Showing 96001 words to 99000 words out of 124441 words

Chapter 33 - Kazar Kwanci Hausa Novel Complete

shiga da zancen farko na Abba mai sauƙi ne kan labarin da ya soma ba su bayan bude taro da addu'a da ma yin doguwar nasiha ga Sadiya har da nunawa kowa na falon muhimmancin yarda da ƙaddara. Kamar daga sama kuma ta ji yana fadin.

"To a ƙarshe da haka ta faru, auren a take bisa umarnin Mai Martaba Sarkin Gombe, aka ɗaura shi da ɗansa Ibraheem da suke kira Maina."

Nan falon ya ɗauki kabbara sai kuma wata guɗa da wata Gwaggonsu ta ɓangaren Malam ta rangaɗa duk da hawayen da suka yi wa fuskarta kaca-kaca saboda ruɗanin da zuƙatansu suka shiga da farko.

Su Anti Hafsatu da Safiyya su kansu sai kukan ya koma dariya.

Inna dama ba ta falon tana can ɗakinta amma kuma cike take da fargabar me ke gudana a falon Malam.

Sadiya har a lokacin kanta tana ƙasa, rawar sanyi sosai take yi. Hawaye kuwa wani na bin wani, wai Hamma ne ya ce ba ya sonta? An ɗaura masa aure da Fareeda? Meyasa duk wanda ta ƙaunata yake gudunta ne? Ko soyayyar ce ba ta karɓe ta ba?

'Maina? Mai..."

Cikin daƙiƙa biyar ta tuno shi, shi ne tabbas. Ɗan uwa kuma aboki ga Hamma ɗan Sarki. Kawai sai ta ji ƙarfin kukanta ya ƙaru. Mutumin da ko ganin juna ba su taɓa yi ba? Za ta iya rantsewa tun wayarsu ta farko kuma ta ƙarshe ta ji bai mata ba, ta tsane shi.

"SubhanAllah, ai zazzaɓi ne a jikinta."

Ba ta ji ma sadda Husna ta kai hannu saman goshinta ba, sai furucin da ta ji ya dakar mata kunne.

"Ki yi hakuri Sadiya, bari a karɓo maki magani. Amma lallai ki sani gobe idan Allah ya kaimu jirgin safe za ku bi zuwa Gombe tare da mijinki."

Abin da Abba ya furta kenan. Nan kuma ya ba wa kowa umarnin tafiya yace a bar Sadiya a falon ta huta bayan ya ba Baba Habu umarnin siyo mata maganin zazzaɓin. Bayan kowa ya watse a falon daga shi sai Malam sai Sadiya dake dunƙule a gefe tana kuka murya a shaƙe. Abba ya ƙara yi mata doguwar nasiha ya kuma roƙe ta kar ta ba su kunya, kamar yadda shi AbdulMajid ya so su kunyata amma Allah ya rufamusu asiri, toh ta daure ta yi hakurin zama da mijin da Allah ya zaɓar mata.

Ta jinjina kai tana share majina da hankicif dake hannunta. Sai da ya kammala sannan Malam shi ma ya sanya mata albarka ya ƙara da ƴar guntuwar nasiha kafin su ce ta kwanta ta huta za su koma sallamar baƙin da suka zo daga nesa waɗanda ke can babban gida. Bayan fitarsu ta haye saman doguwar kujerar mai cin mutum uku ta kwanta, ba jimawa sai ga Zahra ta shigo. Ganinta yasa Sadiya miƙewa ta fada jikinta ta buɗe sabon shafin kuka. Ita ma Zahra hawayen ta ji sun zubo mata, ta yi mata murna da wannan sauyi, sai dai kuma hakan bai hana jin tausayinta ba. Ta riga ta san irin zafafa so da ƙawarta ke yi idan ta tashi, komai na son ba ta iya shi ba. Ba ta tafiyar da kanta a duniyarsa a hankali, tana zurfafawa ne gaba ɗayanta ta shige. Toh irin wannan ranar ake tsoro. Can kuma ta share nata hawayen don bai kamata ita da za ta lallaɓa ba, ta sanya ta wani kukan.  Sadiya ta ɗago kai ta na dubanta.

"Ki na ganin hakan daidai ne? Ya rayuwata za ta kasance a Gombe? Zahra na taɓa baki labarin Maina, ba kalana ba ne. Ya fi ni aji da ma dukkan wani abu da zan ɗaga na yi tutiya da shi. Babu wanda ya hango shi ma kamar dole aka masa a kaina? Ta ya ya zai so macen da bai santa ba bai san halinta ba? Ni fa? An tabbatar idan muka rayu tare zan so shi?  Kuma da suke batun tura ni Gombe shikenan na bar karatuna?"

Zahra ta yi murmushi a kokarin danne nata damuwar.

"Sadiya godiya ya kamata ki yi wa Allah. Kar ki yi baƙin ciki bisa dukkan zaɓin da ya yi maki. Ki duba iyayenki da ma manyan mutanen da suka hallara a taron ɗaurin aurenki, idan har AbdulMajid bai ko duba su ba ya tsallake ya je aka aura mishi Fareeda, toh ki sani girman sonta da yake yi ya wuce misalin da zan kwatanta maki. Idanunsa sun rufe ya zaɓi ya kunyata iyayensa da namu da ke kanki a idanun jama'a ya bi son zuciyarsa. Dayake Allah ba azzalumin bawansa ba, sai ya yi maki sakayya nan take. Ya ba ki wanda ya fi Abdul kyan nasaba da komai na rayuwa. Don Allah kada ki yi baƙin ciki, addu'a ki ke ta yi na nemawa kanki zaɓin Allah ko? To ki saka a ranki Ibraheem Tafida shi ya zaɓa maki. Kukanki kamar butulci ne ga ni'imar da Allah ya maki. Ke ba za ki gane akwai masu jiran faruwar hakan ba sai idan kin ga yadda Anti Hajara ta fice daga gidan nan kamar kububuwa ta cika ta yi fam! A kan kunnena cikin harshen turanci na ji cikin ƙawayenta na fadin ta gama cika musu bakin yau ba za a ɗaura aurenki ba har tanadin liyafa ta yi a gidanta zasu je can ƙarfe huɗu a yi shagali. Toh Sadiya wannan kaɗai ba..."

Maganganun Zahra suka katse saboda sallamar da Anti Hafsatu ta yi ta shigo hannunta ɗauke da leda mai tambarin wani babban kemis dake kusa da su. Sadiya wacce nasihar Zahra ya shige ta sosai gaba ɗaya ta ji zuciyarta ta sanyaya, abu ɗaya kuma da ta sani har ga Allah ba ta san ta ya za ta fara rayuwa da wanda ba ta ma san shi ba balle ta ji sonsa a zuciya. Ga kuma mamaki da tsoron Hajara da ya ƙara ɗarsuwa a ranta.

"Sannu Sadiya, amma da sauƙi yanzu ko?" Faɗin Anti Hafsatu tana zana a gefenta. Zahra ta mike ta ɗauko ruwan roba dake ajiye a gefe guda kusa da firij ɗin Malam sai kofi. Nan ma Anti Hafsatu lallaɓa Sadiyar ta dinga yi har tana faɗamusu wai Maina zai shigo da daddare ya gaisa da iyaye. Ita dai ba ta ce uffan ba.

"Tsaya kin ci abinci?" Anti Hafsatu ta faɗi tana dakatawa daga ɓallo maganin da take shiri. Girgiza kai ta yi.

"Bari na ɗebo mata." Faɗin Zahra tana miƙewa ta fita. Can kuma ta dawo, sai a sannan Sadiya ta dube ta.

"Ina Nudrat?" Ta furta a sanyaye. Ajiyar zuciya Zahra ta sauke.

"Tun bayan da Ameer ya ce an fasa daurin aurenki ta ɗauki gyalenta da mayafi ta fice tana hawaye. Na tabbata gidansu ta nufa."

Jinjina kai kawai Sadiya ta yi ba ta ce uffan ba. Ta sani dole Nudrat ta ji ciwon abin da yayan nata ya aikata. Hawaye ta ji sun cicciko sai ta share su da sauri. Ba ta son jefa zuƙatan da suka damu da al'amarinta cikin damuwa da rashin sukuni.

***
A gidan su Nudrat kuwa, hankalinsu gaba ɗaya ya tashi bayan labarin abinda ya faru da ya iso musu. Nudrat ma a hargitse ta shigo gidan sakamakon wayar da ta yi da ƴar Yafendonta, Khalisat wacce ta ba ta labarin ai Hamma dagaske ya gudu ya auri Fareeda, kuma wai Mai Martaba sun iso gidan ana ta yi wa Maina busar sarewa da kirarin ya zama Ango wurin Sadiya. .
Kuka wurjanjan haka Nudrat ta shiga yi, ba ta taɓa hasko ƙaddara za ta musu wannan juyin ba. Hamma ne ya yi musu wannan cin kashin? Sadiya da Maina an musu aure?

Haka ta dinga tunane-tunane har ta ƙarasa gidan, wuri a cike daƙyar ta samu ta rufe fuskarta da mayafi ta wuce zuwa ciki kunnuwanta na dauko mata muryar Hasken Fadar Sarki yana ta zuba uban kirari ga Ibraheem Tafida Ango.

Tana ƙarasawa ta ga wuri a hargitse ana yi wa Nene firfita, da gudu ta ƙarasa. Ashe suma ta yi da ta ji tsiyar da ɗanta ya shuka. Nudrat ta rungume Nene ta cigaba da rera kukanta. Tausayin Nenen ta ji, a karan kanta kunyar Sadiya da ma danginta take ji, da wane ido za ta ƙara kallonta? Ƙila ma Sadiyar ta yi zaton ta sani shiru kawai ta yi.

Daƙyar dai ƙura ta lafa a gidan su Nudrat. Bayan tafiyar Sarki da tawagarsa da ma baƙin da aka gayyato na cikin garin da suka zo biki, Baffa ya keɓe da Nene ya taushe ta. Ya kuma ƙara da faɗin.

"AbdulMajid kansa ya yiwa. Ki taushi zuciyarki kar ta kai ki ga yi masa mummunan baki. Zuru ma kaɗai ya ishe shi. Ya zaɓi duniya a kan mu iyayensa. Ya tozarta mu a bainar jama'a, toh ina mai tabbatar maki ko ba ki ce komai ba, zai ga ishara a rayuwarsa. Ki shirya idan an yi Isha'i ku je ku ƙara ba iyayen yarinyar nan haƙuri."

Nene daƙyar ta haɗiyi miyau mai ɗaci tana gyaɗa kanta.

***
IBRAHEEM TAFIDA (MAINA)

Tun shigarsu falon ya yi zaune saman kujera gami da kwantar da kai ba tare da ko cire alƙyabbar da ke sanya a jikinsa ba. Na'urar sanyin da ke kaɗawa a falon bai tafiyar masa da gumin da ke tsastsafowa a goshi da ma cikin gargarsar dake kwance luf a hannunsa ba.

Lamiɗo ya dubi Giɗaɗo kafin su maida duba ga Khamees wanda shi kansa ya yi shiru. Cikin su huɗun aka rasa wanda zai fara furta koda harafi ne. Can Khamees ya dube su, daga yanayin da ya musu inkiya ya sa su miƙewa su ba su wuri. Ya sani kaf ɗinsu babu mai iya tunkarar Maina da kowane irin zance bayan sa.

"Maina." Ya furta bayan ya yi ƴar gyaran murya. Ya ɗago idanunsa da suka yi mugun kaɗawa ya sauke a kansa ba tare da ya ce kanzil ba. Sai dai kallo ɗaya Khamees ya fahimci ran maza ya ɓaci.

Khamees ya ɗan kauda kai yana ƙara shiga taitayinsa kafin ya ce.

"Komai ya faru, ka ɗauke shi matsayin ƙaddara."

"Na ji."

Khamees bai ƙara magana ba sanin hali, har ya fidda ran ma zai ji ta bakin Maina ɗin sai ya ji ya ce.

"Hukuncin nan na Mai Martaba bai yi tsauri a kaina ba? Laifina bai yi girman da za'a hukunta da aure ba. Aure irin wannan ma na huce haushin Abdul. Why me? Yes na yi laifi wurin amsa kira a fili har ya yi sanadin da Abdul ya yi zafafan kalamai ga ɗiyarsu, toh a ba ni hukuncin da zuciyata za ta iya ɗauka. But Khamees aka aura min ita? Sa..Sadiya right? Yarinyar da ban taɓa gani ba, ba ma ni ne a ranta ba. Ni ma kuma ka sani auren ma ba ya cikin abubuwan da na saka a gaba yanzu."

Ya na kai wa nan ya furzar da huci mai zafi kafin ya ƙara kwantar da kai jikin kujera ya lumshe idanu yana jin raɗaɗi a ƙirjinsa.

"Ko mene ne, yanzu bakin alƙalami ya riga da ya bushe. Dama kuma Allah ya tsara matarka ce ba ta AbdulMajid ba. Ka yi hakuri, don Allah kar ka jawo abin da Mai Martaba ransa zai ɓaci fiye da wanda ka jefa shi ciki a wajen ɗaurin auren. Ko meke a ranka, ka bi umarni anjiman mu je can gidan nasu a gaisa da iyayenta. A bi umarni zuwa safen a wuce. Na sa a mana booking na jirgin safe goben."

Maina bai ce uffan ba. Sanin ma ba zai ce ɗin ba ya sa Khamees miƙewa ya fice wajen su Lamiɗo.

Shi kuwa har a sannan jin lamarin yake kamar a mafarki wai an ɗaura masa aure da budurwar AbdulMajid. Da ace ba ya wurin abin ya faru zai kira hakan da wasan yara, sai dai gani ya kori ji ai. Shi dai Maina jinin sarauta gaba da baya? Ya auri yarinyar da bai san ta ko a hoto ba?

Don ba ya mantawa sadda suke tare da Hamma a Gombe, da ya gaisa da ita ta waya Hamman ya nemi gwada mishi hoto ya nuna don me? Ashe ma auren da shi za'a yi.

Guntun tsaki ya ja kafin ya miƙe ya shige ɗaki don wanke jikinsa sai dai kuma ji ya ke daidai da ruwan ma ba ya buƙatar haɗawa da kansa. Sai ya ji inama ya bi shawarar Fulani da ta ce ya ɗauki Baharu (amintaccen bawansa) sun taho tare idan ya so a kama masa ɗaki a hotel din da suke. A dole haka ya rage kayansa ya faɗa banɗakin bayan gabatar da addu'ar da ta ce kafin shiga.

***
  A ɓangaren Hajara kuwa, daƙyar ta iya tuƙa kanta cike da wani mahaukacin gudu ta ƙarasa gidan Bokanta. Sadda ma ta sulale babu wanda ya kula sai munafukan ƙawayenta da suka dinga doko mata kira. Da kuka kashirɓan ta shiga falon nasa ba ta ko jira yaronsa mai cewa ta jira ya sallami matar da ke ciki ba. Ganinta a wannan yanayin ya tashi hankalinsa, nan ya ba matar haƙuri ya ce ta jira a waje. Miƙewa tsaye ya yi yana ƙoƙarin riƙo ta gami da faɗin.

"Hajjaju tawa lafiya?"

"Ba lafya ba! Maci amana kawai! Don me da ka hango fasa ɗaurin auren Sadiya da AbdulMajid ba ka hango aurenta da ɗan Sarkin Gombe ba?! Ashe kai macuci ne! Dama cutata ka yi ka yaudare ni! Yanzu ga shi can an ɗaura aurenta da wanda ya ci uban mutumin da ka yi aiki a kansa! Na shiga uku ni Hajara!"

Ta zube ta cigaba da kuka kamar ranta zai fita, kusan tun zuwanta duniya idan ka ɗauke mutuwar Mahaifiyarta, ba za ta tuna sadda hawayenta ya zuba irin na yanzun ba.  Boka ya sauke ajiyar zuciya ya nemi wuri ya zauna, shi dama wane aikin ya yi? Duk hangensa ma bai hango komai na sha'anin rayuwar yarinyar ba.  Inama aikinsa ke da ƙarfin yin tasiri a kan wannan Sadiyar mai babban tsari a jiki? Ya rasa ma me zai ce ga Hajara sai kuma wata dabarar ta faɗo masa.

"Ki kwantar da hankalinki don Allah, to so kike na faɗi abin da zai tayar da hankalinki? Eh dama na san hakan za ta faru, amma kuma da yake na san auren babu inda zai je shiyasa na ce maki ba ita ba au..."

"Dallah can rufe min baki! Aikin banza da wofi! Ka riƙe ƙaryarka! Ta bar tasiri a wurina! Cuta dai ka riga ka yi min shi! Kuma tsakanina da kai Allah ya isa!"

Tana kai wa nan ta miƙe za ta tafi, ya yi wani irin yunƙura da sauri ya zagayo gabanta ya riƙo hannayen. Zuwa lokacin zai ce ma son Hajara yake ji a ƙoƙon ransa. Ya rantse ta yi masa ɗari bisa ɗari a shimfiɗa don haka ko giyar wake ya sha ba zai yarda ta suɓuce masa ba tare da ya gama cin moriyar ganga ba. Ta yi kokarin fisge hannunta tana kuka da kunduma ashar sai ya saki hannun ta fice amma ko gezau sai ban haƙuri da rarrashi. Ƙarshe ma ya yi nufin kai mata sumba anan ne ta ci nasarar fisge hannun ta sharara masa mari a kunci. A gigice ba tare da ya taɓa tsammani ba ya dafe kuncin yana kallonta da tsananin mamaki. Idanu a waje ta ke binsa da kallon banza kafin ta ja dogon tsaki ta fice har tana bangaje kafaɗarsa.

Ya shafi kuncin da ta mara ya jinjina kai gami da yin ƙwafa. Can kuwa ya yi wata dariya.

"Kin yi babban kuskure Hajara! Mari? Toh kuwa zan nunamaki ƙarfin tsafina!"

Ya furta a fili yana mai cin dogon alwashi a kanta.

***
Sadiya na kwance jikin Innarta wacce ta ture ta ya fi a ƙirga amma a ƙarshe Dada ta hau ta da faɗa wai ta ƙyale ta na bankwana ta ke mata tunda nesa za su yi. Ita kuwa ganin abin kunya ne matsayinta na bafulatana babban ɗiya ta maƙalƙale mata har haka ya sa duk ta kasa sukuni. Su Hafsatu da Safiyya sai shige da fice suke yi wajen ganin an haɗa mata kayanta ba tare sun taɓa ko tsinke a lefenta ba. Dama kuma su a al'adar gidan babu wani abu da ake taɓawa a lefen yarinya har sai ta shiga ɗakin mijinta ta yi amfani da abin ta. Doka ce ta mahaifinsu. Ƙirjinta kawai ke bugu, hawayenta suka zubo daidai sadda ta ji kiran sallar magriba a kunnenta.

'Zai zo bayan sallar isha'i, za ku gaisa.'

Ta tuna maganar da Malam ya faɗi ga Innarta. Maina zai zo gidansu? Wace tarbar zai mata? Ita kanta me za ta ce ga mijin da ba su san komai da ya shafi junansu ba? Ta ji hawayenta sun zubo sa'ilin da Inna ke ture ta don ta fita yin alwala. Ta janye jikinta ta jingina da bango. Har sai da Inna ta dawo, ganin dai kowa na fita zuwa yin alwala ita ma ta mike zuwa ɗakinsu, wata ƴar uwarsu na fitowa daga banɗakin ta shiga ta ɗauro. Koda ta fito sallarta ta yi a nutse, tuni ta goge kwalliyar da ta yi mata caɓa-caɓa a fuska ta kuma sauya sutura zuwa doguwar rigar atamfa da ya sha stones.

Ana idar da sallar Isha'i sai ga Anti Hafsatu ta shigo inda take zaune tare da su Zahra suna hirar abin da ya ƙi wucewa a zuƙatan kowa ma. Ta kula dai har wasu a ƙawayenta da suka ƙi barin gidan burin kowa ya yi ido huɗu da wannan Ango.

"Sadiya taso muje." Gabanta ya faɗi.

"Ke ba wani abu ba ne dallah. Gidan su Zahra zamu shiga. Zahra ke ma taho."

Jin haka sai ta miƙe gwuiwa a sake, ita ma Zahra ta mara musu baya riƙe da wayarta da na Sadiyar da tun da ta kashe ba ta kunna ba.

Dakin Maman Zahra suka shiga, ganin wani arnen leshi fari ƙal wanda a farko shi aka yi za ta saka idan za'a miƙa ta ɗakin Hamma, yanzun kuwa wai an kawo ta ne don ta shirya saboda zuwan da Maina zai yi su gaisa. Hawayen ma kasa zuba suka yi sai zafi da raɗaɗi da idanunta ke yi duk sun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login