Showing 6001 words to 9000 words out of 124441 words
Anti Hafsatu ma ta nuna goyon bayanta, karshe mazan suka mike zasu wuce, cikin zolaya Baba Habu ya dubi Safiyya da Hajara.
"Toh, Safiyya gwara ke kin ma kusa barin gidan abinki, ke kuwa Hajara sai ki shirya tarbar sabuwar Mommy. A kuma yi mata biyayya ba ƙaƙƙautawa."
Aikuwa ta ƙara tunzura ta fashe da wani sabon kuka tana fadin ita wallahi ba ta isa ta kirata da sunan Mommy ba. Haka yana dariya ya fice ya bi bayan ƴan uwansa. Anti Hafsatu kuwa ta dubi Hajara wacce kukanta ya soma kai ta bango.
"Malama ki yiwa mutane shiru haka. Wannan ai hauka ne da rashin hankali, shikenan haka zai zauna babu aure? Idan kin ga dama ki yiwa kanki faɗa ki rungumi ƙaddara don auren Malam babu fashi, idan kuwa kin ƙi sai ki zauna ki yi ta fama da ciwon zuciya tunda ba ki isa ki dawo da abin da yake dama can aronsa Allah ya bamu ba."
Wannan ne dalilin shirun Hajara ta miƙe tana kunkuni ta shige ɗakinsu. Safiyya kuwa ta dubi Anti Hafsatu da mamaki.
"Wai Anti Hafsatu ba kya jin zafin da muke ji a zuƙatanmu dangane da wannan lamari?"
Harara Anti Hafsatu ta doka mata tana mai kunce goyon ɗanta Daddy dake bayanta wanda ya ishe ta da kuka.
"Zafin me zan ji? Ku yanzu kun fi kaunar Malam ya dauwama a haka babu aure? Ba kwa la'akari da cewa kuma aure za ku yi ku bar gidan? Ai idan ita Hajara ta yi wannan wautar ke bai kamata ace har da ke ciki ba. Yaya Mustafa ma sun ba ni mamaki don na tabbatar su kansu ba wani murna suke da hakan ba. Amma kar ku manta, muddin kuna kaunar Malam dagaske, toh taya shi son abin da yake so shi ne mafi dacewa a garemu baki daya."
"Tabɗijam! Shikenan ai, ya yi auren amma wallahi nidai babu abin da zai taɓa haɗa ni da matarsa. Har gobe ba da za ta taɓa maye mana babban gurbin da muka rasa ba a rayuwarmu."
"Ku kuka sani. Aure dai babu fashi da yardar Allah." Daga haka ba ta ƙara tankawa ba, karshe ma Safiyya sai ta mike ta nufi dakinsu don su kara jajantawa juna ita da Hajara.
***
Ranar juma'a aka ɗaura auren Mairamu da Malam Sa'ad bayan saukowa daga sallah. Aka bar tariyarta nan da sati daya bisa alfarmar da Malam ya roƙa don ya ƙarasa gyaran gida saboda a satin da ya wuce bai samu aikata komai ba dalilin tashin hankalin da hakan ya haifar a gidan. Inda Hajara da Safiyya suka yi ta faman kuka su Hajara har da kwanciya ciwo yayinda Safiyya ta tayar da iskokai su fa a dole Malam ba zai ƙara aure ba. Sai da babban yayan Malam ya tsawatar kafin su nutsu, dama abin nasu har da zuga inda facalolin Mama da kuma yan uwa suka dinga tada jijiyoyin wuyar ba haka ba. Musamman ma zawarawan da suka saka rai Malam din zai auri daya a cikinsu.
Sai lokacin ya samu sararin fenti. Gidan dakuna biyar ne, daya mai ciki da falo na Malam ne sai ko falle biyu wanda a baya Asma'u ta maida daya daki dayan kuwa falo, sai ko daki daya na yanmatan yaran. Sai shago a waje na samarin gidan. Babu laifi akwai wadataccen tsakar gida har da ɗan shuke-shuke a gefe daya zagaye bangon tsakar wajen da kuma famfo da aka zagaye wajen da tayil inda ake wanke wanke. Gidan ma dai duka tayil ne a ƙasan.
Ranar da Mairamu za ta tare, daga ita sai yan uwanta hudu, matar dan uwan maihaifinta da suke kira Dada sai kuwa yaran Dada mata uku, sai makwaftansu mutum biyu. Kwanansu uku suna kwasar amarcinsu, sai da ta yi sati ko ƙeyar ɗansa ko ɗaya ba ta gani ba, lokacin Zakari ya tafi bautar ƙasa a Yobe. Hajara da Safiyya kuwa sun koma sun tattare can babban gida wurin dangi tsabar baƙin ciki da takaici. Sai da suka yi sati biyu cif kafin su waiwayi gidan. Gani suka yi ma ai dama suka bayar da Mairamu za ta ci karenta ba babbaka a gidan Mahaifinsu, gwara su zo a yi komai a gabansu.
***
Mairamu na zaune ta kammala suyar kifin da Malam ya kawo na miya, sai kawai ganin mutane ta yi sun faɗo kamar an koro su babu ko sallama har sai da ta ɗan razana. Suka yi tsaye cak su na ƙare mata kallo da kuma bin kifin da ke cikin mai yana soyuwa da idanu, sai kuma suka saki dariya gami da cafkewa.
"Wasssh! Babu a house! An samu na bati!" Fadin Safiyya, suka ƙara tuntsirewa da dariya. Ita dai Mairamu kallonsu kawai take, ko ba a faɗa ba ta san wadannan yaran Malam ne don ta ga tangameman hoton family da suka dauka wanda ke manne a falon Malam.
Ta yi kamar ba ta ji furucinsu ba, da ɗan murmushi saman fuskarta ta ce.
"Ah Safiya ku ne tafe? Sannunku da zuwa. Ku shiga ciki."
Suka watsa mata harara, cike da tsiwa Safiya ta ce.
"Ai ba sai kin ce mu shiga daga ciki ba Mairamu tunda gidan ba na uban wani ba ne."
"Atoh." Hajara ta karɓe. Inna Mairamu ta tauna maganar a ranta, ba ta ji zafi sosai da kiranta da sunanta na ainahi da budurwar ta yi ba kamar zagin ubanta da ta yi. Daga haka ta ɗan yi murmushin yaƙe ba ta ƙara cewa uffan ba ta cigaba da aikin dake gabanta. Tana kallo suka faɗa ɗakin da dama mallakinsu ne, a gyare yake tas don Inna Mairamu mace ce da ba ta son ƙazanta da ƙura, hakan yasa duk bayan kwanaki biyu take shiga ta gyara shi, Malam kan ce ta bari tunda babu mai kwana a dakin amma ta nuna masa babu komai ta san watarana za su zo. Ba kuma ta son su tarar da wurin kaca-kaca. Yakan yi murmushi cike da jin dadi, wato dai ta nunawa nasa kulawa.
Shinkafa da miyar kifi ta yi sai kuwa ruwan shayi na Malam wanda ya zame masa jiki sai ya wuni yana sha idan yana gidan. Ganin haka yasa har ƙaton filas dinta na shayi take cikamasa ta sanya masa a mota ya wuce da shi kasuwa.
Ta kai babban farantin da ta shiryawa mijinta abinci zuwa falonsa ta ajiye sannan ta fito da zummar daukar filas na shayi, turus ta tsaya ganin Hajara ta dauki faranti ta zuba shinkafa tili guda ga miya da kifi nasha-nasha a sama. Suna hada ido Hajara ta watsa mata kallon tara saura tana turo baki gami da fadin.
"Ai dai tunda Ubanmu ne ya yi cefanen babu wata da ta isa ta hana mu ci."
Ɗan murmushin da bai kai zuci ba Inna ta yi.
"Hajara kenan, ko ba ki yi haka ba dama ku din nake niyyar ɗibarwa. Sannan eh Babanku ne ya yi cefane, amma kinga tunda ni na girka ina da iko akan tukunyata ko?"
Hajara ta ɗaga kafaɗa.
"Oho dai, ko me za ki ce ba zan fasa abin da nayi niyya a gidan nan. Kema din arzikin ubanmu kike ci, ban da haka ko ƙayar kifi sai ki shekara ma ba ki gani a kwanonki ba!"
Tana kai wa nan ta kaɗa kai ta yi ciki, can kuma ta dawo daidai sadda Inna Mairamu ke kokarin juye ragowar miyar a wani karamin filas dinta, hannu ta kai da zummar ɗaukar ruwan zafin dake cikin filas, caraf Inna ta riƙe hannun gami da ɗauke filas din.
"Wannan dai na mahaifinku ne. Idan sha kike son yi, ki bari idan ya dawo ya yi amfani da shi sauran ki ɗiba."
Hajara na huci take bin Inna da kallo kamar ta tofa sai kawai ta yi ƙwafa ta koma ɗaki.
Sai da aka soma kiraye-kirayen sallar Magriba sannan Malam ya shigo gidan. Inna na bandaki tana alwala, Hajara suka tarbe shi da oyoyo kai kace wasu yara ne ƴan shekaru goma shima ya yi farin ciki da ganinsu duk da daman sai da ya je can babban gida kai musu tsarabar kasuwa ya ƙara lallashinsu akan su dawo gidan ya iske sun ma taho. Da wannan murnar suka karɓi ledojin hannunsa zuwa cikin falonsa. Koda Inna ta fito sai kawai ta yi dakinta sanin da ta yi shima Malam din masallaci zai nufa. Sai bayan ta idar da sallah ne ta dan yi lazimi, ba ta kai ga idarwa ba ta ji Malam na faman kwalamata kira har kafin ta fita ya banko labulen ɗakin nata ya shigo. Suka yi kiciɓus bayan ta shafa addu'ar da ba ta kai ƙarshensa ba kirjinta har dukan tara-tara ya shiga yi domin dagaske dai ta tsorata da wannan kiran.
"Lafiya? Sannu da dawowa." Shi ne abin da ta tsinci bakinta da furtawa lokaci guda. Bai ko amsa ba cikin ɗaure fuska ya hau fada ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba kamar wanda aka jonawa batiri.
"Ni bana son haka, daga dawowar yara har kin fara hana su abinda Ubansu ne ya kawo? Ba ki ba su abinci ba, don kuma sun nuna su na da buƙatar shan ruwan shayina kika ce ai ba su kika dafawa ba? Mairamu duk abin da nake kawowa gidan nan ba nawa ne ni kadai ba, na iyalina ne, bana son haka. Kin jefa zuƙatunsu cikin kewar mahaifiyarsu, wato kin soma nuna gazawarki a taya ni rikon amanarsu tun a yau da kika soma sanya su a idanunki. Kar ki bani kunya mana!"
Daga haka ya sa kai ya fice a gidan. Inna Mairamu ta kasa motsa koda yatsa balle ta bi bayansa. Wasu ruwan hawaye masu ɗumi suka zubo saman fuskarta, ta shiga ambaton sunayen Ubangiji a cikin ranta. Lallai ta su da wadannan yanmatan ba za ta zo ɗaya ba. Tun yanzu? Tun ba a wuni tare ba sun soma ƙulla mata zarurrukan sharri? Ta sauke ajiyar zuciya, ta daurewa zuciyarta har aka yi sallar isha'i sannan ta fito zuwa falon Malam din. Yana zaune su Hajara na gefensa suna hira da dariya. Sallamarta ya sanya suka haɗe rai gami da amsawa ciki-ciki saboda ganin idanun Malam. Shi kuwa wani irin mutum ne marar riƙo, yanzun zai yi faɗa amma zuwa wani lokacin sai ya manta bar shi dai da daukar magana. Ransa ya dan yi sanyi musamman ganinta cikin ado kamar koyaushe. Murmushi ya yi itama ta mayar masa da martani. Ta nemi wuri ta zauna. Safiya ce ta soma mikewa ta bar falon ranta a jagule ganin haka itama Hajara ta bi bayanta. Malam ya bisu da kallo hakanan Inna Mairamu wacce ta ke musu kallon mamaki na yanda har babu kunya ba tsoron Allah suka haɗa ta da mijinta akan laifin da ba ta aikata ba.
"Don na maki magana wato shi ne ko ki zo ki ba ni abinci ko?"
Ya furta, kai ka ce ba shi ya gama sababin an taɓa yaransa ɗazu ba.
"Ba haka bane, sallah na tsaya nayi. Akan abin da ya faru kuma ina mai ba ka hakuri. Nidai har ga Allah na sani ba zan iya cutar wata halitta ba balle kuma jininka, yaranka ai nawa ne. Ina mai ba ka hakuri bisa abin da suka ce na aikata, sai dai don Allah idan ranka ya ɓaci ka bar saurin yanke hukunci akan magana har sai ka ji daga bakin mutum. Mai yiwuwa kuskuren fahimta ne."
Ya numfasa.
"Shikenan, dama na sani za ki riƙemin amanar ƴaƴa, kawai dai yanayin da na gansu ciki ne ban ji dadi ba. Kin san ba ƙaramin shaƙuwa suka yi da mahaifiyarsu ba, wannan ne dalilin da ya sanya sai a hankali za su saba da ke. Kema kuma ki dinga kokarin jansu a jiki, in sha Allahu za ku ji dadin zama da juna domin yaran ba su da matsala."
"Uhum." Shi ne iyakar abin da ta ce haɗi da ɗan murmushi ba don ta gamsu ba, tun a yanzu ta hango matsalarsu, ta kuma san ba ƙaramin abu za ta fuskanta a zamanta da su ba. Ya shiga jan ta da hira karshe ta watsar da zancensu itama ta sakarwa mijinta tamkar wani abu bai faru ba.
***
Kamar dai yanda Innar ta yi zato hakan ne ya kasance, fitsara da rashin kunya iri-iri haka ta dinga cin karo da su a wurin Safiyya da Hajara. Ko tsinke ba sa kawar wa a gidan sai dai idan ta gyara su ɓata. Sai sun tabbatar ta yi shara sannan za su share nasu ɗakin madadin a kai kwando a zubar sai dai a watso tsakar gidan, ranta kan ɓaci sai dai kawai ta kai zuciya nesa. Abinci kuwa sai a faki idonta su ƙara uban gishiri a cikin nasu kason, idan Malam ya dawo su hau kukan munafurci su ce wai kashe su Inna ke son yi.
Ganin haƙansu na cimma ruwa, Malam din na yarda da su ɗari bisa ɗari idan sun faɗi laifin Inna, ya sa duniyar ta ke gara musu sosai yadda suke so. A haka watarana Safiyya ta kimtsawa Hajara sharrin da ya dace su yi ga Inna wanda take da yaƙinin idan haƙansu ya cimma ruwa to zai wahala auren Inna da Malam bai zo ƙarshe ba.
"Amma kina ganin zai sake ta? Nifa sai naga kamar yana sonta." Cewar Hajara bayan gama sauraron ƙullin da Safiyya ta ke son su aiwatar akan Inna. Safiyya ta ja tsaki.
"Wane so? Ke kike ganin hakan. Malama ba wani sonta da yake yi kawai dai yana maneji ne. So ai ya ƙare a kan Uwarmu. Duk wacce za ta biyo baya kuwa, sai dai wani sunan amma ba so ba. Ke dai kawai ki yi abin da nace, ni na tabbata yau kwanan Mairamu ya ƙare a gidannan."
Suka yi dariya har da shewa.
*©Rufaida Umar*
https://arewabooks.com/book?id=663894ac767a55b1dd421f6a
***
*Kazar Kwanci...*
*Ƙarshen free page*
07
A ranar wata Asabar abin ya faru, hadari ya haɗu sosai a garin, cikin gaggawa Inna Mairamu ta kammala girkinta a gawayi ta kashe ta gyara wajen ta tattara gidan tas, abin rufewa ta rufe, na killacewa ma haka. Sai da ta kai komai ɓangaren Malam kamar yanda ta saba tunda hatta su Hajara sun koma ci tare da shi idan ya dawo hakan yasa ba ta ware musu. Malam din ma ya ce ai ya saba al'adarsu ce tun Asma'u na raye sukan haɗu da yaransa su ci abinci wannan ne dalilin da ba ta karambanin zuba musu daban. Na almajirinta Lurwanu ma sai da ta ajiye mishi a kicin duk da ba ta zaton zai samu ɓullowa sakamakon yayyafin da aka fara kaɗan-kaɗan. Ban da kiɗa babu abin da ke tashi a ɗakin su Hajara, ita ba ta nan ma ta je makaranta sai Safiyya a gidan amma ko leƙe da sunan taya Innar aiki.
Ita dai ɗakinta ta shige bayan ta ɗaura alwala ta ja ƙofa ta rufe da zummar ɗan kimtsawa kafin Malam ya shigo gidan. Tunaninta gaba ɗaya yana kan Hajara, ko ya ya za ta yi da ruwa? Sosai take jin damuwa akan haka tamkar ƴar cikinta. Ta kasa jurewa ta fito ba ta damu da ruwan da ya soma ɗan ƙarfi ba ta shiga ɗakinsu. Safiyya tana ta danne-dannenta a wayarta tana faman hira a 2go ba ta ma ji sallamar Innar ba sakamakon kiɗan da ya cika dakin. Inna ta ƙarasa ta ɗan bubbuga ƙafarta ta kuwa yi zumbur ta miƙe tana huci, ganinta ya sanya ta jan tsaki gami da kashe rediyon.
"Mene ne haka za ki tsorata ni?"
Inda sabo ya ci ace ta saba don haka ta shanye tambayar ta shiga magana.
"Ki kira Hajara ki ji tana ina? Ni ba kati a wayana. Ga ruwa nan ya fara ƙarfi kar ya yi mata illa a waje."
Safiyya ta harare ta.
"Ji? Sai ka ce damuwar ki ka yi dagaske. Uhum, ta ciki dai na ciki na sani. Toh Hajara ta cemin gidan Anti Hafsatu za ta kwana kuma ta sanar da Malam ma."
Inna ta ɗan yi shiru, sai kuma ta amsa da shikenan daga haka ta fice ta bar ɗakin. Safiya ta bi ta da wani murmushi na zallar mugunta. Ba ƙaramin daɗi ta ji ba da abin ya zo musu a daidai, wato sun shiryawa Inna tuggu, sai kuma ga ruwa Allah ya kawo. Shakka babu abin zai ba da citta sosai. Ta dannawa Hajara kira, bai yi ko ƙara uku ba ta ɗaga. Ƙasa-ƙasa ta soma magana.
"Ke ya ake ciki? Kin ga Allah ya na sonmu, ga ruwa ya sauka yanda komai zai fi tafiya daidai ko?"
Tana jin sautin dariyar Hajara ita ɗin ma taya ta tayi.
"Ke dai bari ƴar uwa. Ni kaina ina ganin yanda hadari ya haɗo na ji wani sanyi a raina. Faɗuwa ta zo daidai da zama."
Suka yi dariya. Safiyya ta ƙara da cewa.
"To ina Yusuf din? Ku na tare ko? Kin ƙara masa bayanin komai?"
"Yes, ba mu da matsala da shi. Ya san abin da zai yi. Ina fatan wayar tana hannunki?"
Safiyya ta gyaɗa kai.
"Ai dole. Shashashar ba ta ko yi cigiya ba kin san fa babu dangin da za su neme ta."
Daga haka suka ƙara darawa sannan suka yi sallama. Safiyya ta yi wata ƙwafa kafin a fili ta ce.
"Yau Mairamu za ki kwanan gidanku."
Ana cikin sallar isha'i Malam ya shigo gidan da sauri-sauri ya faɗa ɗakinsa. Kayansa har sun ɗan jiƙa. Inna ta ji shigowarsa amma kasancewar ta tayar da sallah ya sanya sai da ta idar kafin ta nufi falonsa da sallama ɗauke a bakinta, ta tabbata ruwan ne ya tsaida shi har isha'i. Lokacin ruwan ma ya tsagaita sai iska mai karfi da yayyafi, sai ko rugugi da ke nuni da har lokacin akwai sauran ruwa wanda idan Allah ya nufa zai iya zuba a kowane lokaci.
Ganinsa a tsaye da waya a kunne ga Safiyya durƙushe a gabansa tana wani irin kuka mai tsuma zuciya ya sanya kirjin Inna bugawa da ƙarfi, a fili ta kira sunan Allah kafin ta dubi Safiya karo na biyu san nan ta maida duba ga Malam.
"Lafiya? Meyafaru?" Ta furta hannunta a saman ƙirji don sosai ta tsorata. Tunaninta ya fi karkata kan ko wata mutuwar ce aka yi. Malam bai ko kalleta