Showing 99001 words to 102000 words out of 124441 words

Chapter 34 - Kazar Kwanci Hausa Novel Complete

ɗan kumbura sun ƙanƙance, fuskarnan ta yi jazur. Haka ta bi umarninsu ta yi wanka kamar wacce za'a kai ta gidan aure a lokacin, ta shirya bayan an turare mata kayan da turaruka kala-kala masu kyau da aka siya a wurin mai gyaran jiki. Hoda kawai Zahra ta shafa mata sai kwalli. A hakan ma sai ta yi kyau saboda ɗinkin riga da siket ne da aka yi shi ya zauna sosai. Mayafi ta yafe kanta da shi bayan Zahra ta yi mata ɗauri. Maman Zahra dake gefe riƙe da Imam ɗa ga Zahrar sai nasiha ta ke mata da nuna mata dama can Ibraheem ne mijinta ba AbdulMajid ba. Ta yi hakuri ta kuma yi biyayya. Dauriya kawai ta ke na dole don ta sani ko ta yi niyyar kukan ma ba iyawa za ta yi ba, ji take kamar ma hawayen nata sun ƙare. Ana kammalawa suka koma cikin gidan. Kamar jira ake su shiga, motar su Maina ta tsaya da ƙofar gidan. Dama Malam ya ce yaransa maza su tsaya don a tarbe su. Ciki har da babban ɗan Abba a maza, wanda shi ma sunansa Hashim ake kiransa Baba Karami.

Giɗaɗo ne ya fara fitowa ya buɗe wa Maina ƙofar ɓangarensa, sai dai har su Khamees suka fito ba shi da niyyar saukowa. Sanyin Ac na motar har yana bugun na kusa da wurin. Sai da ya gama ƙarewa gidan kallo kafin ya sa ƙafarsa ɗaya a wacce ke rufe cikin takalmi mai rabi sahu ciki (half cover shoe) sannan ya fiddo dayar.

"Nan ma mulkin zai gwada kenan."

Yaya Mustafa ya faɗi kamar mai raɗa a kunnen Zakari dake kusa da shi, hakan ya sa Zakari ɗan murmusawa kaɗan duk da har a sannan bai huce daga abin da ya so afkuwa ba a ɗazun wajen ɗaurin aure. Wato laifin AbdulMajid.

Suka dube shi sadda Hashim yayansu ke musu sannu da zuwa. Maina ya ɗan russuna kai bai ce komai ba sai ɗan murmushi kaɗan wanda ga na kusa da shi sun fi kowa sanin na yaƙe ne.

Haka suka yi mishi jagora har falon Malam wanda ya sha gyara don dama matar gidan gwanar tsafta ce wato Inna. Ƙamshin turaren wuta ma sai tashi ya ke, amma fa duka wannan bai hana ƙamshin turarukan Maina karaɗe falon ba, koda dai ga su Baba Habu ba za su iya tantance waye mai ainahin ƙamshin ba a tawagar ta Maina, sai dai jikinsu ya ba su cewa babban goro fa sai magogin ƙarfe.

A karo na uku, Maina ya ƙara sanya Malam mahaifi ga Sadiya a idanu. A ladabce ya gaishe shi, Malam ya amsa shi ma yana kokarin girmama shi ta hanyar ɗan yin ƙasa da idanu. Bayan gaisuwar ce kuma kowa ya fice ciki har da abokan Maina aka bar shi tare da surukinsa wanda ya zo mishi bagatatan. Shi fa ba mai raina arziƙin mutane ba ne don ba haka a ka tarbiyyantar da shi ba, sai dai bai hango wa Hamma zaɓen mace a gida irin wannan ba wanda ya sani a arziki irin na Baffan, ko kyauta aka tashi zai bayar da fin wannan.

"Ɗana Ibraheem."

Jin haka Maina ya ɗan dube shi kaɗan cikin wadataccen hasken da ya haskaka falon wanda ya sha sabon farin fenti, kafin ya sadda idanunsa yana nanata sunan a zuci. Bai jin ko mahaifinsa ya taɓa jingina sunansa da kalmar Ɗana. Malam ya cigaba da zancensa.

"Zan fara da ba ka haƙuri, ka yi haƙuri idan har an maka ba daidai ba a auren nan. Mu kanmu mun sani wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa. A kuɗi, ilimi, kyakkyawar nasaba, da komai ma na rayuwa na sani kai ɗin ba sa'an auren Sadiya ba ne. Amma kuma kaf ɗin mu babu wanda ke da ƙarfin ikon da Allahnku ke da shi a kanku da mu ma. Kamar yadda ba ka yi zaton aure a lokacin ba, haka mu ma ba mu taɓa hasko faruwar abin da ya faru a yau ba. Ina roƙon Allah da ya ba ku ikon riƙe junanku bisa amana, ya kuma ba ka ikon sauke dukkan haƙƙoƙin da suka rataya a wuyanka."

Malam haka ya yi ta kwararo nasiha da ban baki da rarrashi kafin ya ƙara rufewa da addu'a. Maina da ya yi shiru kawai yana sauraronsa, ko a fuska ba za ka ce ga kalar tunanin da ya ke ba. Jin shirun na Malam ya sa shi motsa leɓɓansa ya soma magana.

"Nagode Baba, zan kuma yi amfani da nasiharku."

Malam ya ji daɗi ainun, ya ƙara godiya a fili kafin ya leƙa ya yi wa su Giɗaɗo magana kan su shigo.

Ba jimawa kuwa su Anti Hafsatu da sauran ƴan uwa aka shigo falon har da waɗanda ma ba a kira ba. Sai dai duk wacce ta ga Maina sai ta raina kanta musamman cikin ƙawayen da suka tsaya ganin ƙwaf. Kusan ma su Lamiɗo ne bakinsa, shi fuskar ba murmushi kuma ba za ka ce yana cikin fushi ba. Hatta da wacce ta shigo da zummar guɗa fasawa ta yi saboda yanayin kwarjinsa sai ta ga kamar idan ta yi to fa laifi ne gagarumi. Kusan samarin dai akwai cika idanu.

Bayan fitarsu kuma bisa jagorancin Baba Haba suka shiga har tsakar gidan zuwa falon Inna aka gaishe ta tana sunne kai. Maina ya ji duk ya gama gajiya, babu abin da ya ke buƙata kamar ya gan shi kwance saman gado yana hutawa.

Karo na uku kuma da ya yi zaton gaisuwar ta isa tafiya za su yi bayan shigarsu falon Malam, aka dakatar da shi wai Amarya za ta shigo su gaisa. Jin haka ya ɗan matse tafin hannunsa na dama gami da ɗan cije pink lips ɗinsa kaɗan, bai ce uffan ba.

Wata yar uwar su Sadiya ce a gaba riƙe da hannunta ta shigo da sallama sai ko Sadiyar da fuskarta ke buɗe, ta yane mayafi ta yi lulluɓi irin na matar aure. Ƙirjinta duka kawai yake yi, ta firgita da irin ƙamshin da ke tashi tun daga tsakar gidansu har shigowa falon Abban.

Giɗaɗo, Lamiɗo da Khamees da ke kallon Sadiya, suka kalli junansu kowanne fuska ɗauke da maɗaukakin murmushi. Khamees har da wani irin hamdala a zuciya kai ka ce shi aka aurawa ita. A hankali ta zauna nesa kaɗan da inda suke zaune. Ta zame jikinta ta ɗan durƙusa ta ce.

"Barkanku da dare."

Daga yanayin rawar muryar za ka fahimci kamar kuka ta ke yi ko kuma ta ke shirin yi.

"Barka dai Ranki ya daɗe."

Kusan lokaci guda suka amsa. Maina bai kalli inda take ba, ba shi kuma da niyya. Muryar dai ya so ya ɗauka tunda yana sane da cewar sun taɓa gaisawa. Sai dai wannan karon cike take da rauni sosai, ƙila ma kuka ta sha don an aura mata shi. A ransa ya ja tsaki, to wa ya kama ta ya yi kukan tsakaninsu?

"Bari mu ɗan ba ku wuri."

Faɗin Giɗaɗo a tausashe yana kallon Maina. Bai ce musu uffan ba, shirunsa na nufin eh koda kuwa ba haka ran nashi ya so ba. Tunanin ma da ya faɗa, a bar su tare ya ce mata me? Bayan zuciyarta ba shi take so ba yaudararta aka yi.

Falon ya yi tsit daga shi sai Sadiya da ita ma ta kasa kallon Mainan, tsoron ma haɗa idanu ta ke da shi har ga Allah. Shirun ya yi mata yawa don haushinsa ma ta ji ta soma ji, ita tun farko dama bai mata ba, ballantana yanzun da laifin Hamma ya shafe shi.

"Goben da misalin ƙarfe bakwai ne."

Ta tsinci muryarsa na fita tamkar an busa sarewa, ta gyaɗa kai a hankali lokacin da hawayenta suka ɗiga saman ƙunshin bayan hannun.

"Toh." Ta faɗi da rawar murya fiye da farko.

'Kuka take.' Ya furta a zuciyarsa. A hankali ya ɗaga kai ya dubi awarwaron da ya cika kunnuwansa da ƙara wanda tun zamanta take wasa da su.

'Fara ce.' Ya ƙara furtawa a ƙasan ransa.

'Ƙila kuma farin mai ne.' Ya nanata duka shi kaɗai. Sai kuma ya ji haushin kansa. Duka me ya kawo wannan.

Sai ta ga ya miƙe tsaye. Ta share fuskarta har a sannan ba ta kalle shi sai ko ƙafafunsa da ta bi da kallo waɗanda suke tamkar ba sa taka ƙasa.

"Asuba ta gari."

Ya furta karo na biyu yayin da shiru ya ratsa. Ta rasa dalilin rashin tafiyar ta sa don haka ta miƙe.

"Allah ya tashe mu lafiya."

Ba ta jira amsarsa ba ta juya, ya juyo kai ya bi bayanta da kallo kaɗan sai kuma ya kauda nasa kan ya nufi hanyar ficewa a falon.

Daren ranar Sadiya raba shi ta yi da yayyunta da Inna ana ta mata nasiha. Tare da Anti Hafsatu da wata Gwaggo Jummai wacce take matsayin Yaya a wurin Malam. Su Adda Ruƙayya da Safiyya kuwa za su biyo su ta mota ne da sauran kayayyakin Sadiya.

Tunani babu irin wanda Sadiya ba ta yi a kan Maina ba. Magana sau biyu kacal ya yi mata, wannan ya sa ta ƙara fahimtar bai karɓe ta ba shi ma kamar yanda yake a wurinta. Madadin hakan ya ƙuntata mata, sai ta ji sanyi kaɗan tunda itama ba ta sonsa. Kuma yanda ba ta tunanin ya kalle ta, ta ji dadi da ba ta ko kalli fuskarsa ba. Har abada ma ta saka a rai ba za ta so shi ba tunda shi ma ba ya sonta. Za dai ta yi masa biyayyar da ake ta nanatawa, duk zaman da ya zaɓar musu ita a wurinta daidai ne.
Babbar matsalarta, karatunta. Sun ce ta kwantar da hankali tunda an san tana karatun ƙila a samar mata mafita. Ta bi yayyun da toh kawai.

***
Washegari...
GOMBE



Cike da tsantsar mamaki Fulani Kausar ta ke duban Mai Martaba wanda ya gama magana. Sai kuma ta kauda kai gar wasu kwalla na tsantsar baƙin ciki da takaici na tarar mata. Ta ƙara maimaita abin da ya ce a ƙwanyarta.



"Mun karɓawa Maina auren da suka so tozarta mu a bainar jama'a, sai a taya shi da addu'a, kuma a ce kiyaye wulaƙanta ɗiyar mutane don gujewa faɗawa fushinmu."



Ta gyara leɓɓanta ya fi a ƙirga tana son magana amma zallar takaici bai sa ta iya firzarwa ba. Ƙarshe ta yi mishi sallama ta fito da saurinta, bayi na mara mata baya. Ba ta nufi ko'ina ba sai ɓangaren Mai Babban Ɗaki. Ta iske ta kishingiɗe tana magana da wata amintacciyar baiwarta Hindu. Ta sani duk abin da zai sa Fulani Kausar takowa zuwa sashenta to ba ƙarami ba ne, kusan ma za ta iya cewa ba alkhairi ba.



Hindu ta kwashi gaisuwa kafin uwar ɗakinta ta ba ta umarnin fita. Fulani kamar jira ta ke a zafafe ta ke duban ta.



"Kin san da batun auren Maina?"



Wani murmushi Hajiya Saratu wacce suke kira da Mai Babban Daki ta yi.



"Bismillah ga wuri ki zauna."



Wani banzan kallo Fulani ta watsa mata.



"Ke kanki ba ki ishe ni kallo ba balle shirginki. Yanzun ma saboda ya shafi ɗana ne. Ashe shiyasa ki ka ba da umarnin a fara shirin tarba? Burinki ya cika an ci zarafina an aura wa Maina ƙasƙantacciya wacce ba jinin sarauta ba?"



Murmushin da har yanzu bai gushe ba a fuskar Haj Saratu, da shi ta dube ta a kokarinta na son hadiye radadin da maganganun Fulani suka haifar mata.



"Na sani Fulani, ban kuma saba tsallake umarnin Mai Martaba ba ke kin sani. Dukkan abin da ya ce, shi za'a yi. Auren da aka riga a ka ɗaura, ai ko a ɗaya daga cikin bayi ne, sai ki rungumi ƙaddara."



"Shikenan, mu zuba ni da ku! Daidai nake da ke da shegiyar da aka aurawa ɗana!"



Tana kai wa nan ta juya a zafafe ta fice, Haj Saratu ta girgiza kai tana fadin Allah ya kyauta don a cewarta, ba ta ga ranar da Fulani za ta yi hankali ba.



***

KANO





"Wannan mutumin ya tashi daga wani da baki sani ba, ya tashi daga sunan aboki ga wanda ki ka sani a farko, ya amsa sunan mijinki a yanzu. Girman haƙƙoƙinsa a kanki, sai dai a ƙara jaddada maki. Idan ki ka yi mishi biyayya ki ka saka tsoron Allah a lamuranki, toh ba ki da kaico. Duk runtsi ki zama mai bin umarninsa, aljannarki ki ke nema. Kuma ki saka a ranki bautar Allah ya kai ki. Ba ruwanki da ɗaukar magana, ki kaunaci yan uwansa. Ki zama mai sirri, ban amince ki zama mai tona dukkan abinda zai faru tsakaninki da shi ga kowa ba. Aure yana buƙatar sirri. Sannan abu na ƙarshe da zan faɗamaki, ki riƙe addu'a. Babu maganin da ba za ta yi maki ba. Mu da muke zaune a gidanmu, ita ce ta zaunar da mu. Ƙarfin addu'a, Allah ya albarkaci aurenku ke da yar uwarki. Ya shige maku gaba. Ameen."



A hankali ta sa hannu ta goge fuskarta tana duban titi. Tafe suke a hanya na zuwa Airport a motar gidan Abba. Ita da Anti Hafsatu sai ko Husna da Zahra'u da Adda Ruƙayya da suka biyo su rakiya. Tunanin maganganun da Inna ta yi mata da asuba take yi, ga Malam shi ma ya yi mata doguwar nasiha sosai. Ya kuma ce koda karatunta iyakar abin da ta samu yi kenan, toh ta godewa Allah kada ta yi baƙin ciki ballantana yana addu'a da kyautata zaton cewa za su bari ta yi koda kuwa a Gomben ne, koda hakan na nufin dawowa daga farko ne a jami'arsu ta can. Ita ma tana fatan Allah ya sa hakan ne, idan har za'a bari ta yi za ta ji sauƙin wani abin.

A ɓangare ɗaya kuwa ta rasa me ya sa Nudrat ba ta yi mata ko waya ba, ga Nene ma wacce ba ta zo ba kuma ba ta yi waya ba. Duk da Dada ta ce a yi musu uzuri ƙila kunyar abin da ɗansu ya aikata ne, amma sai ta ga kamar ya dace ace sun zo ko sun mata magana.

***

Ga Maina haka Baffa ya dinga ba shi haƙurin da kuma yi mishi kyakkyawan addu'ar zaman lafiya da Sadiya sadda suka je yin sallama da su.



"Yarinya ce mai nutsuwa da kirki, in sha Allahu ba za ku samu matsala ba. Yadda ka nuna kai ɗin ɗa nagari ne, ba ka kuma bijirewa umarnin mahaifinka ba, in sha Allahu rayuwarka za ta yi kyau. Ba kuma za ka taɓa dana sanin auren nan ba. Ba iyayen Sadiya kaɗai ka rufawa asiri ba, hatta da ni wanda ɗan uwanka ya nemi ya jawo min zagi da zubewar mutunci ka cece ni. Nagode Ibraheem, Allah ya karawa rayuwa albarka."



Abin da Baffan ya ce kenan, haka ma Nene wacce har hawaye ta zubar sadda ta ke mishi addu'a, ita ma sosai ta yabi zaɓin da Allah ya masa na auren Sadiya. Shi dai ya ji su kuma ya amsa da amin amma kuma sanin taƙamaiman wace ce Sadiya, wannan sai zama ya yi zama. Ya dai gane ba ƙaramin kauna suke yi ga Sadiya ba. Hatta da yarinyar (Nudrat) da zai ce magana ba ta haɗa su da shi bai mance sadda ya zo giftawa zai fice daga falon Nene ba ta dakatar da shi ta hanyar kiran sunansa a hankali. Ya tsaya cak ya na dubanta bai ce uffan ba ganin har da hawaye kwance saman fuskarta, ta yi ƙasa da nata idanun, da wani irin raunin murya ta ce.



"Ina roƙawa yar uwata Sadiya alfarma, don Allah ka kula da ita. Ba ta da matsala, in sha Allahu nasan za ta shiga ranka ɗari bisa ɗari. Koda ba ka so ta ba, ka yi mata gurbi ko ba yawa a wani sashi na zuciyarka. Nagode. Allah ya tsare hanya."



Daga haka ta bar shi tsaye kafin bayan tafiyarta shi ma ya wuce.



"Ai ina jin ga motarsu." Ya tsinci muryar Lamiɗo na faɗi, Khamees ya amsa da fadin.



"Yes su ne, ga kiran Baba Habu." Daga haka ya fito a motar yana amsa wayar gami da ɗaga wa Baba Habu hannu.



Maina na fitowa ya yi gaba zuwa ciki, akwatunansu dama Giɗaɗo da ma'aikacin wurin sun yi gaba da su.



***



Su Sadiya na fitowa aka gaisa da Khamees. Ta kula kamar a hanzarce suke yanayin yanda Khamees din ke tambayar kayayyakinsu. Nan aka sanya akwatunan kayanta da na Anti Hafsatu guda daya a keke aka yi ciki da su. Suka yi sallama cike da kewar juna da su Zahra da Husna da Adda kafin su bi bayan Khamees da Baba Habu wanda shi ma iyakarsa Airport din zuwa ciki.



Kirjinta na yi ta bugu don ta sani yau dai dole za ta ga Angon nata. Koda aka kammala komai suka yi sallama da Baba Habu ya tafi ya bar su, bayan Khamees suka bi har zuwa ɗan falon da matafiya ke zama don jiran jirginsu. Takunta cike da nutsuwa, sanye take da doguwar rigar abaya baƙa mai adon duwatsu, ta yane kanta da mayafin abayar sai ko ƴar jakarta, takalminta mai ɗan tudu wanda ya ƙarawa tafiyarta salo na daban. Fuskarta duk da hoda kadai da man leɓe ta shafa sai kwalli, ta fito fes da ita. Lamiɗo da suke zaune ya ɗan taɓo Giɗaɗo dake latsa wayarsa. Giɗaɗo dake gefen Maina ya kalle shi cike da alamar tambaya. Lamiɗo da hankalinsa ke kan Sadiya a hankali cikin raɗa ya ce.



"His princess."



Hakan ya sa Giɗaɗo shi ma ya dube ta. Kauda kai ya yi yana jan istigfari, har ga Allah wanda zai kalli Sadiya bai yaba tsarin halittarta ba to fa kalle shi kawai.



"Masha Allah. Dama ai babban goro sai magogin ƙarfe."



Wannan furucin na Lamiɗo karaf a kunnen Maina da ya gama amsa wayar abokin aikinsa da ke can babban kamfaninsu na motoci dake London. A hankali ya ɗaga lumsassun idanunsa ya kai duba gare ta. A kallo ɗaya ya gane kyakkyawa ce, farinta mai kyau ne, sai a ɗauka ta haɗa dangi da ƴan Somalia a yanayin halittar fuska. Takunta ma irin wanda ke fisgar hankalin maza ne.



Ya kauda kansa ya maida hankali ga wayarsa. Ƙila da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login