Showing 93001 words to 96000 words out of 124441 words
mishi rantsuwar tana sonsa. Tana roƙon kar ya auri Sadiya ya zo su yi aure. Wannan ke ƙara tada tsumin sonta. Ya ji ma waya da Sadiya ba ya buƙata balle zuwa wajenta. Sai ya shafe mintoci suna waya da Fareeda suna jifan juna da kalamai masu sanyaya rai. A gefe guda kuwa ganin yadda kowa ya duƙufa a shirye-shiryen bikinsa yana ƙara hana shi sakat.
Ya yanke ya samu Baffa da batun Fareeda amma kuma yana shakkar hakan. Ba sa kawo wa Baffa wargi, sai dai yana ji a jikinsa ba zai iya zaman aure da wata bayan Fareedarsa ba. Ai da tsohuwar zuma ake magani. Dama a rashin ta ne ya koma kan Sadiya. Toh buƙatar maje hajji sallah, tunda yanzun ya samu tsuntsu daga sama gasashshe, aikuwa komai ta fanjama-fanjam! Ya shirya wa dukkanin ƙalubalen da zai fuskanta muddin haƙansa zai cimma ruwa.
Yanzun ma yana tsaye a farfajiyar gidan ya yi zurfi a tunanin abin da zuciyarsa ta riga ta yanke mishi, akwai wani Kawunsu wanda kaf duniya ya sani shi kaɗai ne zai iya shige mishi gaba ko ba da sanin kowa ba ya kai ga nasara a auren Fareeda. Ya ji ya gani, idan har kuɗi su ne matsalar Kawun, zai cika mishi asusunsa muddin dai komai zai tafi yadda ya ke so.
Bai ji zuwansa ba, sai ƙamshin turarukansa masu tsada ne hancinsa ya soma shaƙo mishi. Ya juya kai ya kalle shi. Maina ya kauda kansa ya na mai zura hannunsa cikin aljihun wandon shaddarsa ruwan toka da ta sha aiki. Kansa babu hula sai kwantaccen sumarsa mai cika da laushi.
"Duka wannan a kanta ne? Ta cancanci wannan girman sadaukarwar?"
Kan Hamma ya ƙulle, wai meyasa Maina ya karance shi fiye da kowa ne? Kwanakin da Maina suka yi, ya lura duka tarin tambayoyin da su Giaɗo ke yawan jifansa da su, shi ko sau ɗaya bai ce mishi uffan ba sai dai ya san shirun Maina na nufin abubuwa da dama. Kaifin idanunsa a kansa koyaushe ya sa ba ya ma son suna haɗa idanu don sai ya ga kamar a kallon ya gane komi da yake lulluɓe a duniyarsa. Yanzun ma ya ƙara ɗimuwa da jin yanayin tambayoyin nan.
"Iyaye, yan uwa, abokai, duka kana tare da su. No Abdul, kar ka yi gangancin saɓawa umarninsu. Fareeda.."
Ya furta a ƙarshe, ai gaba ɗaya kuma Hamma sai ya yi saranda kirjinsa na bugu da sauri-sauri. Shi ko Maina ba tare da ya ƙara kallonsa ba ya ci gaba da zancensa bayan wasu daƙiƙu.
"Ba ta cancanci dukkan waɗannan sadaukarwa ba. Cikinsu kuwa har da kai, ba ta cancanci zama wata ɓangare a rayuwarka ba. Think!"
Yana kai wa nan ya juya ya bar wurin. Wayar da AbdulMajid ke yi da Fareeda a daren jiyan, babu wanda bai shiga kunnuwansa ba. Ya ji yunƙurin da yake yi, ya ji abin da zuciyar Abdul din ke raya masa. Yana girmama soyayya, amma ya tsani yaudara da cin amana. Bai kuma fiye yi wa mutane kutse a lamuransu ba, amma wannan ba zai iya shiru ba.
Shi kuwa Hamma ya fahimci komai, ko yaya Maina ya san wani abun. Girgiza kai ya yi. Yana girmama shi, girmamawa irin ta yadda ya ke jin nauyin ja da maganarsa, sai dai a wannan karon ya tsinci kansa a kokwanton yin ko bari.
***
Hajara ke ɗirkar dariya yayin da ta yi zaman dirshan a gaban Bokanta wanda shi ɗin ma ke taya ta. Ya katse ta da fadin.
"Ai na faɗamaki komai fa zai tafi daidai da yadda ake buƙatarsa. Ranar ɗaurin auren a nan za ki sha mamaki domin yarinyar nan har abada ba za ta auru ba ni na faɗamaki."
Ta jinjina kai zuciyarta wasai.
"Na yarda yanzu kam. A farko na tsorata ainun, amma yanzu na ƙara yarda da lamarinka ɗari bisa ɗari. Ka cigaba da aikinka, komai yana tafiya daidai."
Ya yi wata shaƙiyyar dariya. Nan kuma da kanta ta nemi su ga juna duk don ta faranta masa. Aikuwa ya shiga washe baki kamar gonar auduga ganin abin nema ya samu. Sun kuwa jima suna sheƙe ayarsu don cikin dake tattare da Hajara ba abin da ya ƙara mata sai kwaɗayi, ba na kowa ba kuwa sai shi din. Ta rasa wannan jaraba amma kuma idan abin ya taso kamar ta yi hauka matuƙar ba ta zo wurinsa ba.
***
Ta danne zuciyarta a daren da aka dawo daga shagalin yinin da aka fita can ɗakin taro na musamman a ka gudanar, ta kira Hamma a waya ganin shi da kansa kamar ya rufe babinta a rayuwa. Ringing ya dinga yi kamar zai katse kafin a ɗaga amma ya yi shiru bai ce komai ba. Ta haɗiyi miyau tana mai danne abin da ke taso mata na ɓacin rai ta yi sallama. Ya amsa mata ciki-ciki.
"Barka da dare Hamma. Ya hidima?"
"Lafiya." Ya amsa a daƙile. Hawayen da take riƙewa suka zubo a kuncinta.
"Dama..dama.."
Sai ta kasa cewa komai ta sa hannu ta toshe bakinta gudun kar ya ji muryarta tana kuka.
"Zan kira ki gobe kin ji? Yanzu ko mene ne ki yi hakuri ki kwanta ki samu bacci don nasan a gajiye ki ke. Sai da safe."
Bai jira amsarta ba ya kashe kiran. Ta kuwa shiga rera kuka tana mai ji a ranta har abada zai wahala aurenta da Hamma ya yiwu.
"Sadiya, kuka ki ke? Mene ne?"
Ta tsinci muryar Anti Hafsatu a kanta, da sauri ta shiga share fuska. Ta yi zaton kowa ya yi bacci don haka ta fito zauren gidan nasu domin amsa wayar, sai dai tun fitowarta Anti Hafsatu wacce motsi ko ya ya yake idan ta ji sai ta farka, ta hange ta za ta fita. A zatonta ma fitsari za ta je yi kasancewar bandakin dake cikin ɗakin yana da matsala don haka ita ma ta miƙe jin fitsarin ya taho mata. Farko kwankwasa bandakin ta yi, jin shiru kawai sai ta ji kamar muryar Sadiya a zauren, dalili kenan da ta ƙaraso jin kuka take yi.
Sadiya tana jin an zo gaɓar da ba za ta iya ɓoye damuwarta ba, ta shige jikin Anti Hafsatun ta na kuka sosai. Hankalin Antin idan ya yi dubu to fa ya tashi. A gigice ta ɗago kanta.
"Innalillahi...ki daure ki nutsu kar ki tashi mutanen gidan. Ki faɗa min mene ne. Wani abu ne ya faru?"
Ta haɗiye kukanta gudun kar ta tashe su kamar yadda Anti Hafsatu ta tunasar da ita.
"Anti, Hamma ne."
Idanu waje Anti Hafsatu ta riƙe ƙirjinta.
"Me ya faru?"
Nan ta zayyane mata irin shariyar da ya ke mata kai ka ce dole aka yi mishi sai ya aure ta. Hatta da labarin soyayyarsa da Fareeda sai da ta sanar da ita har ma da silar fasa aurensu wanda Hamman bai ga laifinta ba. Sadiya ta ƙara da cewa.
"Anti a haka goben za'a ɗaura aurenmu? Kalli yadda yake min. Tsoro nake kar ya ce ba zai aure ni ba. "
Salati Anti Hafsatu ta ja, abin take ji kamar almara. Daga labarin da Sadiya ta ba ta, ta kula a rashin Fareedar ce, ya sanya shi dawowa gareta.
"Tirƙashi!" Ta faɗi a fili zuciyarta na mata zafi.
Hakan ya sa Sadiya yunƙurin fashewa da wani sabon kukan. Nan Anti Hafsatu ta shiga rarrashi kafin ta ja ta su koma ɗaki. Ita ta sanya ta yin alwala ta gabatar da sallar nafila. Addu'a sosai ta yi na nemawa kanta zaɓin Allah. Sai kuma ta ji zuciyarta ta rage nauyin da ta yi a farko. Har ta ji salamar da ta samu bacci ya yi awon gaba da ita.
Washegari da safe Anti Hafsatu ta ɗauke ta zuwa gidanta sakamakon gyara na musamman kuma na ƙarshe a ranar da mai gyaran jikin wurin Nene za ta yi mata. Kusan abubuwan da ta sha ya fi na koyaushe hakanan gyaran ya kasance na daban da sauran kwanakin baya. Ana kammalawa ta yi wanka, dama tuni an yi magana da mai kwalliya za ta zo har gidan ta yi mata. Hakan kuwa ya faru, aka yi mata kwalliya ta fito fess da ita. Farin leshin mai adon zaiba dake jikinta ya zauna ɗas ya fiddo kyakkyawar surarta. Ta ko'ina ta ƙara cika ta yi kumari. Kirjin nan kamar ya fashe tsabar cika hakanan mazaunanta. Ta yafe kanta da babban mayafi.
Duka wannan sha'anin da ake Anti Hafsatu suna zuzuta kyawun da ta yi, hankalinta kusan ya soma rabuwa da jikinta. Kirjinta kuwa na dukan tara-tara. Da zarar ta duba agogo ta ga ƙarfe biyun rana na ƙara gabatowa, sai ta ji kamar a na ƙara mata bugun zuciya ne haɗe da fargaba da tsoron makomarta a yau. Har aka kammala komai suka kama hanyar tafiya can gidan lokacin ƙarfe sha biyu ta wuce ba ta dawo nutsuwarta ba.
***
A ɓangaren Hamma kuwa, tun wayewar garin ranar ya gama yanke shirin da ya ƙulla. Bai nunawa kowa komai ba kamar yanda suka tsara, asalima ya ɗan saki fuskarsa ba kamar kwanaki ba. Maina kallonsa yake amma bai ce mishi uffan ba sai dai a jikinsa ya ke jin wannan sauyi na farat ɗaya a wajen AbdulMajid akwai babbar alamar tambaya a tattare da shi.
Su Baffa kuwa sun wuce ne tarbo Mai Martaba daga Airport. Koda ya zo sai da ya fara isa fadar Sarkin Kano bayan sun gaisa ne ya wuce kai tsaye wurin ɗaurin auren, lokacin ƙarfe biyu saura ƴan mintoci.
Hankalin su Maina da ma sauran jama'a duka ya tafi can. Ba su ko kula da ɓacewar AbdulMajid a tawaga ba suna faman nan da nan da abokansu, wasu ma duk daga ƙasar waje suka zo. Mai Martaba na isowa kuwa aka fara shirin ɗaura aure. Wuri ya cika ba matsaka tsinke.
A sannan ne Baffa ya shiga laluben Hamma a cikin matasan, nan Maina da su Giɗaɗo suka tabbatar ba ya tare da su. Koda aka kikkira wayar a kashe.
Kawu Surajo wanda shi ne matsayin waliyyin Hamma, ya ji shigowar saƙo wayarsa. Kansa ya ɗauki zafi bai ko duba ba, an yanke ɗaura auren kawai idan ya so daga baya a yi batun inda Hamma ya ɓoye. Amma kuma kiran da aka dinga jera mishi ya sa tunanin duba wayar ya zo mishi. Cirowar da ya yi ya duba, sai ya ga missedcalls din AbdulMajid ne. Can ya buɗe saƙon ya karanta.
"Kawu don Allah kar a ɗaura auren nan. Ko mene ne a jira zan zo. Zan muku bayani."
Kawu Surajo ya yi kasaƙe, idan ya kalli Baffa da ke zaune ƙasan kujerar Mai Martaba, sai ya maida hankali ga su Liman da manyan mutanen da wurin ya tara.
"Waliyyin Ango ya matso." Liman ya ƙara fadi a sifika. Maina dake gefe zaune kallo ɗaya za ka yi masa ka gane ransa ya ɓaci, yana tsoron abin da tunaninsa ke ba shi AbdulMajid ya aikata. Hankalinsa ya yi nisa a tunani ya ji muryar Baffa dake gab da shi na faɗin.
"Wane irin wasan yara ne haka? Me AbdulMajid yake nufi da a tsayar da ɗaurin auren?"
Maina ya ɗago kai ya dube su. Nan kuma aka fara ƙus ƙus wanda har ya je kunnuwan Abba da ke wajen matsayin waliyyin Amarya. Hankalinsa ya tashi ainun haka ma Malam da ya shiga salati a ƙasan ransa.
Nan Mai Martaba wanda tuni aka sanar da shi, ya ba da umarni ga Maina ya kira AbdulMajid. Maina ya fiddo waya, da wannan mugun sabon na sa ya danna kiran wayar Hamma bayan ya sanya a handsfree. Kallo ɗaya Mai Martaba ya masa ya kauda kai ransa na zafi har muryar AbdulMajid ta cika wajen. Aikuwa na kusa da wurin suka yi shiru ana son jin ta bakinsa.
"AbdulMajid, kana ina? Duk inda ka ke ka zo ana buƙatarka a nan."
"No Maina, ba zan iya ba. Wallahi ba na son Sadiya. Na rasa ta yanda zan ɓullo wa Baffa da zancen. Yanzu haka zancen da nake maka muna tare da Kawu Ali an ɗaura aurena da Fareeda. Don..."
Kitt Maina ya katse kiran har wani gumi ya ji ya tsastsafo a goshinsa. Wuri ya ɗauki salati. Mai Martaba wanda ransa ya gama kai wa bango da wannan ɗanyen aikin na ɗan nasa wanda a duniya bai iya waya ta sirri ba ya yi wa dogarinsa magana ƙasa-ƙasa. Malam da su Abba kuwa kansu ya yi mugun ɗaukar zafi, ransu idan ya yi dubu to ya yi ƙololuwar ɓaci. Baffa ya rasa ina zai saka kamsa tsabar kunyar da ta lulluɓe shi, ganinsa har wani dusashewa ya yi haka nan jinsa. Wato ka haifi ɗa ba ka haifi halinsa ba, yau a bainar jama'a AbdulMajid ya zaɓi ya tozarta shi? Nan da nan masu jiran ƙiris har sun fice sun fara yaɗa abin da kunnuwansu suka tsinta. Nan da nan aka ja Abba da Malam gefe suka tattauna da Jarmai babu wanda ya san me ake shiryawa.
Su Maina da Lamiɗo sai gani suka yi an cigaba da daurin aure. Kamar a mafarki, kamar kuma almara ya ji muryar mai sanarwa yana shela a lasifika yana fadin.
"An ɗaura auren Ibraheem Tafida ɗa ga Mai Martaba Sarkin Gombe da Sadiya Sa'ad Shagari akan sadaki naira na gugan naira har dubu ɗari biyar."
Sai wuri ya ɗauki kabbara. Malam ya share hawayen tsantsar farin ciki da dadi.
Mutane aka hau kallon kallo, Maina kuwa ya yi ɗif! Ya ji duniyarsa na juyawa, da gaggawa ya kai duba ga Mai Martaba sai dai tuni ya sadda kansa sakamakon haɗa idanun da suka wanda kwarjinin ya yi mishi yawa. Ƙirjinsa ke bugu da ƙarfi, shi kuma? Shi dai Maina ko kuwa akwai wani Ibraheem Tafida bayan shi?
'Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un!' Ya furta a ƙasan ransa.
Sadiya gaba ɗaya ta yi wuri-wuri da ita. Tana zaune ne kawai a ɗakin nasu tare da su Zahra da Nudrat wacce tun safe ta taho nan don ta ce ita ɓangaren aminiyarta take, sai faman kai kawo na ajiyewa ƙawayen Sadiya abinci suke yi.
A farko ma yaƙe take bin su da shi daga baya fuskarta kadai ka kalla za ka shaida cike take da tarin damuwa. Ta ƙara duban agogon wayarta, ƙarfe uku saura mintuna. Hayaniyar da ke falon na ƴanmatan da shewarsu bai sa hankalinta kasa kai wa ga babban dan Anti Hafsatu mai shekaru goma sha uku ba, Ameer. Yanayin yadda ya shigo falon kamar wanda aka jefo ka san cewa da magana a bakinsa haka kuma ya juya da sauri ya fita, kamar ta miƙe ta ji me zai ce tunda ta san ya bi su Abba ɗaurin aure amma kuma bakinta da ƙirji suka yi nauyi lokaci guda. Har ji ta yi fitsari ya cika mararta. Tuni ta ajiye ƴar ƙaramar fankar dake hannunta wanda ke taimakawa gurin sama mata wadatacciyar iskar da zai hana kwalliyarta lalacewa.
"Kai Ameer! Ameer!! An ɗaura auren?!"
Ta ɗaga kai ta kalli Zahra a gaggauce kafin ta bi hanya da kallo cike da fatan Ameer din ya dawo a ji amsarsa.
"Haba ke ma dai kin san ta zama ta Hammana yanzu. Uku fa ina ji ya kusa. Bari na leƙa ma."
Cewae Nudrat tana dariya daidai lokacin da take ficewa zuwa cikin gidan. Nan Zahra ta mara mata baya saboda ta gama karantar Sadiya, ta san kuma tsoron da ta ke yi. Ita ma kuma ta ji nata hankalin ya ƙi kwanciya, so take ta samu labarin ɗaura auren yadda za ta kawo wa Sadiya albishir mai daɗi.
Hayaniyar da ke tashi a tsakar gidan ya sa wasu dake zaune suna cin abinci har ma ita kanta Sadiya miƙewa zuwa can.
Mutane sun yi yawan da ba ta iya hangen fuskokin su Anti Hafsatu da ma Husna da sauran dangi dake maganganu. Sai dai kunnuwanta tsaf suke zuƙo mata muryoyinsu suna buga salati. Can kuma ta ji muryar Antinta Safiyya a hautsine tana faɗin.
"Kai Ameer dagaske ka ke yi? Ango ya gudu? Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un!"
Ita ma sai ta ji bakinta ya hau ambaton Innalillahi da ta ji Anti Safiyya na faɗi. Ta ɗan yi taga-taga, wata ƴar makarantarsu ta yi saurin rungumota ta gefen kafaɗa.
"Kai! Maza ɓace min daga nan! Yara sai ɗauko zance!"
Gaba ɗaya suka maida hankali ga duban mai maganar, su Baba Habu ne. Nan ya dubi kowa.
"Ku kwantar da hankalinku, aure har ma an gama ɗaura shi. Ba wani tashin hankali ba ne."
Nan kuma ya ja hannun Sadiya wacce ta rasa wane yanayi take ciki, ciwon kai, zazzaɓi da ma faduwar gaba fiye da na baya sosai suka tarar mata. Ganin haka su Anti Hafsatu da Hajara wacce ta ga sama ta ga rashi suka mara mishi baya har kuwa cikin wasu a dangin Malam din da ma Inna.
Ta zauna kawai tana duban yayan nata. Falon dai babu wani bare. Kafin Baba Habu ya kai ga cewa wani abu sai ga Abba da Malam sun shigo gidan daga can gidan Baffa inda Mai Martaba ya buƙaci ganinsu aka yi magana sosai.
Hajara gumi ta ji ya fara tsastsafo mata musamman ganin fuskar Abba a sake.
"Habubakar, meke faruwa ne? An saka mu a duhu."
Wata dattijuwa a dangin su Malam wacce ke matsayin Uwa a wurinsa ta fadi tana duban Abba. Ya na murmushi ta ce.
"Babu abin da ya faru sai alheri. Aure kuma an riga da an ɗora shi. Ku zauna a yi magana ta nutsuwa."
Nan kowa ya zauna. Hajara wacce dama tun kafin ya kai aya ta zube ƙasa sharaf babu ma wanda ya kula da ita. Gaba ɗaya jikinta ya gama mutuwa ta yadda ƙafafunta suka kasa ɗaukarta, ɗazun tana tsakar gida ne ta ci uban ado tana tauna cingam a zaune saman kujera ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya tana ƙarewa masu shige da fice kallo zuciyarta wasai, ko a mafarki ba ta yi tunanin wannan baƙin cikin za ta riska a gaba ba don har wata shewa take bugawa ita ce har da gayyatar jiga-jigan ƙawayenta kawai don a zo a taya ta dariyar rincaɓewa da auren Sadiya zai yi. Sai dai me? Jin zantukan da Abba ya shiga yi ya sa ta ji ashe dai firgicin da ta