Showing 39001 words to 42000 words out of 124441 words
dai don Allah kar ki bari ƙibar taki ta fi haka. Masha Allah dai kin yi kyau kowa ya ganki ya san kina cikin jin dadi."
Ta yi wani fari da idanu.
"Ki ce idan na je gidanmu zan firgita Mairamu. Za ta ƙara fahimtar cewa na samu mijin kerewa sa'a da har abada Sadiya ba za ta samu irinsa ba. Momina kuwa miji sai wanda ta zaɓa."
"Mamaki kike ban Autar Mama, koda dai bai kamata na yi mamaki ba, a baya ni ma rashin fahimta ya sa na yi wa Inna..."
Wata dariyar da Hajara ta kwashe da ita ta yi sanadin katsewa Safiyya magana, Hajara ta ɗan yi tafi cikin dariya ta ce.
"Yau Anti Safiyya ke da bakinki ki ke kiran Mairamu da sunan Inna? Ah lallai Mairamu sai ta ƙara wa Bokanta kuɗi, ku dai na san ta gama da ku, ni kuwa ba na jin za ta yi nasara a kaina domin kuwa wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa, kuma ni Hajara ba duk kai ba, na fi ƙarfinta."
Safiyya ta fusata sosai.
"To aikuwa kin yi baƙar asara, tunda dai ke babu wani sauran abu a duniyarnan da zai sa zuciyarki ta yi laushi akan matarnan, sai dai nace maki Allah ya ganar da ke. A bayan ma da na dinga biye maki muna cutar da ita, rigakafi ne kafin ta cutar da mu irin na matan uba, mu nuna mata da wayonmu. Sai ko kishin da muke yi ta aure mijin Mamarmu. Sai dai kuma daga baya na gane tsantsar wautarmu. Koda dai an ce aure ma kaɗai kan koyar da ɗan adam darussan rayuwa, wayasani ma ko shi ne dalilin da ƙannen Mujahid suke takuramin a gidan nan. Kuma wayasani dalilin kenan da har yanzu ban samu ciki ba."
Safiyya ta ƙarasa zancen cike da raunin zuciyar da har ya yi sanadin ciccikowar hawayenta. Wannan duk bai taɓa zuciyar Hajara ba sai ma haushi da ta bata.
"To ke ki ka ga za ki iya ɗora wa kanki wahala. Aure idan babu daɗi dole ne zama a cikinsa? Lallai ma Safiyya. Allah ba don Mujahid yana da kambun susa ba da sai na ce ki kashe auren kawai. Ke ki kashe ma cikin abokan Mijina ba sai ki samu wanda ya fi shi ba. Kuma kar ki kara haɗa ƙaddararki da alhakin waccan matar, wane haƙƙinta aka ɗauka? Dama gida ai na ubanmu ne ina ce? Toh mene ne laifinmu don mun nuna ba ma ra'ayinta? Wallahi uban kuturu ya yi kaɗan ace wai wani haƙƙin Mairamu ne ya shafe ki. Kuma kannen Mujahid su Munawwara ko? To zan shiga gidan nasu yanzu na ci ubansu sai na wuce. Ga tsarabarki nan."
Hajara na kai wa nan ta shiga tattare komatsanta za ta fice. Hankalin Safiyya ya tashi ba don komai ba sai ji da ta yi wai za ta shiga gidan surukanta wanda yake a bayan layinsu. Nan da nan ta riƙe hannunta tana zaro mata ido.
"Ke bana son hauka, dangin mijinki ko nawa? Wallahi ban ba ki iznin shiga ba, ki ka matsa sai kin shiga yanzu zan kira Malam na faɗamasa. Ki rufa min asiri kar ki kashe min aure."
Hajara jin za ta faɗawa Malam ya sa kawai ta yi ƙwafa. Wannan ne kawai zai hana ta zuwa, ta samu daƙyar Abba ya sulhunta su da Malam ɗin, ana kukan targaɗe ga karaya kenan. Sai ta fasa niyyarta. Ta ja guntun tsaki
"Na ji, babu inda zan je. Na fasa. Amma tafiya zan yi, gidan Anti Hafsatu zan wuce daga can zan je gidanmu."
Tana kallon yanda Safiyya ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi, ita Hajara ma sai mamakin wannan tsoron na Safiyya ya kama ta. Tab, ita wa ya isa ya sanya ta tsoraci wasu dangin miji? Ai ko miji ya yi kaɗan ya taka ta balle wata kishiya ko dangin miji.
"Ke, ni ban ma yi maki zancen Sadiya ba. Huzaif ɗan gidan Mami ne ke son ta, batun da nake maki sati mai zuwa zai turo magabata a tsaida magana."
Ta ji zancen kamar an ƙwala mata guduma a tsakar kai. Sadiya? Aure da wuri? Tsabar baƙin cikin da ta shiga da ruɗu ta ma mance su waye waɗanda Safiyyar ta lissafo. Don haka daƙyar ta motsa leɓɓanta da suka yi nauyi ta ce.
"Wane Huzaif? Wace Mami kuma?"
Ita kuwa Safiyya wacce ta ji haushin kanta da yin suɓul da bakan sanar da Hajara wannan batu alhali ta san ba daɗinsa za ta ji ba, ta ji inama ba ta ce mata uffan ba. Daƙyar ta amsa tunda zai ai magana zarar bunu ce, idan ta fito ba ta komawa ciki. Sabon da suka yi irin wanda idan ɗaya ya ji magana a dangi sai ya fesawa ɗaya, ya mantar da ita komai.
"Huzaif ɗan Haj Mariya ɗan gidan Abba fa, mai karatu a ƙasar Indiya."
Sai a lokacin ta tuno waye hakan. Wata uwar ashariya ta lailayo har da fiddo idanu waje.
"Wai dagaske ki ke wannan maganar? Huzaif fa?"
"Toh meye?" Safiyya ta nemi sani.
Girgiza kai Hajara ta shiga yi ranta a matuƙar fusace.
"Aa, na rantse Sadiya ba za ta auru yanzu ba. Har abada Sadiya ba za ta yi auren ba, baƙin cikin da Uwarta ta ɗanɗana min, na rantse ita ma sai ta ɗanɗana shi akan Sadiya. Mu zuba ni da su."
Tana kai wa nan ta yi gaba ba ta ko saurari salatin da Safiyya ta saka ba da kwala mata kiran da ta ke. Safiyya ta girgiza kai. Ta sani babu abinda Hajarar za ta iya tunda dai kowa da kalar ƙaddararsa a rayuwa. In sha Allahu rayuwar Sadiya zai inganta ba dai ta tagayyar ba. Ita yanzun suna ɗasawa da Sadiya don ma ta kula yarinyar ba ta gama mance abin da ya wuce ba, ba kasafai ta ke zuwa gidanta ba sam.
Hajara kuwa da ta fito da zummar ziyartar har can gidansu ko don ta ga Husna da Malam, sai ta ji kamar ta fasa, gidan Anti Hafsatun ma a tsaitsaye ta shiga ta ba ta tsarabar da ta yi mata da yaranta sannan ta wuce. Haka ta daure ta nufi gidan nasu, har wani ƙwalla ta ji sun cicciko mata na jin wani zazzafan ɗaci a kirjinta, hasko Sadiya kawai ta ke yi cikin jirgi ta lula Indiya. Wato kenan ma su haɗa kafaɗa da kafaɗa a auren mai arziki? Aikuwa ta ci alwashin hakan ba zai taɓa samuwa ba.
***
Sadiya na zaune tana tilawar Alkur'ani inda za ta kai hadda a gobe Asabar, kokarinta ta ga ya zauna a kanta yanda ya kamata. Inna ta fita zuwa wurin Kawunta Jibo. Husna kuwa na ɗaki tana baccin yamma wanda ya riga ya zamar mata jiki. Tashin duniya Sadiya ta yi mata amma tana ji ta yi banza da ita. Ita kuwa ganin rashin kunyar Husna gare ta ya dawo har ya ninka na baya sai abin ke ɗaure mata kai, ƙarshe ma ta tattara ta watsar da ita a gefe. Ta ƙara takatsantsan da duk abin da zai sa ta yi mata rashin kunya, waya ce dama wani lokacin idan ta Inna ba ta kusa Huzaif ke kira a na Husnar, daga baya ma sai ta ƙi sanar da Sadiya ya kira sai ko idan ya neme ta ta wayar Inna take sanin ya kira Husna amma ta ce mishi ba ta gida. Yanzu kuwa ta mallaki nata wayar, sabuwa dal a kwali Huzaif ya kawo mata ƙirar Samsung. Ko ɗaukar wayar Husna ba ta yi ba ballantana ta gwada murnarta. Jikin Sadiya yana sanyi sosai da lamarin ƙanwarta, Inna ta ce ta yi shiru kawai ta zuba mata idanu.
Sallamar Hajara da ta yi a can ƙasan maƙoshi, ya dakatar da ita daga ɗora karatun da za ta yi bayan ta kai aya. Sai da ta ji ƙirjinta ya buga ta shiga ambaton Allah. A duniya ba ta san sadda za ta bar shakkar Hajara ba gaba ɗaya, duk sadda ta ji murya ko ta ga ta shigo wuri, to fa irin wannan faɗuwar gaban sai ya same ta. Tana gaba, wasu yara su biyu na biye da ita dauke da wasu manyan ledoji masu rubutun larabci a jiki.
Hajara kuwa sai idanunta ya gane mata Sadiya kamar wani mugun kyau ma ta ke ƙarawa, tana cikin hijabinta ruwan ƙasa take zaune, wato idan har Sadiya ta faɗa gidan jin daɗi ai sai ta ce Hajara kauce ba ki iya gayu ba, don ta sani komai zai fi karɓarta fiye da ita, idanuwanta suka kai ga wayar dake gefen Sadiyar mai ɗaukar ido sosai. Ba ta ko amsa gaisuwar da Sadiya ke mata ba ta ja tsaki na zallar takaici ta wuce zuwa ɗakin da ya ke nasu a baya.
Husna wacce ke bacci ta hau miƙa jin ana ta tashinta, muryar Antinta ta soma ji kamar a cikin mafarki, can ta wartsake ta gan ta zaune a gefenta. Nan ta kurma wani ihun murna suka rungume juna suna dariya.
Sadiya daga tsakar gidan tana jin su, zuciyarta sai ta yi wani iri. Ita da ƴar uwarta, amma babu damar ta nuna kowane irin murna da ganinta. Ta ji karatun ma ya daina shiga don haka ta miƙe bayan ta yi addu'a ta kai Alkur'anin ɗakin Inna, ba ta ko shiga ɗakinsu ba ta dauki wayarta sannan ta zura silifas ɗinta ta fita zuwa gidan su Zahra. Ta sani Inna ba za ta ce mata don me ba idan har ta ji saboda zuwan Hajara ne.
Husna kuwa ai sai ta nemi bacci ta rasa, fita ta yi da sauri ta wanko fuskarta da baki ta dawo.
"Antina na yi kewarki sosai wallahi." Ta faɗi a shagwaɓe kamar wacce ke gaban mahaifiyarta.
Hajara wacce ganin Husnar ya ɗan lafar da ɓacin ran dake cin ta dangane da Sadiya sai ta yi dariya.
"Ni ma ai haka Momin Anti. Ga tsarabarki dai ko fara gani."
Hajara ta ƙarashe tana janyo ɗaya daga cikin manyan ledojin nan ta ɗora saman cinyar Husna. Bakinta kuwa gaba ɗaya ya ƙi rufuwa. Ta zazzage duka a saman gado, dogayen riguna ta gani har kala uku tsula-tsula. Abaya guda biyu, ɗaya kalar ruwan madara sai ko baƙa. Ɗayar kuwa doguwar riga ce mai mayafinta. Sai turaruka har kala uku da kuma wani tsalelan agogo a gidansa. Husna ta rasa ina za ta saka kanta don farin ciki, yanda ta ke ta faman tsalle da murna ya sa Hajara ta dinga dariya.
Haka ta dinga gwajin kayan nan, kuma aka ci sa'a dayake ta san tsayinta, duk wanda Husna ta saka daidai ita cif.
"Inye, kin ganki kuwa, kamar matar wani Alhajin."
Faɗin haka da Hajara ta yi ya sosa mata inda ke mata ƙaiƙaiyi. Sai kawai ta dawo ta zauna jikinta babu kwari tana ɗan yamutse fuska. Nan da nan idanunta suka cicciko da ruwan ƙwalla. Sai ta kasa cewa komai ma. Hankali tashe Hajara ta ɗan tura kafaɗarta ta yi baya suka dubi juna.
"Ke lafiya? Ni sai yanzu ma da na ƙaremaki kallo na lura kin rame. Momi me suke maki?"
Sai ta ƙarasa fashewa da kukan gaba ɗaya tana ɗora kanta saman cinyar Hajara. Ita ma Hajara da ba ta kai ga jin meke faruwa ba sai ta ji ƙwalla sun cicciko mata. Ɓacin ran Sadiya za ta auri miji ɗan gidan manya da kuma na Husnarta da ke cikin damuwa duka suka turniƙe zuciyarta, wani irin ƙauna take yi ga Husna har zuciyarta. Takan ji kamar Mahaifiyarsu ɗaya. Koda za ta cutar da zuri'ar Inna a duniya, alƙawarina ta ɗaukarwa kanta, har abada Husna ta kuɓuta daga wannan cutarwar. Ba ta katse ta ba saboda ba ta san tun sadda ta ke riƙe da shi ba. Sai da Husna ta yi mai isarta sannan kowaccensu ta share fuskarta, ruwan da ta shigo da shi na roba ɗauke a hannunta ta ɗauka a gefen gadon ta miƙa mata.
"Karɓi ki sha." Ba musu Husna ta kwankwaɗa kafin ta kwantar da hankali ta hau labartawa Hajara yadda ta kamu da son Huzaif tun farkon ganin da ta yi masa har ma da shigar saurin da Inna ta yi har sai da ta haɗa Sadiya soyayya da shi sannan hankalinta ya kwanta. Don a cewar Husna, dukkan komai sanadin Inna ya faru, ta ƙara da faɗin.
"Wannan bai isa ba, ita da kanta ta soma sanar da Malam wai akwai soyayya tsakanin Yaya Huzaif da Sadiya. Malam kuwa ya sami Abba da maganar, batun da nake maki har Mami ta amince don har kiran Inna ta yi a waya ta yi fatan alheri."
"Jar Uban can!" Shi ne abin da Hajara ta furta jikinta har wani mazari yake yi.
©Rufaida Umar
*Kazar Kwanci...*
Yadda ta ga Hajara ta yi mugun ɗaukar zafi abin har tsoro ya ba Husna, ta ji kamar ta faɗi da yawa amma kuma idanunta a rufe suke gam! So ya makantar mata su, ta yi nisan da ba ta jin kira.
Hajara ta girgiza kai.
"Na rantse maki tunda har haka zancen yake, toh ki saka a rai Huzaif ba shi da mata a gidan nan sai ke Momina. Ki saka a ranki cewa zan yi duk faɗi tashin da zan yi na ga ke ki ka aure shi ba Sadiya ba. Amma kar mu yi gaggawa, ki ba ni lokaci zan yi tunani mai kyau don mu san matakin ɗauka. Wato shiyasa har fiffiƙa yarinyar ke yi ta samu gidan danshi. Ai nasan zuwa yanzun kin ƙara fahimtar irin son kai na Inna, sam ba ke ce a gabanta ba, ki lura da duka takunta za ki fahimci ta fi kaunar mai sunan uwarta, ke kuwa ai sunan kishiya ki ka ci, ko mene ne ba za ta so ki samu ba ko din ta ƙuntatawa mu ƴaƴan Mama. Ki saka ranki a inuwa, ai tunda na dawo shikenan. Ba zan bari a yi miki irin wannan cin kashin ba. Zamu bi komai a sannu ta yadda idan bom ɗin ya tashi fashewa, zai girgiza su ba kaɗan ba." Hajara ta ƙarashe da wani irin murmushi na zallar mugunta tunawa da wani abun da ta yi. Tabbas tana ji a jikinta lokacin fara ramuwa ya zo. Daga Sadiya har Innar kashinsu zai bushe tunda abin ma ya shafi har rabin jikinta wato Husna.
Wani sanyi ya shiga ratsa zuciyar Husna, ta ji nan duniya dagasken dai babu mai mata so da ƙauna kamar Antinta. Sai ga shi ta dawo da fara'arta.
"Anti ni dai ki tambayar min Malam ya yarda na biki na yi weekend a gidanki."
"Rufan asiri, ki bari a kwana biyu kin ji? Na fi ki son ki zo, amma ki bari mu ɗan ƙara samun daidaito da Malam. Kin ga tun faruwar abin can yau ne zuwana na farko gida, amma ai an kusa hutun zango na biyu (second term) ko?"
Husna ta gyaɗa kai.
"Yauwa, toh ki sa ranki a inuwa, na tabbatar zuwa lokacin komai ya kara zama daidai, zai bar ki ki zo. Shi ma kuma batun Huzaif ki daurewa zuciyarki ki bar nuna musu wata damuwa a zahiri. Ki kuma sakarwa Sadiya fuska ki cigaba da mu'amala da ita yanda kike yi a baya. Ina da hujjata na faɗin haka. Kar ki bada ƙofar da za su fahimci komai, kin ji Momina?"
Cike da shagwaɓa ta amsa.
"To ni fa Anti ban san dalilin da yasa kallonta ma ba na son yi ba. Inna kuwa na gama fahimtar ni ba ta sona, ta fi son mai sunan Mamarta."
Wannan furuci na ƙarshe da Husna ta yi, wato 'Inna kuwa na gama fahimtar ni ba ta sona, ta fi son mai sunan Mamarta.'
Shi ya yi dirar mikiya a kunnen Inna wacce ta shigo har ta yi sallama ba su kai ga ji ba. Kirjinta ya buga da ɗan karfi, sai ta shiga ambaton Allah kamar koyaushe idan ta ji abin da ya firgita ta ko ma dai a wane irin yanayi. Jikinta ke ba ta cewa Hajara ce a gidan, aikuwa ba ta kai ga gama tantancewa ba sai ta ji muryarta tana wata dariya ga dukkan alamu furucin na Husna ya jefa ta cikin nishaɗi. Sallamar Sadiya ce ta sa ta juyowa ta dube ta.
"Inna sannu da dawowa."
Madadin Innar ta amsa sai ta ce cikin rashin walwala.
"Ko wace ce a gidan, hakan hujja ce ta tsallakewa ki fita? Anya hakan da ki ka yi daidai ne?"
Sadiya jikinta ya yi sanyi.
"Ki yi haƙuri." Hakan ta furta, sauke ajiyar zuciya Inna ta yi kai tsaye ɗakinta ta shige.
Hajara da Husna sai bayan sallama da maganar Sadiya ne ya sa suka fahimci Inna ta dawo. Hajara ta ja guntun tsaki.
"Sai ki kula sosai, ki bar nuna kishinta a zahiri. Komai za ki yi, ki yi shi da takatsantsan."
Husna ta amsa da toh. Nan fa suka yi ta hirarsu, Sadiya kuwa miyar da ta yi ne ta tuwo ta ƙara ɗorawa a wuta don ya yi zafi.
Sai dab da Magriba tukunna Malam ya iso gidan. A lokacin ne kuma Hajara ta fito tsakar gidan. Inna ta dube ta, kamar ta share ta sai kuma ta ji ita ai Uwa ce bai kyautu ta yi hakan ba ko don darajar yan uwan Hajara ɗin da suke mata kallon Uwa a yanzu. Murmushi a fuskarta ta ce.
"Hajara, ashe kin shigo gidan. Sannunki da zuwa."
Hajara kamar ba za ta ce komai ba sai ta daure ta ce.
"Yauwa Mairamu, sannunki ke ma."
Cak! Sadiya ta tsaida ɗaurayar murfin filas ɗin da take yi, wannan sunan da Hajara ta kira da ma yanayin amsawa mahaifiyarta ta ji ɗaci sosai. Amma kuma ta sani, ba za ta iya cewa Hajara komai ba, a ranta ta ƙara ji ta tsani koda ganinta ne. Tunda har ta je gaban ka'aba ta dawo ba ta sauya hali ba, to ba ta jin nan duniya akwai abin da zai russunar da zuciyarta.
Hajara kuwa gaba ta yi zuwa falon Malam. Ta iske ba ya falon ya shiga ɗaki don haka ta mike ta fito don ta san koda ta tsaya ba zai saurare ta ba saboda lokacin sallah ya yi.
Bayan an idar ta ƙara dawowa, sannan ya shigo daga masallaci.