Showing 78001 words to 81000 words out of 124441 words
wani loko na asibitin inda ake wanki da ma alwala.
***
Kwana biyu Sadiya ta ƙara a ka sallame ta. Gangar jikinta dai ya warke amma wannan ciwo na kaunar mutumin da ya yi mata nisa tana nan daram a ƙoƙon ranta. Duk runtsi kuma ba za ta fallasa shi ga kowa ba sai nemawa kanta yayewa daga Allah.
Satin dai gaba ɗaya ba ta shiga makaranta ba amma kuma ta maida hankali sosai ga karatu a gida don ba ta yarda soyayya ta hana ta yin karatun da ta ci ma buri ba.
Ran litinin kuwa da wuri ta yi wanka ta shirya cikin doguwar rigar atamfa sakamakon zafin da aka kwana kuma aka wayi gari cikinsa don har a sannan damina ba ta shigo sosai ba. Inna ta dube ta, duk ta rame sai hasken da ta ƙara.
"Har kin yi shiri? Ga Malam motarsa ta ɗan sami matsala ballantana ya fidda ki ko zuwa babban titi ne."
Sadiya ta yi murmushi. Iyaye dai duk inda suke akwai tausasawa ga yaransu. Wato tana hango mata ƴar tazarar lungun nasu zuwa titi, ita kuwa ai har ta saba ba ta ma ganinsa. Ta san Innar ta san da hakan, kawai dai ƙila ganin ba ta jima da farfaɗowa daga cuta ba ne.
"Babu komai Inna, zan iya zuwa."
Jinjina kai ta yi.
"Shikenan, Allah ya tsare ya ba da sa'a. Kin dai yi Azkar ko?"
Sadiya ta amsa da amin kafin ta ba ta amsar ta yi Azkar din. Daga haka suka kara sallama ta fice don Malam bai ko tashi a bacci ba.
***
Abba ya yi kamar bai ji batun da Mami ke yi dangane da ɗan nasu ba. Mami kuwa ta kai wuya amma ta danne shirun da ya yi mata. Ta sani tun farkon fara batun Husna da Huzaif ya yi mata wani kalami akan yanda ta dinga zazzaga faɗa wai a rabu da ɗanta ya auri wacce ya ke so.
"Zan bar shi, idan har Sadiya ta janye ita ma ta fasa auren ɗan naki, zan bar shi ya auri wacce ya so din. Sai dai ki sani, ko kusa kar ki kuskura ki zo min da wata magana daga baya. Ba na ƙin Husna saboda abin da ya yi Sadiya shi ya yi ta, amma ba na goyon bayan yaudara da cin amana."
Tana kawo wa nan ta sauke ajiyar zuciya har sai da Abba ya ɗan ɗago daga duban wayarsa da yake yi ya dube ta sai kuma ya yi ɗan murmushi ya girgiza kai.
"Ki rage wa zuciyarki damuwa Mariya, ki maida lamuranki ga Allah. Abin da ki ka zo min da shi zargi ki ke yi kuma matsayinmu na musulmai zato zunubi ne. Kin yarda kin yi imani kenan yarinya ƙarama kamar Husna za ta iya bibiyar Bokaye har ta cutar da ɗanki? Babu fa wanda ya isa ya yi wa mutum abin da Allahnsa bai mishi ba."
Mami ta ɗan haɗiyi miyau.
"Na sani, amma kuma asiri gaskiya ne yana ci, tunda tarihi ya nuna ya ci Annabinmu s.a.w, kenan zai iya kasancewa ta yi aiki..."
"Ya isa haka Mariya, ya isa. Ba na son zancenku na mata. Idan dai dagaske kin yi imani Allah ke yi, to ki maida komai gare shi, ki cire zargi ki kuma bar munana zato ga surukarki. Hakan babu abin da zai ɗarsa maki a zuciya face tsanarta. Ba na son wannan magana don Allah, ya isa haka. Ta tsaya iyakar nan."
Yana kai wa nan ya mike, dama fita zai yi ya tsaya jiran direbansa da bai ƙaraso ba, tun kuma yana maganar ya ga kiransa ya shigo hakan ya ba shi tabbacin isowarsa. Daidai lokacin ma sai ga Amir ya shigo da sallama, bayan ya gaishe su ya ɗauki jakar Abban dake saman teburin tsakiyar falon yana shaida wa Abban isowar Isuhu Direba.
Mami ta bi shi da addu'ar Allah ya kiyaye, nan ta yi zaune cikin tunanin mafita. Toh za ta tunkari Inna ta yi mata babban gargaɗi a kan ɗiyarta ne? Ko kuwa ita Husnar za ta kira ta ja wa kunne?
Girgiza kai ta yi. Duka waɗannan ba masu yiwuwa ba ne, kamar dai yadda Abban ya ce ne, addu'a za ta dage da yi wa Huzaif ɗin. Wannan ne kaɗai mafitarta.
***
Bayan Sati Biyu...
Cikin yanayi mai nuni da tsantsar baƙin ciki ta fito daga banɗakin bayan ta gyara jikinta. Bayyanar al'adarta ya rushe dukkan burikan da ta ci. A farko ba ta damu da haihuwar ba, amma kuma a yanzu da tarin mafarkanta ya koma ga son ganin gudan jininta, da ma sauran abubuwa da ba ta ko tunaninsu a baya wanda ba za ta samu ba face sai ta haihu musamman ɗa namiji a wannan gida na Alh Nuhu.
A gefen gado ta zauna gami da riƙe kai. Ta ja tsaki ya fi a ƙirga, zuciyarta na tunzurata a kan ta je kawai ta buɗe firij ta ɗauko kayan aiki ta afa a bakinta ko za ta sami nutsuwa idan ta yi mankas, amma kuma wata zuciyar na kwaɓarta gami da yi mata tuni a kan burinta na samun haihuwa wanda ko ba a faɗamata illar shaye-shaye ga ɗiya mace ba, matsayinta na wacce ta karanta a makaranta, tana da masaniya dangane da hakan. Ta ƙara jan tsaki.
'Kishiyar nan dai da ki ka tsana ita ce za ta zo idan ba ki nutsu ba.'
Ta faɗawa kanta, sai ta miƙe ta fice zuwa falo don zamanta a ɗakin zai iya haifar mata da dana sani marar iyaka.
A wannan gaɓar ba ta Sadiya ta ke ba, babban tashin hankalinta Alh Nuhu ya ƙaro aure bayan ita, sanannen mutum ne kuma fitacce, aurensa ba ɓuya zai yi ba. Balle ma yanzu da suke kan ganiyar zaɓe kuma jam'iyyarsu ce a kan gaba ko'ina maganarsu ake yi. Ta sani idan har ya tashi aure to fa duniya sai ta shaida kuma wannan zai zama babban abin kunya a wajenta. Ƙawayenta su yi mata dariya hakanan ma waɗanda ta gama yi wa gani-gani a rayuwa da cika baki.
Ta tuno ko sadda Likita ta auna ta tabbatar matsalar ba mai yawa ba ce muddin za ta maida hankali wajen shan magungunan da za'a ɗora ta a kai, ta sha har tsawon kwanakin nan, ta kuma saka rai cewa ba za ta fa hailarta ba kwatsam komai ya rushe a yau.
Da kuma ta tsaya ta yi tunani, ta ga ba ta da dabara ko wayo a yanzun face kawai ta kira Atine su koma wajen Malaminta, ita tana ganin ma shi ne ya yi mata aikin da komai ba ya tafiya daidai a rayuwarta.
Wayarta ta jawo, ganin lokacin karfe bakwai na dare ta san cewa ta makara sai dai ko goben. Gwaggo Atine ta dannawa kira amma abin takaici a kashe, koda ta kira ɗaya a cikin mutanen da ke zama a Babban gida, aka ce mata Gwaggon ta haura Nijar kai kayan da ta sara. Ta ja tsaki ta kashe wayar, za ta je ita kaɗai tunda za ta gane wajen. Da wannan ƙudurin ta ji ta ɗan sami nutsuwa.
***
Nudrat ta dubi Nene fuskarta da alamar tambaya ganin yanayin Hamma AbdulMajid kamar marar lafiya. Daga gaisuwa ma ko kallonsu bai ƙara ba ya nufi ɓangarensa. Nene ta yamutsa fuska tana kai ludayin furarta a baka. Nudrat ta gaji ta yi gefe da littafin da take dubawa na makaranta ta ce.
"Nene meke samun Hamma ne? Kwanakin nan gaba daya ya sauya. Ina ta son na tambaya amma karatun jarrabawa ke mantar da ni."
"Me zai dame shi bayan soyayyar da ya sa a gaba? Baffanku ne ya ce ba zai mayar shi ƙaramin mutum ba, ya ce a je a nema masa auren ita Fareeda, kuma an je iyayen yarinyar sun tambaye ta tace ba ta san da zuwansu ba. Shi ne dalilin wannan ƙuncin na sa."
Nudrat ta ji zuciyarta har wani tafarfasa ta ke yi, ita fa ba ta yin wannan Fareedar tun da sadda ta fahimci ba ta damu da sha'anin Yayan nata ba, ta gane shi ke kiɗa da rawarsa. Aikuwa ga zahiri nan ya tabbata. Ta yi ƙwafa.
"Shi ma Hamma kamar babu sauran mata a duniya sai ita? Ni wallahi har na ji ta fice min a kai gaba ɗaya na tsane ta. Mts. Allah ya raka taki gona. Ya kawo masa wacce ta fi ta komai ma."
Ta ƙarashe cike da ƙuncin rai, Nene ta yi murmushi.
"Ke kuma ɗaukar wa kan ki dala ba gammo. To shi kuma bai ga laifinta ba, ya ce shi ne bai tunasar da ita batun zuwan ba. Ai shi ba zai yi fushi da ita ba tunda yana mata makahon so. Uzuri ya yi mata."
Takaici ya ƙara turnuƙe Nudrat, ta ji zancen ma ya ishe ta. Hamman kansa haushi ya ke ba ta. Sai kawai ta ce Allah ya kyauta daga haka ta tattare kayan karatunta ta nufi ɗakin karatunsu (Study Room). Daƙyar ma ta samu yin karatun bayan ta gama kukan tausayawa Hammanta da ta fi so kaf cikin yan uwanta bayan Yayarsu Maryam da ta rasu.
***
A makaranta Nudrat suna fitowa ɗakin jarrabawa labarin damuwarta ta soma ba Sadiya don gaba daya ranar ba ta da walwala. Ba Sadiya ba, hatta sauran ɗalibai sai da suka gane ba ta cikin walwalarta don ita din akwai tsokana da wasa da dariya. Kawai dai ta san wanda ta ke yi wa da kuma sadda ya dace a yi. Da wannan da ma kokarinta a aji, Malamai da daliban suka san ta, ita kuwa Sadiya da fara'ar ba ta cika yi ba sosai, an san ta ne sanadin kaifin kwakwalwarta a karatu sai ko sanadin Nudrat ɗin.
"Allah Sarki, Allah ya yi masa sauyi mafi alheri. Idan kuwa matarsa ce, Allah ya daidaita lamura." Ta furta cikin dakiya bayan gama sauraron Nudrat.
"Ba amin ba ma, in sha Allahu ba zai aure ta ba. Can ga su gada."
Nudrat ta faɗi a gaggauce tana mai tarar numfashin Sadiyar. Ita kuwa murmushin yaƙe ta yi. Ba ta da abin cewa, ba ta sani ba farin ciki za ta yi ko akasin haka. Sai ta ji ma tausayi ya ba ta, ta san zafin son maso wani, da alama shi ya ke yi. Ta ji ina ma za ta iya kawar masa da damuwar Fareeda, amma kuma a take ta ƙaryata kanta sanin da ta yi ba zai taɓa yiwuwa ba.
"Ni wallahi ina ma ya samu mai nutsuwa da hankali irin ki Triple."
Maganar Nudrat ya sa ta kallonta da sauri kuma a firgice, ita ma Nudrat din ita ta ke duba fuskarta cike da rauni tana kuma so Sadiya ta yarda dagaske ta ke yi a kalaman ta.
"Ke ni fa na jima da hango dacewarki da Hammana wallahi."
Nudrat ta ƙara furtawa ganin Sadiya ba ta da ko niyyar tankawa zancenta na farko, asalima kauda kai ta yi. Wannan karon kuma guntun tsaki ta ja kafin ta miƙe.
"Na kula yau dai damuwa ta so ta maki yawa. Ni kin ga tafiyata yamma na yi. Sai Allah ya kaimu goben."
Daga haka ta soma tafiya, Nudrat ta biyo bayanta da sauri ta dafa kafaɗarta.
"Allah kuwa ba damuwa ce ta yi min yawa ba. I am serious Triple. Idan akwai wadanda nake ganin dacewarsu tare a zamantakewar aure to ke da Hammana..."
"Please Nudrat, mu bar zancen nan. Please, na haɗa ki da Allah. Ki bari ma ya ji da damuwar da ke cin ransa a yanzu. Kuma ni na ce maki ina sonsa?"
Nudrat ta sauke ajiyar zuciya.
"Shi ke nan, na bar zancen. Kin ji dadi?"
Harararta Sadiya ta ɗan yi kafin ta ce.
"Ni na wuce, sai goben."
Daga nan suka yi sallama. Nudrat ta bi ta da kallo, haka kawai ta ji ba za ta haƙura ba. Haɗin ya yi mata, za ta so hakan ya kasance. Haka ta dinga wassafo wai har ga Sadiya sun shigo gidansu gaida Nene da Baffa ita da Hamma da yaransu uku.
***
AbdulMajid ba ƙaramin raɗaɗi ya ji da wannan sauyin da Fareeda ta masa ba, duk a kan ya yi gaggawar tura iyayensa gidansu alhalin bai sanar da ita ba. Ya je gidan nasu, ya yi ban bakin a waya amma kuma ba ta sauya zani ba.
"Ba fa ta sonka, ya dace a zo gaɓar da za ka yi wa kanka faɗa ka haƙura da ita Abdul."
Ya tunano kalaman da Maina ya yi mishi a ɗazun da suka yi waya, gaskiya ce mai daci ya sani, ya kuma dace zuwa yanzu ya fita sabgarta dagaske. Ya rungumi ƙaddara ya kuma nemi soyayyar wacce ya ke ji a rai za ta iya maye masa gurbin Fareeda tunda ko babu komai yanayin kamalarta da ma abubuwa da dama na surarta masu fisgar hankalin ɗa namiji suna masa zubi da na Fareeda. Ya sani sanadin soyayyar Fareeda ce ta sanya Sadiya ke burge shi ita ma.
***
Hajara ta kai sama da mintuna ashirin a cikin motarta yayinda karo na farko a rayuwarta ta ji zuciyarta na bugu da ƙarfi saboda tsoron wata halitta, halittar ma Boka. Babban tunaninta da wane idanun za ta dube shi karo na biyu bayan ta gasa masa baƙaƙen maganganu ga kuma uwa uba dariyar da ta ke da yaƙinin zai yi mata. Sai kuma ta ja tsaki a fili ta ce.
"Kunyar mara kunya ma asara ce. Bari na shiga na ga me zai ce min."
Daga haka ta dauki jakarta bayan ta kashe motar ta fita ta rufe. Sai da ya kammala da mutum biyar sannan layi ya zo kanta ta shiga falonsa na biyu. Yana ganinta ya yi wani murmushin mugunta gami da kauda kai ya na gyara zaman alkyabbarsa.
"Ke ce yau tafe Hajara?"
Ba ta sha mamakin yanda bai mance sunanta ba balle kuma fuskarta, ƙila ma har zuwanta zai iya sani tunda hatsabibin kansa ne. Zama ta yi gwuiwa a sake ta gaida shi. Gaisuwar da ko Mijinta ba ya samun irinsa daga wurinta, ta fara da ba sa haƙuri bisa tozarcin da ta yi mishi a baya.
"Riƙe ban haƙurinki Hajara. Yanzu ki faɗa min meke tafe da ke? Har yanzu matsalarki da Sadiyar ce ko kuwa har ta ɓangaren aurenki?"
Ya ƙarashe yana ƴar dariyar da ta yiwa kallon tsantsar rainin wayau amma ta shanye tunda mai nema ba ya fushi kuma tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka.
"Duka biyun ne ya kawo ni Yallaɓai. Na farko dai ina son a yi wa Sadiya aikin da zai sa har abada ta ƙi auruwa sannan a aika mata shashatau ta yanda za ta shiririce ta daina karatu sai wasa da bin maza. Na biyu kuma mijina ne ya tashi haiƙan ya na so ya ga na samu juna biyu idan ko ba haka ba zai yi min kishiya. Ni kuma a duniya na tsani kishiya, shi ne nake son na haihu ko ta wane hali ne don na tserewa wancan bala'in."
Ya yi dariya sannan ya hau tsaface-tsafacensa. Tabbas ya gani, ya kuma shaida ba ya ganin dukkan wani abu da ya shafi Sadiya, ya ƙara yin wani tsafin, nan ma sai ya kula yarinyar gewaye take da kariyar Mahalicci, bai ga ta inda zai iya cutar da ita ba. Irinsu ma yadda suka dage da ibada cutar da su abu ne mai matuƙar wahala. Ƙila ya iya rasa rayuwarsa idan ya dage, ko kuma aikin kacokam ya dawo kansa.
Ya ɗago kai ya a duban Hajara wacce ita ɗin ma idanu ta zuba mishi cike da fargaba, tsoro ta ke a maimaita abin da ya faru a wancan zuwan nasu. Ba ta son jin dukkan abin da ya ci karo da burinta da fatanta, ba ta son ya faɗa mata idan har hakan zai zame shiga tarkon nadama karo na ba adadi.
Ta kauda kai daga kallonsa, ta dai kula a komai kamar ba ta da sa'a a rayuwa, komai ba ya tafiyar mata yadda ta so. Tun daga lokacin ƙuruciya har kawo yanzu da ta yi aure, komai kan zo mata a baibai.
"Ki sha kuruminki, har abada Sadiya ba za ta auru ba. Zan yi maki aikin kwanaki ɗari a kanta. Ina ba ki tabbacin burinki zai cika a kanta. Sai kuma bari na gane maki kan mijinki."
Yana kai wa nan shi kansa sai da ya sauke ajiyar zuciya yana muzurai, ya kula matar ta gama imanin cewa wannan karon ma haƙanta ba zai cimma ruwa ba. Ko babu komai tunda har ta yarda da shi haka ta kuma dawowa izuwa garesa to fa zai yi duk abin da zai yi don ganin ya kwashi rabonsa a asusunta yadda ya kamata. Gwara ya ci banza ya bar wa banza.
Hajara kuwa wannan albishirin ne ya sanya ta sakin doguwar ajiyar zuciya don cikinta har wani ɗurar ruwa ya yi dab take da sakin fitsari, sai kuma sakamakon ya zo mata a bazata, kawai sai ta yi dariya mai cike da zallar farin ciki. Shi ko Boka har mamakin wannan irin ƙiyayya da ta ke yi ga yarinyar da ta kira Sadiya ya ke.
"Batu na gaskiya za ki haihu, haihuwa nan kusa ma. Sai dai ta hanya ɗaya za ki iya haihuwa a yanzu."
Nan da nan murmushin saman fuskarta ya ɓace ya koma firgici da tsoro ninkin na baya. Kallonsa take amma ta kasa cewa uffan. Ya cigaba da zancensa.
"Sai dai ki nemi matashin saurayi a waje ki yi mu'amala da shi bayan kin ba ni haɗin kai. Zai zama shi ne na biyu, mijinki na uku. Muddin hakan ta kasance, toh babu mai hana ki samun ciki." (Wa'iyazubillah)
Ta jinjina kai, a ganinta wannan ba wata babbar matsala ce a gare ta ba muddin kwalliya za ta biya kuɗin sabulu, matashin saurayi kuwa ai ko ta hannun su Waleeda za ta iya samu.
Ba ita ce ta bar gidan Boka ba sai bayan sallar Magriba. Shi jin sa ya ke yi kamar yau kyautar duniya aka ba sa a tafin hannu, ga asusunsa cike fal ga kuma aiki babba da ya yi da Hajara. Shakka babu ta yi masa fiye da tsammani kuma ya ci alwashin