Showing 69001 words to 72000 words out of 124441 words
fi nasu nesa ba kusa ba. Ko daga irin hotunan da ta ke ɗorawa a whatsapp status na yan uwanta, wasu ma ta ga suna tsantsar kama ya ci ta gane daga inda ta fito. Ta zo gidansu sau ɗaya an kawo ta a mota, Malam da Inna duk sun gan ta, kuma sun yaba da hankalin yarinyar, ita ce dai har a yau din da suke zancen ba ta ziyartarsu ba.
"Na sa ki dogon tunani don na ce ki bi ni gidanmu yau ɗaya Triple S?" Faɗin Nudrat kenan. Dama sunan da take kiran Sadiya da shi ne tun sadda ta ji duka sunanta ya fara da harafin S, wato Sadiya Sa'ad Shagari.
Sadiya ta girgiza kai tana ɗan yaƙe kafin ta yi magana Nudrat ta miƙe tana gyara zaman jakarta fuska ɗaure.
"Shikenan, na gane. Alaƙarmu alaƙar ɓangare guda ce, ni kaɗai ke ƙaunarki da zumunci fisabilillah. Na gode. Sai na shigo anjima."
Daga haka ta soma tafiya cikin sauri Sadiya ta bi ta suka jera ko kallonta Nudrat ba ta yi ba don haka ta ce.
"Ke kin fiye ɗaukar zafi, to ki yi hakuri."
Ƴar harararta ta yi kafin su yi wa junansu murmushi daga haka suka ƙarasa waje don direban dake kawo Nudrat ya yi nisa tunda ya sani sai shida na yamma yake dawowa ɗaukarta. Napep suka hau har suka kai Kuntau suna ta hira, bai sauke su ba sai da Nudrat ta yi mishi kwatance har gaban wani tafkeken gida wanda iyakar tsari ya tsaru. Tun ma daga waje ya burge Sadiya fiye da gidan Anti Hajara, tunaninta kuma ya za'a ga ciki.
Nudrat ta sallami mai napep suka nufi ciki bayan sun gaisar da Maigadin. Sadiya dai tana ta bin Nudrat har suka ƙarasa wata ƙofa ta danna ƙararrawar dake jiki ba jimawa aka buɗe. Wani matashi ne wanda da kaɗan zai girme su, Sadiya ta taɓa ganinsa hotonsa wajen Nudrat wai yayanta da take bi ma ne, sunansa Muneeb. Ƙin matsawa ya yi ya ba su hanya sai ma buɗe baki da ya yi cike da mamaki yake kallon Sadiya.
"Whoo, yau wace rana ga Triple S ɗin Jerry a gidan nan."
Nudrat jin ya kira ta da Jerry ya sa ta kai mai duka ya kauce yana dariya, ita Sadiya murmushi kawai ta yi tana fadin.
"Ina wuni."
Muneeb ya yi murmushin shi ma gami da nuna Nudrat da yatsa.
"Kin ji yanda ake yi ko? Gaisuwa, Triple ki koyawa ƙawarki."
"Wai Muneeb a rufe ƙofar nan haka mana, ko sai ƙudaje sun shigo min?"
Sadiya ta ga fuskarta karo na babu adadi a wayar Nudrat, ta kuma taɓa gaishe ta ta waya. Gani dai na ido da ido sai a yanzun ta ga Nenen Nudrat. Sai ta ga a fili ma ta fi tsantsar kama da Fulanin, daga rashin girman jikinsu har ma da hasken fata da siririn hanci har baka masha Allah. Tana zaune a falon ciki doguwar riga marar nauyi ta rufe kai da hular rigar. Nene na ganinta ta saki fuskarta sosai.
"Yau ashe ɗiyata ce a gidan. Sannu da zuwa Triple ɗin Nudrat."
Sadiya cike da jin nauyi ta ƙarasa ta russuna ta gaishe ta. Nene ta amsa tana tambayar su Inna da Malam abin mamaki har Husna da su Anti Hafsatu sai da ta tambaya. Mamaki ya sa Sadiya kallon Nudrat baki sake, Nudrat ta yi dariya sai ta kauda kai ta amsawa Nene.
"Ya na gan ku ko har an tafi yajin aikin?"
Sai a sannan ma Sadiya ta tuna ashe wai ana raɗe-raɗen Malamai za su tafi yajin aiki, maganar ma ɓata mata rai take. Nudrat ce ta ba Nene amsa da cewa suna da tazarar lakca ne sai ƙarfe huɗu za su shiga, dalilin kenan da ya sa suka taho.
"Kun kuwa yi dabara, toh ku shiga ku yi sallah sai ku fito ku ci abinci."
"Ni fa Nene shiyasa ba zan iya makarantun ƙasarnan ba, daga farawa har sun soma tunanin tafiya yajin aiki? Mts. Gaskiya akwai cutarwa a lamarin. Shiyasa ban so karatun Jerry a garin nan ba don dai Baffa ba zai bar ta ta koma ba ne."
Muneeb ke zancen yana yarfe yatsu.
"Ni dai Nene ki ce ya daina kirana da Jerry kamar wata namiji! Allah kuwa ba na so!"
Nudrat ta furta a zafafe tana turo bakinta, Muneeb ya harareta.
"Idan ba sunanki kenan ba me za'a yi kiranki? Ke da ba ki da aiki sai faɗa da Imam kamar masu ganin hanjin juna."
Za ta ƙara magana Nene ta ɗaga musu hannu.
"Ya ishe ni haka. Nudrat tashi ku je ku yi sallah, a gaban Sadiyar ma sai kun raba hali. Kai da Imam din ai baku da bambanci tunda ba ragawa juna kuke yi da ita ba. Allah ya shiryeku."
Sadiya ta amsa da amin ƙasa-ƙasa tana murmushi, Nudrat ta ja ta suka nufi wani ɗan corridor, ɗakin da suka shiga komai na cikinsa fari da green ne wannan ya ba Sadiya tabbacin ɗakin Nudrat ne, a iyakar zamansu tare ta kula tana ƙaunar tufafi da ma komai da ya danganci kalar kore. Ɗakin ya tsaru tsaf sai ƙamshi ke tashi. Nudrat ta nuna mata hanyar banɗaki ta shiga ta ɗauro alwala kafin ta fito ta mata shimfiɗar darduma hakan yasa tana zura hijabinta ta tayar da sallah. Ita kuwa dalilin ba ta da sallah ya sa ta rage kayan jikinta ta shige wanka. Can ta fito lokacin ma Sadiya har ta ninke abin sallah. Doguwar riga marar nauyi ta saka ta rufe kanta da hula, duk yadda ta so Sadiya ta watsa ruwa ko don rage zafin ranar da ake yi ta nuna sam ba za ta yi ba. Haka ta rabu da ita. Suka fito suka iske Nene ta sanya an zuba musu abinci, lokacin Muneeb ya bar falon sai Nene dake wayarta cikin harshen fulatanci wanda daga Nudrat har Sadiya suna ji sai dai ba su mayar da hankali ga tattaunawarta ba.
Sadiya duk jin ta take a takure don haka ma kaɗan ta ci lafiyayyar shinkafar da ta ji kaji da haɗi duk kuwa da daɗin da ta yi mata a baki. Tana ajiye cokalin Nudrat ta harare ta.
"Me kike son cewa? Ba dai kin ƙoshi ba?"
Kafin ta kai ga ba ta amsa wani sassanyan ƙamshi ya mamaye falon, sai ƙarar taku ƙwas ƙwas ƙwas da ya soma sauka a kunnuwansu, kafin wata murya mai surkin harshen Hausa ne, fillanci ko kuwa turanci, ba ma Sadiya ta tantance ba, ya yi dirar mikiya a kunnuwanta. Waya yake amsawa amma sai da ya fidda wayar a kunne ya yi musu sallama suka amsa ya ƙaraso, har lokacin kanta yana ƙasa ba ta juya ba. Shi kuwa zama ya yi a saman kujera ta ba shi baya. Nudrat ke kallonsa, har Sadiya ta soma ƙoƙarin miƙewa da zummar ta ƙoshi Nene ta dakatar da ita.
"A'a Sadiya me kika ci? Ba fa na son baƙuntar nan, ai an zama ɗaya duk gida ne nan ɗin. Zauna don Allah ki ci, ko kuma Nudrat tashi ku shige ɗaki za ta fi sakewa a can."
Sadiya ta buɗe baki za ta yi musu Nene ta hana ta, dole suka bi umarninta, ta kula Nudrat so take ta yi wa yayan nasu magana amma wannan doguwar wayar tasa ta sanya dole ta kwashi farantin ita kuwa Sadiya ta ɗauki ruwa da lemukan suka nufi ɗakinsu Nene na fadin Nudrat ta dawo ta tattara inda ta zubar tunda ita ba ta iya ci ba tare da ta yi ɓari ba.
Sadiya ko kallon wanda ke zaune ba ta yi ba, ta dai ji a jikinta wataƙila shi ne Yayan Nudrat da ta ke yawan zuzuta shi da koɗa shi idan ta ɗora hotonsa a whatsapp status, wato Hamma. Sunan kawai da ta san tana rubutawa a ƙasan hoton kenan, wataran ta ce My Hamma, wataran Hammanmu da dai sauransu.
"Na so kun gaisa da Hammana, amma bari mu gama sai mu je. Ina yawan ba sa labarinki, har tambayata yake ina Triple ɗita. Kusan fa duk sadda ya zo sai na ba shi labarinki."
Sadiya ta yi dariya.
"Na shiga uku, ke kowa sai ya san ni wai? Ni har kin sa na ji kunya ma."
Nudrat ta dara ita ma.
"Toh ai zumuncin kenan. Nawa su sanki, naki su san ni. Ni ma da na je gidanku ai tashi guda Inna ta faɗi sunana. Zahra ma ga shi kullum sai mun gaisa da ita ta whatsapp."
"To ban da gulmata dai."
Nudrat ta dara sannan ta kurɓi ruwan lemo a cikinta, mikewa ta yi ta shige bandaki ta wanko hannu ta fita tana fadin.
"Bari na je na tsaida shi kafin ma ya fice."
Sadiya dai da ido ta bi ta, ita ma ji ta yi ta ƙoshi hakan ya sa ta shiga tattara wajen da Nudrat ta ɓata, da gaskiyar Nene, ta kuka Nudrat idan ta ci abinci sai ta yi ɓarinsa, abu daya ne dai, matuƙar da yatsunta take ci ba cokali ba ta ga ba ta zubarwa a ƙasa. Kowa da irinsa dai. Tsincewa ta yi ta zari tissue dake ajiye a saman dirowar gado ta zuba a ciki. Ita ma hannun ta wanko, ta fito ta gyara zaman ɗaurinta da ya kunce tana kai duba ga agogon dake rataye a bangon ɗakin. Ƙarfe biyu da mintuna arba'in. Suna da sauran awa ɗaya da mintoci kenan. Ruwa ta dauka ta sha tana shirin ajiyewa sai ga Nudrat ta faɗo ɗakin da gudu-gudunta.
"Triple, taso muje ku gaisa da Hamma. Ya ce shi ma yau sai ya gan ki."
Sadiya ta ɗan fiddo idanu amma ba ta ce uffan ba dalilin magiyar Nudrat, a dole ta miƙe ta yafa mayafin da ta zo da shi saman doguwar rigar atamfar jikinta suka fito. Yana magana da Nene amma shigowarsu ya sanya shi maida hankali gare su. Da ido ya bi matashiyar da aka kira da Sadiya wato Triple S ɗin Nudrat. Ba laifi akwai dai kyau ga kuma alamu na nutsuwa tattare da ita. Ta gaishe shi cikin girmamawa ya amsa fuska a sake. Ita ma sai ta ga a fili ya fi kyau sosai fiye da hotuna, don kamar ma rage kyawunsa wayar ta yi.
"Kin ƙwace min Nudrat, ba ta da aiki sai hirarki. Yadda ta damu da ke ma yanzu ba ta wani damu da ni ba."
Sadiya ta yi murmushi.
"Ba haka ba ne."
Shi ma murmusawar ya yi, yana jin hatta da murmushinsa na ɗan burge shi.
"Ai shikenan. Ya karatu? Allah ya baku sa'a. Sai a ƙara mayar da hankali."
"In sha Allah. Amin. Mun gode Hamma."
Fadin Sadiya cikin girmamawa. Ya ƙara dubanta sai kuma ya kauda kai. Ɗakin suka koma suka bar shi da Mahaifiyarsa.
Tun shigar su ɗakin Nudrat ke ba ta labarin Hamma, wai shi ne na biyu a ɗakinsu bayan babbar yayarsu da ta rasu wato Yaya Maryam. Bai yi aure ba amma a cewarta a na dab da kai kuɗin aurensa. Sadiya ta yi masa fatan alheri. Nudrat tace sosai ya shaƙu da Yaya Maryam don ya fi su kusanci da ita sosaima, kuma akwai tazarar haihuwa tsakaninsu don sai da Nene ta haihu har sau biyu suna rasuwa sannan ta haifi Qassim, Muneeb, Nudrat sai Jafar. Yanzun Nudrat kaɗai ce mace a cikinsu wannan yasa suke ji da ita sosai.
Ƙarfe uku da rabi suka yi shirin komawa makaranta bayan sun duba karatunsu, Nene ta dakatar da su ta ce su fita tare da Hamma wanda zai yi Zoo road sai ya sauke su kafin ya wuce.
Nudrat hakan ya yi mata dadi idan ka cire Sadiya wacce har ƙirjinta ke bugu. Na farko ta biyo Nudrat ba da sanin Innarta ba, ga laifi na biyu kuma za ta shiga motar Yayanta. Tsoronta kar a je wani a gidansu ya gan ta, abinka da wacce irin hakan ba ta taɓa aikata shi ba. Idanunta ya yi ƙwal, ta ji kamar ta cewa Nene ta bar su su tafi amma kuma ba za ta iya ba. Haka ta zauna jiki a sanyaye har Hamma ya shigo Nene ta ce ya sauke su. Ya amsa da ok ya yi gaba ya ce su taho.
Ledar da Nene ta ba ta wanda ta karɓa daƙyar don har sai da Nene ta nuna ranta ya ɓaci sannan, ita take riƙe da shi a saman cinyarta sai ko jakarta na zuwa makaranta, tana son buɗewa ta sanya a cikin jakar amma kuma kunya take ji daga karɓar abu da zama a mota a ga tana cusa shi a jaka kamar me jira. Tana ji Hamma da Nudrat dake zaune a gefensa a mazaunin gaba suna ta kwasar hirarsu tana mitar ita ba ta so ya tafi Gombe saboda jimawar da yake yi a can. Ta ƙara da faɗin.
"Haka kawai don yana wani taƙama shi wai Prince ne sai ya dinga wani wahalarmin da Hammana. To ai mu ɗin ma Prince ka ke a wajenmu." Ta ƙarashe tana ɗan turo baki.
Hamma ya yi ƴar dariya.
"Ke daɗina da ke sai yawan rigima. Kamar ba ki san yadda muke da Maina ba. Kodayake zan ɗauke ki mu je wataran. Triple, ba kya magana kin yi shiru."
Ya ƙarashe yana kallon Sadiya ta madubi kasancewar daga bayan kujerarsa take a zaune. Ita ma aka ci sa'a ta ɗago ta kalle shi. Kauda kai ta yi tana ɗan murmushi. Nudrat ita ma ta juyo ta kalle ta.
"Nan fa da kake ganinta kamar a ce mata arr ta gudu haka take ji. Hamma za ka yi mamaki idan na ce maka a ruɗe take."
Sadiya ta ɗan fiddo idanu ta kalli Nudrat, irin kallon ya aka yi ki ka gane? Nudrat ta ɗan murguɗa mata baki.
"Eh mana, ki ce min ba haka ba."
"Ruɗewa kuma? Na me toh?" Ya ƙara faɗi da Hausarsa wacce ba ta nuna ba sosai.
"Faɗan Inna take tsoro tunda ta je gidan Dodanni mun cinye mata nama. Kuma Allah na sani sharrinta ne kawai, Inna ba za ta taɓa cewa wani abu idan ta san gidanmu ta je ba. Ita ce dai farar kura kawai."
Sadiya ta haɗe fuska tana hararar Nudrat dake dariya, a gefe guda kuma kunyar Hamma ta ji ya mamaye ta.
"A'a Jerryn Muneeb, Triple fa ta fi ki gaskiya. Duk wata ɗiya ta gari tana shakkar iyayenta, da kuma aikata abin da ta san zai zame musu abin magana. Wasu za ki ga daga irin wannan suke faɗawa wata hanyar ta daban. Wani bin a karɓi tayin saurayi zuwa shan ice-cream, ko kuma a raka ƙawaye, kinga mafarin ɓarna ya samu. So ban ga laifinta ba, hakan ma yana da kyau. Daga yanzu ma kar a ƙara biye-biye wani wuri ba tare da an sani a gida ba. Har ke nake nufi."
Ya furta yana duban Nudrat, ta amsa da toh sai dai a ganinta mene ne ciki don ita ko Sadiya sun je gidan ɗayansu? Ita ba ta ga wani abu ba.
Sadiya kuwa sosai ta ji Hamma ya burge ta yadda ya fahimce ta. Har cikin makarantar ya shigar da su ya nemi wuri ya tsaya.
"Toh yaran Nene, a maida hankali ga karatu. Iyakar karatun please, ban da shirme da shiririta."
"In sha Allah. Mun gode." Sadiya ta amshe, Nudrat ma ta bi sahu. Ya bi Sadiya da kallo har ta fice a motar kafin ya kauda kai gami da sauke ajiyar zuciya. Ba ya son gasƙata abin da zuciyarsa ke raya mishi game da ita. A iyakar saninsa so guda ɗaya ne, kuma Najma yake yi wa shi.
'Ita tana maka son da ka ke mata?' Wani ɓangare na zuciyarsa ya watsa mishi tambaya. Ya kawar da wannan tunanin ta hanyar jan guntun tsaki gami da dakatar da Nudrat, a aljihu ya fiddo dubu uku yace ta ba Sadiya. Ta kuwa washe haƙora tana godiya kafin ya ja mota ya yi gaba.
Sadiya baki sake ta ke kallon sabbin dubu ukun da Nudrat ta saka a tafin hannunta, ta yi saurin kai hannu za ta jawo ta don ta mayar amma Nudrat ta matsa da sauri.
"Aa Nudrat, ba zan karɓa ba."
Haka ta dinga magiya amma Nudrat ba ta ko kalleta ba. Ganin za ta ɓata mata lokaci kuma tana son gabatar da sallar la'asar kafin su shiga aji sai kawai ta zura a aljihun doguwar rigar atamfarta da zummar idan sun fito lakca za ta mayar mata. Amma har suka rabu Nudrat ba ta karɓa ba.
Inda Sadiya ta ji dadi yadda Inna ba ta mata faɗa ba sai dai cewa da ta yi ta dinga kula kuma ta riƙe kanta, ba ta son zaƙalƙalewa mutane musamman masu hannu da shuni haka. Malam ma ya abin da Nene ta bayar, ya kuma ji dadin yadda Sadiya da Innarta ba sa ɓoyewa mishi komai, ko babu komai zai ƙara sanin ɗiyarsa da mutanen da take mu'amalanta.
***
A kishingiɗe take a falonta, su uku ne zaune a cikinsa. Waleedah, Azeema sai ko ita Hajara cikon ta ukun. Gasassun kaji suke ci suna korawa da lemo ita kuwa tana aikin latsa wayarta. Sallamar ƴar aikinta wato Atine ce ya sa ta ɗago kai, Azeema suka amsa.
"Lafiya?" Hajara ta faɗi a zafafe tana kallonta don ba ta ga dalilin da za ta zo ba a neme ta ba. Matar ta zube jiki na rawa ta ce.
"Ki yi hakuri ranki ya daɗe. Dama Gwaggo Atine ce ta zo ta nemi alfarmar na ce tana so ku yi magana mai muhimmanci. Ta ce don Allah ki ba ta damar nan."
Hajara ta ja dogon tsaki. A fili ta ce.
"Wato matar nan na rufe ta daga kirana na kuma jaddada mata matuƙar ta sake sauya lambar wani ta kira ni sai na manta wace ce ita a wurina na zagi uwa da ubanta, shi ne ba ta daddara ba ta zo gidana?"
Ta yi ƙwafa mai ƙarfi sannan ta dubi Atine.
"Je ki ki ce ta ƙaraso. Yau zan mata wankin babban bargo!"
'A zumuntarku.' Cewar Atine a kasan ranta, a fili kuwa toh kawai ta amsa kafin ta miƙe tana ficewa zuwa falon ƙasa.
Ta iske Gwaggo Atine a zaune ta sha