Showing 81001 words to 84000 words out of 124441 words

Chapter 28 - Kazar Kwanci Hausa Novel Complete

mai raba su sai dai mutuwa. Ita kuwa ta bar gidan zuciyarta wasai, ko babu komai yau ce ranar farko da ta samu kyakkyawan albishir dangane da al'amarin Sadiya. Wannan ya fi komai faranta mata.

***
Bayan Wata Ɗaya...

Ta shafa addu'arta bayan kammala Azkar ɗin safe da ta yi zaman yi, miƙewa ta yi ta ninke dardumar ta kuma cire hijab. A gaggauce ta shiga wanka ta fito zuciyarta fes, wannan yawan damuwar da ta ke yi a kan Hamman Nudrat ya ragu da kaso mai yawa sakamakon yawan addu'ar da ta ke yi ga kuma yanzun da suke da lambar wayar juna suna gaisawa ta whatsapp don babu ranar da ba za ta ga saƙonsa ba. Idan kuwa ba ya kusa har jin ta take yi kamar marar lafiya, ita koda yanda ya ke jan ta da hira ma hakan na faranta ranta.

Koda ta fito zama ta yi gefen gadon tana shafa mai murmushi dauke saman fuskarta, tunanowa ta yi da yadda aka yi suka sami lambobin juna. A wani zuwa da ya yi makarantar tafiya da Nudrat ne bayan sun gaisa kawai kamar daga sama ta ga ya miƙo mata wayarsa yana duban cikin ƙwayar idanunta ya ce.

"Babu ko daɗin ji ace ba ni da lambarki alhalin ke ɗin ma ƙanwata ki ke. A taimaka a sanya min."

Ta tuno murmushin da ya yi a sannan ita ma ta ƙara murmusawa.

"Yes!!" Furucin Nudrat ya faɗo mata a rai kamar a sannan ta furta. Har suka kalle ta, ta sa hannu a lokacin ta rufe bakinta tana dariya. Ta tuno sadda ta miƙa mishi wayar ya ce.

"Thank you. Zan yi saving da sunan Our Triple S."

Sadiya ta lumshe idanunta don ta yi zurfi cikin tunani har ba ta san ta lafci mai da yawa ba sai da ta goga a tafin hannun hagunta kafin ta zaro idanu ta maida shi tana yi wa kanta dariya ita ɗaya a ɗaki.

A gaggauce ta yi shiri cikin kayan gida, murna take yi za su soma zuwa asibitin koyarwa na Akth, burinta na dab da cika kenan. Ta kammala shiri ba ta kai ga fita a dakin ba ta ji wayarta ta ɗauki ƙara. Ta sani Nudrat ce don haka ta ƙarasa ta cire ta a chaji , saura ƙiris wayar ta zame daga hannunta ganin kiran daga Our Hamma ne kamar yadda ita ma ta adana lambarsa. Sai kuma ta ji kirjinta na dukan tara-tara, kada fa ace ko Nudrat ce ba lafiya saboda bai taɓa kiranta a waya ba wannan ne karon farko. Ta daure ta yi sallama bayan ya amsa ya ce.

"Triple kewarki ce ta yi min yawa. Tun jiya ba kya online ina fatan ba laifi na maki ba?"

Da sauri ta kalli madubin ɗakin tana murza idanunta har da bubbuga fuskarta wai ta ji ko mafarki take yi ko kuwa idanu biyu, wani tsalle ta buga sai kuma ta toshe bakinta da sauri tana kallon hanyar waje, duk da ba ihu ta yi ba amma tana tsoro kada murnar ta janyo haka. Sai ta kori shaiɗan ta yi hamdala ga Allah.

"Kin ji zancen wani iri ko? To ki bar mamaki, dagaske na yi missing dinki, kasa hakuri kuma na yi na kira. Please say something na ji ko zan ji sanyi kin ji?"

Ta runtse idanu da kuma tafin hannun hagunta lokaci guda don kunya ta ji kamar yana ganinta.

"Uhum. Karatu na yi kuma ban samu chaji ba sai dare. Ka yi haƙuri."

Ta na jin sadda ya sauke ajiyar zuciya.

"Kima da time zuwa bayan Magrib? Akwai maganganu dauke a harshena, ba guda ɗaya ko biyu ba. An ban damar zuwa?"

Ta zaro idanu tana kallon kanta ta madubi, sai ta yi murmushi mai bayyana haƙora. Kwalla suka cicciko mata, wai Hamma dai da ta ke so da mafarki? Ya Allah, ta ƙara gasƙata cewa addu'a ce kaɗai takobin mumini, idan ka yarda ka yi imani da Allah, to zai maka komai. Yau dai Hamma da ta gama sakawa a rai rabon Fareeda ne, shi ke batun kewa, har ma da zuwa wurinta?

'Ke kuwa daga ganin hadari sai ki fara wanka da kashi? Ai duk gaggawar mai jego ta jira a ba ta ɗan.'

Wani ɓangare na zuciyarta ta kwaɓe ta, ta yi ƴar dariya ciki-ciki yadda ta ke da tabbacin ba zai ji ba.

"Shirunki yana razana ni, ina ji kamar yana nufin No. Ki daure ki ce min eh ko a'a. Ni ma zan daure na karɓa a duk yadda ya zo."

Sai ta tuna fa ba ta amsa ba, da sauri ta ce.

"Eh, ba komai Hamma, sai ka zo din."

Ta ji saukar ajiyar zuciya karo na biyu.

"Nagode. Sai anjima. Ki kula."

Daga nan ya katse kiran bai jira cewarta ba, ita kuwa wani tsallen murna ta yi tana dauke hawayen da suka riga suka zubo. Ji ta ke kamar ta yi tsuntsuwa ta tashi ta yi yawo a sararin samaniya saboda tsabar murna.

Ranar dai kowa ya gan ta ya shaida tana cike da farin ciki, koda suka shiga asibiti ma ba ta samu damar yin zancen ga Nudrat ba duk kuwa yadda ta so yi. Ganin ita ma ba ta yi mata zancen ba ya sa ta fahimci ƙila ba ma ta sani ba shiyasa ta bar wa cikinta sai Hamma ya zo din ta ji abin dabya kawo shi.

***
"Na rasa Fareeda, na kuma sani rashi ne da ko na ƙi ko na so dole na yarda da hakan. Don Allah kar ki saka a rai cewa sai da na rasa ta ne sannan na zo gareki, ki saka a rai ƙaddararmu ce a hakan. Ina so ki maye min gurbin ta ne. Abin nufi, mu ƙulla alaƙar da za ta kai mu har ga aure."
Ta rasa me za ta ce, kanta yana ƙasa tana wasa da zoben azurfanta, kirjinta kamar ya yi tsalle ya fito. Ga dai ranar da ta ke yawan mafarkin gani amma kuma kamar an saka allura da zare an ɗinke leɓɓanta, sun ma kasa motsi balle su ce wani abu. Daƙyar ta samu ta fara kunce zaren ta hanyar murmusawa.

"Oh Triple ki yi magana mana. Shirunki na tsorata ni. Ko dai na maki tsufa?"

Ta girgiza kai tana ƴar dariya shi ma ya taya ta, batu dai na gaskiya zai yi talatin da biyar haka, ya ma girmi Huzaif. Amma kuma ka na ganinsa ba ka ce ya kai ba. Yana da cika ido dai. Ga uwa uba kyawu da nutsuwa.

"Allah ya zaɓa mana abin da ya fi alheri."

Ta furta a sanyaye, ya amsa da amin. Nan kuma ya hau ba ta labarin cewa tun farko ya ji tana burge shi, yana sonta amma kuma ya yi shiru ne bai furta ba kar ya shiga jerin mayaudara tunda ya sani za ta iya jin labarin sanya ranar aurensa.
A wannan rana dai sun fahimci juna sosai, kowannensu ya yi na'am da ɗan uwansa kafin su yi sallama ya tafi.

Koda ta shiga gida ba ta ɓoyewa Inna komai ba, Inna ma fatan alheri ta yi wa lamarin.

Tun daga lokacin sai soyayyar AbdulMajid ta yi wa Sadiya ƙatutu a zuciya, kullum ko bai mata magana a waya ba za ta yi mishi. Ta nemi wani ajinta ta rasa, ta rasa kuma irin son da ta ke masa don za ta rantse ko Huzaif ba ta yi wa ba. Ita abin har tsoro ya ke ba ta. Sanda Nudrat ta gane sun haɗe kansu kuwa ruƙunƙume ta ta yi tana ihu da murna, ita sai ta ba ta dariya ma.

Ko sanda ta je gidan Zahra wacce tsohon ciki ke hana ta fita ta ba ta labarin soyayyarta da Hamma ita kan ta ta ji dadi. Sadiya tana murmushi ta ce.

"Wai meyasa duk wanda ya ga Hamma sai ya ce mun dace? Sai an ce in sha Allahu shi ne mijina?"

"Saboda kun dace din ne, kun ba da kala tare. Kuma ai juma'ar da za ta yi kyau tun daga laraba ake gane ta. Ki duba kirki irin na Nudrat da Nene, sanadinki na san Nudrat amma sau uku tana takowa gidan nan bayan zuwanki da ita, takanas don mu gaisa mu sha hira. Toh wa zai ƙi zuri'a irin tasu da abin hannunsu bai rufe musu idanu ba?"

Sadiya ta yi murmushi.

"Kin san kuwa har Nenen sai da ta kira ni wai na bar zuwa gidanta ita fa ba kallon suruka take yi min ba. Na daina mata haka ko mu yi faɗa, wai ni ƴarta ce."

Zahra ta yi dariya.

"Allah Sarki, kin yi dace sosai wallahi yar uwa. Ke dai Allah ya tabbatar mana da alkhairinsa."

Sadiya ta amsa da amin tana mai jin wani sanyi a zuciya. Sai ta ji ta tuno da Suraj, ta mishi addu'a a fili, Zahra ta amsa da amin.

***
Bayan Wata Biyu...

Tana kwance a tsakar gidansu saman tabarma, Inna ba ta nan ta je gidan Baba Habu wacce ake sunan matarsa da ta haihu. Ita ba wani ɗasawa ta ke yi da ita ba ta dai je mata barka ta kai mata abincin da Inna ta girka a ranar da ta haihu. Wanki ta sha yau duk a gajiye ta ke jin ta ga kuma takaicin yanda suka shafe wata ɗaya zaune a gida dalilin yajin aikin da ake yi ga kewar Hamma wanda kwana biyun nan kawai ya ɗauke mata wuta, kamar yana cikin wata damuwar. Kiran ƙarshe ma da ta masa haƙuri ya ba ta ya ce zai neme ta da kansa.

Ko Nudrat ba ta sanarwa ba da suka yi waya. Fargabarta kar dai soyayyarsa da Fareeda ce ta dawo sabuwa shi ne dalilin wannan sauyi. Amma kuma idan ta tuna ya ce mata ko waya ba sa yi sai hankalinta ya kwanta. Kamar kuwa ya san tunaninsa take yi, sai ga kiran waya ya shigo mata, ta kai hannu ta ɗaga wayar ta duba tana ganin sunansa na yawo saman screen ta miƙe zaune ba shiri ta amsa da sallama. Bayan sun gaisa ya ce.

"Na yi kewarki, ki yi haƙuri da halina kin ji? Tafiya ce ta kama ni, ina Gombe ne. Shekaranjiya kuma ban jin dadin jikina ne, ni idan ina ciwo ko magana ba na son yi ne. Amma yanzu Alhamdulillah."

Ta sauke ajiyar zuciya, ita wannan ma kiran ya wadatar da ita. Zuciyarta ta sanyaya.

"Babu komai, Allah ya ƙara lafiya. Ya Gomben?"

"Gombe ga ta nan lafiya. Ina tare da Maina, bari na ba shi ku gaisa."

Ta ɗan yi jim, ta san Maina a bakinsa, ta kuma san shi tun ma farkon ganinta da Hamma din, sun yi hirarsa da Nudrat a gabanta. Haka nan Nudrat ta ƙara yi mata bayanin waye shi, ɗa ne ga ɗan uwa ga mahaifinsu, wato Mai Martaban Gombe ne, sun haɗu ne ta ɓangaren iyayensu mata, kuma amininsa ne suna girmama lamarin juna, sai dai Nudrat na jin haushin Maina ne saboda ta ce yana da izza da ji da kai. Ga kuma kaunarsa da Hammanta ke yi kusan ma fiye da yadda yake ƙaunarta. A nata cewar. Ba ta kai ga magana ba, sannan ba ta yi zato ba ta tsinkayi muryarsa a cikin dodon kunnenta.

"Assalamu alaiki."

Sadiya ta ji murya kamar an busa sarewa, ta tsinci nata muryar da ƙara ƙanƙancewa cike da girman da ba ta yi shirin ba sa ba ta ce.

"Wa'alaikumussalam. Barka da yamma. Fatan ka na lafiya?"

Ta ji shiru na sakanni kamar ba za a ce komai ba sai ta ji ya amsa.

"Barka dai, a gaida su Mama."

Kafin ma ta amsa ta ji muryar Hamma ta wayar yana fadin.

"Ok My Triple, zan kira ki anjima. Take care."

Ta kasa magana har ya katse kiran, ta harari wayar ta ja tsaki guntu. Ta kula dagaske dai Nudrat ta ke a kan wanda aka kira da Maina. Ai shi abokin saurayinta ne, toh kuma babu wani fara'a a muryarsa haka yake? Ta dauka a na gaisawa sosai kamar an san juna ne da abokin wanda za'a aura? Sai kuma ta taɓe baki, ƙila sarautar ce ta motsa mishi zai sauke a kanta.

"Yo sarauta ai a garinmu ta ƙare. Har zai nuna mana mulki da ƙasaita?"

Ta yi zancen a fili, sai kuma ta yi wa kanta dariya na wannan ƙarfin halin nata, miƙewa ta yi ta shiga hidimar ɗora musu girkin dare zuciyarta fari ƙal, jin muryar Hamma ya fiye mata komai daɗi.

Da daddare ta whatsapp suka sha hirarsu, zancensa na ƙarshe ce mata ya yi.

"Ki shirya fa, da zarar na dawo su Baffa za su zo nema min aure. Karatun nan na faɗamaki dama sai dai ki ƙarasa shi a gidana."

Ta karanta ya fi a ƙirga, daɗi ya yi mata, emoji kawai na kunya ta aikamasa ba tare da ta ce uffan ba. Idan har shi za ta aura to fa ta shirya su yi auren ta je makarantar daga gidansa.

***
Sun tashi da labarin haihuwar Aminiyarta, ta rasa ina za ta tsoma ranta ta ji dadi sadda Maman Zahra ta shigo ta sanar da su. Lokacin ma ta yi shirin tafiya asibitin ne wajenta. Ta samu ɗiyarta mace. Sadiya ce ta shirya ta bi ta yayinda Inna ta ce daga baya za ta zo.

Ranar suna yarinyar Zahra ta ci suna Fatima ake kiranta da Batool. Nudrat ta jibgo siyayya kuwa ta kawo, Sadiya tana jin dadin yadda kowa nata Nudrat tana mutuntawa. Wannan ya ƙara musu shaƙuwa su uku tamkar dama har ita suka taso a unguwa. Husna ma da nata tsohon cikin ta zo, gaba ɗaya duk ta ƙara kumbura.

"Anya wannan kumburin na lafiya ne Husna? Ki na zuwa awo dai ko?"

Matar Yaya Hashim ta furta tana dubanta. Husna ta gyaɗa kai.

"Ina zuwa Anti Rashida, sun ce wai hawan jini ne sun ban magani. Kuma na bar cin gishiri."

Nan kowa ya tausaya mata, Inna na wurin ba ta ce komai ba sai tausayinta da ta ji ita ma. Koda suka tashi tare da ita suka wuce gida don dama tare aka wuce gidan sunan ta dawo gida sai ta haihu. Ita ma ta fi kaunar hakan, kwanakin nan ta rasa kan Huzaif, ba ta san dalili ba amma kamar ya ɗan sauya, kusan ma magana ba ya so ta cika yi mishi. Idan an ce shi ne ma silar hauhawar jinin nata ba za ta yi musu ba. Fargabarta kada ace aikin ne ya soma lalacewa. Tana son yi wa Anti Hajara bayani amma kuma tana jin tsoron kar shirkar ta yi yawa, kar ta wuce gona da iri. Ƙila ma wani abun ne ya ɓata masa rai ba wai dalilinta ba ne. Hakan ta saka a rai. Ta ga dai ko musu bai mata na da tace gida za ta je wanka. Tun tana ganin kamar shirye-shiryen bikin Meenat da ake yi ne ya dauke hankalinsa har dai ta gane dagasken haushinta ya ke ji kuma ya rage wani rawar ƙafa a kanta.

***
Zaman Husna a gida ne ya sa ake ganin Hajara lokaci zuwa lokaci sai dai ba ta taɓa katari da AbdulMajid yazo wurin Sadiya ba. Kuma sam ba ta da labarin komai ƴar hirar ba ta zo wa Husna ba.

Ita kuwa ɓangaren Sadiya sai zamanta da Husna karo na biyu ya ƙara musu shaƙuwa, sun koma makaranta a lokacin. Idan ta dawo haka za ta zauna su yi ta hirar karatunsu da ma yanda wasu lokutan suke fuskantar ƙalubale a ciki musamman idan sun je asibiti. Abin kan burge Husna gaba ɗaya sai ta ji damuwar rashin zuwan Huzaif ko kuma kiransa ya ragu a ranta idan suka yi irin zaman nan da Sadiya. Ita kuwa Sadiya ta fuskanci ƙanwarta na cikin damuwa ko ba ta fito ta furta ba, Inna ma kwanaki ke cewa ba ta ga gilmawar Huzaif a gidan ko wani a danginsa da sunan an zo ganin Husna ba. Amma ba su yi zancen a gabanta ba gudun ƙara jefa ta cikin damuwa. Sadiya ta sha ji tana waya tana kuka tana ƙorafi ga Huzaif a kan yanzu ba ya sonta amma kuma ba ta taɓa nunawa ta jin ba tunda ba ta son su sani.

Meenat ce ma ta shigo gidan, ita ma kawo cingam da katin biki ne ya kawo ta. Sama sama ta yi wa Husna magana suka gaisa da tambayarta jikinta. Sadiya sai ba ta ji dadi ba, ita ta sakarmata fuska sosai amma kuma ai jini ɗaya ba ƙarya, abin da ya shafi Husna ya shafe ta. Koda ta taka mata zuwa waje bayan sun yi sallama ta ce.

"Don Allah Meenat ki yi hakuri ki ba Husna ko wuri kaɗan ne a zuciyarki. Ni komai ya wuce a wurina amma meyasa ke har yanzu ba za ki hakura ki rungume ta matsayin yar uwa ba. Kar ki manta, ko aure bai shiga tsakaninta da Yayanki ba, mu da ku an zama ɗaya."

Meenat ta yi murmushi mai ciwo. Don Sadiya ba ta san me ke faruwa ba ne. Ita da kanta ta je gidan Yayanta Huzaif don yin gyara saboda kwana biyu gidan ya yi ƙura tunda ba mace a ciki, bincike haramun ne amma kuma ta kasa haƙuri sai da ta dinga yi a gidan sai dai ba ta ga komai da za ta kama Husna da laifin aikata asiri ko tsafi ba. Ba da nufin bincike ta ɗaga gado ba sai don shara, manyan layun da ta gani dunƙule wuri guda ya mugun razanata. Hotonsu ta yi a waya amma ta kasa kiran Mami balle su Yaya Radeeya da Lubna, gani take yi kamar idan ta fadi za ta yi sanadin auren Husna. Da bismilla ta ciro su ta zagaya bayan gidan ta ƙone ƙurmus. Ko Mami ba ta faɗawa ba, amma kuma hakan ya ƙara rura wutar tsanar Husnar a zuciyarta. Ta kuma ƙara dagewa da addu'o'i ga ɗan uwanta bayan shi ma ta roƙe shi akan ya dage. Bai kuma musa ba sai ma godiya da ya yi mata duk da ba ta ce mishi ga dalili ba. Kuka kam ta sha a ranar.

"Ke, duk a kan na nemawa ƴar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login