Showing 3001 words to 6000 words out of 124441 words

Chapter 2 - Kazar Kwanci Hausa Novel Complete

tana maida duba ga Sadiya dake tsaye gefen Innarta, kamar ba za ta yi ba sai kuma ta tuno marin da ta sha ta ƙarasa ta karɓi jakar hannun Husna ta shige dakinsu idanunta cike taf da kwalla, ban da gidansu, ina ne gidan da ƙarami ya raina babba ya mayar da shi tamkar bawansa. Ɗaki ne wanda ba ta da makwanci sai ƙasa a katifa yayinda Hajara ta maida gadon nata ita da Husna. A farko ma a ƙasa Sadiyar ke kwana sai da Inna ta yi magana ne sannan Malam ya siyo katifa maidaidaiciya ya ce Sadiyar ta dinga kwanciya a ƙasa acewarsa ai gaskiya Hajarar ta faɗi, gadon ya yi musu kaɗan su uku duk kuwa da girmansa.
A tsakar gidan kuwa Hajara ba ta ko gaida Inna ba ta yi ɗakin, Sadiya ta fito da sauri gudun kada ta yi mata wani laifin. Inna ta bi ta da kallo sannan ta maida ga Anti Hafsatu dake sallama riƙe da jaka ganin haka Sadiya ta karɓa ta kai ɗakin ta ajiye. Falon Inna suka shiga gaba daya aka zauna ana gaisawa. Husna da har lokacin ba ta bar yiwa Inna kallon mai laifi ba da ta tauye rayuwar Yayarta ta hana ta aure saboda ba ita ta haife ta ba, zama kawai ta yi amma fuskarta gaba ɗaya babu wani annuri.

"Ku ɗan bamu wuri toh, zamu yi magana." Cewar Anti Hafsatu tana dubansu, Husna ɗan taɓe baki tayi sannan ta miƙe, Inna ta bi shigar ta da kallo. Wani leshi ne wanda ko ba a faɗa ba a ido an san mai tsada ne an mata ɗinkin riga da siket da ya kama jikinta don ma dai babu wani abin a zo a gani a surar domin duka duka shekarunta goma sha biyu a sannan amma sai ka dauka ta gurmi Sadiya saboda girman jiki. Wannan leshi yana ɗaya daga cikin irin ɗinkunan da Hajara ke mata. Ko kusa Inna ba ta kaunarta da ire-iren ɗinkunan masu kama jiki sai dai ba ta isa ta yi magana ba Malam zai hayayyako mata ya goyi bayan ƴar gaban goshinsa Hajara.

Bayan ficewarsu Anti Hafsatu ta soma magana fuska dauke da damuwa.

"Inna na sani dole za ki fuskanci matsaloli game da fasa auren nan na Hajara da ake yi. Amma don Allah ina roƙon ki ƙara hakuri kuma ki toshe kunnuwanki daga dukkan wani abu da zai je ya zo ko a ɓangaren ƴan uwana ko danginmu. Mutane ne a yanzu sam ba su da tawakkali, gutsiri tsoma ya yi musu yawa. Ki yi hakuri da dukkan abin da su Gwaggo suka ce maki."

Inna Mairamu ta ɗan yi murmushi, hankali da nutsuwa irin ta Hafsatu da Zakari yana matuƙar burgeta ainun. Tun faruwar al'amarin idan ka cire ɗaiɗaiku daga danginsu, babu wani ko wata acikin yaran mijinta da ya tare ta da irin wannan kalaman masu sanya nutsuwa da kwantar da hankali sai Zakari sai kuwa Hafsatun don ita Safiyya ma har iskokan ƙarya ta tayi ta zage ta tas.
https://arewabooks.com/book?id=663894ac767a55b1dd421f6a


*Kazar Kwanci free pages 1-5 sun sauka a arewabooks, kuna iya bin link ku sha karatu.*

***


*Kazar Kwanci...*

*Free page*

*05*



"Kar ki damu Hafsatu, da ace zan dinga damuwa da abin da mutane ke faɗi a kaina game da lamarin nan ai da yanzu na ƙare a kwance. Allah shi ne shaida ina zaune da ku da zuciya daya, kaf dinku ina muku kallo tamkar na yaran da na raina da hannuna. Komai zai wuce da yardar Allah. Itama Hajara in sha Allahu mijinta zai zo, Allah ya bata ikon yarda da ƙaddara."

Anti Hafsatu ta share kwalla na tausayin Inna Mairamu, mace mai nunamusu kauna da zuciya ɗaya, ga hakuri da kawar da kai da kuma maida lamarinta gaba ɗaya ga Ubangiji. Kafin Anti Hafsatu ta kai ga cewa wani abu sai ga Hajara ta shigo ta musu tsaye a kai. Wani kallo take watsawa Inna kamar ta ga kashi fuskarnan jage-jage da ruwan hawaye tun bayan Husna ta fesa mata cewa Anti Hafsatu ta fito da su wai za ta yi magana da Innar ta yi saurin fitowa ta laɓe. Komai a cikin kunnenta suka faɗi.

"Ke Hajara wane irin rashin ladabi ne wannan? Mu kika tsayawa a kai haka tamkar wasu sa'anninki?"

Hajara ba ta ko bi ta kan Anti Hafsatu mai wadannan zantukan ba ta ɗora nata zancen.

"Duk abin da ka yiwa ɗan wani a rubuce yake sai an yiwa ɗiyarka. Abin da kike fatan ya kasance a kaina, Mairamu (kamar yanda take kiranta tun farko wanda har ta koyawa Husna) ki sa a ranki har abada ba zai tabbata ba sai dai ki gani akan Sadiya. Zama ba aure, karuwanci, cikin shege duk za ki gani a jikin wannan ɗiyar taki mai kama da zabiya. Aure kuma ko ana ha maza ha mata zan yi shi, ki zuba idanu ki ga ikon Allah. Ƙaryar mutum wallahi!"

"Ke Hajara!" Anti Hafsatu ta mike lokaci guda tana kiranta murya a ɗage, hannu ta ɗaga da niyyar marinta ko me ta tuna sai ta dunƙule ta fasa ta ɓige da nuna ta da yatsa idanunta na fitar da hawayen baƙin ciki. Ita ko Inna Mairamu kanta a ƙasa ta runtse idanu tana ambaton sunan Allah, zafin kalaman da Hajara a yau ke jifan ɗiyarta da shi da mummunan bakin da take yi gareta ya sanya ta kasa jure yin shiru wannan karon ta ɗago kai tana kallonta.

"Hajara kar ki bari Allah ya kama ki da laifin ƙazafi da kuma ƙage. Sadiyar dai da kike aibatawa kin fi ni kusanci da ita don ko yau rabuwar aure zai iya zama dalilin da zan nisanta da ku gaba ɗaya, ita ɗin kuwa babu yanda za ki yi da ita saboda dolenki ce kuna tsatsonki."

"Hajara ba ki da hankali, kin manta wace ce ita kike a wajen mahaifinki? Wallahi ki kiyaye harshenki domin nan gaba zai iya haifarmaki da dana sani marar iyaka. Yau ace Mama na raye an fadamaki za ta ji dadin irin wannan abu da kike aikatawa? Ko kuwa an faɗamaki Husna za ta so ki dinga yiwa Mahaifiyarta irin wannan cin kashin?"

Idanun Hajara har ƙanƙancewa ya yi tsabar bala'i ta dubi yayarta murya a sama ta ce.

"Ki bar kiran Mamana a wannan sha'anin, tana can kwance cikin kabarinta. Alhamdulillah ta rabu da mutane lafiya, uwa uba ta rabu da mijinta lafiya yana mai addu'a da nema mata gafarar Ubangiji. Sannan Alhamdulillah uwata ba ta cutar da rayuwar kowa ba. Husna kuma ita kanta ta fahimci wace ce Babarta Mairamu, ta soma gane ita ke haddasa rashin yiwuwar aurena. A hankali za ta gane komai."

Inna Mairamu zuwa lokacin ma ta kasa ƙara uffan, Anti Hafsatu kuwa zagin Hajara take yi kawai tsabar takaici, abin da ya hana ta kai mata duka bai bwuce dokar da Malam ya sanya musu akan Hajara ba, har Allah ya isa ya yi ga duk wanda ya sa hannu ya taɓa masa ita. Koda dai ba akan Hajara ba kawai, shi tun fil'azal mutum ne da babu wanda ya isa ya dokar masa yara.

"Lallai yau na ƙara yarda ba za ki taɓa sauya hali ba. Wannan rashin hankalin da kike yiwa Inna wallahi muddin ba ki bar yinsa ba sai kin ga sakamakonki a rayuwa. Shashashar banza da wofi wacce ba ta san girma da mutunci Dan Adam ba."

Ita dai Hajara guntun tsaki ta ja ta fice tana banko labulen, Sadiya dake kicin tana ganin ta shige ɗakinsu ta fito a guje ta yi wajen Innarta tana kuka sosai a duniya ta tsani Hajara ba don komai ba sai saboda cin zarafin Innarta wanda nata ya ninka na sauran yan uwan, sukan ma nuna halin ko in kula irin na ƴan boko ga Inna, amma ita kuwa idanunta take murjewa ta ci mutuncinta son rai.  Itama Innar nata hawayen ba su bar zuba ba. Anti Hafsatu kuwa hakuri take ta ba Inna kamar harshenta zai tsinke. Har sai da Innar ta dakatar da ita da nuna nata kar ta damu babu wani abu.

  A can ɗakin kuwa, Husna ta ji komai da ya wakana zuciyarta ta ɗan yi babu dadi, babu wanda zai so a dinga cin zarafin mahaifiyarsa haka, amma kuma ai a ganinta gaskiya Antinta ta faɗi, duk abin da ka yiwa wani za'a yi wa naka. Har Hajara ta shigo ba ta motsa daga inda take zaune rike da babbar wayarta ƙirar Infinix da Antin ta siyamata wai ta dinga kallo. Akan wayar ma sai da Malam da Inna suka yi faɗa, ba ta ga dalilin da za'a ba Husna waya ba, duka-duka a ganinta yarinyar shekarunta nawa a duniya? Karshe dai da Malam ya yi mata kaca-kaca dole ta zuba idanu, takan yiwa Husna nasiha da nunamata irin hakan da ake mata sam ba gata bane, amma yarinyar sai take ganin kawai Innar ta takura mata ne.

"Anti Hajara."

Cewar Husna fuskarta dauke da tsantsar damuwa, ita har ta rasa ma bayan wa za ta bi, takan ji ciwo idan aka yiwa Inna, kuma takan ji zafin asirin hana aure da aka ce Inna ta yiwa Antinta.

Hajara ta dube ta sai ta ƙara fashewa da kuka ta janyo hannunta cikin nata.

"Momina, meyasa Mairamu ba ta kaunar ta ga nayi aure? Me nayi mata da take fatan na dauwama a gida? Shikenan don uwata ta mutu sai na zama marar gata? Kinga don nace abinda ta yimin za ta gani a kan Sadiya shi ne Anti Hafsatu har kusan dauke ni da mari ta yi. Wato ba ta son a yiwa Sadiya amma idan da ace ke nace a yiwa babu abin da zai dame ta ko? Na fadamaki, saboda kina kaunata shiyasa Mairamu ta fi nunawa Sadiya so sama da ke, hum, ai shikenan. Ki yi addu'a na samu miji na yi aure, wallahi gidana za ki koma."

Husna itama kukan take yi, bilhakki tausayin Antinta take ji, tana kuma jin zafi idan ta tuna wai Mairamu ta fi kaunar Sadiya saboda ita. Ta kuma soma yarda da hakan, kuma Hajara ta ce ba don komai ba ne sai ganin Sadiya kyakkyawa ce za ta yi amfani da ita domin ta zame mata tamkar jari, ita kuwa tunda ba ta da kyawun fuskar Sadiyar, kuma wai Sadiyar sunan mahaifiyar Innar ta ci, ita kuma saboda sunan maman su Hajara ce kuma matar da Babansu ya fi kauna shi ne dalilin da yasa komai ta aikata sai ta ce bai yi ba ta daina.

"Kiyi hakuri Anti, kinji? Nima na fi so kiyi aure na bi ki gidanki. Na gaji da zama tare da Mairamu tunda ba ta kaunata."

Hajara ta murmusa ba tare da ta ce komai ba sai aikin kallon lallen da aka zana mata a hannu don bikin aurenta har ma ya soma gogewa.


©Rufaida Umar.
https://arewabooks.com/book?id=663894ac767a55b1dd421f6a


*Kazar Kwanci free pages 1-5 sun sauka a arewabooks, kuna iya bin link ku sha karatu.*

***
*Kazar Kwanci...*

*Free page*

06


Anti Hafsatu ba ta kuma bi ta kan Hajara ba, abin da ya faru kuma bai sa ta iya zaman jira har Malam ya dawo su gaisa ba, tana yin sallar azahar ta ci abinci ta tattara ta bar gidan. Sadiya kuwa kamar yanda ta saba haka ta zauna tana taya Inna da wanke-wanken kwanukan da suka ɓata na abincin rana, Hajara da Husna ko ta kan abincin ba su bi ba, tana nan tana gyara wurin da ta kammala aikin Husna ta fito yafe da siririn gyale ta shuri takalmanta ta fice daga gidan. Da idanu kawai Sadiya ta bita, can kuma sai ta dawo hannunta riƙe da leda babba sai ɗaya dauke da lemo da ruwa ta shige ɗakin. Ita kuwa Sadiya tana kammalawa ta nufi dakin Innarta, kamar yanda ta bar ta haka ta tarar da ita. Ta zauna fuska dauke da damuwa.

"Haba Inna, don Allah ki bar damun kanki da tunanin abin da ba za ki iya gyara shi ba."

Inna ta sauke ajiyar zuciya ta dube ta.

"Kar ki damu Mamana, ba wannan ke damuna ba, rayuwar Husna nake tausayawa, an ɗauki turbar lalata min tarbiyyarta amma ina ji ina gani ban isa na yi magana ba. Wannan shi ne damuwata."

Sadiya ta sauke ajiyar zuciya.

"Ki cigaba da addu'a Inna. In sha Allahu komai zai yi daidai."

Ta gyadamata kai.

"Allah ya dafamana."

"Amin inna."

***

WAIWAYE...

Malam Sa'ad Shagari ya dubi Mairamu cike da nutsuwa. Ita kuwa kanta na ƙasa tana ɗan murmushi. Shima sai ya tsinci kansa da murmusawar kafin ya soma magana.

"Sai kika yi mamakin gani na ko Mairamu? Ban ji kin tambayi abin da ya kawo ni ba?"

Ba tare da ta dube shi ba ta amsa.

"Ba komai, nasan ko da me ka zo alheri ne ai Malam, ya gida ya kuma ƙarin hakuri? Naji a wurin Malama Fauziyya cewa uwar gidanka Allah ya yi mata rasuwa, Allah ya gafarta mata na so shiga da na dawo na yi maka gaisuwa duk da ya dauki lokaci amma Allah bai nufa, kuma sadda aka yi rasuwar sai nima abin ya zo kan gaɓa, an yi min wata rasuwar a can gida na tafi, yayata da muke uwa daya uba daya, shi ne ma dalilin jimawata ban dawo ba."

"Allahu Akbar, Allah ya gafarta mata."

Mairamu ta amsa da amin, shiru ya ɗan biyo baya kafin ya ɗora.

"Mairamu, koda ban faɗa ba, nasan Malama Fauziyya ba za ta rasa sanar da ke kaɗan daga dalilin da yasa na zo wajenki ba. Amma zuwa da kai ya fi saƙo. Kamar yanda kika sani, Marigayiya matata Hajiya Asma'u, da mahaifina da mahaifinta uwa daya uba daya, hakanan iyayenmu mata su ma auren dangi na zumunci ne ya faru tsakaninsu har suka haife mu. Wanda cikin iko na Allah soyayya ta ƙullu tsakanina da Asma'u tun tana matsayin ɗalibata har Allah ya nufa ita za ta zamo uwa ga ƴaƴana bakwai. Ba zan ɓoyemaki ba, ta kasance mace mafi soyuwa a gareni, bana jin a duniyata na taɓa son wata ɗiya mace irin son da na yiwa Asma'u. Mace mai hakuri da kuma kauda kai, a tsawon shekarun da muka rayu da juna da ita, saɓanin da za ki ga ya haɗa mu sai dai ko irin na harshe da haƙori, kinsan ɗan adam ajizi ne. Lokaci ɗaya cutar annobar amai da gudawa ya zo da ajalinta, ta rasu."

Ya ɗan numfasa, Mairamu ta ɗan dube shi cike da tausayawa, ko daga yanayin fuskarsa da yanda yake magana za ka fahimci cewa har a lokacin yana jin zafin rashinta, ta samu bakinta da furta addu'ar neman rahma gareta. Ya amsa da amin sannan ya ɗora.

"Shekara guda kenan da rasuwarnan, manya sun matsa akan zamana a haka babu aure, nima kuma ban ga amfaninsa ba ko don kare mutuncin kaina da na iyalina. Wannan ta sa na nemi zaɓin Allah kuma cikin ikonSa muka haɗu da Malama Fauziyya ta zo shagona neman wani littafi, anan Allah ya kawo zancenki na ji har a raina zan iya zaman aure da ke, wannan shi ne dalilin da yasa na nemi ta nema min izninki kafin na zo gareki. Ba zan yi maki dole ba Mairamu, zan ba ki lokaci nan da kwanaki uku kiyi tunani zan dawo, idan har kin amince sai na samu magabatanki tunda dai mu yanzu ba yara bane ko? Koda dai na fiki tsufa."

Ya ƙarashe da ƴar dariya itama sai ya ba ta dariyar, ta ɗan murmusa. A haka suka tsaida maganar cewa zai dawo ya ji amsa nan da kwanaki uku.

Bayan kwanaki uku kuwa ya dawo, ya samu kyakkyawar amsa inda a take ta amince da yin fatan alheri a lamarin.

Malam Sa'ad bai yi ƙasa a gwuiwa ba ya ja amininsa Alhaji Abubakar wanda ya kasance shahararren ɗan kasuwa a kwari, suka rankaya wajen ƙanin mahaifin Mairamu wanda ta ke zaune gidansa tun bayan rasuwar iyayenta.

A sati biyu aka kammala komai, aka tsaida ranar daurin aure. Sai a wannan lokacin ne kuma Malam Sa'ad ya tara yaransa kaf domin sanar da su.

Ya dube su, su din ma shi suke kallo, sun riga sun ji labari a wajen ƴan uwa sai dai su na fatan ji daga bakinsa. Ai kuwa yana faɗi, Hajara ta shiga kuka.

"Wayyo Mama, shikenan mutuwa ta raba mu da ke. Yanzu Malam zai ƙara aure. Na tabbata marainiya."

Malam ya bita da kallon tausayawa, Safiyya ma sai da zuciyarta ta karye. Anti Hafsatu kuwa ba ta ce komai ba sai fatan Allah yasa ko wace ce ta maye musu gurbin Mamarsu. Caraf kuwa Mustafa ya karɓe.

"Aa Hafsat, bar wannan magana. Ai babu wata da za ta iya maye gurbin Mama a zuƙatanmu. Malam dai ya yi aurensa kawai, muna mishi fatan zaman lafiya."

"Wannan hakane. Ai babu kamar uwa. Malam Allah ya sanya alheri." Cewar Baba Habu.

Hashimu kuwa babu abin da ya dame shi, kusan shi ya ma fi su halin ko'in kula da irin wadannan al'amuran, a ganinsa mene ne don Abban ya yi aure? Matar dai ai ba zama za su yi da ita ba tunda duka suna da gidajensu sun yi aure. Safiyya ma an saka ranar aurenta an kusa sai ko Hajara auta ƴar sakandire.

Haka dai Malam ya kammala maganarsa ya tashi ya bar su don kukan Safiyya da Hajara na neman karya masa zuciya. Sai da Hashimu ya tsawatar kafin su nutsu su bari.

"Murna kake yi kenan da auren Yaya Hashimu?"

Baba Habu ya tambaya. Hashimu ya ja tsaki.

"Ina ruwana don Malam zai yi aure? A kanmu za ta zauna? Ku mene ne naku ciki? Kuna fa gidajenku, idan ma ba ku so ba, ba za ta taba sanya ku a idanu ba ballantana wani mu'amalar ta haɗa ku da ita? Ni fa da dai ya auri wata cikin dangi gwara wata can bare da ba mu san ta ba."

"Wallahi kuwa, nima haka na gani Yaya, da dai Malam ya kwashi wata a ƴan uwa da suka yi zumunci da Mama, gwara ya yi aurensa daga can waje." Zakari ya furta don shi dagaske ya ma ji dadin auren mahaifin nasu, zamansa haka tausayi yake ba shi koyaushe idan ya dawo gida sai dai ya yi zaman jugum da tunani.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login