawai ya gyaɗa yana ƙare mata kallo. Anya kuwa za'a kira surarta da ciko? Kai wannan ya bar yi masa kama da acuci. Ya kauda kai yana lumshe idanunsa cike da ɗan jin haushin kansa, to wai mene ne dalilin da zai dinga yi wa 'yar mutane kallon ƙurilla? Alhalin so ya ke kawai su saba su ɗan shaƙu ya zame mata kamar abokin shawara? Ya tuna wayar da AbdulMajid ya yi mishi a jiya bayan fitarsa, ƙin ɗagawa ya yi saboda bai ma san me zai ce masa ba. To kiran na mene ne bayan da ya gama aikata abin da ransa ke so? Idan ya ce ba ya kewar dan uwan nasa ma ya yi ƙarya, amma kuma har yanzu yana fushi da shi sosai kan wannan zalunci da ya yi ga 'yar mutane da ma watsawa iyayensu ƙasa a idanu. 


Ya buɗe lumsassun idanunsa waɗanda gajiya da ma yunwa da bacci ke ɗawainiya da su ya na duban Sadiya ta nutsu wajen zuba masa shinƙafa da miyar kayan ciki. 


Toh wai shi ya san Fareeda amma kuma idan har zatonsa akan Sadiya na ciko ya kasance ba haka ba ne, ya rantse bai ga abin da Fareeda za ta nuna mata ba. Ƙuruciya, hasken fata, dogon hanci, dara-daran idanu, leɓɓanta kamar da reza aka yanka 'yan...


"Bismillah." 


Muryarta ta katse shi daga tunanin da ya cilla, gaba ɗaya sai ya kauda kai yana ɗan shafa sumarsa cike da jin kunyar kamun da ta yi mishi kafin ya waske ya zauna sosai. 


Ita kuwa Sadiya da rawar hannu ta kammala zuba masa abincin saboda ta saci kallonsa ya fi a ƙirga tana ganin idanunsa da ke mata matuƙar kwarjini a kanta, ƙirjinta ya cigaba da lugude. Ta kasa gane dalilin wannan kallon ƙurillar. Daƙyar ma ta iya samun damar mishi magana, ganin ya gyara zama ne ya sa ta ɗan miƙewa ta buɗe firij ɗin dake falon, gorar ruwa da lemu ta fiddo ta ajiye gami da ɗaukar kofi ta tsiyaya masa ruwan. Kasancewar hailarta ya zo ya sa ba ta yi yunƙurin tafiya gabatar da sallah ba sai ta soma kokarin shiga ɗakinsa da zumar gyara. 


  "Abinci fa?" Maina ya furta ba tare da ya dube ta ba wannan karon. 


"Na sha fruitsalad ba na jin yunwa sai zuwa anjima."


Bai ce komai ba ya yi bismillah ya fara cin abincin, ita ma ta yi wuf ta faɗa ɗakinsa, sai a lokacin ta sauke nannauyan ajiyar zuciya na samun nutsuwa. A hankali ta taka ta fara da kwashe kayan da ya cire ta saka a kwandon dake can gefe na kayan wanki. Undies ɗinsa kuwa ta tattare, tana tunanin ko ta wanke su ko kuma ta bar su? Duk da a huɗubar da yayyunta suka yi mata har da na wanke su tas. Amma kuma gudun wata fassarar daga Maina ya sa ta tattare su wuri guda ta ajiye bayan ta ninke. Ta fito ta ɗauki tsintsiyar laushi da makwashin shara ta koma har a sannan bai kammala ba, duk da ba ta ƙara kallonsa ba ta ji a jikinta dai kamar ya bi ta da kallo. 


Sai da ta kammala gyaran ɗakin kafin ta faɗa wankin banɗaki bayan ta cire abin hannu da agogonta ta ajiye a gefen gado. Ta saba ko a gida idan za ta yi muddin siket ne a jikinta to fa sai ta ɗage shi sama har zuwa ya wuce gwuiwarta ko kuma ta cire shi ta ɗora zani idan ko ba haka ta yi ba to ba ta yi cikin daɗin rai. Don haka ta tattare siket din har ya haye gwuiwarta, tunaninta ai ba zai shigo ba tunda dai ya san tana ɗakin don haka hankalinta kwance ta shiga aiki. Cikin Jacuzzi ɗin ta shige ta hau wankewa da ruwan omo mai ƙamshi da ya sha hypo. 


"Ba ki kamma..."


Muryarsa ya sa ta razana garin ta juyo ta santsi ya kusa kwasarta da sauri ta kama makunnin shower ba ta ankara ba kuwa ruwan ya soma jiƙa ta tsabar ma tsoro ya sa ta kasa kashewa. Ba ta yi aune ba ta ji hannun Maina a saman ƙugunta, ya jawo ta da sauri kafin ya sanya hannu ya kashe shower ɗin. Inda ma Allah ya taƙaita mata na ruwan sanyi ne. 


Idanunta a runtse ta kasa buɗewa sai da ta ji ya ɗaga ta cak ya fiddo ta daga cikin wajen kafin ta zaro duka idanunta tana kallonsa, shi kuwa bai ko dube ta ba har sai da ya dire ta a ƙofar banɗakin. Matsananciyar kunya ta saka ta sadda kanta a ƙasa tana gyara zaman siket dinta. Shi kuwa kauda kansa ya yi daga kallon ƙurillar da yake bin surarta da shi tun daga sama wanda ruwa ya jiƙa mata saman rigar ya yi kwanci luf a fatarta har zuwa santala-santalan ƙafafunta farare ƙal don har sun ma fi fuskarta hasken ya koma banɗakin ya ɗauko farin tawul wankakke a jikin towel hanger ya miƙa mata yana satar kallon zilin kitsonta da ya yi kwance luf a gadon bayanta sakamakon ɗankwalinta da ya zame ya fice sadda zai ɗauko ta. 


"Ki na iya amfani da shi. Take care please."


Ta sa hannu ta karɓa don godiyar ma ta kasa sai ƙirjinta da ke lugude. Ba ta ƙara sauraron komai ba ta shige banɗakin karo na biyu har da ɗan gudunta. Maina da ya ƙarasa wajen kayansa da nufin sauya tshirt ya juyo yana murmushi ya dubi hanyar da ta bi, wannan karon ma har da rufo banɗakin. Ɗan taɓe baki ya yi yana son kawar da abin da idanunsa suka gani na daga ƙirarta amma kuma ya kasa. Har ya sauya riga ya fice zuwa banɗakin falon don kama ruwa da ɗora alwala ba ta fito ba. Wayoyinsa ya ɗauka da muƙullin mota ya fice har a sannan murmurshi ke zuwar masa da zarar ya tuna Sadiya. 


Ita kuwa sai da ta ji ficewarsa a ɗakin kafin ta ƙarasa da sauri gaban madubin dake a bangon banɗakin tana kallon jikinta, ƙirjinta daga sama a bayyane ga kuma ruwan da ya jiƙa mata rigar daga sama ta kwanta a jikinta. Haushin kanta ya kama ta, ta cije leɓɓanta, yanzun da wane idon za ta ƙara duban Maina? Ta ɗan dunguri kanta da yatsa kafin ta ja guntun tsaki, har ta juya ta kuma juyowa a hankali ta kai hannu ƙugunta, wai nan fa ya riƙe mata ko?


'Na shiga uku.' Ta furta a zuci, kamar lokacin ya faru, ta tuna ai har ɗaga ta ya yi cak ta kuwa yi saurin rufe fuskarta da tafukan hannayenta. Ranar dai haka ta ƙarasa gyarawa Maina wurare cikin tunanin ta yadda za ta yarda su haɗa idanu da shi kuma. 


***

 Khamees ke zuba zance amma gogan kusan rabin hankalinsa ba ya gare su, da zarar ya tuna yanayin da a yau ya gani a Sadiya sai ya hau murmushi. Tun Khamees bai ankara ba har dai ya fahimci Maina ba ya tare da shi don haka ya ajiye laptop ɗin ya zuba mishi idanu. Ganin haka Maina ya kalle shi. 


"An yi wani abu?" 


Shi ma Khamees wannan karon murmushin ya yi. 


"Kai zan tambaya ranka ya daɗe don na kula kamar an fito ne daga gida kawai amma zuciyar tana can."


Nan da nan Maina ya ɗan sha mur yana waskewa da ɗan jan hanci kai ka ce mura ya ke yi. 


"Shirme lokacin aiki?" 


Khamees ya yi dariya. 


"Kuma kamar ba daga gare ni hakan ya ɓullo ba ko?" 


Ɗan guntun tsaki Maina ya ja yana ɗaukar wayarsa ya shiga dannawa. 


"Ya batun tafiyar?"


"Tana nan. Sai dai ni bana jin zan je saboda motocin da za su iso daga Lagos, zan jira. Dama an fi buƙatarka a can ɗin. Zai fi kyau ku tafi tare."


Cikin rashin fahimta Maina ya dube shi dakyau ba tare da ya ce komai ba, Khamees kuma ya riga da ya fahimci ƙarin bayani yake nema. 


"I mean tare da Madam ɗinka."


Shiru ne ya biyo baya, toh akan me zai je da ita? Me za ta yi a can shi da aiki ne zai kai shi? Sai ya haɗe rai don kar Khamees ya cigaba da zancen. 


"Ba wasa zai kai ni ba. Ka fi kowa sanin ba na haɗa aikina da komai."


Jinjina kai Khamees ya yi yana murmushi, kamar kuma ba zai ce komai ba sai ya ce. 


"Hakane, ba lallai kuma tana da passport ba, nan ma zai iya janyo a ɓata lokaci."


Ya ƙarashe yana danne dariyar da ke cin sa, ya san tayin ya yi wa Maina kwarai, amma kuma bai gama yarda kamar ya fara son Sadiya ba alhalin alamu sun fara nunawa musamman ga shi da ya san waye Mainan tun ƙuruciya. 


Shi kuwa Maina ya kasa cewa uffan ma sai danna wayar dole, bai taɓa tunanin kodai ya je da ita ba sai yanzun. Ƙila ma su saba da ita sosai. Kawai so yake ya ga suna tare ta sake da shi tana masa hira sosai. 


***

 Fulani ke duban Jidda fuskarta ɗauke da zallar takaici. 


"Ki ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login