Showing 120001 words to 123000 words out of 124441 words
ce ita ke gyara ɓangarensa da kanta?"
Jidda ta ƙara ƙasa da kanta a ladabce ta ce.
"Hakane ranki ya daɗe."
"Makira! Wato ita bariki za ta gwada mana. Hum!"
Shiru ya mamaye ɗakin, ita dai Jidda ƙirjinta sai lugude ya ke yi, ta san duk ranar da ba ta yi wa Fulani ba daidai ba kashinta ya bushe don ta rantse idan ta same ta da cin amanarta sai ta kashe ta kuma ta kashe banza tunda ita dai marainiya ce gaba da baya.
"Shikenan, ki cigaba da aikinki, ki kula da duk wani motsinta. Na tabbata sai mun kama ta da wani laifin mai muni."
"An gama ranki ya daɗe. Zan bi umarninki zan kuma yi yadda ki ka ce."
Fulani fuskarta a ɗaure ta mata alama da ta tashi ta bar wajen. Sailuba dake gefe ta dubi Jidda.
"Tashi ki je an sallame ki."
Jiki na rawa Jidda ta miƙe bayan ta zuba uban godiya kai ka ce kyautar wani zinaren aka yi mata.
"Sailuba."
"Na'am Fulanin Mai Martaba." Ta faɗi sunan da Fulani ta fi kaunar a kira ta da shi.
"A cigaba da lura da takun yarinyar nan, kar ta kusa ta raɓi wasu bayin."
"Ina kan yi zan kuma ƙara zage damtse. Ba za'a samu wata matsala ba."
Fulani ta jinjina kai tana ɗan murmushi. Tana ji a jikinta Sadiya ba matar arziƙi ba ce musamman da ba ta kasance jinin sarauta ba. Jikinta yana ba ta ma za ta yi kokarin mallake Maina don haka za ta zuba idanu ta ga gudun ruwanta zuwa lokacin da zai auri zaɓinta.
***
Duk yadda ta so ta yi wa Maina ɓoyo saboda kunyar da ta ke ji idan ta tuna yadda ta kasance tsakaninsu hakan ya faskara saboda dole a daren ta kai masa abinci. Inda dai ta ji daɗi bai nuna wani abu ko a fuska ba sai dai yawan satar kallonta da yake ɗan yi jifa-jifa. Daƙyar ta iya cin lomar tuwo biyar saboda jin ta da take a takure.
"Ki ƙara." Abin da ya furta kenan daga haka ya maida hankali ga cin nashi tuwon semovita miyar kuka da ya ji manshanu da nama. Ba ta yi musu ba ta ɗan ƙara sannan ta ƙara yunƙurin bari.
"Ƙara." Ya ƙara nanatawa, ta yi narai-narai da fuska, cikin muryar shagwaɓar da ya zo mata ba da niyya ba ta ce.
"Allah kuwa na ƙoshi."
Sai da ya ɗan kalle ta, sai ta ji kunya ta sunkuyar da kai tana tunasar da kanta ba a gaban Innarta take ba. Ita ke matsawa sai ta ci abinci sosai wai kullum cikin a shafe kamar ba a sanya abinci a ciki. Shi kuwa sai da ya ji kamar ba ita ba, muryar ta ƙara yi mishi zaƙi a kunne. Yau kawai ya ji so yake su yi hira su ƙara fahimtar junansu, don haka koda shi ma ya kammala ya ga ta soma tattara wurin da zummar sauka ƙasa sai ya ce.
"Idan kin kai ki zo, zamu yi magana."
Ta ɗan kalle shi kafin ta amsa da toh. Tana saukowa ta ji shiru dama kuma ta san hakan ne zai kasance tunda sun yi sallama da su Bintu. Sai dai ganin Jidda zaune ya yi masifar ɗaure mata kai. Ita ma tana ganinta ta ɗan firgita, gaba ɗaya sai ta ji ta rasa na cewa saboda ba ta da hujjar zama alhalin dama ana yin sallar isha'i Sadiyar ke cewa su tafi.
"Jidda, lafiya ba ki tafi ba?" Ta tambaya tana ɗan kula da yanayin yarinyar, dama kusan kullum idan ka gan ta kamar a firgice ma ta ke. Tun sadda ta zo kawai ba ta kwanta mata ba, babu ma kamar idan ta tuna labarin da su Dada da Anti Safiyya suka dinga yi kan tsaface-tsafacen wasu a gidan sarauta, kuma an gargaɗe ta a kan saurin yarda da mutane, su Bintu ma ta san irin hirar da take yi da su idan sun zauna balle kuma wacce ta fito daga ɓangaren surukarta da aka shaida ba ta yi marhaba da ita ba.
Jidda ganin kwandon da ke riƙe a hannun Sadiya ta yi saurin sunkuyar da kai a ladabce ta ce.
"Dama na ɗauka za'a wanke kwanukan ne Anti. Shi ne na dakata."
Girgiza kai Sadiya ta yi kafin ta ce.
"A'a ki bar shi ba buƙatar ki yi hakan, zan yi da kaina. Ki je kawai sai da safe. Nagode."
Jidda har gumi ya tsastsafo a goshinta kamar ba fanka a falon. Ta yi mata sallama ta fice ta ja ƙofar. Tsaye ta yi a bakin barandar shiga wurin tana ta tunani, haka za ta tafi ba tare da ta kai wa waccan muguwar Sailubar gamsasshiyar amsa na inda Sadiya ke kwana? An ce ta saka idanu ko idan ta kammala ba Maina abinci shikenan ba ta komawa saman, amma kuma babu damar hakan tunda ba ta da hujjar zama alhalin matar gidan ta sallame ta. Ta fasa tafiyar don haka ta juya bayan ta kula babu idanun maza masu aikace-aikace a gidan, kai tsaye baya ta zagaya daidai wata barandar da aka ajiye shukoki a cikin tukwane guda biyu hagu da dama, sai ko dogon window da ke a rufe wanda akan iya buɗe shi a sha iska, Allah ya taimaketa labulen dake wurin shara-shara ne, duk da hanyar hawa benen ya yi lungu, amma kuma ƙofar kicin da ma na ɗakin Sadiya tarr ta ke iya hango su.
***
Sadiya kuwa ƙarasawa ta yi kicin ta ajiye kayayyakin, a gaggauce ta juye abincin a kwanukan plastics ta sanya a firij sannan ta wanke komai ta kife su ta rufe. Har ta kashe fitilar kicin ta rufo ta nufi bene, sai ta dawo ta koma falon farko ta rufe ta kashe fitilun haka nan ƙofa ta biyu.
A kan idanun Jidda ta yi hanyar da zai sada ta da benen ɓangaren Maina, ganin har fitilun falon ta kashe su kafin ta hau ya sa kawai Jidda ta kawo a can ɗin za ta kwana. Don haka ta sulale ta fice, ko babu komai tana ɗauke da labari duk da ba mai daɗi ne a wurin waɗanda za ta kai wa ba, amma ita me ruwanta tunda ta cika umarninsu na ranar.
***
Ita kuwa Sadiya ta iske ba ya falon don haka ta nemi wuri ta zauna tana bin wayarsa da saƙo ya shigo da ido. Saman screen ɗin hotonsa ne sanye da kayansu na sarakai a saman doki, ya sanya baƙin gilashi da ya fiddo hasken fatarsa da kuma kyawunsa tsantsa. Ta kasa kauda idanu daga kallon hoton don sai ta ga kamar wani ado da ya shafi gidan sarauta bai taɓa yi wa wani kyau kamar Maina ba. Can kuma hasken ya ɗauke, ta sauke ajiyar zuciya ta na mai ɗan waigawa ta ga ko ya fito ma ya kama tana kalle shi, ganin babu kowa ya sa ta gyara zama ta nutsu. Can ya fito, ƙamshin turarukansa ta soma shaƙa kafin ya ƙaraso ya zauna, jallabiya ce fara ƙal a jikinsa irin mai santsin nan, hakan ya sa ta kwanta ta fiddo ainahin cikar halittar ƙirjinsa da ma tsawonsa mai tafiyar da hankulan mata da dama musamman ma'abota kallon haramun wato na ƙurilla.
Sadda kanta ƙasa ta yi da sauri tana wasa da yatsun hannunta.
"Afuwan, na bar ki ki na jira."
Ya ƙarashe da kai hannu ya ɗau wayarsa, sai da ya duba saƙonnin da suka faɗo kafin ya sanya ta a silent mode ya zauna fuskanci Sadiya sosai, cikin muryarsa ƙasa-ƙasa ya soma magana.
"Ba wani dogon zance ba ne, tafiya zan yi end of this week, on Sunday kenan in sha Allah. Zan iya yin wata guda kafin na dawo. Kar ki ga kamar na sanar da ke a ƙurarren lokaci, matso da tafiyar na yi dalilin ayyukan da nake da su masu muhimmanci a can."
Shiru ya ɗan biyo baya yana dubanta amma bai iya ganin yanayin fuskar sosai ba kasancewar ta yi ƙasa da kanta. A ɓangaren Sadiya kuwa, ta lissafa ƙarshen satin ta ga ai jibi kenan ma zai wuce, ba ta san dalili ba sai hakan bai mata daɗi ba. Kuma har tsawon sati huɗu? Ita wa ta sani a duniyar masarautarnan ta su bayan shi ɗin? Maganarsa ta katse tunaninta.
"Dalilin sanar da ke, idan an cire haƙƙoƙinki da ke rataye a wuyana, sai don na ɗan nusar da ke wani abu. Zan iya kiranki da baƙuwa a masarautarnan saboda ba ki san komai dangane da ita ba. Don haka please ba na son kowa ki ja shi a jiki, ina so ki kiyaye duk wanda za ki mu'amalanta. Sannan ba na son fita, komai da ki ke buƙata ki yi list ki ban zan sa a kawo maki. Fitarki koda za ki yi kar ya wuce idan an kwana biyu ki na iya shiga ki gaida su Mai babban ɗaki da mutan gida. Sai kuma..."
Ya ɗan yi shiru yana sauke numfashi gami da shafa sumar kansa lokaci guda yana ɗan lumshe idanunsa kafin ya ce.
"Surutu, ba na son surutu. Ba ki yi kama da mai buɗe sirrin mijinta ba, so please ki kiyaye. Na shiga ɗakinki ko ban shiga ba, wannan ya kasance tsakaninmu kin ji?"
Ya ƙarashe da wata murya mai nuni da kewa da ma abubuwa marass ƙidayuwa da suka girmi fassarar kwakwalwarsa.
Sadiya wacce ta kauda kai daga duban da ta ɗan ɗago a farko tana mishi, ta gyaɗa kai cike da jin nauyi. Bakinta da ya yi nauyi daƙyar ta yi ɗan gyaran murya yadda zai fita sosai maganarta ta ce.
"Zan kiyaye dukkan abin da ka ce. Ina roƙon Allah ya ba da nasarar abin da za'a je nema, ya kuma tsare ya dawo da kai lafiya."
Maina da ke dubanta, ya amsa da amin. Shirun da ta ji ya sa ta gane ya gama magana don haka a sanyaye ta ce.
"Zan je na kwanta, Allah ya tashe mu lafiya."
Daga nan ta miƙe.
"Ɗakin Maina fa? Ba wuri ne da za ki iya miƙe ƙafa ki kwanta ba?"
Ta juyo da sauri ta dube shi, shi ma lumsassun idanunsa suna kanta don haka da saurin ta ƙara kauda kai, sai gaba ɗaya ta daburce, wai Maina? Shi dsi ya ke so ta dawo nan da kwana? Ta ma rasa me za ta ce.
"Idan har babu matsala, daga yanzu ba na son kwananki ke ɗaya a ƙasa kamar aljana. Gidan akwai faɗi, kuma ke amanar Mai Martaba ce." Ya ƙarashe da murmushin da ko ba ta kalle shi ba ta ji ɗan sautinsa.
"Toh, zan je na dawo."
Ta furta a hankali. Ta dai ji kamar ya amsa ko bai amsa ba, ita dai gaba ta yi. Ba ta samu damar jan numfashi mai kyau da furzarwa ba sai da ta sauka daga benen. A ɗakinta kuwa gefen gadon ta nemi wuri ta zauna tana cigaba da sauke ajiyar zuciya a kai a kai, ta dafe ƙirjinta da ke lugude. Tunani take yi ta je ko kuwa ta basar da shi ta yi kwanciyarta a nan? Daƙyar dai ta miƙe ta faɗa wanka ba don da yamma ba ta yi ba sai don tana gudun duk da ƙamshin da ke fita a jikinta kar kwanciya a gadon Maina ya sa ya ji wani wuri na tashi a jikinta. Ta san dai ba ya sonta don haka tana ji ba zai taɓa ta ba. Koda ta fito bayan shafe jikinta da turaruka iri-iri masu daɗi da sanyin ƙamshi, ta ɗauki rigarta mai kauri na bacci doguwa ta zura. Ta rufe kanta da hula. Sai kuma ta kasa fita a ɗakin tana tunani, kada fa ta bayar da kanta, daga kira kawai ace har ta tafi kamar jira take?
'Mijinki ne, ba ke kika nemi zuwa makwancinsa ba, shi ya nemi wannan alfamar, duk kuma abin da za ki yi ki tuna cewa sama yake da ke.' Wani sashi na zuciyarta ya tunasar da ita. Ta kuwa miƙe ta ɗauki wayarta ta kashe fitilu ta rufe ɗakin sannan ta koma saman. Yana falon zaune, ga dukkan alamu ita yake jira don haka tana zuwa ta ga ya miƙe ya nufi inda fitilun suke ya rage ya bar guda ɗaya marar haske sosai.
"Bismillah." Ya furta a hankali, ba musu ta bi hanyar ɗakin da ya nuna ta yi gaba, ta kai duba da gadon, wani mulmulalle da shi wanda duk sadda ta zo gyarawa burge ta yake yi. Ta tuna sadda ta gwada kwanciya a kai, yau ga shi nan za ta yi kwanan ƴanci, irin wanda nema aka yi da ka zo.
Haka suka kwanta kuma suka wayi gari ba tare da wani abu ya gifta tsakani ba, sai dai ga dukkansu, bacci ɓarawo ne ya sace su kawai. Kowannensu na jin baƙon lamari a jikinsa, sun saba kwana su ɗaya, yau kuma abin ya zame musu banbarakwai babu ma kamar Sadiya da gaba ɗaya ta takure jikinta. Da asubahi dai ta farka ne ta ga kanta a ƙirjin Maina, inda ta godewa Allah kuma ta riga shi miƙewa gaba ɗaya sai ta ji nauyin hakan. Ita fa dagaske takura mata zai yi ma idan ya matsa ta dawo kwana wajensa don jiyan ma daƙyar baccin ya ɗauke ta. Ƙarar alarm ɗin wayoyinsu lokaci guda ne ya farkar da Maina, ita kuma ta yi saurin kai hannu ta waske da ɗaukar wayarta tana kashewa. Maina da bacci ke cin idanunsa daƙyar ya riga ta miƙewa ya nufi banɗaki don kama ruwa da ɗauro alwala. A irin lokutan nan idan ya ji ya kasa tashi saboda bacci, yakan ji wani ɓangare na zuciyarsa na nusar da shi, mene ne ribar baccin da ba za'a tashi a bautawa Mahalicci ba? Wannan ke zaburar da shi koyaushe har ya yakice baccin ya miƙe.
Ita kuwa fita ta yi zuwa ɗayan ɗakin nasa ta shiga banɗakin, koda ta dawo tuni ya fice zuwa masallaci don haka itama ta yi nafila kafin ta gabatar da sallah. Niyyarta ta zauna kamar koyaushe yin Azkar har sai rana ta fito, amma a zaunen ma ji ta yi gyangyaɗi na kama ta har tana mance me take karantawa dole ta sallame da zummar ta yi anjima ta koma bacci.
***
Washegari ya ce ta shirya su shiga ta gaida su Fulani. Ta shirya kuwa tsaf cikin leshinta swiss light pink colour mai ratsin silver ya sha adon stones wanda da shi ya zo. Ta yafa mayafinta silver sai ko takalminta flat. Ta yi tsaf da ita, sadda ta fito ya dube ta sai da ya kasa ɗauke idanu kafin can kuma ya janye.
Ɓangaren Mai babban ɗaki suka fara zuwa, duk wanda ya gan su sai ya zube ya hau gaisuwa, jama'ar gidan kowa ya cika da mamaki. To ko dama suna son juna ne tun a baya? Yanayinsu dai ba su yi kama da waɗanda aka wa dole ba.
Haj Saratu fuskarta a sake ta ke dubansu har suka ƙaraso inda take zaune saman kujera, kusan a tare Maina da Sadiya suka zube suna gaida ta. Ta amsa musu tana tambayar Sadiya lafiyarta.
"Alhamdulillah." Amsar da ta ba ta kenan. Sun zauna nan sun ɗan jima har wasu maza biyu suka shigo yayyun Maina yara ga Haj Saratu. Nan ma gaishe su Sadiya ta yi. Ba su wani jima ba suka shiga sauran sashe biyun na matan Mai Martaba kafin a ƙarshe su je na Fulani Kausar.
Ba su iske ta a falo ba sai su Najma da Ummullhair, har da Hindatu da ba ta iske a ɓangaren Fulani Amarya ba wacce a yanzu Sadiya ta fahimci ita ce mahaifiyarta daga bakin su Karima da Bintu masu taya ta aiki. Ganinsu tare da Maina sai 'yanmatan da sun kai su biyar da wasu samarin su huɗu suna ta hira suka shiga taitayinsu. Nan kowa ya hau gaishe su. Maina da fuskarsa kamar ba ya wani abu wai dariya, ya ce.
"Ban hana ku irin wannan cakuɗewar a dinga hirar shirme ba?"
Kowa ya yi shiru an rasa mai bakin magana. Ya nemi wuri ya zauna, ita ma Sadiya ta zauna wani gefen daga saman kafet. Maina ya dai dube ta amma bai ce komai ba ya juya ya dubi Ummulkhairi bayan fitar samarin da ma su Hindatu da Nasiba.
"Fulani fa?"
Kafin Ummulkhairi ta amsa sai ga ta ta fito cikin shigarta na alfarma. Ta yi kyau sosai kai ka ce wani wurin za ta je sai dai ga duk wanda ya san Fulani Kausar an san mace ce mai gayu ga ta ba ta rabo da lalle. Duk sadda za ka ga yatsun nan akwai lalle a jikinsu. Fuskarta a sake hango ɗan nata mafi soyuwa a rai, ɗa namiji tilo da Allah ya mallaka mata, ko kusa ba ta kula da Sadiya ba sai bayan ta zauna, nan da nan ta haɗe rai. Sadiya ita ma ta yi ƙasa da kanta kirjinta na dukan tara-tara, daga yanayin kallon da ta ga Fulanin ta watsa mata ya sa ta ƙara fahimtar har a lokacin ba ta sami karɓuwa ba a wurinta.
"Barka da safiya My Fulani. Fatan kun tashi lafiya?"
Maina ya faɗi a ladabce yana murmushi kamar bai ga yanayin fuskar mahaifiyartasa ba. Duk a kan Sadiya da ba ta yi mata laifin komai ba sai na auren ɗanta.
Fulani ta amsa ba kamar yadda ta saba ba da annuri da komai a samna fuska. Wannan karon laifin Sadiya ya shafe shi.
"Barka da safiya." Faɗin Sadiya da sanyin muryarta. Wani banzan kallo Fulanin ta bi ta da shi duk da a banza saboda idanun Sadiya na bisa ƙafafun Fulanin, sai dai kawai kallo take amma hankalinta da kunnuwanta su na ga Fulanin ta ji ko za ta amsa gaisuwar. Sai ma ta ji muryar Fulanin na faɗin.
"Ban ce maka ba na buƙatar matarka a sashena ba?"
Maina ya ji babu dadi, don haka a nutse ya dubi Ummulkhair da ke kokarin ajiye masa tray ɗauke da ruwa da lemu sai ko kofi guda biyu wanda a farko ɗaya ta bada umarni a saka amma tsoron faɗan Maina ya sa ta sa aka ɗauraye na biyun aka saka.
"Ki kai Antinki ɗakinki."
Ummulkhairi ta ji kamar ya watsa mata garwashi a