Showing 57001 words to 60000 words out of 124441 words
da mijinta tun samun juna biyunta ya sa yake lallaɓata. Auren da mahaifiyarsa ke kokarin tilasta shi yi, yanzu ita ma ta fasa amma burinta bai wuce Safiyya ta haifi ɗa namiji ba. Wannan yasa suka san akwai sauran rina a kaba muddin ta haifo ɗiya mace. Wataƙila uzzurawar da aka yi mata a baya zai dawo sabo fil.
Inna da Malam sun ji dadi sun kuma yaba. Zakari dake zaune a tsakar gidan inda suka sha ruwa sakamakon zafin da ake a gari, ya dubi Sadiya.
"Ke na ga kayayyakin ma sun maki yawa. Ga Baba Habu ya aikomaki, ga Abba ma har kala uku, ga Yaya Mustafa. Toh ni dai sai dai na siyamaki jaka da takalmi kenan."
"Yaya har da jalbab za ka ɗinko min."
Ta faɗi tana murmushi. Ya jinjina kai.
"Dakyau, in sha Allahu kuwa za ki same su duka. Allah ya nuna mana sallar lafiya."
Gaba ɗaya suka amsa da amin har Hadiyya matar Zakari da ta biyo mijin nata yi musu barka da shan ruwa. A ƙarshe Malam da Zakari suka fice masallaci.
***
Ranar sallah kuwa zuciyoyin kowa cike da farin ciki da murnar sallah ciki har Sadiya. Ta yi shirinta tsaf cikin adon farin jalbab da Yayanta Zakari ya kawo mata ta sanya baƙin takalmi, ta yi kyau tsaf, Inna ma ta sa sabon hijabinta suka ɗunguma zuwa masallaci har Malam. Ranar wuni suka yi ana kawo musu ziyara daga makwafta, dangin Malam har da yaran su Adda Ruƙayya.
Washegari ta yi shirinta tsaf cikin leshinta baƙi mai kwalliyar ruwan madara a jiki, ya sha stones ɗinkin doguwar riga sai walwali take cikin rana, ta yafa mayafinta ruwan madara, tsayawa fasalta irin kyawun da ta yi ma ɓata lokaci ne. Gidan Zahra za ta je kai mata ziyara daga nan ta wuce gidan Yaya Mustafa wanda ba shi da nisa da Zahra.
A jikinta ta ji ana bin ta a baya amma kuma sai ba ta juya ba har ta ƙarasa ƙofar gidan Zahra ta shiga bubbugawa.
"Assalamu alaiki." Ta tsinci murya a gefenta, ta ɗago ta dube shi fuskarta a ɗaure, dogo ne marar jiki kamarta, fari ne tas. Ba shi da wani kyau na a zo a gani sai kwarjini ga shigar kamala. Duk yadda ta so yin tsiwa sai ta kasa ta daure ta amsa sallamar, daidai sadda Zahra ta bude mata ƙofar ta washe hakora za ta yi magana ta hango mutum da sauri ta koma bayan kyauren kasancewar ba ta da gyale a jikinta.
"Au ashe ba ke kaɗai ba ce." Daga nan ta yi saurin komawa ciki, ita kuwa Sadiya da Allah da Annabi s.a.w ya shiga haɗa ta dole ta dakata ta fasa shiga amma ta ƙudurta a rai duk maganganunsa zasu shiga ne ta dama su fice ta hagu. Ta dai ji yace sunansa Suraj, yana kuma zaune ne a unguwar da ta shigo, wato Ɗorayi. Har ga Allah kuma bai zo mata da wasa ba, ƙaunarta yake yi da aure.
Sai a lokacin ta katse shi.
"Ka yi hakuri. Ni yanzu karatu nake yi ba ni da lokacin kula kowane ɗa namiji ma."
Daga haka ba ta ƙara jin me zai ce ba ta shige ciki ta rufe ƙofar.
"Waye shi? Ni kamar kallon sani ma nayi masa duk da a fisge ne."
Tambayar Zahra kenan, Sadiya dake ƙokarin zame mayafin da ta saka ta ja guntun tsaki.
"Ke kika ma kula da shi. Malama na kwaso rana ki ba ni abu mai sanyi."
Murmushi Zahra ta yi tana ƙaremata kallo.
"Kin kuma ja magana ba. Ke kin ga kyan da kika yi ne masha Allah? Kinga fa yadda ƙunshin nan ya kama a yatsunki. Kin rikita ɗan mutane kuma ki.... Ke! Na ma tuna waye, wallahi na gane shi. Amma don Allah me yace sunansa? Suraj ko?"
Sadiya da ke kokarin buɗe firij ta zaro ruwan sanyi na roba tana kokarin buɗewa ta dube ta.
"Haka yace sunansa."
Ai sai Zahra ta hau murna.
"Na rantse maki kin yi sa'a Sadiya, kin san kuwa waye babansa a unguwar nan? Taɓ, ai babban ɗan Alƙali ne. Gidan ƴan boko ne na ƙarshe kuma fa kar ki ce iyakar nan suka tsaya, a'a, akwai ilimin addini da girmama ɗan adam. Sannan akwai rufin asiri daidai gwargwado, shi wannan Suraj ɗin da kike gani kasuwanci yake yi bai dogara da..."
"Zahra, wai zuwa na yi mu yi hirar zumuncinmu ko kuwa dai wancan sillan karan ya biyaki ki yi masa kamfen idan na zo? To kodai bakinku ɗaya?"
Zahra ta yi dariya.
"Ai shikenan, idan ma rabo ne zai tabbata ba sai na ɓata bakina wurin koɗa shi ba. Allah ya yi maki zaɓi."
Yamutse fuska Sadiya ta yi, ta sanyo mata wata hirar daban, haka suka yi watsi da batun Suraj suka yi ta hirarsu. Yan uwan mijin Zahra suka zo nan aka haɗu don dama an ɗan saba suka yi ta hirarsu.
Kwanaki biyar tsakani a yammacin ranar wata Juma'a, Sadiya na zaune tana tattare inda ta kammala yankan farcenta yaro ya yi sallama ya shigo.
"Wai a na sallama da Sadiya."
Daga jin sunanta da aka kira ta tabbata ƴan layi ne, koda ace ma ba su ba ne ba ita ba ta fita sai Inna ta tsawatar. Yanzun ma godewa Allah ta yi saboda Inna ta ɗan shiga duba Iyabo da ke ciwon ƙafa.
"Kai, jeka ka ce ba ta nan."
Ya juya kuwa ya je ya isar da saƙonta. Shiru har Inna ta dawo ba'a ƙara aike ba, sai bayan sallar Magriba ta ƙara jin sallamar yaro ya shigo kiranta. Kafin ma ta amsa Inna ta ce ya je yace tana zuwa. Bayan fitar yaron ta dube ta.
"Mene ne dalilinki na korar duk wani da ya zo wurinki? A tunaninki ba za'a fassara hakan da cewa har yanzu soyayyar yaron can ke ranki ba? Ko a ganinki rashin sauraron kowa ne zai sa a gane an baƙanta maki? To ai ba ki rama ba muddin dai ba za ki ba wani damar fitowa ya aureki ba. Zamanki a hakan ba zai haifar da komai ba gareki sai kananun magana. Idan kin ga dama ki je ki saurari wanda ke tafe, idan kuwa ba za ki ba, ki na iya yanda kika so."
Inna na kai wa nan ta miƙe ta tada kabbarar nafilarta. Jiki a sanyaye Sadiya ta miƙe, ba ta taɓa ganin Inna ta ɓata rai sosai kamar na yau ba wannan dalili ya sanya ta bin umarninta amma daga ita sai hijab din sallar dake jikinta, takalmi kawai ta zura ta fita.
Ta sha mamakin ganin wanda ke tsaye, da ta tuno da yadda Zahra ke kiran waya tana zuba mata naci akan ta saurare shi kuma sai ta shanye mamakin. Ta sani ita ce za ta yi masa kwatancen gidan. Ya yi mata maganganu irin na wanda ya san me yake yi, babu ƙarya sai iyakar gaskiyarsa. Ya kuma nuna mata daidai da gini ya kammala aure ne ya kawo shi ba wasa ba. Idan ma ta yi izni zai gabatar da kansa ga Mahaifinta don a san da zamansa.
Sadiya ta yaba sosai da kamala da mutsuwarsa, ta amince dai su dinga waya amma ta ce kar ya ƙara zuwa har sai ta yanke shawarar kula shi. Abin sai ya ba shi murmushi, ai a ganinsa tunda dai ta ba sa damar waya, shi kuwa ba zai hana ya shawo kanta ba ta amince da aurensa idan Allah ya nufa.
***
Bayan Watanni Biyu...
Ɓangaren Amarya Husna da Angonta komai na tafiyarmata yadda take so, gaba ɗaya soyayyar Huzaif ta ƙara ninkuwa a zuciyarta. Ta rasa ƙarfin sihirin da Antinta ta yi, amma tabbas ko wanne ne, mai azabar ƙarfi ne. Huzaif ta kula har rawar jiki yake yi idan ta nuna tana buƙatar wani abun. Har suka gama cin duniyarsu a ƙasashe uku da Alh Nuhu ya ɗaukar musu nauyin zuwa da sunan Honeymoon idan an cire zuwansu Umarah, sun je Dubai, London sai Misra kafin kuma suka dawo Nijeriya, babu abin da ya sauya daga soyayya da kulawar da yake gwada mata. Ta yi wani irin ƙiba da kyau. Fatarnan ta murje. Shi kansa ya yi kyau abin sa tsaf sai ramar babu dalili da ya yi.
Ranar da suka ziyarci iyayensa, bai samu tarbar kirki a wurin Abba ba bayan gaisuwar da ya amsa mishi. Husna ce ma Abban ya ɗan ja da hira sannan ya fice daga gidan zuwa kasuwa. Mami kuwa ta rasa ina ta saka ina ta ajiye surukarta domin ita fa duk abin da Huzaif ke so, ba ta jin ƙinsa. Ta dai nuna damuwa da yanayin ramarsa. Meenat ko kallo ba su ishe ta ba asalima tana ganinsu ta shirya ta fice zuwa gidan Amira don dama can za ta je da yammacin, amma ganin su Husna a gidan ta fice a tsakar rana.
Sai yamma suka nufi gidan su Husna. Zuwa lokacin Husna ta samu nutsuwa tunda dai suna waya da Innarta da Malam ɗin. Kuma tsabar kissa tana yawan tambayarsu Sadiya har takan nuna damuwar rashin samunta a waya. A lokacin Sadiya ba ta da waya don duk wani abin Huzaif ya bar burge ta, koda Malam ya siyamata wayar ba ta ko buɗe whatsapp ba iyakarta amsa kira kawai. Zuwa sannan ma ita ma ta share tambayarta hankalinta ya kwanta ganin iyayen sun ɗan saki jiki da ita musamman da Hajara ke sanar musu cewa tana ɗauke da juna biyu, sun saka a ransu dama wani ba ya haifar ɗan wani.
Inna sakin baki ta yi da mamakin ganin uban ƙibar da Husna ta ƙara narkawa. Sai kuma ta yi ɗan murmushi tana amsa gaisuwarta, shi Huzaif kasa shigowa ya yi cikin gidan, iyakarsa can falon Malam suna gaisawa.
"Inna na yi kewarku sosai, don Allah ina ƙara neman gafara idan na."
"Ya isa Husna, komai nufi ne na Allah, ita kanta Sadiya a yanzu zancen da nake maki ta samu mijin aure. Ai matar mutum kabarinsa."
Husna ta ji wani farin ciki sosai a ranta, dama ai tana son ƴar uwarta kawai dai soyayyarta da Huzaif ne ya sa ta fice a ranta. Yanzu kuwa tunda ita ke aurensa, to Sadiya ta auri duk mijin da ta so babu abin da ya yi mata zafi.
"Kai amma na yi murna, Allah ya sanya alheri. Amma Inna shi ne kika aike ta gidan Kawu alhalin kinsan da zuwana?"
Ta ƙarashe murya a shagwaɓe, Inna ta yi murmushi karo na biyu. Sadiya tun da ta ji daga gareta cewa Husna zasu zo gidan ta ji gaba daya ba ta da sukuni. Dole ta ƙirƙiro fita zuwa gidan Yayanta Zakari wajen Hadiyya. Inna ta fahimci yanayinta wannan yasa sam ba ta hana ta barin gidan ba. Ai sam ba ta fatan a maimaita irin wahalar da aka ci a baya kafin Sadiya ta mance Huzaif don sai da aka haɗa da roƙon Allah. Ta faɗawa Husna cewa ita ta aike ta wurin Kawunsu Jibo ne gudun kada ta ce za ta bi sahu tunda gidan Zakari babu nisa sosai da nan ɗin.
Sun sha hira har bayan sallar Magriba sannan suka tafi. Malam ma bai nuna musu komai ba har Huzaif ɗin. A iyakar tunaninsa ai ba zai yiwu gaba daya su tarar masa ba ya kasa samun walwalar kowanne a cikinsu shi da Abban. Dalili kenan ya saki fuska kamar komai bai faru ba. Tsaraba leda guda suka dire musu har da na Sadiya. Sai da suka bar gidan tukunna Sadiya ta dawo. Ko kallon tsarabar ba ta yi ba don ba sa gabanta. Zuciyarta yanda gaba ɗaya ta tafi ga Suraj mai tsantsar nuna soyayya da kulawa gareta.
***
"Aure? Sadiyar ce ta samu miji?" Shi ne tambayar da Hajara ta watsawa Husna ta waya.
"Eh Anti, Inna ta ce komai ya wuce na bar damun kaina." Husna ta ƙara faɗi cike da wauta. Ita duk murna ta ishe ta yanzun za ta dawo alaƙar zumunci da ƴar uwarta tunda dai ta samu wani da take so. Kuma ita ma ta auri zaɓin ranta Huzaif. Ko kaɗan ba ta so ta tuna cewa ƙwace ne ta yi wa Sadiya, ta saka a rai dama can mijinta ne.
"Yaushe za su turo neman auren?" Hajara ta ƙara neman haske.
"Oho, ni ban ma tsaya bincikawa ba. Kawai dai Inna ta ce min ta samu miji aure za ta yi nan kusa."
Hajara ta danne abin da ke taso mata ta ce.
"Hakan ma ya yi daidai, Allah ya nuna mana. Na mata murna."
Ta faɗi ne kawai gudun zargi daga Husna don ta fahimci lamarin ya yi mata daɗi. Bayan sun yi sallama ta kife wayar gami da zama a bakin gadonta tana maida numfashi. Kirjinta har wani ciwo ta ji yana mata duk a dalilin baƙin albishir da Husna ta yi mata wai Sadiya ta samu mijin aure. Girgiza ƙafafu ta shiga yi a fili ta ce.
"Ba zai yiwu ba! Mairama sai kin ɗanɗani baƙin ciki fiye da yadda na ɗanɗana kafin na samu mijin aure. Na rantse ko zan yi yawo tsirara, Sadiya ba za ta yi aure a duniya ba da ƙuruciyarta."
Tana cikin wannan yanayin aka shiga kwankwasa mata ƙofa. Kusan a fusace ta ce.
"Waye?!"
"Gwaggo ce ta zo"
Ta tsinci muryar ƙanwar mijinta da ba ta wuce sa'arta ba, Zuhura. Da sauri ta miƙe tsaye, duk abinta tana girmama Uwar mijin nata Gwaggo don ba ƙaramin fada ta samu a wajenta ba. Domin a wauta irin na Uwargidanta Haj Nuriyya, ba ta ko damu da kowa a zuri'ar mijin nata ba musamman da ya kasance mafi yawansu ƴan ƙauyen Rano ne. Ita kuwa Hajara da kissa da kisisina ta ja mahaifiyarsa a jiki, kyaututtuka iri-iri take aika mata. Wasu lokutan ma girki na musamman za ta sanya a yi a kai mata. A nan ta ciri tuta sosai fiye da Haj Nuriyya. Duk rashin mutunci irin na Hajara ba ta taɓa yin sa ga Gwaggo ko yaranta.
"Ke ki na girmama taki uwar mijin ni kuwa a baya kin so ki tunzura ni na yi wa tawa Uwar mijin rashin ta ido."
Abin da Safiyya ta taɓa ce mata kenan sadda ta zo gidan ta ga yanda ta sa aka shirya garar abinci aka kai gidan uwar mijin nata.
Gyara zaman ɗankwalinta ta yi ta yafa mayafi saman doguwar rigar atamfar dake jikinta ta fito. Zuhura tuni ta juya ta koma falon ƙasa. Ita ma sai ta bi bayanta. Gwaggo ce sai Zuhura, Atine ta kawo musu ruwa da lemo kamar yadda ta sanya mata doka duk sadda Gwaggon ta zo a yi mata tarba mai kyau.
Fuska ɗauke da fara'a ta gaishe da Gwaggo, ita ma Gwaggon amsawa ta yi fuskarta a sake kafin Zuhura ta gaishe ta.
"Kin gan mu hanya ta biyo da mu daga gidan barka na haihuwa nace bari na shigo na ga ɗiyata kafin mu wuce."
'Taki ce dai ta kawo ki.' Abin da ta ayyana a rai kenan, aikuwa can ba jimawa ta hau kawo mata ƙorafin ba ta da kudi ga bikin jikan aminiyarta ya tashi, faɗi take.
"Ni ma Allah ya sa watarana na ɗauki jikana da hannuwan nan nawa."
Hajara kamar mai jin kunya dagaske ta sunne kai tana murmushi, Zuhura kuwa na amsawa da ameen. Miƙewa Hajara ta yi zuwa ɗakinta a ranta faɗi take 'Idan haihuwa kike so na yi to kina yaudarar kanki Gwaggo. Ban ga ranar haihuwa da wannan ɗan naki mai shan jinin jarirai ba.'
Ta faɗi ne sanin dukkan wani munanan ɗabi'u na Alh Nuhu, babu abin da ba ta sani dangane da tsaface-tsafacen da suke fita yi tare da abokansa su Alh Garzali ba. Ai ko farkon haɗuwarta da shi, aikin da suka ba su kenan. Ta dai rasa dalilin da ko a hira ba su ƙara tayar da zance tsakaninta da su Waleedah ba waɗanda har gobe ta sani suna tare ba ta da ƙarfin hana su mu'amala. Anan ta sani ta gaza. Kuma son abin duniya da ya rufe mata idanu, ta ma ɗanɗana riƙe maƙudan kuɗaɗe hakan ya haifar mata da jin cewa ko sata Alh Nuhu ke yi yana kawo wa za ta ci na cin ta.
Dubu hamsin ta ba Gwaggo, Zuhura jiki da rawa ita ma ta karɓe dubu goman da ta ba ta. Gwaggo saura ƙiris ta zube ƙasa don godiya ga Hajara. Haka suka tattara suka bar gidan bayan sun ci sun yi nak da shinkafa da miyar kaji. Koda suka tashi tafiya direba ta saka ya kai su har gida ya sauke.
Tana dawowa falon ta ja dogon tsaki tana toshe hanci. Can ta buɗe ta kwala wa Atine kira ta zo.
"Ki tattara falon nan ki goge min a saka turaren wuta."
Atine ta amsa cike da girmamawa. Ita kuwa Hajara dama babban burinta su fice ta samu damar yin dogon tunani akan hukuncin da ya dace ta ɗauka kan Sadiya da Innarta waɗanda suka zame mata ƙahon zuƙa.
***
Ta kasa kallon ƙwayar idanunsa, sai wasa ta ke yi da gefen mayafi tana zuba murmushi. Shi kuwa ya samu damar ƙarewa kyakkyawan fuskarta kallo.
"Ina son wannan kunyar taki. Yana ƙara fisgar zuciyata zuwa gareki."
Suraj ya furta yana ɗan matsa yatsunsa wuri guda su bada sautin ƙas. Har sannan Sadiya ba ta ce uffan ba tun da ya soma batun ya matsu a yi komai ta zama mallakinsa.
"Jibi war haka ai an gama tsaida ranar aurenmu nan da babbar sallah ko?"
Ta ɗan turo baki.
"Don Allah ni dai ka bari."
Ya yi dariya.
"Ok ba kya son batun? Shikenan na bari Honeyna."
Ta lumshe idanu kadan tana murmushi, a duniyarta wannan sunan yana mata daɗi. Akan Suraj ta yarda ba duka maza aka taru aka zama ɗaya ba. Tana kuma ji a ranta halinsu ya bambanta da na Huzaif. Ta ma gane ƙaddararta ce a haka, shi Huzaif mijin ƙanwarta ce. Sun jima sosai suna hira kafin su yi sallama tamkar kar su rabu ya tafi. Ita ɗin ma zuciyarta wasai ta shiga gida tana jin farin ciki idan ta tuno a jibin za'a zo kawo kuɗi da kuma tsaida bayan babbar sallah matsayin lokacin bikin nasu. Malam ne ya ce ba ya son a ja lokaci, shi