Showing 36001 words to 39000 words out of 124441 words
saka kansa ya ji daɗi?
Tana daga tsaye tana wasa da zoben dake cikin ɗaya a yatsanta na hagu ta ce.
"Ina fatan Allah ya shiga lamarin, ya yi mana zaɓi mafi alheri."
Tana kai wa nan da sauri ta juya ta a murmushi ta fice a falon. Ta bar Huzaif da sakin nannauyar ajiyar zuciya a lokaci guda yana zuba uban murmushin da ya fito tun daga ƙarƙarshin zuciyarsa.
"Alhamdulillah." Ya tsinci kansa da furtawa a fili.
*Kazar Kwanci...*
Gaba ɗaya sai ta tsargu ganin uffan Inna ba ta ce mata ba akan jimawarta tare da Huzaif. Zahra ma tare da Inna suna hira, sai ta kasa zama a wurinsu ta nufi ɗaki. Duk sai ta ji kamar ma turaren Huzaif ne ke yawo a hijabinta da sauri ta cire ta yi jifa da shi saman katifa. Ganin hakan ma zai ƙara sanya wa Inna ayar tambaya sai kawai ta yi shahada ta fito tsakar gidan. Zahra sai waƙe-waƙen soyayya na tsokanar ƙawarta ta ke yi, ita kuwa ta fakaici idanun Inna ta watsa mata harara. Ita dai Inna Mairama murmushi kawai ta yi ba ta ce uffan ba. Can ba jimawa sai ga Huzaif ya fito.
"Ah wai har tafiya? Na yi zaton ma za ka jira Malam ya shigo ku gaisa."
Cike da girmamawa ya shafi kansa yana murmushi.
"Na fito Innarmu. Abincinki duk sadda na ci sai na yi santi. Allah ya ƙaro zaƙin hannu."
Dariya Inna ta yi. Ɗakinta ta shiga bayan ta ce ya jira tana zuwa.
Shi kuwa sai ya hau waige ta inda zai ga Sadiya wacce tun fitowarsa ta bar tsakar gidan ta faɗa ɗakinsu. Ya kalli Zahra wacce ke dariya.
"Ki ta ya ni yaƙin nan kin ji?"
Ta zaro ido.
"Har ka soma karaya?"
Ya girgiza kai yana murmushi.
"Aa, amma ina buƙatar wannan taimakon."
"Zan maka iyakar ƙoƙarina kuwa."
Kafin ya ba ta amsa Inna ta fito hannunta riƙe da leda ta miƙa masa.
"Ga wannan ka kai wa yaran gidan. An gode sosai da ziyara."
Ya karɓa cikin ladabi ya ƙara godiya shi ma sannan ya fice bayan ya amsa sallamar da Zahra ke mishi.
Ranar ko daga yanayin annashuwarsa za ka gane ba ƙaramin farin ciki ya ke ciki ba. Koda ya ƙarasa gida, Allah ya taimake shi ya ci karo da yaran a farfajiyar gidan suna wasa da kekunansu. Kai tsaye ya miƙa musu ledar.
"Ga tsaraba daga Inna Mairama."
Zee Mama ce ta karɓe nan suka sauka saman keke aka shiga buɗe ledar da Inna ta cika da kayan ƙwalam.
***
"Na fahimci yaron nan ke ya ke son magana da ita ta waya, idan har saboda ni ki ke kasa amsa wayarsa, to ki sani, ba zan hana ki kula shi ba. Amma kuma kar ki zurfafa soyayya Sadiya. Ba komai muke so ya ke zame mana alkhairi ba. Ki yawaita addu'ar nema maku zaɓin Allah. Idan ku ɗin rabon juna ne, komai zai zo muku da sauƙi. Addu'a koyaushe ina maki ita, ke ma kar ki fasa yi."
Inna na kai wa nan ta fice a ɗakin ta bar Sadiya riƙe da wayarta wacce har ta gaji da ƙara ta yanke. A sanyaye kuma cike da jin nauyi ta kai duba ga wayar karo na biyu sa'ilin da Huzaif ya ƙara danno kira karo na biyu. Ɗagawa ta yi ta amsa da sallama. Ta ji sadda ya sauke ajiyar kafin ya amsa mata.
"Sai yaushe ne? Zuwa yaushe za ki saurare ni ma ji muryarki ki bar wahalar da zuciyata? Sati ɗaya ya rage min a garin nan zan tattara na koma bakin karatuna. Anya kuwa zan jure rashin waya a hannunki? Zan iya jure rashin ƙwakkwarar magana tsakaninmu?"
Ta ɗan runtse idanu kaɗan, sati ɗayan da ya ce ya yi mishi saura a ƙasar Nijeriya, sai ta ji kamar kwana ɗaya yake nufi.
"Ka yi haƙuri. Ina jin nauyin karɓar wayar Inna shiyasa. Amma komai ya wuce."
"Shiyasa zan zo mu yi magana mai muhimmanci, dalili kenan da nake son mallaka maki waya har ma da kaina kafin na bar garin nan. Ma'ana, na kai zancenmu gaban iyayenmu. Idan sun san cewa muna son junanmu, komai zai zo mana da sauƙi."
Idanu ta ɗan fiddo kamar ya na ganinta.
"Bai yi wuri ba Yaya Huzaif? Don Allah ba yanzu ba, ka jira zuwa wani lokacin. Ba na son su Abba su san komai yanzu. Idan dai waya ce, Allah kuwa zan dinga amsa maka. Ka ji?"
Ta ji sadda ya ɗan yi shiru kafin ya ce.
"Zan iya zuwa gobe mu yi magana? Wajenki zan zo, ko gidan ba zan shigo ba."
Ta na wasa da gefen ɗankwalin atamfarta da ya biyo ta wuyanta tana murmushi ta gyaɗa kai tamkar tana kallonsa gami da faɗin "Uhm." Ita ma ta yi kewarsa, kwanaki uku da zuwansa gidan, da ma kafa gwamnatin soyayyarsa a zuciyarta, amma ta na ji kamar sun fi watanni suna tare da juna. Musamman ma da ya kasance yau ɗin ne suka ji muryoyin junansu karo na farko a waya. Duk irin kiran da zai yi ba ta yarda ta ɗaga sai dai ta miƙawa Inna. Shi kuma yana jin nauyin ya ce da Innar ta ba ta. Dole sai ɓige da gaishe gaishe. Sai yau ta ƙara yarda da zancen Zahra da ta ce Inna fa ta san son juna suke yi don ta fesa mata tun ma ranar da Huzaif din ya zo gidan. Dalili kenan da ya sa ta kasa ce mata komai kan maganar.
"Magana za ki yi."
"Na yi ai. Na ce ka na iya zuwa. Amma zan je boko, idan na dawo muna zuwa islamiyya ba ma tashi sai ƙarfe shida na yamma."
"Ok, kenan na shigo bayan Magrib?"
"In sha Allah."
"Nagode."
Bai ja ta da hira ba suka yi sallama. Sai a lokacin ta kula da Husna da ta shigo ta yi mata tsaye a bakin ƙofar ɗaki. Tun soma wayar kusan tana ji, amma ta kasa gane da waye Sadiya ke waya. Gaba ɗaya ta sha jinin jikinta. Fargabarta ya ƙaru da ta yi tunanin ko dai da Huzaif ne?
"Ke kuma da wa ki ke waya?" Ta tsinci harshenta da furtawa tana bin Sadiya da ke faman doka murmushi da kallo.
"Ina ruwanki?" Shi ne amsar da ta ba ta kafin ta fice ta bar ta da bin bayanta da kallo. Gaba ɗaya jikin Husna ya yi mugun sanyi. Ta ji ba za ta iya sukuni idan ba ta ga wanda Sadiya suke wayar ba hakan ya sa ta bi bayan Sadiya wacce ta shiga ƙuryar ɗakin Inna ta ajiye mata wayar a saman dirowar gefen gado. Har karo suka kusan yi yayin da Sadiya ta zo fitowa, ba ta kawo ma ga abin da zai kai Husnar ɗakin ba ta fice ta bar ta. Da rawar jiki ta ɗauki wayar ta buɗe logs. Sunan 'Huzaifa' kamar yanda Inna ta yi saving ya fito ƙarara a saman screen. Ta kasa gasƙatawa har sai da ta buɗo lambar sosai ta karanta. Yanda ta haddace lambar Huzaif din ya sa ta tabbatar shi ɗin ne ba waninsa ba. Ba ta san sadda ta sulale ta zaune gefen gadon ba gami da ajiye wayar jiki a saluɓe. Hawaye masu zafi suka kwaranyo mata. Ashe Inna da Sadiya yaƙin da suke yi kenan? Dama raba ta aka yi da Huzaif ta bayan fage? Shikenan ta rasa farin cikinta? Mutumin da tun sadda ta ɗora idanu a kansa take mutuwar ƙaunarsa?
Wani ƙunci da raɗaɗi suka yi wa duniyarta dabaibaiyi, ta rasa ina za ta tsoma rayuwarta ta ji daɗi. Kawai sai ta share hawayenta saboda ta rasa mafita ban da haƙura da Huzaif ɗin. Me za ta iya bayan son maso wani ta ke yi wanda hausawa ke kira da ƙoshin wahala.
Ranar Sadiya ta yi kwanan farin ciki da walwala a gefe guda Husna ta kwana cike da damuwa mai ɗumbin yawa. A yau ta ji wata irin kewar Antinta Hajara a rai, duk da dama ba gaba ɗaya ta watsar da ita ba, takan amsa maganarta jifa-jifa a whatsapp. Ba su shirya sosai ba sai da buƙatar kuɗi ya taso mata za su haɗa wata fita a ɓoye da kawayenta daga makaranta, a nan ne ta tuna da Hajarar, lokacin ko sati biyu ba ta cika a gidan aurenta ba. Hajara har dariya ta yi har da cewa ita ta san koda kowa zai yi fushin duniya da ita, to fa babu Husnar a ciki. Har ce mata ta yi ta zo gidanta amma ta yi fuska don ba ta gama hucewa da ita ba. Sai dai a halin da ta shiga na yau babu wacce ta ke kewa sama da ita. Abin da kwakwalwarta ke ba ta game da lamarin Sadiya da Huzaif bai wuce cewa haɗin bakin Innar da Sadiya ba ne. Watakila ma yabawa da hankalinsa Inna ta yi hakan ya sa ta jona shi da ɗiyar da ta fi ƙauna a yaranta.
Cikin bacci Sadiya ta ji sheshsheƙar kukan Husna, zumbur ta miƙe tana salati gami da ɗan mirgino da ita. Husna ta share fuskarta ganin Sadiya ta yi amfani da wayar Inna da ke hannunta ta haska mata fuska.
"Innalillahi... Husna, lafiya? Mene ne ya same ki?"
Sai ta ɗauki tambayar a matsayin na rainin wayo tunda ai ido ba mudu ba ya san kima, ko makaho ya laluba zai gane tana son Huzaifa amma tsabar mugunta irin nasu sun rufe ido sun kasa ganewa daga yanda take ta zancensa da ma yawan hira da take yi da shi ta waya.
"Ki rabu da ni, kaina ke ciwo. Amma na sha magani."
Sadiya ta numfasa, ta sani a irin sangartar da Anti Hajara ta yi wa Husna, hatta idan tana ciwo takan ɓata dare wurin lallaminta koda ciwon bai taka kara ya karya ba ita kuwa ta yi ta shagwaɓe mata.
"Sannu, Allah ya sa kaffara. Ki daina kukan, ba zai ƙara maki komai ba face zafin ciwo. Ki yi addu'a ki kwanta." Haka kawai Sadiya ta ce mata sai ta juya ta gyara kwanciyarta bayan ta kashe fitilar wayar Inna, dama mafi yawan lokuta a wajenta take kwana, musamman yau ɗin kuma da suka ɗau lokaci a daren su na waya da Huzaif wanda silar hakan ne ya sa hankalin Husna ƙara tashi, ta kasa jurewa a daren sai da ta yi kukan ta samu sassauci.
Dakyar bacci ɓarawo ya sace Husna a wannan daren. A ranta ta zagi Sadiya ya fi sau cikin carbi, har da su Allah ya isa akan ta raba ta da abin da ta ke so.
***
Washegarin ranar da safe Inna ta kasa haƙuri musamman jin cewa Huzaif zai zo hira wajen Sadiya, ta ga dacewar ta sanar da Malam gudun abin da zai je ya zo. Dalili kenan da bayan Malam ɗin ya kammala karin safe ta sanar da shi batun zuwan Huzaif wajen Sadiya a ranar. Malam cike da rashin fahimtar inda zancen ya dosa ya ce.
"Ban fahimta ba Mairama, wajen Sadiya? Son ta yake yi?"
Inna ta yi murmushi.
"Ni ma ban sani ba Malam. Amma ina tunanin haka."
Ai sai ya faɗaɗa fara'arsa.
"Kai Alhamdulillah. Idan kuwa hakan ya tabbata zan fi kowa farin ciki. Kin san kuwa Alh Abubakar da kansa sai da muka yi zancen nan kwanaki? Ya ce ba don yaran zamani da ba a yi musu dole ba, ai da ya nemawa Huzaifa auren ɗaya a cikin ƴanmatan nan. Muka yi dariya, har na ce to ko hakan za'a yi. Ya girgiza min kai ya ce ba zai so a aikata hakan ba, zai zama kamar dole muke son yi wa yara, mu bari dai Allah ya yi ikonsa. Idan da rabo sai mu ga ya kasance. Ashe kin ga rabon kan Sadiya zai faɗa."
Inna da har lokacin murmushi ta ke yi ta jinjina kai.
"Ai shikenan, Allah ya tabbatar da alheri." Malam ya amsa da amin bar yana cewa shi zai fara yi wa Amininsa albishir.
Misalin ƙarfe takwas sai ga wayar Huzaif, Sadiya na ɗagawa ya ce mata ya zo yana ƙofar gidan. Husna na kallonta ta hau shiri cikin doguwar rigar abayarta baƙa mai adon ruwan madara a tsakiya. Ta zagaye fuskarta da mayafin abayar, hoda kawai ta shafa da man leɓe. Ta yi tsai tana kallon yayarta, ta sani dole ne dama Huzaif ya zaɓi Sadiya sama da ita. Ta saka a ranta hakan ya faru ne saboda kyawun da Sadiya ta fi ta. Ita kanta ta ga kyan balle kuma a kai ga maza masu cikakken lafiya waɗanda don su aka halicci matan. Ta kauda kai tana ji zuciyarta na tururi. Kamshin humrar da Sadiya ta shafa ya buɗaɗe ƙofofin hancin Husna, kawai sai ta maida kai ga wayarta tana cigaba da dannawa amma fa idanunta cike suke taf da ruwan ƙwalla don ko ganin abin da ke saman screen ɗin ba ta yi.
Sadiya ta dube ta, kamar ta yi magana saboda ta kula da yadda Husnar ke faman basar da ita tun wayewar gari tana cin magani. Ba ma ga ita kaɗai ba har ga Inna. Babu dai wanda ya ce mata uffan. Ta ɗauka Husna za ta ce wani abu ko kuma ta tambayi wajen wanda za ta fita amma ganin ba ta ce uffan ba ta basar sai ita ɗin ma ta ɗauke kai ta zura takalmi ta fice.
A wannan daren Huzaif da Sadiya suka ƙara ƙulla soyayyarsu mai tsafta. Har Malam ya gan su ya kuma ce daga ranar ko Huzaif din ya zo su dinga shiga falonsa wanda anan ya ke saukar baƙi. A cewarsa shi ɗin ba baƙo ba ne. Har addu'a ya yi musu kan Allah ya tabbatar da alkhairi. Babu abin da ya ruɗa Sadiya irin da ta ji Malam din ya ce zai samu Abba su yi magana. Ta kasa ɓoye tsoronta har sai da Huzaif ya lura, sai ta ba shi dariya ma.
"Kina tsoron me? Har yanzu ki na kokwanto a kan son da nake maki ko kuwa wanda ki ke min?"
Tambayar da ya watso mata kenan, ta girgiza kai kamar ta yi kuka ta ce.
"Ya yi wuri fa. Likita nake son zama."
Dariya ta ba shi sosai. Aikuwa ya hau darawa har sai da ta ɗan yi turus don a ganinta ba ta abin dariya ba, iyakar gaskiyarta ta faɗa masa. Girgiza kai ta yi.
"Yaya Huzaif ko Waec ban yi ba."
"Yaya Sadiya ko kammala karatuna ban yi ba. Ki na zaton Abba da Malam za su ɗauke ki su ba ni? Kin fi ni gata ga a wajensu."
Yanayin kwaikwayon muryarta da ya yi sai ya ba ta dariya. Gaba ɗaya suka dara a tare.
"Ki saka ranki a inuwa please, babu wanda zai min wannan gatan na aura maki Huzaif a yanzu a shiga haƙƙinki. Kin ji ko?"
Murmushi kawai ta ke ba tare da ta ce uffan ba don sai daga baya ne ma ta ji kunya.
"Oya mu yi magana, karatun likita kike son yi?"
An sosa mata inda ke ƙaiƙaiyi.
"Eh."
Ya jinjina kai.
"Field ɗaya muke da ke. Ni ma da zarar na koma zan haɗa degree ɗina na MBBS. Zan tattara na dawo gida in sha Allah. Nan da watanni ƙalilan."
Ta murmusa. A nan ya gane inda aka fi samun bakin Sadiya, a hirar da ya shafi karatu. Sosai ta zage ta na ba sa labarin karatu da yanda ta ke burin zama likitar mata. Shi kuwa ya maida hankali ya ba ta nutsuwarsa gaba ɗaya yana ƙaremata kallo yana murmushi. Har a ƙarshe ta ji kunya ta yi shiru. Ta ji sadda ya sauke ajiyar zuciya.
"Ina ƙaunarki sosai, zan yi kewarki idan na tafi."
Ta kasa amsa mishi sai ta ji duk babu daɗi, ita kanta ya shiga ranta ta yanda ta ke jin za ta yi kewar tasa har fiye da yanda zai yi nata.
Sun jima tare kamar kar su rabu. Haka ta shiga gida ranta fari ƙal tamkar an mata albishir da sauke farali.
***
©Rufaida Umar
*Kazar Kwanci...*
Mamin Huzaif ta yi mamaki ƙwarai hakanan ta yi farin ciki marar misaltuwa jin cewa Huzaif na son Sadiya. Ita tun daga yanayin haƙuri na Inna da ma abubuwan da ta ganewa idanunta sun faru lokacin bikin Hajara, ta ji har a ranta tana kwaɗayin haɗa zuri'a da mai halin haƙuri da kauda kai irin nata. Ta jima tana jinjina lamarin da ya faru a gidan don ta sani da ace a kanta ya faru to ba lallai ta cigaba da rayuwa a gidan ba. Hatta Hajara ta sha faɗa sosai don har fushi ta yi da ita daga baya kuma ta sauko ganin yadda ta dinga nacin kiran waya da ban haƙuri.
"Kin yi shiru Mamin yara, ba ki ce komai ba."
Maganar Abba cikin fara'a ya katse mata tunani. Shi kansa a jiya da yake jin zancen daga Malam, kuma ya ƙara samun tabbaci a bakin Huzaif ɗin, ba ƙaramin farin ciki ya shiga ba. Allah ya sani amintarsu da Malam ta kai inda wani ma ba ya tunani, don haka ba ya shakkar haɗa zuri'a da shi. Ya ɗauki abin da Hajara ta yi matsayin kuskure da ruɗin shaiɗan. Kamar yanda shi ne ya duba roƙon Hajarar ya yi tattaki har wurin Malam a babban gida aka hadu da manya aka naushe shi, aka kuma nemi ya yafe mata ya cire takunkumin hana ta zuwa gidansa.
"Allah ya tabbatar da alheri. Abin ya yi min daɗi ƙwarai."
Abba ya sauke ajiyar zuciya gami da hamdala a fili. Ya amsa da amin.
Su Radeeya da Lubna koda suka ji su kansu sun yi murna da kuma fatan alkhairi. A cewarsu Sadiya yarinyar kirki ce ga uwa uba tana da nutsuwa. Huzaif ya rasa ina zai saka ransa don farin ciki.
***
Amarya Hajara koda ta sauka a Nijeriya bayan dawowarsu daga Umarah, gidan Safiyya ta fara yi wa tsinke. Safiyya hangame baki ta yi kawai tana kallon yanda kuɗi suka zauna a jikin ƙanwarta. Ta ƙara ƙiba, fatarta kuwa sai ƙyalli ta ke yi. Ga haƙorin Makkah da ta sanya.
"Wai ni wannan kallon na mene ne?"
Faɗin Hajara tana dariya. Safiyya sai lokacin ta sauke ajiyar zuciya gami da murmushi.
"Ai dole na kalle ki Autar Mama, kin ga yanda ki ka zama ne? Ni