Showing 12001 words to 15000 words out of 124441 words
kallo za ka san jinin Malam Sa'ad ce saboda kamanninsa da ta ɗauka gaba ɗaya. Baƙa ce amma baƙinta bai kai na su Hajara ba sai ita ta kasance mai ɗan haske sakamakon nonon farar mace da take sha.
Hajara tun sadda Malam ya raɗawa jaririyar sunan mahaifiyarta Asma'u ta ce a dinga kiranta da Husna. Abin da yake bai wa Inna Mairamu mamaki bai wuce ganin yanda Hajara kan tsallako ta shigo har ƙuryarta ba ta sa hannu ta dauki Husna ta fita da ita tana bata kulawa. Ta yarda lallai dagaske ba karamin so da kaunar Mahaifiyarta take yi ba. Ba ma ita kaɗai ba, hatta Safiyya sai da ta zo gidan ganin Husna har da kayan jarirai ta kawomata. Mustafa da Hashimu da Baba Habu su kansu wannan karon sun zo sun ga Husna.
Inna Mairamu da ɗiyarta, amma Hajara babu irin tuggun da ba ta shirya mata ba sanadiyyar Husna.
©Rufaida Umar
https://arewabooks.com/book?id=663894ac767a55b1dd421f6a
*Akwai pages na gaba har guda biyu a manhajar arewabooks. Kuna iya bibiya a can*😃🥰
***
*Kazar Kwanci...*
A kwana a tashi yau fari gobe baƙi, har lokacin da Hajara ta yi candy.
Sun zana jarrabawarsu ta ƙarshe sannan suka haɗa ƴar ƙwarya ƙwarya da abokan karatunta don taya juna murna. Ranar walimar makarantar na graduation, kaf yayyunta da dangi sun je. Inna Mairamu haka ta kai zuciya nesa duk kuwa da furucin Hajara na cewa ba ta gayyatarta da zabiyar ƴarta, hakan bai hana ta shirya ta bi Malam ba. Husna dake gidan Safiyya kwananta biyu a can. Sadiya kuwa tana aji biyu a firamare yayinda Husna take na farko a nursery.
Malam na iyakar kokarinsa wajen ganin yaransa sun yi makaranta mai kyau kuma cikin rufin asiri, kaf a yaransa babu wanda ya taɓa yin ta gwamnati sai Hashimu babban ɗansa wanda ya yi karatun tun duniya na kwance, makarantun gwamnatin ba su lalace da rashin karatu yanda ya kamata ba. Daga kan Baba Habu kuwa dukkansu ta kuɗi ce. Sai dai kuma irin ta kuɗin da na baya suka samu, su Sadiya ba irinta suka samu ba sakamakon chanjin yanayin samun na Malam. Amma kuma daidai gwargwado a na karatu.
An yi bikin walimar yaye ɗalibai an kammala, Hajara kasancewar tana cikin farin ciki ko kallo Inna Mairamu ba ta ishe ta ba. Sam ba ta san da zuwanta ba ma sai da ta ji wata ƙawarta a murya ƙasa-ƙasa tana faɗin.
"Kai Hajjo, dama kuna da fara a gidanku? Baby girl ɗin nan ta yi min kyau."
Furucin ne ya sa ta ankara da Sadiya wacce Inna Mairamu ta sanya mata kayan sallarta da ya wuce, rigar shadda ruwan bula mai haske wanda ya ɗan ɗage mata, an yi aiki a wuyan sai ko ɗankwalin da aka yi mata ɗauri daidai da zamani. Ta yi kyau yarinyar kamar irin wacce ta fito daga gidan masu hannu da shuni.
Wani abu ya zo wa Hajara wuya, sai ta ja tsaki ta maida dubanta ga ƙawarta.
"Malama wannan kinga sun yi kama da ƴan gidanmu? Toh makwaftanmu ne suka zo gayyar soɗi. Dallah muje."
Ta faɗi tana sa hannu ta ɗauki Husna wacce a farko take riƙe da hannunta. Inna Mairamu ta ji amsar da Hajara ta ba ƙawarta sai dai ba ta ji furucin ƙawar ba, girgiza kai kawai ta yi gami da yi wa Hajarar fatan shiriya a zuciya.
Hotuna sun yi shi sosai kafin kuma su tattara su tafi gida aka bar Hajara a nan. Gaba ɗaya gidan Malam suka nufa, anan aka ci girkin da Inna Mairamu ta dafa musamman domin wannan ranar. Safiyya na ci tana korafi wai kamar maggi ya so ya yi yawa. Harararta da Hafsatu ta yi ne ya sanya ta taɓe baki ba tare da ta tanka ba.
"Allah ya gafartawa Mama, nasan da ace tana duniya wannan ranar ta zo, ba ƙaramin farin ciki za ta yi ba. Na so ace points dinta ya kai na samun medicine dinnan da Mama ke buri."
Cewar Mustafa kenan bayan an kammala cin abinci an yi zaman hira. Malam ya yi murmushi.
"Ai akwai wata shekarar, tunda har ranta itama ya fi son ɓangaren likitan, sai ta ƙara hakurin zama ta maimaita jamb, idan Allah ya nufa sai a dace a wannan karon."
"Ni kuwa sai na ga da zaman jiran ba gwara ta haƙura ta yi nursing ba?" Faɗin Yayansu Hashimu. Baba Habu ya cafe zancen.
"Kayya, Auta za ta yarda da wannan shawarar taka? Ta fa ƙwallafa rai."
"Gaskiya dai ni ma ina bayan Baba Habu, ina ma ta hakura. Ai dai duka fannin asibitin ne ko? Zaman jiran ba shi da amfani." Faɗin Hafsatu.
Malam ya girgiza kai.
"Ku bar ta ta kara gwada wa. Na yarda da ita, na san za ta iya."
Ganin haka kowa ya riƙe na shi ra'ayin, aka bi lamarin da addu'a. Kamar koyaushe Malam ya shiga tuntuɓar kowannensu idan akwai mai wata matsala koda a ɓangaren iyalinsa ne, kowa ciki yace babu. Daidai gwargwado asirin kowannensu a rufe. Mazan suna kuma zaune da matansu lafiya, idan ma akwai mai matsala a matan ba ta wuce matar Hashimu ba wacce kwana biyun ta tada hankali akan ginin da ya ke yi mai ɓangaren mace biyu, ita ta sani aure zai yi a cewarta bai isa ba. Amma ganin wannan ba matsala ba ce yasa bai kawo ta gaban Malam ba. Ko babu komai ai shi namiji ne, yana buƙatar sirri a rayuwarsa.
Hafsatu ce ta miƙe tare da Safiyya suka bar falon zuwa tsakar gidan inda Inna Mairamu take zaune tana kiciniyar sauyawa Sadiya kaya ganin duk ta ɓata rigar shaddar da maiƙon abinci. Dama tun kammala cin abincinsu ta miƙe ta basu wuri don su tattauna da mahaifinsu. Safiyya ta ja gujera ƴar tsuguno ta zauna tana faman taunar cingam wanda ba ta rabo da shi saboda gudun tashin zuciya. Nan Inna Mairamu suka yi ta hira da Hafsatu ban da Safiyya wacce a ƙarshe ma miƙewa ta yi ta nufi ɗakin Hajara ta kwanta ganin Husna ma sharar bacci babu abokin hira.
A bakin Hafsatu ma Inna Mairamu ke ƙara jin cewa Safiyya na da juna biyu. Murmushi ta yi da fatan rabuwarsu lafiya da cikin, dama ai ta ga alamomin da ke nuni da hakan sai dai tunda ba huruminta ba ne ya sa ta ja baki ta yi shiru abin ta.
***
A haka rayuwar ta cigaba da tafiya a gidan Malam Sa'ad, Hajara ba ta fiye zaman gidan ba, mafi yawan lokuta idan babu makaranta alhamis da juma'a, jan Husna take yi su je gidan Safiyya ko kuma can dangi su kwana. Farko har a lokutan islamiyya fita take yi da ita, sai da Inna Mairamu ta nunawa Malam ba ta son hakan sannan ya yi magana don shi ma sam ba ya son wasa da karatu ya san darajar ilimi tunda malamin makaranta yake. Hajarar ma ya so ta koma bayan saukar Alkur'ani da ta yi don cigaba da samun karatukan litattafai na hadisi da fiqhu amma abu ya gagara dole ya rabu da ita. Da dai boko ne, tana da matukar kokarin dagiya wajen karatu da ganin ma Husna ta yi don ita ke koyar da ita aikin makaranta har wani lesson na musamman take mata a gida. Takan cewa Sadiya,
"Ki je Nanny ta koyamaki, kodayake me ma ta sani ban da wankin kashi da fitsarin yara da sharar aji. Sai dai ki yi ta daukar ta ƙarshen aji yarinya idan dai ni zan koyar da ke karatu."
Inna kuwa sai dai ta yi murmushi, don tana matsayin Nanny a makaranta ba yana nufin ko yaya ba ta da ilimin ba, a baya ta soma na yaƙi da jahilci sadda mijinta ya rasu, kuma ilimi na addini sai dai ta godewa Allah don Kawunta Jibo ya tsaya tsayin daka wajen ganin sun yi. Sau da yawa kuma ita koyar da Sadiya aikin makaranta da aka basu, yarinyar ba ta taɓa zuwa ta karshen aji ba tunda ita ma da ɗan kokarinta. Daga baya ne kuma ma Abba ya cewa Malam ya dinga turo su ana musu lesson da yaransa a gida, Malam ya yi godiya don shi a yanzu bai cika samun lokacin koyar da su ba ganin Hajara na yi don tace masa har Sadiya tana mata.
Gidan Alhaji Abubakar babban gida ne don ya fi Malam rufin asiri sosai, dan kasuwa ne wanda har yakan fita ƙasashen duniya sarin kaya, wani lokacin kuma ya tura babban yaronsa a kasuwa. Allah ya sanyawa kasuwancinsa albarka sosai. Matansu biyu kuma suna zaune lafiya kowacce da ɓangarenta. Ba su zauna sun dogara da abin hannun mijinsu ba, Hajiya Mariya uwargidansa kuma aminiya ga Marigayiya Asma'u mahaifiyar su Hajara, haifaffiyar garin Kano ce kamar mijin nata shi ma. Sun yi aure cike da so da kaunar juna. Yaransu tara cif.
Babban ɗansu Hamza ya girmi Hashimu babban ɗan Malam, saboda Alhaji Abubakar ya riga Malam aure. Sai da ya shekara sannan aka yi bikin Malam da Asma'u.
Sai da Haj Mariya ta yi haihuwa biyar kafin Abba ya ƙara aure. Duk yanda aka kai ga zigata sam ba ta tayar da hankali ba don dama tsakaninta da shi bai taɓa yi mata alƙawarin cewa da ita kaɗai zai rayu ba. Kuma ya sha faɗa idan har Allah ya ƙaddaro masa aure zai yi fa, shi ba mai ra'ayin zama da mace ɗaya ba ne. Tun tana kallon abin a wasa har ta soma jin haushi da kishi, karshe ma sai ta saduda. Wannan ne dalilin da yasa auren bai ɗaga hankalinta sosai ba sai dai abin da ba a rasa ba tunda kishi ya zama dole idan da so da kauna. Marigayiya Asma'u tana daga cikin masu kwantar mata da hankali da nuna mata muhimmancin hakuri, ta sani sarai Asma'u ba fa da kishi irin na jahilai. Matar ta san me take yi sosai. Kuma tana ji a ranta koda ace ma Malam ya dauko aure, Asma'u ba za ta tashi hankalinta ba, sai dai soyayyar da kowa ya shaida Malam na yi wa Asma'un ne yasa babu wanda ya taba kawo mata zama da kishiyar. Ga shi kuwa sai bayan rasuwarta ne ya yi auren.
Lokacin da aka yi auren Abba da Amaryarsa Zulfa'u ne, Malam ya yi rashin matarsa Asma'u. Abba ya yi angwancinsa cike da jimamin mutuwar matar aminin nasa. Kar Haj Mariya ta ji labari, don zafin mutuwar Asma'u da tashin hankalin da take ciki ya kara mantar da ita wani abu wai kishin Zulfa'u. Girkin ma gaba daya sakarmata ta yi har tsawon sati biyu saboda ba ta cikin nutsuwarta.
Hamza, Radeeya, Lubna, Huzaifa, Amir da Amira, Husna, Khalid da Affan. Su ne yaran Haj Mariya.
Amarya Zulfa'u wacce aka auro daga Maiduguri kuwa yaranta uku. Musaddik, Amina (Meenat) da autarta Zainab (Zee Mama).
Hamza ya yi aure yana zaune da iyalinsa a Kaduna inda yake a barikin soja, Radeeya da Lubna su na zaune a nan Kano da mazajensu. Sai ko Huzaifa da ke ƙasar India inda yake karantar fannin medicine. Amir da Amira suna dab da yin candy, Husna da Musaddik kuwa suna aji na farko a babban sakandire, yayinda Meenat ke aji na biyu a firamare, tare suke tafiya da Sadiya. Sai ko Zee Mama da suke tafiya aji guda da Husna.
Wadannan su ne zuri'ar Alhaji Abubakar B Sharaɗa.
Tun daga sadda ya yi magana kuma, Sadiya da Husna suka koma lesson a gidansa a daki na musamman wanda ya ci sunan Study Room don babu komai a ciki sai litattafai da sauran kayan karatu, nan inyamurar malamarsu ke koyar da su tare da Meenat da Zee Mama sai ko Husna da Musaddiƙ.
***
A lokacin ne samari suka dinga ɓullowa suna son Hajara, aikuwa duk wanda ya kawo kyauta to fa ita da Husna ke sanyawa a gaba su karar, idan na amfani ne na manya ta yi abin ta, idan kuwa kudi ne siyayyar akan Husna yake ƙarewa. Sadiya ko oho, sai ko idan Husna ta turje akan lallai sai an yiwa Sadiya ne saboda tana kaunarta sannan Hajarar ke yi tana kiranta da mayya kwadayayya.
Shekara na zagayowa ta sake maimaita jarrabawar Jamb. Sai dai wannan karon ma sakamakon bai kai yanda ake buƙata na medicine ba, ta sha kuka a karshe don kanta tace ta hakura za ta nemi nursing. Shi kuma cikin ikon Allah ta hannun Alhaji Abubakar wanda tsabar aminta ne yasa Malam sanyawa dansa sunan suke ce masa Baba Habu, ya nema mata gurbin nursing din. Sadda aka yi jarrabawa ta yi nasarar tsallakewa. Murna kamar ta yi me. Shi kansa Alhaji Abubakar wanda suke kira da Abba ya yi farin ciki kwarai da Hajara ba ta watsa mishi ƙasa a ido ba.
Aikuwa ana soma karatu ta maida hankali sosai, hakan ya sa ma ta rage shiga harkar Inna Mairamu, ita ma ta samu salama.
Sadiya ta taso yarinya marar son hayaniya a wasu lokutan kamar dai Innarta, amma fa ko a kafa ba ta kama Inna a bangaren hakuri ba, Inna takan ji za ta iya yafewa mutum, ita kuwa Sadiya abu daya ta rike a ranta, Hajara da Safiyya da ma sauran yayyunta idan an cire Yaya Zakari da Anti Hafsatu, babu wanda ke son su ita da Innarsu. Shiyasa ita ma ba ta son su, koda dai tana mugun tsoron Anti Hajara don ko muryarta ta ji sai gaba daya ta ruɗe, ko wasa take yi a ɗaki za ta hankaɗe kayan wasan nata wani lokacin har tana bugewa haka za ta shige har bayan gadon Inna ta ɓuya tana rawar jiki. Sai da Inna ta haɗa da roƙon Allah da yawaita addu'a kafin wannan tsoron ya ragu da kashi talatin. Ko inda Malam yake Sadiya ba ta zuwa idan Hajara na wurin, wani lokacin abinci kasa ci take yi idan an yi zaman ci sai dai daga baya ne Inna ke zuwa ta kai mata ɗaki ta ci.
A hankali kuma tana girma tana ƙara wayo tsoron na ɗan raguwa ba kamar a baya ba.
***
Tafiya ta yi nisa, Sadiya na ajin farko a sakandire, Hajara ta kammala karatunta na Nursing. Lokacin shekarunta goma sha biyu a duniya, yayinda Husna ke da shekaru tara. Ita kuwa tana firamare aji huɗu . A wannan shekarar dai Hajara ta fara aikinta a karamin asibitin dake kusa da su kafin a cewar Malam, ta samu aiki a babban asibitin gwamnati. Tun fara aikinta kuwa sai idanunta ya kara buɗuwa. Ita dai ba ta da kyau na a zo a gani, sai dai akwai dirin jiki ga uwa uba iya daukar kwalliya. Da wannan take jan hankalin maza. Kanta yana ƙara rawa da yanda suke ruɗewa su na sonta. Haduwarta da wata abokiyar aikinta mai suna Nusaiba, ya kara jefa rayuwarta cikin ruɗin shaiɗan. Sanadiyyar Nusaiba ta koyi sakin jiki ga duk wani likita ko abokin aikinsu da ya nemi ya latsa ta, farko takan biye musu ne kawai don son zuciya da kuma jin dadin abin, sai daga baya ta fara karɓar kuɗi. Sai ya kasance ba ruwanta, hatta club takan bi Nusaiba su je ta dinga fakewa da tana da night duty, sau daya Malam ke kawo ta a motarsa da magriba asibitin ya yi tafiyarsa, yana barin wajen za ta hau abin hawa ta nufi gidansu Nusaiba idan a ranakun ita ma ba ta da aikin kwana.
Manyan mutane sosai Hajara ta sansu, inda ba ta taɓa tunanin takawa ba ta taka, sai ta ji a duniya ba ta da burin da ya wuce ta auri wani shahararren mai kuɗin. Don a yanda take ɗanɗana rayuwar kwana ko wuni a cikin AC ba ta jin za ta iya auren talaka.
Sanadin wannan yawace yawacen nata ne ta ja Malam da Inna suka yi fada kawai don Innar ta ce Malam din ya sanya idanu a kan Hajarar don tana tunanin da matsala. Aikuwa ya hau ta da fada sosai kan cewa tana zargin ɗiyarsa. A karshe har yajin kwana a shimfida daya ya yi da ita. Ya bar cin abincinta, sai dakyar Inna Mairamu ta samu suka dawo daidai. Tun daga lokacin ta dauke idanu akan Hajara, ba dai ta cire ta cikin addu'o'inta ba da yi mata fatan shiriya.
Ta sanadiyyar wani babban Alhajin da take mu'amala da shi kuma mai faɗa a ji a gwamnatance, ta samu gurbin aikin jinya a asibitin gwamnati na Malam Aminu Kano. Ta rufe Malam da cewa neman aurenta yake yi shi ne dalilin da yasa ya nemar mata. Malam sosai bakinsa ya ƙi rufuwa musamman da ya ga babban mutum irin Alhaji Habibu Tofa ya tako har gidansa ya zo sun gaisa ya kuma yi masa bayanin cewa shi ya nema mata aikin saboda yana sonta da aure. Har da ba da hakurin rashin soma gabatar da kai kafin yin wannan karambanin, Malam ya nuna babu komai ya yi godiya sosai.
Koda suka fito daga wurin Malam sai da suka yi wata dariya da cafkewa ganin an shirga mahaifin mata. Har a ran Hajara za ta so ya kasance mamemin aurenta dagaske amma ya nunamata shi gaskiya ba zai iya ƙara aure yanzu ba tunda bai jima da yin ta uku ba. A motarsa ma da sunan suna hira sai dai ya ɗan yi wasa da ita sosai kafin su yi sallama.
***
Zakari wanda ya samu aiki a wani kamfani kuma daidai gwargwado ana biyan kirki, nan da nan ya gingimo aure, tarin lefensa sai ya kasance a wurin Inna Mairamu yake yi. Hajara na kyallara idanu ta gani ai sai ta sanar da Safiyya da ma wasu a danginsu. Nan da nan abu ya nemi zama rigima wai don me sai a wurin Inna Zakarin zai yi tarin lefe. Malam bai dauki maganar wani abu mai zafi ba, ganin ma abin kamar zai tashi hankalin gidansa ya tsawatar ya kuma hana kowace mace a dangi zuwa don yin maganar. Anan kam Inna Mairamu ta samu sa'ida, amma fa zagi takanas Safiyya ke zuwa ta yi mata har da su Allah ya isa. Ga kuma na Hajara. Mustafa da su Hashimu dai Zakari suka yi wa caa wai don