Showing 66001 words to 69000 words out of 124441 words
na je Ni..."
"Yes Gwaggo na sani, an faɗa min. Ki hanzarta ki gama magana ce mai matuƙar muhimmanci nake son mu yi."
Gwaggo Atine ta kai ƙarashen samosar hannunta zuwa baka ta cinye ta ƙara kai hannu ta ɗau wani. Hajara dai kallo kawai ta ke bin ta da shi, a duniya ba ta jin ta san wata mai hali irin nata. Matar da ke da kuɗaɗe da kadarori daidai gwargwado ita ke hannu baka hannau ƙwarya haka. Koda dai idan har a kan abin duniya ne, Gwaggo tana masifar sonsu ga shegen maƙon tsiya. Na wani na banza ne, amma fa kuɗinta kuɗinta ne.
Gwaggo sai da ta ƙarashe cinye na hannunta ta kora da lemo kafin ta dubi Hajara.
"Mu fara da abin da ya sa ki ke nema na Autar Mama. Daga ji kiran na san samu ne, ko mene ne dai, abu ne da ya girmi kaka. Ina jin ki."
Hajara ta ɗaure fuskarta tamau shaidar babu wasa a abin da take shirin faɗi.
"Na sani, kuma ke ma kin sani, mun haɗu ne akan turbar tsanar mutum ɗaya. Ko ban kama suna ba kin san ina nufin Mairamu."
Fadin sunan Mairamu ya sa Gwaggo Atine ji kamar ta watsa mata garwashin wuta a ƙirji. Cikin ɗacin rai ta ce.
"Hakane, a duniya idan da matar da na tsana to Mairamu ce. Kuma kin fi kowa sanin dalili."
Ɗan murmushi Hajara ta yi tana ɗan matsa yatsunta da suka sha zobunan gwal suna ba da sautin ƙaƙaƙas.
"Dakyau, kina da labarin Sadiya ta soma zuwa jami'a? Kuma abin da take karanta fannin da na so samu ne amma Mairamu ta yi min baƙin asirin da na kasa cin jarrabawa duk ƙoƙari da nacin karatuna sai ƴarta ce ta haye?"
Ai sai Gwaggo Atine ta wani buɗe idanu a hargitse da kuma ɗan ɗaga sauti ta ce.
"Me? Kambala'i! Sadiyar? Kenan Likita take karanta?! Na shiga uku! Kin ga abin da nake nusar da ku ke an akan matar nan amma kuna ganin kamar ƙage na ke mata ko? Idan akwai wacce ba ta ƙaunarku a duniya to Mairamu ce. Makirar ƙarshe ce, son kanta da nata ya yi wa zuciyarta ƙatutu. Ba za ta taɓa bari ku cigaba ba, ke ɗin ma don kin fi ƙarfinta ne amma saura duk ta bi ta shanye su. Toh wai an taɓa matar Uba mai zama da yaransa da zuciya ɗaya?"
Hajara ta jinjina kai cike da gasƙatawa. Ta furzar da huci.
"Hakane. Ba kuma za'a taɓa yin su ba har abada. Shiyasa nake son a wannan karon na karɓi tayinki na kai Mairamu gaban mutanenki a san me za'a yi masu ita da ƴarta. Yadda ban yi karatun abin da nake muradi ba, haka ma nake buri da son ganin Sadiya ba ta yi ba."
Wani murmushi Gwaggo ta yi, a ranta faɗi take an zo wurin. Za ta mallaki kadarori ashe tunda har Hajara ta shigo tafiyarta.
"Ba zan fasalta maki daɗin da na ji ba Autar Mama. Ai dama yanzu fa ba a zama, miƙewa tsayen da ake cewa ba na wani wurin ba ne sai gaban Bokaye. Ah, mun san komai."
Ta ƙarashe tana kora ruwan lemo mai sanyi a maƙoshinta kafin ta dire kofin ta yi gyatsar da ta sa Hajara jan tsaki. Ta soma fusata, ita ba ta son wasa da lokaci, musamman yanzun da suke shirya kalar makircin da za su aiwatar a kan waɗancan biyun. Lura da hakan Gwaggo Atine da ta yi sai ta saita kanta.
"Gobe ki ke so mu je ko kuwa yau?"
Hajara ta numfasa ta ɗan saki fuska.
"Ai ba a sanya, mu je a yau ɗin nan."
Gwaggo ta yi dariya.
"Shiryo mu je." Hajara ta miƙe ta yi hanyar ɗakinta, Gwaggo kuwa ƙwalawa ƴar aikin kira ta yi, bayan ta zo ta dube ta.
"Takwara, haɗe min waɗannan a leda da su zan tafi. Idan da wasu ma a ƙara min."
Atine ta amsa cike da ladabi ta ɗauka ta juya. Suna saukowa Atine ta fito a kicin ta miƙa mata leda ta karɓa. Gwaggo dai ƙara kalle gidan take yi, ji take a ranta inama ita ce mamallakiyarsa. Kai da ace tana da ɗiya ai babu abin da zai hana ta aurawa mai kuɗi irin Alh Nuhu koda kuwa Hajara ce a ciki. A cewarta ai so so ne, amma kuma son kai ya fi.
***
Hajara wani irin gumi ne ke yanko mata, kawai jira take ta ji ne zai fito a bakin ƙasurgumin ƙaton da ya sha babbar riga da rawani ya yi zaune saman buzu. So take yi ko mene ne ma ya yi daidai da burinta, fatanta. Ya ba ta tabbacin yiwuwar rushe karatun Sadiya. Sai dai kuma daga lokacin da ya soma magana har ya kai aya, ba ta san sadda ta miƙe tsaye tana ɗura uban ashariya ba kafin a tsawance ta ce.
"Ƙarya kake yi! Na rantse sai na ga bayan karatun Sadiya! Waye kai da za ka ce min hakan ba mai yiwuwa ba ne?!"
Gwaggo a ruɗe ta ke dubanta kafin ta maida duba ga mutumin da ya gama shaƙar wannan hargagi na Hajara,shi tun da yake aikinsa ba a taɓa raina wayonsa irin yau ba. A ƙundumo masa ashariya sannan a ƙaryata bincikensa?
Kafin ya ba ta amsa ta juya ta fice, Gwaggo hankali a tashe ta shiga ba shi haƙuri. A matuƙar fusace ya dubi Gwaggo.
"Ki tashi ki bi bayanta! Ku je duk inda za ku je! Ba ta san ni ba! Amma ki mata albishir cewa mu zuba ni da ita! Hajara ko? Toh kuwa duk inda za ku je za ku dawo nan ku durƙusa ku nemi yafiyata! Ina nan ina jiranta!"
Yana kai wa nan ya miƙe bai ko saurari magiyar Gwaggo ba ya bi wata hanya zuwa cikin gidansa. Gwaggo ke ta ban baki a mota yayin da Hajara ke tuƙi ranta a mugun ɓace, babu abin da take so yanzu da ya wuce ta ganta tana shan maganinta na gusar da tunani.
"Haj Hajara, ina mai tabbatar maki da cewa yarinyar nan akwai wani haske da ke mamaye da rayuwarta a yanzu wanda ya yi mata katanga daga dukkan sharri. Zan iya rantse maki ko za ki yi yawo tsirara, sai dai ki yi nasara a wasu ababen a kanta amma ban ce maki su din ma cikin sauƙi ba. Yarinyar akwai wata ɗaukaka da ke bibiyarta, kuma..."
Iyakarnan ta iya ji, daga nan ne ta ƙaryata shi. Ɓaɓatun Gwaggo ya ishe ta don haka ta daka mata tsawa gami da buga sitiyarin da ya razana ta.
"Ya ishe ki haka Gwaggo! Ya isa! Ki bar ni na ji da guda ɗaya! Ki bar ni da damuwar da ke cin zuciyata! For God sake ki bar yi min wannan banzayen kalaman naki! Shi ɗin banza ne! Shi kaɗai ne malamin tsibbu da har kike tsoron kar ya cutar da ni! Ƙaryarsa don ubansa! Kuma na rantse da ace na san inda za ki kawo ni kenan da ban ɓatawa kaina lokaci ba. Aikin banza kawai! Mts!"
Tana kai wa nan ta yi wani wawan U turn ta juya ta faka motarta.
"Sauka maza ki bar ni! Sauka na daina ganinki a motarnan."
Gwaggo da jikinta ke tsuma ta kasa cewa uffan sai rawar baki, duk gogewarta a duniya ba ta yi tsammanin za ta ji shakkar wani ba sai ga shi ɗiyar cikinta ta nawa ma amma tana tsoronta. Ta sani yanzu ko me za ta ce Hajara a fusace take ba sauraronta za ta yi ba don haka ta nemawa kanta lafiya ta fito a motar daƙyar ta ce.
"Don Allah kudin mota."
Hajara sai da ta watsa mata harara da idanunta da suka kaɗa tsabar baƙin cikin jiyo labarin ɗaukakar Sadiya kafin ta ja tsaki ta buɗe jaka ta fiddo dubu uku ta wurga mata. Da sauri Gwaggo ta tsince su, ta na kokarin sanyo kai ta gilashi don ta taushe ta ba shiri ta yi baya da gudu ganin yadda ta figi motar. Haɓa Gwaggo ta riƙe.
"Oh ni wannan shegiyar za ta kai ni ga rami ban shirya ba. Da ni kike zancen, na rantse tunda na saka rai sai na ci kuɗinki to fa babu abin da za'a fasa. Gobe ma ina tafe zuwa gidan naki."
Ita kaɗai ke zuba zantukanta kafin ta tari abin hawa ta koma inda ta fito.
***
Da murmushi ɗauke saman fuskar Sadiya ta amsa sallamar ɗalibar da sati guda kenan suna haɗuwa da juna, sunanta Nudrat Mustafa. Ba ta son sakin jiki da ita don tana tsoron faɗawa hannun gurɓatattun ƙawaye amma ta kula kamar yarinyar na da nutsuwa kuma ga dukkan alamu za su yi sa'annin juna. Fara ce tas itama amma tana da ƴar ƙiba ba kamar Sadiya da take ƴar firit ba sai surar gaba da baya. Wuyanta babu rama dai.
"Wash! Za ki ce na fiye naci da takura ko? Na kula kamar ba ki gama sakin jiki da ni ba. Ni kuma fisabilillah na ke ƙaunarki, ganinki nake kamar Yayata da ta rasu sanadiyyar cutar sankarar mama, Yaya Maryam. Ita ma ƴar siririya ce tubarakAllah, yaranta biyu kafin ta rasu. Daga nesa fa idan na hangoki har faɗuwar gaba nake ji wallahi don a zatona ita ce. Ki yarda mu yi rayuwar makaranta tare cikin aminci da tsoron Allah. In sha Allahu ba za ki yi nadamar haɗuwa da ni ba."
Sadiya ta ji ta samu nutsuwa, ta kuma tausaya mata rashin Yaya Maryam. A fili ta ce.
"Allah Sarki, Allah ya ji ƙan ta, sunan Mamana gareta."
"Wow, wataƙila ma shiyasa na ji Allah y sanya min ƙaunarki. To Allah ya bamu sa'ar abin da muka zo nema."
Da murmushi Sadiya ta amsa wa Nudrat da amin. Daga haka suka shiga duba abin da aka koya musu a ɗazun, ga mamakin Sadiya ita ma Nudrat akwai ƙoƙari sosai, ta kuma kula yanayin ma turancinta kamar ba na ƙasarnan ba ne. Kamar ta tambaye ta daga ƙasar da ta fito ko kuma ta yi karatu a baya sai kuma ta share kar shishshigin ya yi yawa daga farawa, ta bari da zummar ai za ta sani watarana.
***
Tun sadda ta ji labarin komawa karatun Sadiya ta dawo cikin hayyacinta, ta farka daga baccin da take yi a baya. Dagaske ta taya ta farin ciki har a ranta, amma kuma ta soma gane ba ta da wayo. Makahon son da ta ke yi wa Huzaif na ko a mutu ko a yi rai sai ta aure shi, shi ya zama babban dalilin da ta sa ƙafafunta ta ture batun karatu a rayuwarta.
"Mijinki ɗan boko na ƙarshe Husna, amma ki yi wasa da damarki ki ƙi maida hankali ga karatu. Ko sakandire fa ba ki kai ga kammalawa ba. Ina jiye maki halin maza a can gaba. Ai ko ba don ki yi aiki ba, ace ki na da takardunki. Amma tunda haka kike ganin ya fiye maki shikenan, Allah ya ba da sa'a."
Ta tuna kaɗan daga cikin maganganun da Anti Hafsatu ta yi mata farkon zuwanta gidan tana Amarya kafin ma su kai ga tafiya Umrah. Kawai sai ta ji hawaye, ta shafi cikinta da ya ɗan soma girma, watanninsa huɗu. Ta ina za ta fara karatu yanzu?
Wayarta dake gefe ta sa hannu ta ɗauka ta lalubo lambar Antinta ta danna kira. Ƙara uku a na huɗun ta ɗaga.
"Hello, Momina ya ne? Ba dai jikin ba ne ko?"
Furucin da Hajara ta soma kenan ganin ɗazun da safe sun yi waya.
"Antina, ina son komawa skul ni ma."
Tana jin ajiyar zuciyar da Hajara ta saki kafin cikin sanyin murya ta ce.
"Saboda Sadiya ta koma ko Momina? Dama ban faɗamaki ba tun a baya ki cigaba da karatunki ki ka nuna min bakya so. Ni kuma a duniya kin fi kowa sanin ba na son abin da zai takura rayuwarki."
"Anti sai da ta koma ne na ji ni ma ina son komawa. Na gama tunanina, nan gaba kar Yaya Huzaif ya guje ni saboda rashin ilimi mai zurfi."
"Shi ya ma isa? Ke tun aurenki da shi kin ga daidai da daƙiƙa ya nuna maki yatsa ko ya bi ki da kallon banza? Faɗa min na ji ko akwai sadda hakan ya taɓa faruwa?"
Husna ta yi shiru cikin nazarin zantukan Antinta Hajara, da gaskiyarta, tun aurenta da Huzaif bai taɓa ko ɗaga murya sama da nata ba, ita abin har kunya da tsoro yake ba ta idan sun shiga cikin jama'a. Rawar jiki ya ke yi gun hidimta mata, ta sani ko batun karatun nan ba ta ma shakkar tunkararsa da shi saboda tana da yaƙinin ba ma zai ce a'a ba. Ba ta taɓa zuwa da zance ya ce ba zai yiwu ba. Har wataran tana so ta ga sun yi faɗa irin na mata da miji ya yi mata ɗan fushi amma duk yadda za ta buga sai dai fa ta ga yana ba ta hakuri da magiya.
Jikinta ya yi mugun sanyi.
"Anti bai taɓa ba, kuma ni abin ma yana ban mamaki. Anti don Allah dagaske sona ne ya yiwa Yaya Huzaif yawa da har ya ke kasa hukunta ni akan komai? Komai fa zan aikata daidai ne a wurinsa."
"Toh mene ne son idan ba hakan ba Husnata? Hakan da yake maki shi ne son ai. Ke ki bar min wannan magana kin ji ko? Ni dai na sani aikin da ke kan Huzaif ina rantse maki har abada kin fi ƙarfin wulaƙanci a wurinsa. A kanki zai iya fito-na-fito da kowa a duniya ciki kuwa har iyayensa. Don haka ki saki jiki ki ci karenki babu babbaka kin ji ko?"
Husna ta ji ƙirjinta ya buga da ƙarfi, ta kasa magana. Ta sani dagaske kam Anti har wasu magunguna ta ba ta ta sha da ma wasu layu da ce ta bar su da'iman a tsakanin katifarta da falankin gado. Duka ta aikata hakan amma a mugun tsoroce, sai dai ta nuna mata duka wadannan fa ba wani abu bane sai na kore shaiɗan a shimfiɗarsu. Ƙarshe da ta matsa da tambaya ta dube ta tsakar ido ta ce muddin dagaske tana son Huzaif ya ƙaunace ta su yi zama na lumana toh har abada ya kasance ita ke gyaran ɗakin kwanciyarsa kuma kar ta sake ta cire layar da ta ba ta. Har ce mata ta yi ba wannan ne kaɗai aikin ba, an mata wasu zafafa amma kuma wannan ɗin shi ne sirrin shimfiɗarsu. Duk ranar da ta cire shi, to ta tabbata zai tsane ta a shimfiɗa koda bai fasa rawar jikin yi mata sauran abubuwa ba.
"Momina kin ga ki cire komai a ranki, batu kuma na karatunki za ki yi koda a bangon duniya ne. Ke dai yanzu ki bari ki haihu lafiya kin ji ko? Ni da kaina zan yi wa Huzaif din zancen. Yanzu ina hidima da jama'a ne kin san gangar siyasa ta buga ba zama muna aikin taya Alh Garzali kamfen, zan kira anjima idan na sallami matan nan."
Tana kai wa nan ba ta jira Husna ta ƙara uffan ba ta katse kiran, Husna kuwa kasa motsi ta yi. Kirjinta kuma ya ƙi barin bugu, ta fa tuna har yanzu akwai layu a ƙarƙashin shimfiɗarta da Huzaif. Sai ta ƙara tsorata, to kodai idan ma babu su sakinta zai yi? Mene ne kuma makomar wannan aikin da ta yi?
Ba ta manta akwai sadda suka je gidan su Huzaif din, Maminsa da kannensa suka ga yadda yake ta rawar jiki da ita. Tun Mami na kawaici har ta ɓata rai ta ce ya tashi ya wuce idan a wuni sai ya dawo ya ɗauke ta. Abin kunya sai da ya dubeta saboda ya ji ita mene ne ra'ayinta, ta gyaɗa masa kai kafin ya yi musu sallama ya tafi. Tana ji tun lokacin ne Mami ta sauya mata, duk wani rawar ƙafa da take yi da ita idan ta je gidan ta daina, wajen Anti Zulfa'u ne take samun tarba mai kyau. Amma dama Meenat ko gidanta ba ta taɓa takowa ba. Sau ɗaya ta taɓa kawo mata dambun nama daga Mami, shi ma a waje ta tsaya ta ba Maigadi ya shigo da shi. Abba kuwa koda ace bai so auren ba, ba ya nuna mata komai, har tambayarta yake yi ko akwai wata matsalar, amma tana gani bai ƙarasa sakin jiki da Huzaif ba.
Husna abubuwan suka yi mata yawa a kwakwalwa, ga nauyi da ƙirjinta ya yi sai kawai ta shiga zubar da hawayenta fiye da wanda ta soma a farko. Tana so ta fidda layu da suke ƙasan katifarta amma kuma tana ji a jikinta dagaske Huzaif zai juyamata baya a shimfiɗa. Idan kuwa namiji bai ƙaunar haɗa shimfiɗa da kai, ai duk sauran abubuwan da zai biyo baya a banza.
"Zan yi ta istigfari, amma ba zan iya cire wa ba. Allah ka sani ina son Yaya Huzaif, Allah ka sanya masa soyayyata ninkin wanda nake yi masa a zuciya."
Ta furta hakan a fili kafin ta share fuskarta ta miƙe ganin yamma na ƙara yi ba ta kuma ba ƴar aikinta umarnin abin da za ta girka na dare ba. Son jiki da sangarta irin na Husna ya sa ko ruwan zafi ba ta dafawa sai dai ƴar aikinta ta yi. Sai dai har gobe bisa umarnin Hajara, ba ta taɓa bari ta shigar mata turakar miji ba, ita ke gyarawa duk domin kar a hango binnin da suka yi a ƙasan katifarta.
***
Yau tun sha biyu Sadiya suka fito daga aji, ba kuma za su ƙara shiga ba sai misalin ƙarfe huɗu na yamma. Magiya Nudrat ke mata akan kar ta yi zaman yini a makaranta ta bi ta zuwa gidansu dake unguwar Kuntau ta gaida Nenenta. Faɗi take.
"Allah kuwa tana ta so ta ganki, kuma ni na tabbata Inna ba za ta yi faɗa ba. Don Allah yau ki zo mu je tare."
Sadiya ta yi shiru jikinta a sanyaye, ita fa ba ta son shishshigewa Nudrat Yaqoob don a iya sati ukun da suka jera su na karatu tare, ta fahimci duk inda yarinyar ta fito, to fa gida ne na masu hannu da shuni da suka