Showing 123001 words to 124441 words out of 124441 words

Chapter 42 - Kazar Kwanci Hausa Novel Complete

zuciya, wai Antinta, ta ina ɗin? Ita fa tunda ta fahimci Anti Najma na sonsa ta ji inama ita ya aura ba wannan 'yar talakawar bayinsu ba.

"Sadiya."

Ta ɗago idanunta da suka ɗan cicciko da ƙwalla ta dube shi kafin ta sadda kai gudun kar ta ƙara janyowa kanta tsana a wurin Fulani  ace tana kallon mijinta. Murya na rawa ta amsa kiran da Maina ya yi mata.

"Tashi ku je ɗakin Ummulkhairi."

Ta amsa da toh sannan ta miƙe ba tare da ta ƙara gangancin kallon Fulani ba don tsoron kuma me za ta tsinta a saman fuskar karo na biyu.

Ummulkhairi ta yi gaba tana turo baki, ita kuwa Sadiya tafiyar take yi amma a ɗar-ɗar, gani take yi kamar Fulanin tsawa za ta daka mata sai dai har suka shige ba ta ji ta ce uffan ba.

Rai a ɓace Fulani ta dube shi, kafin ta yi magana ya riga ta da taushin murya ya ce.

"Ki yi hakuri, don Allah kar ku dinga irin haka a gabanta. Ba girmanku ba ne. Ya dace ku girmama zaɓin Mai Martaba, ku ba ta dama ko yaya ne kafin ku yanke hukuncin tsanarta. Ina jin ciwon akwai wani abu da a rayuwata da na aikata wanda bai muku daɗi ba. Kar fa ku manta, ni ma bin umarnin Mai Martaba nake saboda ban isa kaucewa ba. Kuma ba na jin zan iya. Kamar yadda ku ka isa da ni, toh don Allah ku taya ni addu'ar sauke nauyin da Allah ya ɗora min."

Jikin Fulani ya ɗan yi sanyi, duk abin da Maina ya ce ta sani iyakar abin da ke ransa ya faɗi, yana tsananin gudun ɓacin ranta, ba ya ƙaunar abin da zai sosa ranta. Ta sani dagasken yana cikin damuwar hakan. Toh ya za ta yi? Haj Falmata ta ƙara jaddada mata kar ta yarda ta ba da ƙofar da Sadiya za ta sake a gidan. Ba ma girmanta ba ne haɗa surukata da dangin matsiyata da ba su gaji sarauta ba. Duk sadda ta ji kamar ta bi shawarwarin manyan yaranta mata waɗanda ba su ɗauki auren Maina da wani muhimmanci ba, akan hakan ba wani abu ba ne tunda dai an yi wa iyayenta kyakkyawar shaida, da zarar ta yi magana da Haj Falmata sai ta ji zuciyarta ta ƙara tunzura da tsanar Sadiya. A gefe kuwa ɗiyarta ta biyu, Gimbiya Juwairiyya ce dake zama a Abuja mai auren wani ɗan majalisa ita ko garin ba ta shigo ba duk a sanadin tsanar labarin auren da ta yi don a cewarta Mai Martaba ya nuna ƙarara ya fi fifita farin cikin yaran Haj Saratu a kan nasu.

"Amma dai ba tare da ita za ka tafi ba ko?"

Maina ya girgiza kai.

"A'a. Kun ce ba da yawunku ba."

Ta sauke ajiyar zuciya. Wani tunani ne ya faɗo ranta, me zai hana ta saka Sadiya dawowa ɓangarenta da zama? A nan ne za ta ƙara gane take-taken yarinyar da ma inda ta dosa. Wata ɗaya dai ai duk wasu munanan ɗabi'unta za su fito fili. Hakan ya sa ta dubansa.

"Ina so matarka ta dawo ɓangarena da zama har ka dawo."

Ya kalle ta da sauri, har ransa ya sani ba haka kawai ta nemi hakan ba. Ya ji a jikinsa ƙuntatawa Sadiyar kawai za'a yi, toh amma kuma me zai ce?

"Umarni fa na ba ka, ba shawara ba."

"Toh." Abin da ya furta kenan kawai, ita kuwa ta ji ɗan sanyi a rai, ta ƙudurta a wata ɗayan da Sadiya za ta yi a gabanta sai ta gwammace inama ba ta yarda ta tako Gombe ba, balle a yi maganar shigowa masarautar da sunan matar ɗanta.

A ɗakin kuwa, wata kujerar da ke gefe kawai Sadiya ta nemi ta zauna. Komai na ɗakin fari da pink ne har da wasu ɗirka ɗirkan teddies a saman gadon, ita kuwa Ummulkhair kai tsaye ta wuce gadon ta kishingiɗe ta na danna wayarta. A haka Najma ita ma ta shigo. Ganin Sadiya a gefe ya sa ta ɗaure fuska ta ma fasa gulmar da ta shigo yi natan, haushi ne ya cika ta sakamakon laɓen da ta yi wa Fulani da Maina ta ji a na batun zaman Sadiya a wajensu kafin dawowarsa daga tafiya.

"Matar Yayana me ya ɓata min ranki?"

Sadiya sai ta ɗago kai ta dubi Ummulkhairi duk kuwa da tana mamakin ya kasance wai da ita take. Sai kuma ta ga Najma saboda ba ta san ma ta sadda ta shigo ba ita ma ta shagala can a bai wa Zahra amsar saƙon da ta turo mata tana tambayar meye labari. Najmar sai da ta kalle ta suka haɗa idanu kafin tana wani murmushi ta kauda kai cike da jikin daɗin wannan suna da Ummulkhairi ke yawan kiranta da shi ta yi farr da idanu ta ce.

"Ke ma dai Auta da zolaya ki ke, ni ce matar Yayan? Toh wanne ki ka ban a cikin yayyun naki?"

Ummulkhairi ta yi dariya.

"Ai ke ɗin babban goro ce don haka kuwa sai magogin ƙarfe. Ki saka a rai Maina na dawowa kamar an yi aurenku an gama ne. To wa muke da shi da ta fi ki?! Ai gado sai ɗan gado, kuma jinin sarauta ya fi ƙarfin zama da rayuwa da wata baiwa can ƙazama. Ke ce daidai Yayana. Allah dai ya kai mu lokacin."

Suka yi dariya da cafkewa lokaci guda gami da shewa. Ta nuna kamar ba ta san suna yi ba amma kuma a ƙasan ranta maganar ta ɗan shige ta. Baiwa kuma ƙazama? To waye ba bawan ba? Ita kalmar ƙazamar ma ya fi baƙanta ranta. Da me mutanen nan suke taƙama ne haka?

Kusan dai yinin da ta yi a wajen Fulani ba mai daɗi ba ne don ko kallo ba ta ishe ta ba, asalima bayan tafiyar Maina sanya ta aka yi fitowa daga ɗakin Ummulkhairi ta komo falon ta raɓe a gefe. Haka dai ba ta ishi mutanen falon kallo ba sai ma habaici da akan jefa mata kaɗan kaɗan, abinci ma Sadiya ba ta iya sakin jiki ta ci ba. Sai bayan sallar isha'i ne ma Fulani ta dube ta sadda suna zaune su biyu sai ko Sailuba da ke gefe. Su Najma waɗanda suka fita unguwa wai bikin wata ƙawarta a sannan ne suka dawo. A lokacin ne kuma Maina ya zo ta yi wa Fulani sallama suka fice gaida Mai Martaba. Sun iske shi zaune, bayan sun gaisa ya ke ƙara tambayar Sadiya lafiyarta yana murmushin ganinsu tare haka. Ta amsa a sanyaye. Sallama ta yi ta miƙe ta fita don ba su wuri. Koda Maina ya ƙara yi wa Mai Martaba batun tafiyarsa a washegari, sai da ya ɗan yi shiru sannan ya ce.

"Sati huɗu bai yi yawan da ya kamata ka ɗauki matarka ba?"

Ya kasa cewa uffan, ya ji har ransa inama hakan zai iya kasantuwa amma kuma ba ya son Fulani ta yi fushi da shi don haka a ladabce ya ba da uzurin ayyukan da yawa kuma ba lallai ne ya cika watan ba.

"Allah ya sa albarka. Ita kuma zan yi wa Hajiyarku magana a samar mata wanda zai taya ta zama."

"Allah ya taimake ku, wai da Mami ce ta nemi ta zauna a ɓangarenta har zuwa lokacin da zan dawo."

Shiru ya yi bai ce uffan ba, ko a jiya sai da Fulani Kausar ɗin ta zo mishi da batun wai Maina ya ƙara aure ya nuna bai amince ba, anya babu ƙuntatawa a faɗin da ta yi cewa Sadiyar ta zauna a wajenta? Da kuma ya yi wani tunani sai ya yi ɗan murmushi da girgiza kai.

"Hakan ma ya yi."

Maina bai so ba, ya so ace Mahaifin nasa ya nuna ƙin amincewa da batun Maminsa, ya san shi kaɗai ne zai iya takawa Mamin burki akan Sadiya. Amma kuma jikinsa sai ya yi sanyi jin abin da ya fito daga bakin Mai Martaba. Haka ya yi mishi sallama ya fito ya iske Sadiya zaune a ɗan barandar shiga falon tana jiransa.

Har suka je gida yana kula kamar ranta babu daɗi amma tana ta ƙoƙarin duk abin da ya ce ta amsa da murmushin yaƙe.

A ɓangarenta kuwa, suna isowa ta faɗa ɗakinta ta zauna gefen gado tana fitar da hawaye. Karshe ma kwanciya ta yi saboda gaɓoɓinta da ke ciwo na zama a wuri guda da takura. Tunani take wai kuwa wannan tsanar da Fulani da su Ummulkhairi suka yi mata akwai ranar da za su ƙaunace ta? Me ta tare musu? Kawai saboda ita ba 'yar kowa ba? Ta jima a haka kafin ta iya miƙewa ta rage kayan jikinta ta faɗa wanka.

***
KANO

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login