Showing 18001 words to 21000 words out of 124441 words
Sadiya. Da yawa sun ce sai Inna Mairamu ta ga sakayya a kanta. Hakan ba karamin damuwa ya haifarwa Inna ba dannewa kawai take yi.
Sun kwana biyu a gidan Hafsatu sai yanzun da Malam ya nemi su dawo zaman ya isa hakanan.
Wannan Kenan!
***
*Kazar Kwanci...*
Misalin ƙarfe biyar da mintuna na yammacin ranar Malam ya shigo gidan.
Sadiya da ke wanke kwanukan da Inna ta kammala aiki da su ta amsa sallamarsa fuskarta dauke da murmushi. Shi ma kallonta ya yi da murmushin yana amsa gaisuwar da ta yi masa bayan sannu da zuwa. Daga nan sai ga Husna ta fito da ɗan gudunta ta ɗan riƙo hannunsa tana oyoyo. Ya dafa kanta yana dariya.
"Autar Malam an dawo?"
Sunan da yake kiranta da shi kenan bayan Hajara a baya. Kasancewar Husnar ƴar gaban goshinta ce, sam ba ta jin zafin hakan. Ta ƙara narkar da fuska.
"Eh. Ba kai ne ka ce mu dawo ba."
Ya yi murmushi a daidai sadda ya ke miƙawa Sadiya ƴar jakar hannunsa mai ɗauke da na'urar laptop sakamakon hakan da ta buƙata. Kai tsaye falon nasa ta shige ta bar su da Husna dake faman zuba ruwan shagwaɓa. Inna ta mishi sannu da zuwa kafin ya tambayi Hajara.
"Ta sha magani ta kwanta, kanta ke ciwo." Faɗin Husna cike da jimami da tausayawa Antin nata.
"Ya Salam, Allah yasa kaffara. Amma dai ta daure ta tashi yamma ta yi. Kar hakan ya haifar mata da wani ciwon kuma na daban."
Husna ta turo baki, don me Malam zai ce a tashi Antin alhalin bai san irin baƙaƙen maganganun da Anti Hafsatu ta yarfa mata ba.
Inna da Malam suka yi gaba zuwa falonsa wanda tuni Sadiya ta fito ta ja tunga a gefen shiga falon don ta ba su hanyar wucewa ta ƙarasa aikinta. Tana ji Malam na tambayar Anti Hafsatu, Innar na ba sa amsa da cewa dalilin ta bar yara a gida ne ya sanya ta saurin tafiya. Ɗan murmushi ta yi, Allah Sarki Inna, wato ita dai koyaushe kokarinta ɓoyewa Malam rikicin cikin gida wanda kuma babu ɗaya da ba shi da masaniya a ciki.
"Assalamu alaikum."
Sallamar da aka ƙara yi ce ta sanya Sadiya wacce ita kaɗai ta yi saura a tsakar gidan, don Husna ta koma ɗaki amsawa. Faɗaɗa fara'arta ta yi ganin ƙawa kuma aminiyarta kaf layin nasu, Zahra. Ɗiya ce ga Habiba makwafciyarsu wacce ba ta taɓa ko kallon banza ga Inna ba a tun baya ma da makwaftan ba sa shiga harkarsu. Sai yanzu ne ma sauran makwaftan ke kula Inna wasu kuwa har gobe ba sa wani gayyatarta koda sabga kuwa. Dama Habiba da Mama Iyabo su ne da'iman ake zaune tare a na zumunci.
Zahra ɗan durƙuso ta yi a gefe ta harareta.
"Ke dai ba ki da kirki, shi ne ko ki ce min tafiyar kwana ta kama ku. Sai biyo maki na dinga yi don mu tafi makaranta Inna na cewa ba ki dawo ba. Yau ɗin ma Musan gidanmu ne ya ganku kun fito daga motar Anti Hafsatu shi ne fa ya ruga ya sanar da ni."
Kafin Sadiya ta ba ta amsa sai ga Inna ta fito. Zahra ta gaida ta, ta amsa ita ma fuska a sake.
"Yau dai ga ki ga mutuniyarki taki hankali ya kwanta ko?"
Sadiya da Zahra suka yi ƴar dariya.
"Ya Umman taki?"
Inna ta wuce don kai wa Malam ƙaramin cokali da zai saka zuma cikin shayi. Ita kuwa Zahra ta shiga taya ta. Koda suka kammala suka shara wajen sai suka faɗa falon Inna.
"Wai ni an ƙara karatu kuwa? Malam Nura fa ba kirki, kar ya yi min bulalan fashi." Faɗin Sadiya tana ɗan fito da idanu.
"Ni daina zaro min idanun nan naki kar ki tsorata ni cikin dare. Ke wai an fadamaki za su yi zaman jiranki dama? Tab, wallahi dai an ɗora karatu an shiga Suratul Najm."
Ta ɗan sauke ajiyar zuciya cike da jin babu dadi.
"Ai shikenan. In sha Allahu zan kai haddar na baya gobe."
"Ke, kuɗin aure fa za'a kawo, za'a sanya rana shekara da zarar mun yi candy."
Wata ƴar zabura Sadiya ta yi ta dafe cinyarta.
"Ki ce wasa ki ke? Shu'aibu turo wa zai yi? Hum, wannan mutum, ai shikenan. Ke kika ja wa kanki, kin san yanayinsa da kishin bala'i amma ki ka tsaya da wani har ya ganki. Gwara ma ya yi maki hakan. Amma kuma batun karatu, wai dagaske ba za ki ɗora daga sakandire ba? Rayuwar fa sai da ilimi Zahra."
"Wajenku ba, ƴan gidan boko. Ni kuwa wa zai bar ni na ɗora wata jami'a a gidanmu? Hum, to zuwa sakandiren ma da ya ya? Kullum ina cewa ki godewa Allah don kin samu damarmaki da yawa a rayuwa waɗanda wasu ke nema, iyayenki su na da halin tsayamaki ki yi karatu, ni kuwa nawa yayyun ma ba su kai ga ƙarasa sakandiren ba aka yi musu aure. Ke a gidanmu fa na fita zarra ma da aka bar ni na kai har yanzu ina karatun. Nan ma na sani don dai Babanmu samunsa ya ragu ba kamar a baya ba, dalilin kenan da ya hana ya tashi zancen aurena da wuri. Ya haƙura har na kammala wannan din. Kuma Shu'aibu bai min alƙawarin boko ba. Ke ma kin san ba zai bari ba tunda bai ga wata a cikin Sajida da Zinnira ba suna yi. Balle kuma yayanmu Nura da yake namiji ma iyakarsa sakandire sai ko kasuwanci da ya faɗa."
Ajiyar zuciya Sadiya ta saki kawai tana kallonta, kallo irin na tausayawa. Yanzu idan ace ita ce za'a hana karatu ya za ta yi? Ita da kullum ba ta da mafarki face na zama likitar mata. Babban burinta ta taimaki mata masu ciki da ma masu larurori da dama wanda ta sha jin kokensu ana kawo wa gidan rediyo neman taimako. Sai ko wanda ta ji ko gani a makwafta ko asibiti idan sun je dubiya da sauransu. Zahra gaskiya ta fada, mahaifinta ba wani mai ƙarfi ba ne. A baya dai suna da ɗan rufin asiri don kasuwarsa ta gara sosai amma yanzu kam komai sai a hankali. Sanin ba za ta samu ma karatun ba ne ya sanya ba ta ma ɗorawa ranta kwaɗayinsa ba.
"Allah ya sa hakan shi ne mafi alheri a rayuwarki. Amma dai za ki cigaba da sana'ar ƙunshinki ko?"
Sadiya ta furta har lokacin ba ta ɗauke idanu a kan Zahrar ba. Ta yi ƴar dariya.
"Eh bai hana ba, amma fa kinsan komai akwai ƙa'idarsa, ya ce babu ranakun juma'a, asabar da lahadi saboda duka yakan jima a gida kafin ya leƙa kasuwa. Kuma ni ma wai ina buƙatar hutu na kwakwalwa da jiki."
Suka yi dariya. Sadiya ta kara yin addu'a da fatan Allah yasa su ga lokacin.
Nan kuma Zahra ta sako tambayar ko yaya Anti Hajara yanzun? Sadiya ta ce da sauki dai. Ta ɗora da faɗin.
"Ni kaf batun nan ma ba sonsa nake yi ba, eh ina jin ciwon abin da ke faruwa a rayuwarta, sai dai meyasa sai Innata? Meyasa ita mafi yawa ke zargi da wannan ɗanyen aiki? Ashe ba su yarda cewa Allah ya isa ya gudanar da mulkinsa yanda ya so ba? Allah da kansa ya ce zai jarraba waɗanda suka yi imani, ta ya ya idanun jama'a ke rufewa ba sa ganin gaskiya? Son zuciya ko kuwa dai tsantsar rashin tawakkali ne?"
"Son zuciyar ce Sadiya, sai kuma tsanar Inna da ya riga ya dasu a ransu har ta yi girma kuma ta yi rassai. Ki ma bar tunanin nan, babu abin da za ka yi ka burge wasu mutanen, maida hankali kawai ga rayuwarku, shiyasa Inna ke burge ni. Tana iyakar kokarinta wajen kulawa da su da zuciya daya, abin da ta ga ya fi ƙarfinta kuma ba ta matsawa kanta, sai ta maida komai ga Allah."
Sadiya ta share hawayen da ba ta san sun fara zubo mata ba. Girgiza kai ta ɗan yi.
"Inna tana da karfin zuciya ba irin tawa ba. Ni na san yanda nake ji a kirjina duk lokacin da Anti Hajara ko Anti Safiyya suka yaɓa wa Inna magana a cikin gidan nan. Ba zan iya maida musu martani ba na sani Zahra, amma kuma hakan ba ya hana zuciyata jin wani irin zafi."
"Ki yi hakuri Sadiya, ki ƙara hakuri da addu'a. Komai zai zo ya wuce kamar ba'a yi ba."
Ta yi wata ƴar dariya marar sauti ko hayaniya.
"Ki ka ce kamar ba'a yi ba? An yi da yawa, abubuwa sun faru ba kaɗan ba wanda koda ace sun manta, ba zan iya mancewa ba."
Zahra ta share hawayenta, tana da saurin kuka da raunin zuciya musamman akan abin da ya shafi rayuwar Inna da Sadiya. Ba ta son ta ƙara mata damuwa sai kawai ta wayance da miƙewa tsaye.
"Ni zo ki raka ni, mu bar wannan maganar. Ba zamu iya gyaran komai da baki ba, duk abin da ya fi ƙarfinmu bai fi ƙarfin Allahu ba. Don haka mu cigaba da addu'a. Haba ta Isma'il, ɗan murmusa mu gani. Yace yana son fara ko mayya ce, da ya tashi sai ya haɗu da ke." Ta ƙarashe da dariya. Sadiya ta ja tsaki tana kai mata duka ta goce.
"Allah ya yi min tsari, ai ko maza sun ƙare ba zan auri wannan mayen matan ba. Gwara ma ya tattara komatsansa ya koma ƙauyensu ya cigaba da noma."
Ta ƙarashe tana kokarin warware hijabinta da ke ninke a hannun kujera, sadda ta idar da sallar la'asar ne ta bar shi a nan.
Zahra wacce har a sannan dariya take yi ta amsa.
"Ke fa ƴar rainin wayo ce, Jigawar ce ƙauye?"
Taɓe baki Sadiya ta ɗan yi tana mai kokarin fita daga falon ta ce.
"Ni dai muje ki gaida Malam sai ki tafi. Kar ya ga na fita da yamman nan."
Suka ƙarasa kuwa da sallama falon Malam din, yana zaune har ya watsa ruwa ya sanya ƴar tshirt mai gajeran hannu da dogon wando marar nauyi, Zahra a ranta tace gidan ƴan boko kenan. Ita a gidansu babansu ai ba ta jin ta taɓa ganinsa da kananan kaya da girmanta dai. Shi kuwa Malam babu ruwansa, sam ba ya son abin da zai takura jikinsa. Wasu lokutan ma idan bokon ya motsa, shigar riga da wando irin na ma'aikata banki yake yi ya wuce kasuwa abin sa musamman a yanayin sanyi.
Malam ya amsa gaisuwarta fuska a sake yana tambayar baban nata. Ta amsa da lafiyarsa kalau. Nan ta yi sallama da Inna suka fice tare da Sadiya.
A hanya ma hirar makarantarsu suka dinga yi da sauran ƴan ajinsu har sai da Sadiya ta saki ranta sosai. Ba su yi wani nisa ba suka rabu don ta rantse ba yau za ta shiga gidan su Zahrar ba. Sun saba dama irin wannan rakiyar tunda layinsu daya amma akwai tazarar sosai a tsakanin gidajensu. Su na farkon shigowa layi, ita kuwa Zahra suna can ƙasa kaɗan. Idan Sadiya ta je gidansu ana hira a hanya har sai ta rako ta ƙofar gida zasu ankara, hakanan ita ma idan ta tashi yi wa Zahrar rakiya. Wannan karon ba ta bari sun yi hakan ba ta ja tunga jin an fara kiraye-kirayen sallar Magriba, haka suka rabu da zummar sai goben idan an haɗu a islamiyya don ba bokonsu ɗaya ba kuma ana cikin hutu ma sauyin aji za'a yi idan sun koma. Ita Zahra ta gwamnati ma take yi yayinda Sadiya ta kuɗi ce.
***
Da sallama Haj Mariya ta shiga falon Abba wanda ke amsa waya, ta ƙarasa ta nemi wuri ta zauna ganin yanda yake ta fara'a ta ji kamar ta canki da wanda yake wayar. Ba ta tabbatar da zatonta ba sai da ta ji ya ce.
"Toh ni dai wannan maganar ba ni ya dace na yiwa Mamin taka ba, kai ya kyautu ka sanar da ita. Ga ta nan."
Nan da nan fuskarta ta cika da annuri, ta karɓi wayar tana mai duba sunan. "Huzaif Abubakar." Haka dama Abban ke adana lambobin yaran nasa a waya. Cike da zumuɗi ta amsa wayar da sallama. Bayan gaisuwa ta tsinci muryarsa mai taushi yana fadin.
"Mamina, na yi kewarki sosai."
Murmushi ta yi mai sautin da ta san zai shiga kunnuwansa.
"Kai fa daɗina da kai kenan, idan ka yi abu sai ka ce Affan ko Zee Mama. Ina ce jiya ma mun gaisa da kai."
Ta na jin sautin nasa murmushin kafin ya ce.
"Na fi shekaru uku rabona da gida kinga kuwa ai ba ni da maraba da su, sun ma fi ni gata tunda koyaushe kuma tare da su. Ni ma toh albishir zan maki cewa ina dab da zuwa na ganku na koma. Amma fa ba zan ce ga lokaci ba, sai dai kawai ku gan ni. Watakila nan da kwanaki, ko sati, ko watanni."
Ta ɗan ɓata rai.
"A'a Huzaifa, faɗamin rana ɗaya don a shirya maka tarbar da ta dace."
"No Mamina, ke dai ku zama cikin shiri. Watakila ke ma jikinki ya ba ki isowata ƙasar irin yanda ya faru a film din Kabhi Kushi Kabhi Gam."
Ta yi dariya.
"Sannu ba'indiye, zama cikinsu ya sa ka fara daukar ɗabi'unsu ko? Toh ni ban koyar da kai wannan hali ba. Allah ya kaimu, ya dawo da kai lafiya."
Ya na dariya ya amsa da amin.
Nan ta miƙawa Abban nasa suka yi sallama kafin kuma ta dube shi.
"Wai dagaske yake yi? Kuma bai tsayar da ranar zuwa ba?"
Abban ya yi dariyar zancenta. Ya na taunar dabinon da ya siyo mai taushi irin na Saudiya ya ce.
"Huzaif ne fa, ko kusa bai ba ni rana ba. Ya dai ce a yi maki albishir ya kusa zuwa gareki, shigowarki ta sanya na ba ki wayar. Kin san shi ya maida mu kamar kakanni a wasu lokutan."
Ta ɗan ɗaure fuska don ita dagaske ta matsu yaron nata ya dawo kusa ta gan shi duk kuwa da cewa sukan yi video call wasu lokutan.
"Shikenan ai, Allah ya kawo shi lafiya."
Abba ya amsa da amin ba tare da ya ce komai bisa sauyin fuskarta ba. Idan da sabo dama ta saba mitar rashin dawowar Huzaif din, balle kuma yau din da ya yi mata ɗanɗani haukaci, gaba ɗaya za ta dinga zuba idanu ne ta ga ta inda zai ɓullo kuma yaushe.
Dakyar ya samu ta saki fuska ta mance da batun Huzaif a ɗan taƙin.
***
"Wai Hajara dagaske fitar za ki yi? Ba za ki yiwa kanki faɗa da biyewa su Waleeda ba a wannan asibitin?"
Nudrat ke zancen tana dubanta cike da mamakin ganin yanda ta yi shiri tsaf cikin wani arnen leshinta ruwan madara wanda ta samu tun a lefen da Sunusi ya yi mata. Gaba daya kirjinta a buɗe sai ko ƙugunta wanda tsabar matsa da siket ɗin ya yi mata kamar zai yage. Mamakin Nudrat bai wuce yanda Hajara ta ƙi karatun ta nutsu a rayuwarta ba, ta ya ya za'a ce neman aurenki na tarwatsewa amma har ki kasa barin munanan ayyukan da ki ke aikatawa? Kuma babban abin da ya tsorata ta bai wuce ganin yau har allurar hana ɗaukar ciki ta yi ba, kenan hakan na nufin za ta soma bada kai bori ya hau?
"Please Sister Nudrat ki fita a rayuwata! Wai mene ne dalilinki na yi min kutse haka? Duk cikinmu ni kaɗai ki ka takurawa! Sauran da suke fitar me ya hana ki sanyamusu idanu haka?"
Murmushin takaici Nudrat ta yi sa'ilin da Hajara ta dauki zundumeman hijabinta har yana sharar ƙasa ta zura.
"Allah ya baki haƙuri, ina yawan yi maki maganar ne saboda na damu da ke ne. Ina tausayin yanda ake fasa aurenki. Kuma ina maki kallo kamar wata ƙanwata ku..."
"Ya ishe ki, kar ki fama min tabon da har gobe ina jin raɗaɗinsa. Ki bar yi min kallon ƙanwartaki tunda dai babu abin da ya haɗa mu sai aiki. Ba na son sa ido da shiga sharo ba shanu. Mtsw."
Wayarta dake ƙara ta cire a chaji don tsabar ɓacin ran da Nudrat ta jefa ta ciki har tana kokarin mantawa da ita. Ganin sunan Dakta Sani na yawo saman wayar ya sanya ta ƙin ɗagawa tana mai jan guntun tsaki. Ita fa ba ta son takura, mutum ba wani abin kyautar arziki ya ke yi wa mace ba amma sai jarabar tsiya. Gaba daya ta saka wayar da chajar a cikin jaka ta zuge zif kafin ta fice ta yiwa sauran ma'aikatan sallama da zummar ta tafi gida alhalin wasu a ciki sun san dawan garin. Wasu kuwa har gobe sun kasa yarda da abin da ake faɗi a kanta, suna yi wa hakan kallon ƙarya da kuma ƙage.
Sai da ta fice daga asibitin gaba daya kafin ta tari abin hawa zuwa Zoo road inda anan me su Waleeda ke jiranta domin ziyartar gidan wani babba kuma hamshaƙin ɗan siyasa dake gidan hutunsa tare da wasu abokan ashararancinsa suna jiransu. Saurin da take yi don ta je bai wuce jin cewa wannan karon akwai wani babban aiki da zasu ba su ba wanda hakan zai ba su damar mallakar kuɗaɗe masu nauyin gaske da ba su taɓa zato ba. Ana sauke ta daidai gaban wani katafaren Mall dake wajen ta dubi Waleeda, Blessing da Azeema abokan aikinta da halinsu ya yi mugun zuwa ɗaya don wata ƙazantar ma da suke shukawa ita ba ta ko rabinsa ta ce.
"Sorry, na ɓata maku lokaci."
Blessing wacce ta ji hausa kamar jakar Kano ta ce.
"Ai mun dauka wancan mayen Daktan ne ya tsaida ki."
Ta yamutse fuska, ba wanda bai san nacin da Dakta Sani yake yi ga nurses mata ba a asibitin babu ma kamar sabbin zuwa. Wacce halinsu ya zo daya su daidaita, wadanda kuwa ba halinsu kenan ba su nemi tona musu asiri sai ya ja jikinsa.
"Rabu da dan duniya, na ga yana ta kirana har a hanya da nake tafe, banza na yi na rabu da shi. Ana harka da manyan ƙwari wa yake ta shi? Ai yau da shirina na fito ko me zai faru ya faru."
Suka yi dariya gami da shewa. Daidai lokacin da Waleeda ta shiga amsa waya tana yiwa direba kwatancen inda suke. Ba jimawa sai ga wata lafiyayyar