Showing 84001 words to 87000 words out of 124441 words

Chapter 29 - Kazar Kwanci Hausa Novel Complete

uwata wannan alfarmar ne ki ka tsunduma kogin tunani haka?"

Sadiya da ta jijjiga ta da ma maganar da ta yi ya maido ta hayyacinta, ta sauke ajiyar zuciya tana kauda kanta don tuni ƙwalla sun cicciko mata. Ta waske da fadin.

"Toh ba ga shi nan yanzun har zuwa duba jikinta na yi ba? A sannu komai zai zama tarihi fa. Bari na je akwai sauran wuraren da zamu je. Sai mun haɗu."

Sadiya ta gyaɗa mata kai tana murmushin da bai kai zuci ba. Jikinta kuma ya yi sanyi, tausayin Husna ta ke ji sosai. Ta dai bi Meenat da fatan alheri ta koma cikin gida zuciyarta ta yi mata wani nauyi.

***
Ranar da Husna ta fara ganin Hamman Sadiya suka gaisa kusan kwana ta yi tana yi wa Sadiyar santi. Fadi take.

"Kai sis, na rantse kun haɗu. Kamar fa na ɗauke ku na gudu tsabar kyau da matching da na ga kun min. Allah ya sanya alheri ya nuna mana auren nan."

Sadiya ta yi dariya kawai.

Satin Husna biyu a gidan ta soma naƙuda kuwa, an ci sa'a dai kafin haihuwar Huzaif ya zo har sau biyu, hankalinta ita ma ya kwanta. Lokacin da naƙudar ta taso ita Sadiya ma ta a makaranta sai Inna a gidan da Mama Iyabo makwafciyarsu da ta shigo. Ita ce ma ta fahimci Husna naƙuda ta ke. Nan suka nufi asibiti, cikin iko na Allah kuma bai zo da gardama ba, ba ta ɗauki dogon lokaci ba ta sauka lafiya ta haifi ɗanta namiji mai kama da babansa kamar an yi kaki sai dai kalar fatarta ce. Huzaif tun sadda Malam ya kira shi ya shaida masa suna asibiti ya zo. Haka ma Mami tana nan sai cika da batsewa ta ke, sama-sama suka gaisa da Inna da ba ta san dawar garin ba.

Sosai ɗan ya shiga ran Mami sai ta ga kamar Huzaif dinta yana yaro, bayan ya mishi addua a karɓe shi ta riƙe. Inna ta kula Mami ta ɗan kawai ta ke yi don sau daya da ta kalli Husna ta yi mata sannu ba ta ƙara bi ta kanta ba. To haka ma Huzaif din.

Mama Iyabo ce ta taimaka wajen gyara Husna, can ba jimawa Mamin ta wuce, Huzaif kuwa sai da ya tambaya ko akwai abin da ake buƙata. Inna ta ce a'a, ya karasa wurin ma'aikatan asibitin ya biya dukkan abin da ya dace sannan ya wuce da zummar sai anjima.

Tafiyarsa ba jimawa Hajara ta dira a asibitin. Bakinta ya ƙi rufuwa, sai waya take tana sanar da mutanenta haihuwar ƙanwarta Husna. Sosai ake taya ta murna sanin yadda suke da Husnar.

Husna ba ta jima ba aka sallame su tunda komai lafiya lau.

Haka aka dinga zuwa barka kusan kullum sai sun karɓi baƙi. Dangin Huzaif da ma ƙawayen Hajara don ta rantse a abokanta duk wacce ba ta zo mata barka da sunan ɗan Husna ba to fa babu ita babu shi.

Haka su Sadiya suka dinga ganin manyan masu hannu da shuni da ta ke mu'amala da su suna zuwa da sha tara na arziki. Nudrat ma sadda ta zo duk kallon da Hajara ke mata sai da ta ji ta burge ta saboda kayayyakin da ta jibgowa jariri ta kawo. Wai sai ga Hajara da Nudrat na hira da dariya. Abin ya ɗaurewa Sadiya kai. Amma kuma da ta tuna girman so da kaunar da ta ke yi wa Husna wanda ya shafi jaririn da ta haifa yanzu, sai ta bar mamakin.

Ita ce dai ko ɗaukarsa ta yi Hajara sai ta ci gyaranta wai ba ta san ya ake riƙe yaro ba ta bar wuyansa na tangal-tangal. Abin kan mata ciwo har ta gaji ta bar ɗaukar yaron sai idan Hajara ba ta kusa.

Ba ta ma da masaniyar zuwan da iyayen Hamma za su yi batun neman aure ya kama ranar sunan Husna wacce Hajara takanas ta kama Hall za'a yi shagali a can, sai a na gobe sunan Hamma ke sanar da ita. Ta so a bari bayan suna amma kuma ba ta ga hujjar da za ta musa ba tunda suna ai sabga ce ta mata.

***
"Ayyiririi! Kai masha Allah Alhamdulillah. Ku ce min ɗiyata ta yi goshi. Allah ya kaimu da rai da lafiya. Watanni uku ai kamar yau ne."

Abin da ya shiga kunnuwan Hajara da Husna kenan waɗanda sanyo ƙafarsu gidan ko tsakar gida ba su kai ga ƙarasowa ba suka tsinci muryar wata a dangin Malam da suke kira Umman Rabe tana wannan kalami.

Dama fita suka yi kwalliya aikuwa Husna ba karamin kyau ta yi ba ta fito sharr dama an mata ƙunshi da gyara gashi. Hajara ke riƙe da yaron da ya ci sunan mahaifin Huzaif wato Abubakar ake kiransa Sadik.

"Wai har an kawo kuɗin?" Tambayar Husna ta sa Hajara saurin kallonta, kenan ita ma ta san sha'anin da ake yi? Ita kadai ce ba ta sani ba?

"An kawo Amaryar ƙarni, Sadiya ta yi goshi har dubu dari uku cas kudin aurenta. Nan da wata uku za ta zama rabon AbdulMajid."

Hajara ji ta yi kamar an buga mata guduma a tsakar kai, auren Sadiya? AbdulMajid? Waye kuma AbdulMajid? Yaushe duk hakan ta faru ba ta da labari?

'Ki daure, ki danne ki ɓoye abin da ke ranki kar a ankara da ke.'

Wani ɓangare na zuciyarta ya yi mata tuni. Don haka daƙyar ta iya yin murmushin yaƙe.

"Masha Allah, na taya ta murna. Mu je Husna ki sauya kaya mu tafi lokaci na ƙurewa."

Ta fadi ne tana sauri ta shigewa ɗaka, ita ta mance ma Husna tun a wurin kwalliyar ta saka kayanta. Da ace mutanen wurin sun kula da furucinta ma da kuma yanayinta za a gane a firgice ta ke. Gwaggo Atine tsaf ta karanci abar ta, ita ma baƙin cikin ne ya sa ta kasa kataɓus don jin labarin ta yi bagatatan. Ta tsome hannunta daga kwanon dambun da suke ci ta miƙe. Kamar ta bi bayan Hajara amma kuma ta fasa gudun zargi da ƴan tsurku.

Dama sunan kashi biyu ne, da wanda Inna suka yi a gida sai ko wanda Hajara ta hada za a fita wanda tun kafin lokacin ta sanar ba kowa zai je ba sai wanda aka ba kati. Sadiya dai ba ta saka a ka ba amma kuma katinta da na Nudrat yana wajenta Husna ta ba ta. Dolenta kuma ta je tunda ba ta da hujjar cewa a'a.

Taron ranar duka bai yiwa Hajara daɗi ba. Ko fara'a ta ke yi sai ta ji muryar Umman Rabe na amsa-kuwwa a kunnuwanta tana shelar kawo kudin auren Sadiya da aka yi. Hakan na nufin aikin da aka yi bai ci Sadiya ba ko kuwa ya ya? Tana da buƙatar komawa Bokanta don jin inda aka haihu a ragaya. Ta ya ya tufkarta ke warwarewa?

Amsar na wurinsa.

A ɓangaren Sadiya kuwa farin cikinta ba ya misaltuwa, mamakinta yadda har Mamin Huzaif sai da ta taya ta murna. Matar da tun auren Husna da Huzaif din ta bar shiga sabgarta kamar dama can ba ƙaunarta ta ke yi ba. Ita dai ta san Mamin ba ta da alƙibla sam. Ba ta ɓoye son abin da yaranta ke so, haka ma ƙiyayyar abin da suka nuna ba sa so. Komai ta ya su take yi.

***

Ya kauda kai yana wani murmushi na yaƙe. A ransa faɗi ya ke.

'Wannan hatsabibiyar ba dai za ta haƙura ta bar yarinya haka ba.'

A fili kuwa sai ya haɗiyi miyau kafin ya ce.

"To ban da abin ki Hajara, hangen dala ai ba shiga birni ne ba. Kawo kuɗi ba ya nufin auren ai, na fa san dama za'a yi haka. Kuma abin ba zai je ko'ina ba. Ke dai ba na ba ki tabbacin har abada ba za ta yi aure ba? Toh ki kwantar da hankalinki ki saki ranki. Ko a fuska ki dinga dauriya kar ki nuna musu baƙin cikinki, ki shiga ko me za'a yi a yi shi tare da ke. Ke dai ki dinga ban haɗin kai, komai zai zama sai yadda ki ka ce. Hatta da uwarta sai kin juya ta kamar waina a tanda."

Hajara jin haka ta sauke ajiyar zuciya, ji ta yi har hankalinta ya kwanta. Nan kuma ya nemi su je ɗaki karo na biyu, ba ta yi musu ba don ba ta san ma meke jan ta gare sa ba. Haka suka sheƙe ayarsu son rai kafin ta kimtsa ta bar gidan. Ya bi ta da kallo yana dariyar mugunta, a fili ya ce.

"Aure kam sai yarinyar nan ta yi shi, ko mutuwa za ki yi sai dai ki mutu. Shashasha, ni da ke mutu-ka-raba kuma takalmin kaza."

***
Kwanaki biyu ya yi saura a fita daga watan da suke ciki, Hajara ta gama tabbatarwa wannan karon dagaske tana dauke da juna biyu saboda ta ga alamomi da yawa matsayinta na Nos ta kuma fahimta. Farin ciki kamar ta yi me, wannan ne ma ya mantar da ita wasu damuwoyin, kasa hakuri ta yi sai da ta sanar da Alh Nuhu ta waya. Wata dariya ya kyakyata na jin dadi da farin ciki. Ya tabbatar mata zai sauya mata mota da waya saboda kyakkyawan albishirin da ta yi masa. Kanta ya fasu sosai.

Ba ta damu da sanin ko cikin waye ba, ta dai sani ga Yusha'u saurayin da ta kwana da shi, ga kuma Bokanta ga kuma shi mijin nata. Ita ko ma na waye muddin dai za ta haihu ai shikenan kwalliya ta biya kuɗin sabulu. Ai an yi mai wuyar. Ko me zai biyo baya dai ba zai sauyawa tuwo suna ba tunda kowa ya sani ba a shege a gidan miji.

Ba ta san haka Alh Nuhu ke son haihuwa ba sai yanzu don har Gwaggo mahaifiyarsa da kannensa sai da aka zo wai duba jikinta ya ce ba ta jin dadi. Ita kuwa sai kara tanƙwashe murya ta ke, a dole tana jin jikin laulayi. Gwaggo ta so bar mata bazawarar ɗiyarta ta zauna amma ta nuna babu komai ai ta ji sauƙi don ba ta buƙatar wata takura.

Can ɓangaren su Hafsatu ba kowa ya taya ta murna da fatan sauka lafiya.

***
Sadiya ce tafe a barandar da zai sada ta da ɗakunan jinya na mata dake asibitin Malam bayan ta amsa wayar Nudrat ta sanar da ita suna can. Tafiya ta ke cikin nutsuwa tana shaƙar iskar da ke kaɗawa na hadari da ya haɗu a garin. Murmushi ɗauke saman fuskarta tana hasko ta tare da Hamma a zaune gaban tafkeken ruwa suna shan iska da hirar masoya.

"Sadiya."

Ta tsinci muryar kamar a mafarki a gefenta, ta juyo ta dube shi. Yana sanye cikin riga da wando ya dora farin coat na likitoci a sama. Ya rame amma kuma fatarsa ba ta wani sauya ba. Ta kauda kai kamar babu wani abu da ya taɓa giftawa tsakaninsu wai soyayya ta ce.

"Lah Yaya Huzaif ina kwana. Dama a nan ka ke?"

Huzaif wanda ya ji bakinsa ya ɗan mishi nauyi, jikinsa kuma gaba daya ya mutu. Sadiyar ce ta ƙara kyau ta kuma cicciko amma ba ta yi ƙiba ba, sai dai hatta da tafiyarta ta isa fisgar hankali. Idan ka gan ta sai ka ɗauka ɗiyar wani ko wata ce a ƙasar nan tsabar aji da ma kyawun fata. Har gobe yana sonta yana kaunarta, har goben kuma ya rasa dalilinsa na karkata aƙalar so da ƙaunar zuwa ga Husna. Wacce bai dauke ta komai a baya ba face ƙanwarsa. Ajiyar zuciya ya sauke ganin har ta soma shirin cigaba da tafiya ya katse hanzarinta da sauri.

"A nan nake, kwanaki ai na ganki a can wurin Emergency, kafin kuma na yi maki magana na neme ki na rasa. Ya karatun? Fatan komai na tafiya daidai?"

Sadiya ta murmusa.

"Ayya, ban kula ba ai da na maka magana. Alhamdulillah."

"Allah ya taimaka."

Ta kauda kai tana duban agogon da ke ɗaure a tsintsiyar hannunta lokaci guda tana amsawa da amin. Ya kula ta ƙagu su rabu don haka ya yi mata sallama aikuwa ba ta jira komai ba ta cigaba da tafiyarta. Huzaif ya ɗan bi ta da kallo, ta mishi kyau ainun cikin doguwar rigar leshinta ruwan madara sai Lab coat da ta dora a sama, ta zagaye kanta da mayafi madaidaici, sai ko ƴar jakar da ke rataye a kafaɗarta. Sassanyan ƙamshi ta ke yi mai haifar da nutsuwa.

Ya juya ya cigaba da tafiya gwuiwarsa a sake. Wallahi ya yi rashi, rashin da har abada ba zai bar jin ciwonsa ba. Ya kara jin tsana da haushin Husna sosai, amma kuma yanzun tana cin darajar Sadik, yaron ya ɗora wa son duniya.  Ya ji ina ma a na maido hannun agogo baya.  Da ya gyara ɓarnar da ya tafka, amma kuma ina! Bakin alƙalami ya riga da ya bushe.

Ji ya yi idanunsa sun kaɗa, kwalla suka cicciko masa, dalili kenan da ya fiddo baƙin gilashinsa ya manna fuskarnan kamar bakin hadari saboda yadda take a murtuke.

***
A hankali rayuwar tana gangarawa, lamura a ɓangaren Sadiya da Hamma sai abin da ya ƙaru. Soyayya ce mai tsafta ke gudana, tun ba a je ko'ina ba ta fahimci nata son ya fi na sa yawa amma kuma iyakar yin ta da kokarinta ta na yi wajen dannewa da ƙin nuna masa natan a fili. Idan a wuni bai kira ba ya ba ta uzuri, takan danne maitarta na son jin muryarsa ta yi ta harkokinta kamar babu komai.

Haka har Husna ta yi kwanaki talatin da takwas cif, a sannan an yi bikin Meenat har ta tare a gidanta. Gyara sosai Inna ta yi wa Husna, ga Hajara da ke kawo mata wasu tsadaddun kayayyakin gyara na mata. Amma duka wannan buduri da ake a ɓangaren Husna ba ta wani rawar ƙafa face ma fargaba tsantsa. Ba ta san kalar zaman da za su yi da Huzaif ba wanda ya gama chanza mata.

Ana gobe za ta tafi haka ta zauna tana kuka, Sadiya da ke jin ta ta gaji, ta ji ba kuma za ta iya shanye damuwar Husnar ba ba tare da ta yi mata magana ba don haka ta mike zaune, a gaggauce Husna ta hau share fuska don dama akwai hasken wayar da ta kunna, Sadik ke  kuka ta tashi shayar da shi har ma ya koma bacci sai uta a zaune.

"Husna wai me ke damunki ne?"

Husna ta dubi Sadiyar wacce ita ma idanunta ke kanta fuskarnan cike da matsanancin damuwa, ajiyar zuciya ta sauke. Ba za ta iya fitowa ta faɗa mata komai da komai ba, amma za ta gutsuro mata kaɗan daga cikin matsalarta da Huzaif.

"Ban san me na mishi ba Sis, ya sauya min gaba ɗaya. Kira da zuwa inda na ke sai ya ga dama. Haka ma Maminsa, yanzu duk sadda za mu haɗu daure fuska ta ke yi, ba ma hira kamar a baya. Na rasa ina zan saka kaina na ji dadi. Damuwar ta yi min yawa. Tsoro da fargabar da na ke ciki yanzu bai wuce rayuwar da zamu yi da shi ba idan na koma. Na tambaye shi ko akwai abin da na masa ya ce min babu. To ina zan saka raina?"

Ta ƙarashe da muryar kuka. Tausayinta sosai ya ƙara ninka na farko a zuciyar Sadiya. Ta kamo hannunta gami da girgiza mata kai.

"Ki daina kuka, wa ya faɗa maki kukan ne zai magance maki matsalolinki? Kin tabbata kuma babu wani abu da ki ka yi mishi ko Maminsa?"

"Na rantse maki babu shi Sis. Mami kullum burina na kyautata mata, yabona ta ke sosai a baya kafin wannan sabon sauyin. Dama Meenat ce ba ma shiri amma kaf sauran yan uwansa su na shiga sabgata ina shiga na su. Sis dole na shiga tashin hankali, na rantse maki ina son Yaya Huzaif sosai."

Ta sauke ajiyar zuciya.

"To sai ki miƙa dukkan lamuranki ga Allah. Babu fa wanda zai maka maganin komai a duniyarnan Husna sai Allahn da ya halicce mu. Duk wani mai imani da shi ya dogara. Sallolin nafila musamman na dare, karatun Alkur'ani mai girma, azkar safe da yamma, yawan addu'a. Na rantse da Allah sun isa su yi maki maganin matsalar nan. Kuma ki dage da kwantar da kai da biyayya da kiyaye ɓacin ransa. Babu matakin da ba za ki iya kai wa ba muddin ki ka yi hakuri. Ki fawwalawa Allah komai, Husna babu wani mai tsibbun da zai iya magance maki kowace matsala face Allahn da ya halicce ki. Kin ji ko?"

A ɓangaren Sadiya ta yi amfani da zancen da ta ji Hajara na mata da yammaci da ta zo gidan, tana dab da shigowa ɗakin ta ji Hajara na ɗura ashar tana cewa ta kwantar da hankalinta za ta kai wa wani hatsabibin malaminta kuɗi ya ƙara yi mata sabon aiki a kan Huzaif din. Hankalinta sosai ya tashi da jin haka, har Inna ta faɗawa saboda tsoro, Inna ita ma kanta ta tsorata amma ta ce kar ta damu da yardar Allah za ta yi wa Husnar nasiha a faƙaice, ita ma kuma ta dage da taya ƴar uwarta a addu'a.

Ita kuwa Husna, sai da cikinta ya ɗuri ruwa jin abin da Sadiya ta ce, ko dai ta ji hirarsu da Anti Hajara? Ta ƙara tsinkayar muryar Sadiya karo na ba uku.

"Wallahi kin ji na maki rantsuwa da Allah ɗaya, dukkan wani aiki da za ka haɗa da wanin Allah don ya biyamaka buƙata ɓata ce zallarta. Kuma biyan buƙatar zai kasance na ɗan lokaci, da zarar alkadarin ya karye, komai kan iya sauyawa. Idan na ce komai to fa ina nufin ko mene ne da ma zurfin da aka yi don cimma manufa. Lokaci bai ƙure maki ba, Allah mai ƙarbar tuba ne, ki roƙe shi yafiya ki kuma miƙa lamuranki gare sa. Za ki yi mamaki wataran idan kin wayi gari soyayyarki mai tsafta ta wanzu a zuciyar mijinki. Amma fa sai kin yi hakuri kin kuma daurewa dukkanin ƙalubalen da za ki fuskanta tunda ki na kaunarsa. Kin ji ko?"

Cike da tsananin kunya Husna ta gyaɗa kai, ta ma kasa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login