Showing 105001 words to 108000 words out of 124441 words

Chapter 36 - Kazar Kwanci Hausa Novel Complete

za ki samu matsala da ita ba. Yanzu duk ba mu isa yankewa kowa hukunci ba sai zama ya yi zama. Ki fidda komai a ranki."

Sadiya ta yi ɗan murmushi sannan ta jinjina kai ba ta ƙara cewa komai ba, amma tabbas jikinta na ba ta cewa ba ta samu karɓuwa a wurin surukarta ba yadda ta samu a wajen sauran matan Mai Martaba musamman Haj Saratu da suke ɗakinta.

Su Safiyya ba su ne suka iso ba sai dab da sallar Magriba. Su ma nan suka sauka amma ɗakinsu daban shi ma babba, su kansu sun jinjina irin tarbar arziƙi da aka yi musu. Zahra kamar ta shiɗe don farin cikin wannan daular da Allah ya jefo ƙawarta a ciki. Ranar dai kusan raba dare aka yi hira ya yin da tuni Zahra ta shiga IG tana kallon bidiyon da tuni ya yaɗu na Sadiya a cikin alkyabba. Wannan ba ƙaramin ɓata mata rai ya yi ba. Kamar jira ake yi har an ɗora ta? Kuma ma har da fuskarta a waje? Toh amma ya za ta yi tunda ba ta ma san ko aikin waye ba, kuma koda ta sani ina ta ga ƙarfin cewa wani abu?

***
Misalin ƙarfe tara da mintuna na washegari Litinin, Hajara da Husna suka iso. Anti Hafsatu wacce suka yi waya da Khamees ta sanar mishi da zuwan nasu, tuni ya aika mota can a yi jiransu. Suna kuma zuwa, aka shaidawa direban, ta hanyar waya ya gane su ya ɗauko su. Tun daga motar Hajara ta san an zo wajen. Sadiya ta samu duniya yadda ya kamata. Husna kuwa bakinta ya ƙi rufuwa tana rungume da Sadik da ke bacci tana bin hanya da kallo kamar ta yi fiffike ta gan ta cikin masarautar a gefen yar uwarta.

A fakaice Hajara ta watsa mata harara gami da jan tsaki a zuciya.

'Banza marar zuciya. Maimakon ta yi bakin ciki ba ita ce a wannan matsayin ba, sai faman rawar jiki ta ke yi.'

Ta ayyana a ranta. Babban dalilinta na zuwa bai wuce abu biyu ba. Ta wanke kanta a wurin dangi daga zargin tana yi wa Sadiya hassadar da aka fara mata saboda lura da yanayin ficewarta a gidan ba a hayyaci ba ranar da aka ɗaura auren. Sai ko ganewa kanta muhallin Sadiya, har yanzu ganin komai take kamar a mafarki, za kuma ta so ta ganewa idanunta. Ta san Inna na can ta a farin cikin ta aurar da duka yaranta da ƙuruciyarsu. Ta kuma sani Sadiya ta taka sa'ar da Husna ba ta kama ko ƙafarsa ba. Wannan baƙin ciki da shi za ta mutu. Sai dai ta yi rantsuwar gallazawa Inna, ta ci alwashin sai ta zama abar tausayi. Gwara su biyun duka ta yi maganinsu ta haɗa musu zafi ta ko'ina. Zai fi kyau da ta zo Gomben da kanta don gane ta inda za ta fara ƙulla zaren makircinta.
Wani irin gumi ne ya shiga tsastsafowa Hajara tun daga irin yadda bayi suka shiga zubewa a sashen Haj Saratu su na gaishe su. Ga uwa uba daular da aka narka a falon.

"A yi musu jagora zuwa Gimbiya  Sadiya."

Wannan laƙabi na girma da aka jingina sunan Sadiya da shi ya ƙara tayar da hankalinta. Dama ta san a rina, wai an saci zanin mahaukaciya. To amma ai ta gama ayyana dukkan hakan a rai bai kyautu ace ya mata zafi kamar haka ba. Abu ne da ta kwana da sanin jin fiye da shi idan sun zo. Haka ta daure da yaƙe saman fuskarta suka bi bayan baiwar don dama akwatinsu na kaya ya riga su yin gaba.

Su Anti Hafsatu duka suna falon, Sadiya na zaune cikin wani leshi ɗan ubansu kalar purple an bi patterns dinsa da adon stones har ƙasa daga gaba. Ta yi ɗaurinta tsaf haka ma fuskarta ta sha kwalliyar da Zahra ta tursasa mata yi acewarta ko don masu shige da fice suna zuwa ganinta, su gan ta tsaf.

Baiwar nan ta zube ta fara da yi wa Sadiya gaisuwar ban girma. Sadiya ta amsa hankalinta na ga Husna suna yiwa juna murmushi. Hajara kafafunta daƙyar suka ƙarasa da ita ga kujera ta zauna tana yaƙen dole. Nan kuma hira ta ƙara ɓarkewa har sadda aka kawo wa Husna da Hajara abin kari. Nan ma kayyakin abinci ne iri iri. Daƙyar Hajara ta iya cusawa a cikinta, ƙarshe ma ta ce amai take ji tana buƙatar kuma ta huta. Zahra ce ta yi mata rakiya ɗakin da babu wanda ya sauka a ciki wanda a nan aka ajiye kayanta ita da Husna.

Tana shiga ta rufe kofar ta zauna gefen gadon ta shiga fidda hawayen baƙin ciki.

"Wannan gidan bai dace da Sadiya ba!  Na rantse ko zan yi yawo tsirara sai na fisge Sadiya daga gidan nan don uwarta!"

Ta firta a fili tana share fuskarta. Ta rasa meyasa take shakkar Boka ta yadda ta kasa fushi da shi. Wuyarta ya ɗauki waya ya kira ta akan ta zo, ban hankalinta ke tashi ta rasa nutsuwa jiki na rawa take amsa mishi za ta zo din. Idan ta zauna kamar irin na yanzu, sai ta dinga mamakin abin, amma kuma a karshe dole take watsarwa tunda ta rasa mafita, wuyarta dai ya kira. Ga kuma alƙawarin da ya ƙara yi mata da ta tsinci kanta da amsa mishi da toh, wai zai yi iyakar yin sa ya raba Sadiya da gidan. Ita kam dama a inda ya fadi a nan ta bar shi, ta sani ba zai iya ba. Abu ne da ba zai faru ba sai dai faɗi a baka.

***
Maina bai samu sukunin zama tare da Mahaifiyarsa ba sai a safiyar ranar dalilin umarnin da Mai Martaba ya bayar na ya tsaya ya tabbatar da kammaluwar komai na ɓangarensa saboda Sadiya ta shiga ɗakinta. Ba don yana so ba sai don bin umarnin da ya zama dole, bai kuma isa ya kauce masa ba koda giyar wake ya sha.

"Ibraheem."

Sunansa da Fulani Kausar ta kira a kausashe kuma kai tsaye madadin Kakan da take kiransa da shi ya sanya Maina ɗago idanunsa a hankali ya dubeta kafin ya mayar.

"Na'am."

"Ban amince da auren nan ba."

Ya rasa me zai ce, bai kuma sauya daga yanayinsa na farko ba. Ya sani duk abin da kowa zai ce, to fa sai dai gareshi ɗin, amma babu wani a cikinsu da zai ja da Mai Martaba. Wannan a rubuce ya ke.

"Ni Kausar da Mahaifina ya kasance Ɗan Sarki jika na Sarki, sarauta mai girma irin ta Daura, na auri jinin sarauta, babu kuma wani a gidanmu da ke auren maƙasƙanciya ko maƙasƙanci, don me zan zuba idanu ka yi zaman aure da talaka? Ita ba wai iyayenta wasu ba ne. Meyasa Mai Martaba zai min haka? Saboda ya ƙara nuna min fifikon yaran Saratu a kan nawa ko?"

Maina ya lumshe idanu ya furzar da huci kaɗan, buɗe su ya yi ransa gaba ɗaya babu dadi da maganganun Fulani.

"Shirunka na nufin kai kana sonta? Ka yarda ka yi zaman aure da ita? Hakan na nufin..."

"Hakan ba ya nufin duk abin da ku ke tunani Ummi. Sai dai shirun na nufin ba ni da zaɓin da ya wuce bin umarnin Maihaifina."

Fulani Kausar ranta ya ɓaci, ta kuwa ɗaure fuska tamau tana harararsa. Ita ta haife shi kuma ta fi kowa sanin halinsa, mutum ne da ba ta taɓa ganin ya wulaƙanta wani ko wata ba, yana da halayya irin ta mahaifinsa. Ko bai son abu, ba zai nuna ba. Hakanan son ma ba kasafai ake gane yana yin sa ba, yana da wuyar fahimta wasu lokutan. Ta sani ko giyar wake ta sha auren nan ba zai mutu ba don al'adar gidan ce ba sa sakin aure sai da dalilai masu ƙarfin gaske sai ko kaddarar da babu yadda aka iya. Yaranta goma cif, dukka guda taran mata ne, Maina shi kadai Allah ya ba ta namiji. Yayyunsa biyar duk suna gidajen aurensu sai ko ƙannensa uku, su ma an yi auren autarta Ummulkhair ce kaɗai a gabanta sai ko Najma da Hidaya yaran yan uwanta da suke jini ɗaya da take riƙonsu. Burin duniya ta ɗora a kan Maina ɗa ɗaya tamkar da dubu a gareta saboda Allah ya ba shi farin jinin jama'a. A na ji da shi matuƙar a gidan, duk da ba shi da hira da sakin fuska sosai amma kuma maza da mata kaunarsa suke. Tana kuma ji a jikinta ko bai yi sarauta yanzun ba, watarana zai yi ɗin. Gudun sarautar yake ita kuwa ta sha alwashin sai ya riƙa.

"Ina iya tafiya? Mai Martaba ya..."

"Saboda ni ban isa da kai ba shi ne kadai ya isa da kai ko? Muna magana ka na kawo min uzuri?"

Ɗan lasar leɓɓansa ya yi.


"Allah ya huci zuciyarki."

Ta yi ƙwafa tana murza yatsunta da suka sha adon gwal. Maina ya yi shiru, shi fa bai ga abin tayar da hankali ba don wai ya auri Sadiya. Umarni ne kuma ya ji ya gani zai bi, zai kuma kula da ita wato sauke haƙƙoƙin da ya san zai iya, shi hakan ma da ya yi tunani kamar wani katanga zai zame mishi daga harin da ƴanmatan zuri'a da na waje suke kawo mishi.

"Goben za ta tare?"

Tambayar Fulani ta ƙara katse shi.

"Hakane." Ya ba da amsa.

"Uhum. Ka na iya tafiya."

Maina ya yi godiya ya miƙe, har zai fice sai kuma ta ce.

"Kakana."

Ya juyo ya dawo yana ɗan yamutse fuska ga dukkan alamu ba ya son magana.

"Ka na sonta?" Ta tambaya tana dubansa. Bai san sadda ya yi murmushin da ya ƙara bayyana tsantsar kyawunsa ba. Wani bin idan Fulani na ririta shi kamar ƙwai, ji take da shi sosai. Wasu lokutan kuma idan ta birkice har mamaki yake.

"Wannan ya ba ni tabbacin ka na so. To dama tun kuna tare da ɗan uwan naka ka na son ta Ibraheem?"

"Please Ummi, ki min iznin tafiya."

Ta kara harararsa, shi kuwa ya ɗan ƙara murmusawa.

"Je ka."

Ya kuwa fice. Ta bishi da kallo ta sauke ajiyar zuciya. Tunanin mafita take yi, toh idan kuma dukkan wannan abin da take yi shi yana sonta fa?

'Ibraheem ba zai taɓa son yarinyar nan ba. Ni na san waye ɗana.'

Ta ba kanta amsa a zuciya.

***
Washegari gidan ya ɗauki haramar shiri na biki da za su gudanar wato buɗar kai wanda daga shi kuma Amarya za ta shiga ɗakinta. Hajara ta firgita da irin tsadadden suturar da ta ga an kawo wai Sadiya ta yi amfani da su. Komai na babban kamfani, har da wani sarƙa ƙarami na diamond. Sai da ta kai zuciya nesa matuƙa kafin ta iya danne baƙin cikinta ba tare da ta bari ya bayyana a fili ba. Ta kula kamar haba-haba ake yi da Sadiyar. Fuskar Gimbiya Saudatu da ma Gimbiya Bilkisu (diya ga Haj Saratu) da suka shigo kawo kayan wannan karon su ma fuskokinsu a sake har aka yi wasa da dariya tare. Ta kula dai lokacin ne Gimbiya Bilkisu ta sanya Sadiya a idanu sai tasbihi take yi wai Sadiyar ta dace da Maina.

Aka gudanar da buɗar kai bisa al'adar masarautar tasu. Kyaututtuka kam Sadiya ta sha su masu firgitarwa. A karshe aka ƙara kai ta dakunan matan gidan kafin a sanya ta a mota zuwa ɓangarenta dake ginin masarautar wanda ya ke da ƴar tafiya tsakani.

Tun kafin a kai ga shiga ciki daga waje kawai ka ga gidan sai ya burgeka. Gini ne babba mai zaman kansa, bai raɓu da jikin wani ba, don wurin ma daga gefe garden ne lafiyayye sai can idan an yi tafiya kadan a iske ginin ɗan Mai Babban Ɗaki, Yarima Zubair. Farin fenti ne gaba ɗaya daga waje, sai ko baƙaƙen gates hakanan rufin kwanon ma baƙi.

Jikin Hajara tun a lokacin ya fara rawa, Sadik dake hannunta ta tabbata ba za ta iya cigaba da riƙonsa ba don haka ta miƙa shi ga Gwaggo Atine wadanda suka iso da yammacin da sha tara arziki da Malam da Abba suka haɗa su kawo matsayin gara don a cewarsu ba za su zuba idanu a ɗauki ɗiya sukutum, a kuma hana su zubamata kayan ɗaki su zauna ba su yi komai ba. Daidai gwargwado sun yi kokarinsu kuma koda wasu ba su yaba ba wasu kam sun ga kokarin.

"Hajiya ki daure, kar ki fallasa zuciyarki. Fuskarki gaba ɗaya ta sauya." Cewar Gwaggo Atine cikin raɗa-raɗa dab da kunnen Hajara yanda za ta ji sosai, don ma dai ana ta bushe-bushe da guɗa da zuba kirari ya sa babu wanda ya lura. Hajara ta ɗan dube ta sai kuma ta kauda kai tana ƙaƙalo murmushin yaƙe.

Da aka shiga gidan kuwa, sai da numfashinta ya tsaya cak na wasu daƙiƙu kafin ta jawo shi da ƙarfin gaske. Tsayawa fasalta ma tsaruwar falon ɓata baki ne. Falukan biyu ne, na farko bai kai na biyun tsaruwa da kayan more rayuwa ba. A na biyun ne kuma akwai hanyar matattakala, daga gefe, sai ko ɗakuna har huɗu a cikinsa. A nan aka shigar da Sadiya ɗaya daga cikin ɗakunan.

Ba Hajara ba, hatta su Zahra da Husna sai da jikinsu ya yi la'asar da dukiyar da aka narka. Kuma tunanin da suke yi duka a kwana biyu aka zuba ko dama can ya shirya gidansa sai ƙarashe?

Anti Hafsatu kuwa wacce ta ji daga bakin Gimbiya Saudatu cewar dama ginin Maina an jima da kammalawa haka ma ɓangarensa a shirya yake, na Sadiya ne aka zuba kayayyakin da ya dace da mace aka kuma yi komai yadda ya dace bisa umarnin Mai Martaba. Sai dai ita kanta ba ta yi zaton tsaruwar gidan ya kai haka ba.

Sai da kowa ya watse a cikin yan uwan Maina da ma iyaye dangin Sadiya da suka zo na ɓangaren Inna dake Gomben da ma kuma su Dada su Gwaggo Atine waɗanda suka koma masauki cike da santi, Hajara ma bin su ta yi don ta rantse idan ta cigaba da tsayuwa a gidan da aka kira wai na Sadiya ba. Yarinyar da ta ke yiwa kallon ƙasƙantacciya irin uwarta a duniya, wacce ko suturar arziƙi ba ta da su kamar nata da Husna, yau ita ce a wannan daular da har wata ƙanwar Malam mai shegen surutu ke cewa ai haƙurin Sadiya ne ya sa ta dafa dutse har ta sha romo. Har ita za'a faɗawa haƙuri? Ita da ake fasa aurenta a ranar da ya dace a yi shi? Aikin banza kawai.

***
Idanu waje cike da alamar tsoro ta ke bin ɗakin da kallo. Sai ta inda ma wardrobe dinta yake ya yi nisan taku ya kai ashirin daga gadonta da ya zo da wani irin labule. Kayan ɗakin gaba ɗaya adon baƙi da ruwan golden ne. Ga fitilun da suka ƙawata shi mai zuwa kala uku, ja, fari da kuma blue. Duk sadda ka kashe ka kunna to fa zai sauya kala.

"Anti wannan gidan zan zauna na rayu ni kaɗai?"

Ta faɗi idanunta suka yi rau rau. Su Zahra suka dara.

"Sadiya wannan gidan, shi Allah ya baki. Gidanki ne. Don ma ba ki ga falukanki da kicin ɗinki ba. Komai na gidanki an ƙawata shi, sai dai mu yi addu'ar Allah ya zaunar da ku lafiya ya baki aljanna fin haka. Amma fa Sadiya samun aljannarki to yana ga bin mijinki. Don Allah Sadiya kar ki ba mu kunya, ki bi Maina sau da ƙafa. Ki zauna lafiya ku yi rayuwar mutunta juna. A hankali za ki fahimci waye mijinki, shi ma kuma na san zai fahimceki ya so ki in sha Allahu. Mun samu kyakkyawar tarbiyya daga iyayenmu, mun gani yanda suke girmama miji da lamuransa, Sadiya ki kauda komai a zuciyarki ki rungumi aurenki da hannu bibbiyu. Mijinki shi ne komai naki a yanzun, ki yi hakuri da dukkan abin da za ki gani ko ki ji wanda zai zo maki a hagunce, watarana a hankali za ki fahimci kowa kuma ki ci maganin zama da su. Allah ya sanya albarka a aurenku, yadda ki ka yi biyayya ga su Inna da mu kanmu yayyunki in sha Allahu rayuwarki ba za ta tagayyara ba. In sha Allahu wataran za ki yi alfahari da aurenki da Ibraheem Tafeeda."

Su Zahra suka amsa addu'ar Anti Hafsatu da amin. Sadiya wacce jikinta ya ƙara sanyi ta share hawayenta ta na mai yin godiya ga Antinta.

Jikinta ya ƙara sanyi sadda aka watse aka bar ta ita ɗaya ƙwallin ƙwal a gidan. Ta yi wuri-wuri da idanu tana zagaye idanunta cikin ɗakin kafin ta sauke ajiyar zuciya. A jikinta take jin ba zai shigo inda take ba. Dalilin kenan da ya sa ta miƙewa ta cire alƙyabbar da aka ɗoramata a saman wani tsadadden voyel sku blue mai adon dark. An yi mata beadwork a wuyan da ma bakin hannayen. Tana shirin kai hannu saman ɗankwalin ta tuje shi ne ta ji shigowar mota, sai da ƙirjinta ya buga don ta san babu mai zuwa a wannan lokacin face Maigidan.

***
Ya fito daga motar, Baharu na riƙe da ledoji yana bin sa a baya har suka shigo falon, iyakar Baharu falon farko, nan ya ajiye ledojin ya rufe musu ƙofar. Maina ya ƙarasa ya sanya muƙulli sannan ya nufi falo na biyu ba tare da ko kallon ledojin ba. Har ya soma taka matattakalar da za ta sada shi da na sa ɗakunan ya tsaya cak. Rashin kyautuwar duba kiwon da Allah ya damƙa mishi ya ji, ga Mai Martaba a gefe da ya ɗaure shi da jijiyoyin jikinsa da nasihohi, a gefe ga wasu a yayyunsa da kuma Haj Saratu. Duka sai ya ji ba zai iya shigewa alhalin bai leƙa ta ɗin ba, ya tabbata kamar yadda auren ya zo mishi a bazata to ita ɗin ma hakan ne, toh a wane dalili zai ƙuntata mata tunda dai ba wai shi take so ba?

Dawowa ya yi da baya ya koma falo na farkon ya ɗauki ledojin da bai ma san me da me Khamees ya siya ba ya ƙarasa.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login