Showing 63001 words to 66000 words out of 124441 words
suke jin labarin wai Abba ne ya yi wa Malam maganar a bar ta ta cigaba da karatu shi ne ta ƙara zana jarrabawa. Hajara ta rasa me ke mata daɗi, ta kuma kasa ɓoye hassada da baƙin cikinta a zuci har sai da ta fiddo shi waje.
"Medicine? Daɗaɗɗan burina da bai cika ba shi ne Sadiya ta samu?"
Hakan da ta furta a hankali wanda ya shiga kunnuwan dukkansu ya sa suka dube ta. Sai ta share hawayen da ya zubomata wanda a zahiri ta sauya masa manufa, a baɗini kuwa na zallar baƙik ciki ne.
"Sadiya na maki murna, na so zama likita a rayuwata amma Allah bai nufa ba. Don Allah kar ki yi wasa da damarki. Ki maida hankali kin ji?"
Yanda ta yi maganar a sanyaye ya sa Inna jin ta ba ta tausayi, ta san irin nacin son karantar fannin Likita da Hajara ta yi amma kuma ba ta samu ba. Ta tuna duk da cewa tana takun-saƙa da ita a lokacin sai da watarana da ta ga tana lazimi za ta shige ɗaki ta tsaya ta dube ta a sheƙeƙe.
'Ke Mairamu ki sanya ni a addu'a na tsallake wannan banzan Jamb ɗin. Na ga ba laifi akwai ki da sallar dare da ibada. Ni dai ko bai kai zuci ba ki roƙa min.'
Daga haka ta shige ɗakinsu. Aikuwa duk abin da zai sa a lokacin Hajara ta karya bille ta nemi alfarma a wurinta, to ba ƙarami ba ne. Kuma ba ta ƙi taya ta addu'ar ba amma komai na Allah ne. Wataƙila ba alherinta ba ne.
"To ai sai ki ji daɗi tunda yar uwarki ta samu. Ƙila ita ki ke yi wa mafarkin. Kowa da ƙaddararsa. Ki yi hakuri."
Anti Hafsatu ce ta ba Hajara amsa. Ta jinjina kai tana ɗan matse yatsun hannu damarta, ji take yi kamar ta yi tsalle ta shaƙi wuyan Sadiya har lahira, abubuwa da yawa suna mata raɗa na huɗubar shaiɗan, daƙyar ta haɗiye komai ta ƙara mintuna goma sha biyar a gidan sannan ta yi musu sallama ta fice.
A hanya ma tuƙin kawai take yi amma fa rabin hankalinta na ga tunanin wai Sadiya ta sami gurbin karantar likitanci a B.u.k. Ba ta kula da cewa an tsaida hannunta ba a junction sai da ta yi dab da motar dake gabanta, kafin ta yi kokarin taka burki har ta kai mata wawan bugu, ita kuwa kanta ya bugi sitiyar har gilashin gaban motarta sai da ya tarwatse ta ji rauni ba kaɗan ba ƙarshe ma ta suma.
Gaba ɗaya hankalinsu a tashe suka ɗunguma zuwa asibitin malam (akth) da aka sanar da su an miƙa Hajara. Sun iske ta farfaɗo an mata ɗinki a goshi. Tana kwance don har sannan kanta yana sarawa.
"Hajara, sannu. Oh Allah, rai ba a bakin komai yake. Allah ya ƙara kiyayewa." Inna ce ta furta cike da jimami, sosai ta ji tausayin Hajara. Hafsatu dake waya da Safiyya da aka bari a gida tana kwantar mata da hankali gami da nuna mata da sauki sosai. Suna ajiye wayar ta matso ita ma tana yi wa Hajara sannu. Idanunta a runtse don ji ta yi kamar zantukan Inna baƙar magana ce kawai a ciki. Ta ɗan buɗe idanun karo na biyu daƙyar ta dubi Sadiya dake tsaye a gefe sai shaiɗaniyar zuciyarta ta dinga kissima mata wai murmushi ta ke yi.
Sallama da shigowar Likita ya sa aka nemi gaba ɗaya su fita, har faɗa ya yi wai don me za'a bar mutum sama da ɗaya ma su shigo. Su dai suka janye jiki suka fice.
"Allah ya nuna mana ki kammala karatunki ki fito a ƙwararriyar likita, hum! Ai asibiti guda zan gina maki idan na yi kudi in sha Allahu." Faɗin Zakari kenan ga Sadiya bayan sun fito waje, Sadiya ta yi murmushi kawai lokacin da take bin wasu ɗalibai da idanu, sun sha uniform din asibiti suna biye da wani babban mutum kuma ga dukkan alama likita ne babba, har suka bi wata baranda miƙaƙƙa suka wuce su ba ta bar waigensu ba. Sun yi matuƙar burgeta. Sai a sannan ma ta tsinci hirar da su Anti Hafsatu ke yi, tambayar Zakari ta yi ko Huzaif ya soma aiki. Tana ji Zakari ke fadin ai yanzun yana karɓar training na wata shida kafin ya zana jarrabawa Mdcn daga nan kuma idan ya ci zai soma aiki (Housejob) na shekara guda sai a yi ma batun service da sauransu. Ta yi kamar ba ta ji su ba, dama kusan ta ɗan san wasu bayanan na daki-daki na tsarin abin a bakin Huzaifa. Inna ce ta ba ta umarnin tafiya don ɗora girkin yamma. Sun ma ji a wurin Nurse cewa a yau za'a sallami Hajara.
"Ki je ki kimtsa idan kin kammala, sai ki bi ta gidanta ki kwana biyu kafin ta warware."
Sadiya ba ta san sadda ta juyo dubi Inna kamar za ta yi kuka, sai ta haɗiye maganarta don ba ta taɓa yin musu gareta, haka kuma idanun Anti Hafsatu da Yayanta Zakari ya sa ta amsa da toh.
"Aa Inna, ai ba sai Sadiya ta je ba fa. Mun yi waya da mijinta wai zai ɗauke ta ne su je babban asibitin da yake ganin likita a auna masa ita sosai. Kuma a can akwai masu jinya ba sa ma buƙatar wani ko wata."
Ajiyar zuciya Sadiya ta sauke don ji ta yi kamar an mata albishir da shiga aljanna. Inna ta amsa da shikenan, ta juya ita dai ta bar su a asibitin don jin ta take kamar a kan ƙaya. Tana ji sadda Yaya Zakari ke ta mita wai ya za'a yi duk ƙwarewar likitocin asibitin nan ace Alh Nuhu ya yi waɗannan kalaman. Ba ta ma ji amsar da Anti Hafsatu ta ba shi ba ta yi gaba.
A hanya tana tafe ne tana ɗan murmushi idan ta tuna cewa watarana za ta wayi gari cikin asibitin nan da sunan ɗaliba. Motar Malam ta ga ta shigo, ta ɗaga mishi hannu, ya gan ta don haka ya ɗan tsaya daidai wajenta, ta gaishe shi. Ya tambayi jikin Hajara da kuma inda suke. Nan ta ce mishi Emergency daga haka ya yi gaba ita kuma ta fice titi ta samu abin hawa ta koma gida.
Anti Safiyya ganin yanayi na fuskar Sadiya ya sa ta samun tabbacin jikin da sauki, ta iske ma wasu a dangin mijin Anti Safiyyar sun zo barka. Ta gaishe su sannan ta shiga hidimar ɗora girkin dare.
Sai Magriba Inna da Malam suka shigo gidan bayan an sallami Hajara mijinta ya tafi da ita.
***
Bayan Sati Biyu...
Hajara sai safa da marwa take yi a falon Waleedah ƙawa kuma aminiyarta a yanzu, ta shafi goshinta da ya sha ɗinki har ya warke amma kuma tabon ta sani har abada ba zai ɓace ba. Ita mai tsantsar kula da jikinta, ta tsani ganin ko ɗigon tabo ya fito mata. Ba fara ba ce amma kuma koyaushe fatarnan sumul da ita tsabar kuɗaɗen da ta ke kashe wa a kansa. An wayi gari sanadin Sadiya ta samu mugun rauni.
"Wai First Lady (kamar yanda suke kiranta tun aurenta da Alh Nuhu) , za ki taho mu je a ci maki uwar yarinyar can ko kuwa za ki tsaya nan ki na cizon yatsa da ba zai sa ki huce ba?"
Waleedah ta yi furucin bayan ta zuƙo hayaƙin shisha ta fesar a sama. Hajara kuwa tsaki ta ja ta nemi wuri ta zauna.
"Duk abin da zan mata ji nake ban rama ba Waleedah, ji nake kamar bai kai hukuncin baƙin cikin da aka ɗanɗana min ba. Ni fa ba iyakar tabon nan ne matsalata ba, a'a, kin san kuwa yarinyar nan ta samu gurbin karantar MBBS a B.u.k? Daɗaɗɗan burina Waleedah, a kan ban samu ba ƙawayena na sakandire sun min dariya sun ce dama cika baki ne. Na sha raba dare ina kuka duk sanadin rashin cikar burina. Ke bari na faɗamaki, rashin samun gurbin da nake son karanta shi ya soma sanadin biyewa Nusaiba tsohuwar abokiyar aikina na fara kula ƴan banzan samari irin nata. Yau an wayi gari wai ɗiyar Mairama ta samu abin da ni na rasa. Ki faɗa min ta ina zan samu nutsuwa da kwanciyar hankali?"
"Tirƙashi! Ah dole ki ji kamar ki hadiyi zuciya ki mutu! Toh ki saka a kashe maki ƴar banza mana! Mene ne amfanin irinsu a doron ƙasa?"
Hajara ta yi murmushin da ya fi kuka ciwo tana share hawayen da suka zubo mata, kwanaki goma sha biyar da samun wannan mummunan labarin kuma daga bakin ɗan uwanta uwa ɗaya uba ɗaya Zakari, bai ko ji shakkar faɗin maganar a gabanta ba, bai ji nauyi ba. Bai tuna yadda ta dinga fafutukar nema ba ta samu ba, haka ya zo da kyakkyawar albishirin ga maƙiyarta.
"Kin san shekarun da na kwashe ina jin tsanar matar nan a raina wai? Ai idan na kashe Sadiya na so ta huta kenan Waleedah, a'a, da ranta na fi kaunar na gasa wa Mairamu aya a hannu. Aure dai da matar nan ta so hana ni yin sa, har ta mutu ba za ta ga auren Sadiya ba. Babu abin da na fi buri a yanzu da ya wuce na ga karatunta ya ƙi yiwuwa kuma ta yi baƙin jini a idanun maza."
Waleedah tayi murmushi sannan ta zuƙo shisha ta fesar. Hannu ta sa ta gyara jelar kitsonta na attach gami da cewa.
"Shegiya tawan! Kin san ta kan mugunta. Yanzu dai wajen shi kike so a koma ko wani wuri ki ke da buƙata?"
Hajara ta numfasa.
"Wani, wanda ya fi shi hatsabibanci, wanda zai yi mana aiki ba tare da haɗa fata da ƙazamin jikinsa ba."
Dariya sosai Waleedah ta kwashe da ita gami da zuba uban ashariya.
"Ki ce ke ma ya maki irin nawa, ni fa daga kai masa sunan wani shu'umin bayarabe mai kuɗi nace ya shawo min kansa shikenan ya neme ni da lalata, aikuwa na kira shi na mishi tas a waya saboda aikin bai yiwu ba. Ƙarshe ma baram-baram muka yi da Bayaraben."
Hajara ta yi ƙwafa.
"Dama ai na so na gane yaudara ce, tunda wancan karon ai ya yi min na baƙin jinin Sadiyar, amma me ya faru? Sai ga shi ta haɗu da wancan mataccen Suraj din. Kin ga kenan na shi babu wani abu."
Waleedah ta jinjina kai. Kafin ta yi magana Hajara ta ɗora.
"Shiyasa tun farko na tsani aikin asirce-asircen nan, ni fa duk abin da ba zai zama dauwamamme ba sai ka na tisa aiki ba zan jura ba. Na fi gane na zuba salon makirci da kisisina, ƙazafi da mugunta iri-iri muddin haƙana zai cimma ruwa. Haka fa Gwaggo Atine ta taɓa yi min tayin wani bo...Yes! Gwaggo Atine!"
Ta katse zancenta tana mai tunanowa da Gwaggon wacce har gobe ta tsani Inna da Sadiya musamman da ta kunyata a sanadinsu.
"Ban gane Gwaggo Atine ba? Ke bayan ni har akwai wani na danginki da za ki iya fallasawa sirrinki?"
Waleedah ta nemi sani tana bin Hajara da kallon wawiya. Hajara ta yi dariya.
"Da ace kin san wace ce Atinen Mamman da ba ki ce wani abu ba. Ni na mance da ita ne gaba ɗaya tsabar ƙullewar kai. Yo matar da ke juya mijinta? Tsabar mulki da baƙar azabar da ta ganawa kishiya da mijinsu ya sa da ƙarfin tuwo iyayensa suka sa ya sake ta. Ƙarshe ma har sauya gari suka sa ya yi duk domin ita. Kuma duk bala'in nan ba ta taɓa haihuwa ba, yanzu aikin dillanci take yi har Aljeriya tana kai kayayyaki. Gwaggo fa baƙar muguwa ce ina faɗamaki, ta fi ki hatsabibanci nesa ba kusa ba."
"Toh yanzu ni ma ya za'a yi ina so na je."
Guntun tsaki Hajara ta ja gami da miƙewa.
"Kya bari na fara magana da ita ko?"
Waleedah ta yi dariya. Ta miƙe tana faɗin.
"Ai shikenan."
Har sun kai ƙofa Hajara ta tsaya gami da juyowa.
"Akwai wancan abin naki?"
Waleedah cikin rashin fahimta take kallonta, can kuma ta yi dariya.
"Au, yau kuma? Ko ke fa, da ace ma tun farko ki na ɗan gwadawa da wasu damuwoyin naki sun kau. Bari na ɗauko maki da sanyinsu kuwa."
Daga haka ta juya ta koma firij ɗinta ta kwaso kwalaben maganin maye har uku ta kawo mata, daidai sadda ita kuma ta buɗe jakarta aka saka mata a ciki. Motarta sabuwa ɗaya daga cikin na mijinta da yake da su wanda a yanzu ya zama mallakinta, har nan Waleedah ta yi mata rakiya.
Sai da ta ga ficewarta sannan ta koma cikin gidan da sauri ta ɗauki waya ta hau danna kira, ba jimawa a ka ɗauka.
"Ta tafi, anjima zan shigo zan maki bayanin duk yadda muka yi."
Daga haka ta cire wayar daga kunnenta, ta yi wurgi da ita saman kujera.
***
Kasa bacci ta yi, juyi kawai take ga uban gumi da ta haɗa sakamakon mafarkin da ta yi marar daɗi, ita ba ta ma san ya za ta fasalta mafarkin ba, ta dai gan ta a wani yanayi marar dadi, ta buɗe idanunta da salati ɗauke a saman lebɓanta. Ta kai duba ga Malam, munshari kawai ke tashi shaidar baccinsa yake yi haiƙan. Inna ta share zufarta sannan ta miƙe ta shige banɗaki, ruwa ta kama ta ɗora alwala, falon Malam ta dawo, hankalinta ya kai ga agogo, lokacin ƙarfe uku da mintoci na dare. Darduma ta shimfaɗa ta yi sallah raka'a biyu sannan ta yi wa Annabi s.a.w salati. Ta karanta surorin Alkur'ani masu girma da ta rike a kanta sannan ta ɗaga tafukan hannayenta sama ta soma addu'a. Sosai ta ke roƙon Allah ya ba yaranta kariya daga dukkan mai nufarsu da sharri kowane iri ne. Ta roƙawa Husnarta shiriya kamar koyaushe kafin ta roƙarwa Sadiya fara karatu cikin sa'a da kuma nema mata tsari daga dukkan sharri. Ta jerawa Allah kirari iri daban-daban har hawayenta na ɗiga kafin ta kai ga shafawa. Haka ta zauna saman dardumar tana jan istigfari gyangyaɗi na kwasarta. Ƙarshe dai ba ta san ya aka yi bacci ya ɗauke ta ba sai jin Malam ta yi yana tashinta ta yi sallar Asuba. Haka ta mike ta ƙara ɗora sabon alwala tukunna.
Washegari da safe ta aika almajirinta ya siyo mata ƙosai ta yi sadaka. Sadiya na ta shirin tafiya makaranta, a sannan Safiyya ta koma gidanta don dama wankan satittika ne za ta yi a nan kasancewar haihuwar fari ce.
"Ki dage da azkar safe da yamma Mamana, ina yawan faɗamaki ki rage baccin dare. Duniyar nan sai mutum ya tashi tsaye wajen nemawa kansa kariya daga sharrin masu sharri. Ban ce wani ko wata na nufarki da sharri ba, amma kuma babu wani da ba shi da magauta komai ƙankantarsu. Ki dage da addu'a, ko babu komai ƙarin kusanci za ki samu tsakaninki da Mahaliccinki. Za kuma ki fi ƙarfin mai jin yana da ƙarfin ya zalunceki ko ta yaya."
Inna ta tsaya domin ta numfasa, Sadiya kuwa gaba ɗaya ta ji jikinta ya yi sanyi, gaskiya Innarta ke faɗi, tana da sakaci a nafilfilu da ma azkar. Ba ta manta akwai group din da take a whatsapp, wata baiwar Allah safe da maraice ba ta gajiyawa da turo musu azkar gami da tunasar da su su yi. Haka take tsallakewa ta tafi wani sha'anin na daban. Muryar Inna karo na biyu ya maido ta cikin hayyacinta.
"Ki ji tsoron Allah Sadiya, duk abin da za ki aikata idan kin fita ko a gida, ki ji tsoron Allah a ciki. Idan kin kama mutuncinki, ba ki ba kowane ɗa namiji fuska ba, ire-irensu ba za su raɓe ki ba ballantana su kawo maki zancen banza. Ke dai karatu ya kai ki, domin Allah ki yi iyakarsa kar ki jawo mana abin magana Mamana. Na yarda da ke na kuma yarda da tarbiyyar da muka ba ki, ni na san in sha Allahu ba za ki ba mu kunya ba. Allah ya yi maku albarka, Allah ya shiga lamuranku. Ya shirya mini ku. Allah ya ba da sa'ar karatu."
Inna na kai wa ƙarshe ta miƙe ta fito daga ɗakin tana kauda ƙwallar da ba ta san dalilin cicciko mata ba. Sadiya ita ma hawayen ta share ta miƙe tana mai ji har cikin zuciyarta da yardar Allah nasihar Innarta ba za ta tafi a banza ba. Za ta yi iyakar yin ta wajen aiki da shi.
Malam ma da suke tafe a motarsa zai kai ta makarantar zuwan farko, nasiha iri-iri kusan hannunka mai sanda ya dinga yi mata akan abin da Hajara ta aikata a nata lokacin yana haska mata illolin biye wa son zuciya. Sadiya sosai take adana dukkan nasihohin iyayen nata, ta sani su na ƙaunarta matuƙa, ba kuma za ta watsa musu ƙasa a ido ba.
***
Hajara a gaggauce ta ajiye wayar da ta amsa na mijinta dake sanar da ita tafiyarsa zuwa Abuja don halartar taro na jam'iyyarsu. Jira take yi kawai ya kammala maganarsa na batun atamfofi da ma kekunan ɗinki da za ta rarrabawa mutane duk don taya abokinsa kamfen wanda Uwargidansa Haj Nuriyya tuni ta yi nisa a harkar siyasarsu don ita sosai ake damawa da ita.
Hajara duk ba wannan ne a gabanta ba jin Gwaggonta ta so gidan ya sa ta koge zuci-zucin ajiye wayarsa ta yi abin da ke gabanta. Tun zuwanta gidansu ta tarar Sadiya ba ta gidan ta je makaranta kamar yanda Inna ta faɗamata ta ji hankalinta ya yi mugun tashi. Shagala ta yi a shaye-shayen da ta tsunduma a ciki yake ɗebemata kewa ta ke bacci son rai don gusar da damuwa, koda dai Gwaggon ce ma sai daren jiya Laraba ta dawo daga Nijar ta kai kayayyakin siyarwa irin waɗanda take sara.
A falon sama ta iske ta zaune, ƴar aikinta Atine ta kawo mata kayayyakin motsa baki ta dage sai ci take. Ganin Hajara ya sa ta shiga gaisuwa cike da girmamawa tsabar son abin duniya ba ta ko jira ita a matsayinta na ɗiya ta gaishe ta ba.
"Gwaggo kenan, sannu da zuwa."
"Yauwa Autar Mama. Ki na ta nemana, nace Allah yasa samuwa ce. Ai da yake