Showing 72001 words to 75000 words out of 124441 words

Chapter 25 - Kazar Kwanci Hausa Novel Complete

wani uban leshinta mai shegen nauyi kalar na inyamurai, fuskarnan sai maiƙo take yi amma kuma bakin an shafe shi da jan jambaki. Dariya ce ma ta kusan suɓucewa Atine sai ta danne ta ce.

"Yauwa ta ce ki hau."

"Ok." Gwaggo Atine ta furta don ita a wasu lokutan jin ta take kamar wata baturiya. Ta dai yi karatunta har sakandire, tsalle-tsallen da iyayen suka kula tana yi ne yasa aka yi mata aure don kanta ya fiye rawa a lokacin.
Da rawar jiki ta haye saman ta shiga falon da sallama. Waleedah da Azeema suka dube ta kafin su dubi junansu su fashe da dariya har da cafkewa. Gwaggo Atine kuwa ta kalle su a sheƙeƙe, ta san dai duk kusancinsu da Hajara ba su kai ya ita ba. Hajara dake ƙare mata kallo cikin takaici ta ja tsaki. Miƙewa ta yi ta na fadin.

"Biyo ni." Daga haka ta nufi hanyar ɗakinta, Gwaggo Atine ta bi su Waleedah da harara sannan ta bi bayan Hajara.

Waleedah duk sai ta kasa sukuni, hankalinta gaba ɗaya ya tafi a kansu, to me za su yi? Babu damar sani don haka kawai ta fiddo waya ta yi dogon rubutu ta tura saƙo ta ajiye.

A ɗakin kuwa suna shiga Hajara ta rufe cike da masifa ta ce.

"Wai ke ba na yi maki katanga da shigo min gida ba? Ko don ba ni da karnuka? Ko kuwa don kin ga ban nuna fuskarki ga Maigadina ba ta yadda ko kin tunkaro ƙyauren zai dakatar da ke?"

Ta ƙarashe tana huci da jijjiga jiki tana watsawa Gwaggo Atine banzan kallo. Sai Gwaggo Atine ta zube gwuiwa a ƙasa.

"Na tuba Autar Mama, ki yafe ni. Na rantse maki wannan mutumin hatsabibin gaske ne, ya san aikinsa akasi kawai aka samu. Amma ai ba a rasa nono a ruga, ga su nan da yawa kuma waɗanda su ma sun san ta kan aiki? Ki ba ni wata damar na rantse maki ko so ki ke yi a haukata maki yarinyar can da uwarta sai an yi. Ai mantawa na yi da Zakanyar Daji."

Hajara ta yi shiru tana nanata sunan ƙarshe da Gwaggonta ta fadi. Zama ta yi gefen gadonta. Gwaggo kuwa sanyin na'urar yana ta ratsa ta amma fa ba ta bar gumi ba, ita babban burinta kar wannan garaɓasar na samun kuɗaɗe daga Hajara ya wuce ta.

"Wace ce ita kuma?"

Wannan tambayar ta sa Gwaggo jan numfashi ta furzar cike da samun nutsuwar zuciya, ko babu komai ai an zo wajen don haka ta gyara zamanta har da tanƙwashe ƙafafu ta soma magana.

"Wata hatsabibiyar bokanya ce, matar da idan ta yi maki aiki zai wahala ki isa gida aikin bai riga ki kai wa ba. Ina tabbatar maki Autar Mama za ki sha mamakin yadda za ta kassara maki rayuwarsu. Ke ni ina ji a jikina ma kukanki ne ya zo ƙarshe. Ai da ma can na so kai ki tun farko, toh matsalar gaskiya ita ba nan take ba."

"A bangon duniyar ina zan je na same ta?"

Kai tsaye Hajara ta furta tana kallon Gwaggo, ji take dagaske ko a ina matar take za ta je gareta matukar kwalliya za ta biya kuɗin sabulu toh me zai dame ta? Ai buƙatar ma je Hajji sallah ne.

"A Mubi take."

Hajara kanta ya ƙulle ta ma rasa ina ne Mubin? Kafin ta nemi ƙarin bayani Gwaggon ta ɗora.

"Can Adamawa."

"Kin kuma tabbatar da ba zan yi zuwan banza ba?"

Dariya Gwaggo Atine ta yi.

"Autar Mama kenan. Ai ba zan kawo maki gaibu ba. Saboda na ga zahiri lokacin da na yi tashen rayuwa a gidan..."

"Ya isa, ban nemi ki ɗauko min tsohon tarihinki ba marar cikakken tushe. Ki shirya, a goben nan zamu wuce."

Da girmamawa Gwaggo ta amsa tana washe baki.

"Yauwa yanzu na ji batu, ai da zafi-zafi daman ake bugun ƙarfe. Bari na koma gida na dauki abin da zai min amfani sai na dawo nan na kwana. Zai fi kyau ace sammako muka yi."

A wulaƙance Hajara ta dube ta.

"A wane gidan za ki kwana ki ke nufi?"

Jikinta ya yi sanyi.

"Wai da a nan, kin ga zai fi mana sauƙi ko?"

"Babu wajen kwananki a nan ai Gwaggo, ki tashi ki kama hanya. Ke yanzu babu kunya goɗai-goɗai da ke ki wani zo ki tattare a gidan ƴarki? Auren ki ke son kashe min mu haɗu mu durƙushe?"

Gwaggo ta kama baki, abin kuma ya fi ƙarfin ta mayar da martani don haka ta miƙe kawai, ai tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwan kan doka. Tana son ta nemi na mota amma tana shakkar a yaɓa mata wata baƙar sai dai kuma ta sani ba za ta iya jurar tafiya daga gidan nan ba tare da ta tatsi Hajara ba ko yaya. Don haka ta juyo tana ɗan gyara zaman ɗaurin da ta yiwa zanin leshinta a saman riga ganin zai kunce.

"Toh, Allah ya huci zuciyarki dai. Amma a taimake ni da na mota. Kinga goben ma durof zan ɗauko gudun kar su tsaya neman fasinja da Asubar fari mu je mu makara."

Tsaki Hajara ta ja. A fili ta ce.

"Dama idan ba ki tambayi kudi ba ai ba kya ji dadi ba."

Gwaggo dai mamakin yadda raini ya gifta haka tsakaninta da ɗiyar ƙanwarta take. Koda dai, ba a fushi da masu kuɗi wannan ne dalilinta na danne ɗan zafi-zafin da ta ji zuciyarta ta fara ta saka hannu ta kwashe ƴan ɗari biyar sabbi da Hajara ta wurga mata saman ɗan teburin da ke haɗe da gadonta. Godiya ta yi ta fito bayan ta musu wuri a jakarta.

Ko kallon su Waleedah ba ta yi ba ta fice, ita kuwa Waleedah da kallo ta bi ta don ta karanci yanayinta, ta gane kamar ma sun shirya komai ya wuce. Hakan ba ta gasƙata ba sai bayan da Hajara ta fito fuskarta dauke da walwala irin wanda tun zuwansu ba su gan shi a tattare da ita ba.

***
Tunani iri-iri babu wanda bai zo mata ba a kwakwalwa. Idan ka ture wahalar doguwar tafiyar da ta biyewa Gwaggo Atine ta yi, da kuma taka tudu da gangare da ta dinga yi har ba don ma Allah ya kiyaye ba ta kusa faɗawa wani tafkeken rami. Ga raunin da ta ji a ƙafarta dalilin faɗuwar da ta yi dab da ramin. Duka waɗannan ba su ne ke sanya Hajara ji kamar ta shaƙe wuyan Gwaggo Atine a tsakar daji ta kashe ta har lahira ba face saboda rashin nasarar da zuwanta ya haifar. Koda dai Bokanyar ta yi mata ɗan albishir na cewa za ta yi komai don ta ga ta karya mugun sihirin da wancan la'anannen Bokan ya yi mata don ta tabbatarwa Hajara duk inda za ta shiga, aikinta zai matuƙar wahala ya cimma ruwa saboda da baƙaƙen aljanu ya yi wani haukataccen tsafi a kanta. Duk da haka ta dire wa matar kudade da ta ba ta tabbacin shafawa Sadiya baƙin jini a wurin kowane ɗa namiji.

Hajara ta ƙara furzar da huci tana mai duban saitin da Gwaggo Atine ta ke, baccinta take shara tamkar babu wani abu da ya faru. Ta ja dogon tsaki ta kauda kai ta maida ga kallon dajin da suke ratsawa da ko sunan wurin ba ta sani ba.

Ranta a jagule haka ta shigo gidanta don dama ana shigowa cikin garin Kano ta sallami direban da ta ɗauka haya da kuma Gwaggo Atine ta tuƙo motar da kanta.

Motar mijin nata da ta gani a farfajiyar ya ba ta tabbacin ya dawo. Duk da cewa ta san bai ko damu da ina ta je ko za ta je ba, amma sai da ta ji kirjinta ya ba da dam saboda kwananta ɗaya a Adamawa. A zatonta ma yana can Abuja suna harkar kamfen dinsu.

Kai tsaye ta nufi ɓangarenta ta soma da ajiye komatsanta kafin ta fito ta wuce zuwa ɗakin Maigidan. A falonsa ta iske shi zaune yana waya, yadda yake ba da umarnin a yi musu aiki da gaggawa don ganin komai na zaɓensu ya tafi daidai ya sa ta nemi wuri ta zauna ta yi shiru. Har a sannan ba ta gama huce zafin doguwar tafiyar da ta sha zuwa wajen da bai haifa mata ɗa mai ido ba.

"Kin je Adamawa ba ki sanar da ni ba? Tafiyar ta mece ce?"

Da wani irin mamaki ta kalle shi. Tunanin ya aka yi ya sani take? Don ko direbobin gidan ba ta yi amfani da ko guda ba, ita ce ta fice a motarta, suka hadu da wani direban daban da ta dauki hayarsa ta kuma biya shi maƙudai kawai don ya kai ta ya dawo da su saboda ta dauki aikin na sirri ne da ya shafe ta.

Ƴar dariya Alh Nuhu ya yi.

"Oh, kallon sakarai ki ke min ne Hajara? Ko a zatonki ina zaune da ke ba tare da ina gadinki ba? Ai ke ma kin san ba zai yiwu ba. Kin ga nan?"

Ya yi mata nuni da tafin hannunsa.

"Ko me kike yi yana nan ɗina. Babu abin da za ki iya ɓoye min. Ba zan matsa akan lallai sai na san abin da ya kai ki ba. Amma ko sani, ko me za ki yi, ki dinga aikata shi a sirri hakan na da kyau. Ni dai kar ki jawo a ɓatan sunana. Duk abin da ki ke aikatawa ina saka idanu ne don kar ki ƙetara iyakata, ma'ana ki shiga sabgar da ta shafe ni da abokan hulɗata. Shi ne kawai. Sai magana ta gaba, haihuwa nake so. Idan ma kin san akwai wani abin da ki ke sha to tun wuri ki dakatar. Idan kuwa ba ki shirya ba ki faɗa min, zan auro wacce za ta haifar min."

Yana kai wa nan ya miƙe ya kwashi wayoyinsa ya nufi hanyar ɗaki. Hajara ta bi shi da idanu kirjinta na duka fiye da sadda za ta shigo, ba wai fargabarta akan meyasa yake bibiyarta ba ne, wannan ya kau a ranta. Maganar ta haihu ko kuma ya ƙara aure ita ta fi kaɗa mata ƴan hanji. Aure? Dama zai iya tunanin ya auri wata mace bayan ita? Duk irin zantuka da romon bakan da ya dinga zuba mata sadda zai auro ta? Meyasa wai idan ta kalle shi ba ta iya gaggasa mishi maganganu koda ta so hakan? Meyasa wasu lokutan take ɗan jin shakkarsa duk kuwa da cikakken ƴancin da ya ba ta na aikata yadda ta so a rayuwa? Ita ce ma ta ke kaucewa abubuwa da dama, to ai don kudi ta biyewa ruɗin shaiɗan ta ke bin maza a baya, yanzun kuwa ta auri mashahurin mai kudi irinsa na mene ne wani zai burge ta a waje? Dama komai tana yin sa ne don ta samu duniya, ga duniyar a tafin hannunta ai kuma zance ya ƙare. Ranta ta ji yana tafarfasa, ta ji ƙwalla ta cicciko mata, idanun nan sun kaɗa jawur. Ta miƙe har jiri na son ɗibarta, madadin ta shiga ɗakinsa sai kawai ta juya zuwa nata ɓangaren. Kai tsaye firij ɗinta ƙarami dake cikin ɗaki ta buɗe ta fiddo kwalbar abin mayenta da ya yi sanyi rau ta bude a take ta kwankwaɗe. Zama ta yi dirshan babu batun yin sallar Magriba da Isha'i da da ta rasa su a hanya, tana yin sallolinta sai dai dama a kurarren lokaci kuma ma ba a nutse ba. Tana salla ne kamar za ta tashi sama. Wani bin kuwa idan har ta kwanta a gado da zummar bacci, ta tuna ba ta yi sallar isha'i ba, shikenan ta wuce ba za ta tashi ta yi ba.

Tun tana iya lissafo abubuwan da suka ɓata ranta a waɗannan kwanakin, har saboda ƙarfin mayen da ta ke bacci ya yi awon gaba da ita a wurin bayan gama sumbatu iri-iri da tsinewa Sadiya kai ka ce ita ce ummul-aba'isin komai.

***
Mami ta yi shiru tana kallon ɗanta wanda ya ke amsa wayar Husna. Ta dai kula wani abin ta ke son ya taho mata da shi gaba ɗaya ya ba da hankalinsa ga wayar, ya nutsu, irin nutsuwar da za ta iya rantsewa ita da mahaifinsa ne kaɗai suka cancanci irinsa a halitta.

"Mami ni dai jikina yana ba ni Yaya Huzaif ba ƙalau yake ba. Mami ki ga fa yadda ya ke rawar jiki idan suna tare, kalli irin yadda daga ta yi magana ya ke cafewa. Anya kuwa Mami?"

Ta tuno da zancen Meenat a wata rana da Husna da Huzaif din suka zo gaishe su. A lokacin karyata zancen ta yi ta rufe ta da faɗa don a ganinta ta ya ya ma za'a ce wani asiri ne zai ci ɗanta? Kawai dai Meenat din ta faɗa ne saboda ba ta jituwa da Husna tun bayan ƙwacen da ta yi wa Sadiya. A yanzu kuma ta fara dawowa hayyacinta, tabbas ta soma yarda, wata zuciyar na raya mata ko saboda juna biyu ne, amma wani sashin na ankarar da ita akwai gyara a lamarin.

"Mami shikenan zan iya tafiya ko?"

Abin da Huzaif ya furta kenan bayan ajiye wayarsa da Husna. Mami ta girgiza kai cike da tsantsar takaici.

"Huzaif, shikenan fa ka ce? Ina maka zance mai muhimmanci dangane da mai zuwa wurin Meenat saboda Uwarka ta kira a waya ka ke ce min shikenan? Anya ka na cikin hayyacinka? Ko dagaske Husna ta shanye min kai?"

Ya hau kame-kame yana murmushin yaƙe.

"Kai haba Mamina, duk duniya ai babu mai raba ni da ke. Ke ce fa mahaifiyata. To ki yi hakuri. Yanzu me ya rage? Yaron yana da wata matsala ne ko kuwa?"

Yadda ya ƙarasa zancen yana duban agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa ya ƙara wa Mamin nasa takaicinsa.

"Huzaif kana Azkar safe da yammaci? Ka na sallolin dare da karatun Alkur'ani? Anya kuwa ka na tsayawa ka yi addu'ar kirki idan ka idar da sallolinka?"

Tambayar da ta watsa mishi kenan idanunta a kansa har a sannan cike da tsantsar mamaki.

Ba ya yi, ya sani ya mance rabonsa da buɗe littafin Allah ya karanta, ya kuma ma mance rabon da ya tsaya ya yi addu'a wa iyayensa da shi kansa bayan sallar farillah balle kuma ga ayyukan nafilfilu da ba su zame mishi dole ba. Sunkuyar da kai ya yi ya rasa me zai ce.

"Anya Huzaifa? Maganar matarka yanzu har ta fiye maka tawa? Ina magana da kai, ka kasa ba ni nutsuwarka? Soyayyar Husna ta fiye maka tawa?"

Nan ma babu bakin magana, shi bai ce ba, amma ya san yana jin wata muguwar soyayya da shakka ta Husna. Yana ji komai zai iya sadaukarwa dominta. Yana ji har a kasan ransa da ace Husna ce ya hangi ɓacin rai haka a saman fuskarta, sai inda ƙarfinsa ya kare. Amma kuma sai ya ji na Mamin bai wani dame shi ba, bai ɗaɗa shi da ƙasa ba don haka ya shafi sumarsa ya ce.

"Ki yi hakuri." Ita ce kawai kalmar da ya furta.

"Tashi ka tafi kawai, tashi ka wuce kafin matarka ta ƙara kira. Je ka."

Jikinsa ya yi sanyi, ya ji babu dadi amma kuma bai san dalili bai ji zafin sosai ba, yana so ya zauna ya cigaba da ban hakuri da rarrashi, amma ankarar da shi da ta ƙara yi da jiran da Husna ke mishi ya taho mata da gasasshen kifi da take muradin ci, ya sanya shi miƙewa yana fadin.

"Sai da safe Mami.".

Daga haka ya fice bayan ya zura takalmansa, baki buɗe ta bishi da kallo, can kuma ta hau salallami ta ji kwalla sun cicciko mata. Tabbas dole su tashi tsaye da addu'a akan ɗansu, za ta sami Abba da zancen. Kuma ita ma daga rana irin ta yau za ta duƙufa kai wa Allah kokenta. Ji ta yi tsanar Husna na dira a ƙoƙon ranta, da ace ta san haka halayyarta suke, da babu abin da zai sa ta biyewa makauniyar soyayyar da take yi ga Huzaif ta ba shi goyon bayan aurenta madadin Sadiya.

***
Ta tsaya masa a rai, ya kuma rasa dalilin wannan nacin da kwakwalwarsa ke masa da tunaninta alhalin kaf tarihin soyayyarsa babu wacce aka sani a ciki irin Fareeda. Shi kaɗai yake kiɗa da rawarsa, soyayya ce tun suna jami'ar Oxford dake Ingila. Idan ana neman kyau, wayewa da ma ilimi, ka samu Fareeda an gama. Ja mishi aji take yi ba ƙarami ba. Ya kuma yadda ya ji cewa ta kai ta isa a jira ta har ta gama yangar a jajirce a same ta matsayin matar aure. Ya sani ba ta yaudare shi ba, tun a sannan ta faɗamasa akwai wanda take so, ya kuma ji ya amince zai gwada sa'arsa, shi da kansa ya ji ba zai iya haƙura da ita ba. Kusan a kan Fareeda ma ya san soyayya, bai iya ta ba sam. Haka suka kammala karatunsu, ya dawo ya bar ta a can saboda akwai tazarar aji biyu tsakaninsu a makaranta, tsawin shekaru biyun nan kuwa ita yake jira, zuwa yanzu tana sauraronsa sosai. Ta kuma ba shi tabbacin ta yarda ta aminta da tsayar da shi matsayin mijin aure. Ta haƙura da wancan tunda har ya kasa jiranta ya yi aurensa. Wannan albishirin shi ne ya yi wa AbdulMajid da suke kira da Hamma daɗi fiye da komai a duniya. Dalili kenan da ya sanya shi yi wa Baffansu magana kan ya samu matar aure kuma nan kusa za'a kai kuɗi a tsaida rana. Iyayensa sun ji daɗi ƙwarai, ko babu komi aurensa suke matuƙar so su gani sai ga shi bayan Nene ta gama tallata masa yaran dangi, don kansa ya zo musu da magana a kan Fareeda.

A yanzun kuwa bayan Fareeda, ya samu Sadiya. A jikinsa ya ke ji zai iya aurenta koda ace ya rasa zaɓinsa na farko. Bai ma taɓa ganin halittar da bayan Fareeda ya ji ta masa kuma zai iya aure ba irin ta.

Ajiyar zuciya ya saki ya ja guntun tsaki gami da miƙewa daga kwanciyar da ya yi saman doguwar kujerar da ke falon. Daidai lokacin wayar sa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login