Showing 30001 words to 33000 words out of 124441 words
sakandire. Haƙiƙa an rusa farin ciki da burinta na zama ƙwararriyar likita a fannin mata. Wannan abu yana nukurkusarta kwarai. Husna kuwa ta yi sanyi sosai kwanakin har kunyar Innarta take ji na irin maganganun da ta yi ta yada mata duk a dalilin Antinta wacce komai ya bayyana ita ce marar gaskiya. Gaba ɗaya ta dawo wata shiru-shiru, hatta da tsiwa ta rage yi ga Sadiya. Dama can wasu abubuwan sun faru ne a dalilin Hajara. Amma don ƙauna tana ƙaunar ƴar uwarta ta, duk da hakan akwai abin da ya riga ya ginu a zuciyarta na cewa Inna ta fi son Sadiya a kanta. Sai ya kasance komai aka yi takan auna shi da rashin kaunarta ne ya sa Inna ta yi mata.
***
A ɓangaren Amarya Hajara kuwa, ta watsar da damuwar kowa ban da na mahaifinta da ya yi mata tsaye a ƙoƙon rai tana cin amarcinta. Satinta ɗaya a gidan auren kamar yanda Alh Nuhu ya yi mata alƙawarin ziyartar ɗakin Allah, haka kuwa ta kasance. Nan da nan aka shiga cuku-cukun yi mata passport na tafiya. Ta kira wayar Safiyya ya fi a ƙirga amma don haushinta da take ji ba ta ko ɗaga ba. Hafsatu ce mai sauƙin ciki muddin za ka haɗa Allah da Annabi s.a.w ka roƙe ta abu da niyyar ba za ka ƙara aikatawa ba to nan take zuciyarta za ta yi sanyi. Babu ma kamar da Hajarar ta sanya mata kuka a waya tana faɗin idan ba Hafsatun ba wace ce madadin Mama a gareta, meyasa zs ta hukunta ta kan abin da ya wuce ta ƙi waiwayonta a ɗakin aure. Dole Hafsatu a cikin satin ta je gidan Hajarar ta ziyarce ta. Ita ce ta lallaɓo mata Safiyya suka shirya. Safiyya kuwa ta ce har a ranta ta tuba ba za ta ƙara yi wa Inna wani wulaƙancin ba koda wasa kuwa. Idan da abin da ya ƙara baƙantawa Hajara to fa wannan kalamin ne na Safiyya. Tsanar Inna ya ƙara ginuwa a zuciyarta, ta kuma ci alwashin rusa dukkan farin cikinta, ai ta san yanzun Inna kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha haka ta ke ji saboda duniyar ta mata daɗi tunda asirinta yana waje.
***
Cike da fara'a Malam ya sauke wayar dake a kunnensa yana duban Inna da ita ma ke murmushi don ta fahimci da Amininsa yake wayar kuma ga dukkan alamu baƙi za'a yi a gidan.
"Kin ji fa, anjima da yamma yaran Alh Abubakar suna tafe. Me ya kamata a shirya musu ne? Kin san har da baƙon Indiya, Huzaifa. Ya same ni a can babban gida tun wancan satin an gaisa da kowa, ai na faɗamaki kamar?"
Inna ta gyaɗa kai tana murmushi.
"Ka faɗa min Malam. Nan ne dai bai zo an gaisa ba."
Malam ya yi ƴar dariya.
"Shi ne ai yanzun zai zo da ƙannensa. Bari na wuce kasuwa da Sadiya sai ki lissafa mata duk abin buƙata ta taho da shi."
Inna ta amsa da toh. Kasancewar ranar Asabar ce kuma aka yi sa'a yau ɗin basu da makarantar islamiyya sakamakon rasuwar da aka yi wa mai makarantar.
Tana zaune ta kammala gugar kayanta da ta wanke, zuciyarta fara sol take jin ta a yau ɗin adalilin wai yau Baba Habu ne ya shigo har cikin gida ya gaida Innarta, shi ne har da zama a falon Innar, hakan kawai ta san nasara ce, kuma addu'a ba ta faɗi a ƙasa. A sannu-sannu komai zai wuce tunda kusan duka yayyunta sun sassauta wa ransu tsanar da suka yi ga Innarta.
"Kin gama? Tashi ki sanya hijabi za ki bi Malam kasuwa, cefane za ki yo muna da baƙi."
Nan Inna ta zayyana mata dukkan abin buƙata ita kuwa ta kwafe a ƙaramar wayar Innar wanda kusan rabin amfani ita ke yi da shi.
"Inna su waye zasu zo?" Faɗin Husna dake kwance saman katifa tana buga game a wayarta.
"Yaran gidan Abbanku ne."
Husna ta yamutsa fuska ta yi shiru ba tare da ce uffan ba. Ai su Meenat ɗin ba baƙin gidan ba ne, ita ba ta ga dalilin da yasa duk sadda wani a ahalin Abba idan ya tashi zuwa Malam ke sanya a yi musu hidima babba.
Sadiya kuwa suna kammala lissafinsu da Inna ta kai kayanta cikin sif ta ɗauko gogaggen hijabinta ta zura. Jin hon ɗin Malam a waje ya sanya ba shiri ta fice.
Malam bai wuce shagonsa ba sai da ya kai ta ƴan kura sabon gari ya tabbatar ta siya komai na buƙata sannan ya ɗora ta a ɗan sahu ya biya a kai ta har ƙofar gida tukunna ya wuce shago. Ba kasafai ya ke zuwa a irin ranakun nan ba, sai idan yana da abu mai muhimmanci da zai yi a kasuwar.
***
Sadiya da Inna suka shirya koma, dambun shinkafa da ya ji kayan lambu da hanta wanda aka yanka ƙanana a ciki. Sai ko chicken pepper da aka yi daban. A gefe kuma kunun aya ne mai sanyi da garɗi a baka. Har suka kammala Sadiya ta gyara tsakar gidan tas baƙin ba su iso ba. Ganin haka tana idar da sallar la'asar ta faɗa wanka saboda wani irin gumi da take haɗawa. Koda ta fito ɗakinsu ta shige, lokacin ƙamshin turaren wutar da Inna ta saka ya baɗaɗe tsakar gida tamkar a nan aka saka ba ɗakuna ba. Takaicin wannan bacci na Husna da yammaci ya kama ta. Ba ta da aikin da ya wuce ta gama danna wayarta ta kwanta bacci. Ta sa hannu ta ɗan bubbuga ƙafarta. Husna a ɗan firgice ta buɗe idanunta.
"Malama ki tashi kin san dai Inna ta shigo ta ga ki na baccin yamma ba za ki ji ta daɗi ba ko?"
Husna ta hau turo baki, kafin ta kai ga cewa wani abu suka tsinci sallamar mutane a tsakar gidan. Suna hango su ta labulen ɗakin mai shara-shara wanda kai na ciki za ka iya ganin na waje, amma na waje ba zai ganka ba idan da haske. Meenat ce kan gaba sai ko su Amir da Amira, Zee Mama, Affan. Kai duka dai yaran gidan Abban ne kamar yanda Malam ya ce idan ka ɗauke su Radeeya dake gidajen aurensu. Inna ce ta tarbe su hannu bibbiyu, ta kai su zuwa falon Malam wanda ya ce anan za'a sauke su idan sun zo. Meenat kuwa kai tsaye ta shigo wajen su Sadiya. Ganin Sadiya na shafa mai ta saki baki galala.
"Kar ki ce min sai yanzu ki ke wankan safe?"
Harara kaɗan Sadiya ta jefe ta da shi.
"Sai aka ce maki ni ke ce ko? To zafi ne ya ishe ni Malama."
Meenat ta yi dariya. Tana maida duba ga Husna wacce ba su wani fiye ɗasawa ba, yanzun ka ji kansu tamkar wasu sa'annin juna.
"Sannu kaasa uwar bacci, ke dai aikinki kenan."
Husna ta ja guntun tsaki.
"Oho dai, ai baccin ma lafiya ce wasu su yi ma mana. Aikin ɓurr."
"Ku, dallah tare fa muke da Yaya Huzaif, ya dawo daga Indiya."
Dukkansu sun san shi, amma a can ɗin ma babu wani sabo tsakaninsu don ba zuwa gidansu yake ba. Su ɗin ma idan sun je lesson, ba kasafai suka fiye haɗuwa da shi ba. Amma duk da haka sun taya Meenat wacce ba ta da hira sai ta sa idan suna tare murna. Ai sai Husna ta miƙe.
"Ke bari na gyara fuskata na je na ga Yaya Huzaif."
Dariya Meenat ta yi. Ita ko Sadiya juyamusu baya ta yi ta cigaba da shirinta tana murmushin wautar Husna.
Doguwar rigarta na shan iska kalar baƙi da ruwan toka ta saka. Irin rigunan nan masu zuwa haɗe da mayafi. Ƙarshen mayafin an yi adon fararen zarurruka mai gashi gashi. Ta saka hula a kanta. Daidai lokacin Inna ta shiga kwala musu kira daga tsakar gida akan su je can a gaisa. Meenat ta mike ta koma cikin ƴan uwanta, Husna kuwa daga bandaki ta fito bayan ta gama wanke fuskarta da sabulunta mai ƙamshi irin wanda Hajara ke kawo mata sadda suna tare. Sadiya ko tuni ta fita zuwa kicin don taya Inna hidima. Faranti babba da aka ɗora kayan ruwa da kofuna ta ɗauka.
"Idan kin ke ko Meenat ki kira ta zo ta taimaka maki." Faɗin Inna, Sadiya ta amsa da toh. Ta sani sam ba ta saba da sanya Husna aiki ba, a baya ma ba ta isa ta sanya ta ba hakan ya sa wasu lokutan har mancewa ta ke yi da ita. Sai idan ko Husnar ta ce za ta yi wani abin sannan ta sakar mata. Yanzun ma hakan ce ta kasance, kamar an jefo ta ta shigo kicin ɗin, ba don Sadiya ta kauce ba ƙiris ya rage ta sanya ta yi ɓari.
"Inna me za'a kai? Kawo na tafi da shi." Inna ta dube ta. Riga da siket ne a jikinta ƴan kanti, ganin ba su kama jikinta ba kuma ta yane kan da mayafi ya sa ba ta yi magana ba ta nuna mata ƙaton dispenser irin ta zamani mai mariƙi da ake zuba lemu ko ruwan sanyi a ciki, ita ma yana daga cikin siyayyar da Hafsatu ta yi mata da azumi kuma ya samu kulawa sosai don ba ta fiye amfani da shi ba. Da sauri Husna ta ɗauka ta bi bayan Sadiya.
Sadiya tun kafin ta kai ga shiga falon Malam ɗin ta soma jin tashin muryoyi, dukkansu ba baƙinta ba ne ba idan ka ɗauke mutum ɗaya da ta jima ba ta sanya a idanunta ba, wato Huzaif.
Sallamarta ya sanya su maido hankula gare ta har Malam da ke shan dariyar labarin da Huzaif ke ba su na bambancin al'adarsu da na Indiya, har ma da irin ƙauyancin da wani ɗan Nijeriya ya tafka a can.
Ya amsa sallamar tabbas, ya kuma bi hannun da kallo sa'ilin da ƙaton farantin ya riga gangar jikinta bayyana. Ya maida duba ga wayarsa wacce sam bai kula da sadda aka kira shi ba sai missedcall da ya tarar har sau uku kasancewar tana silent.
"Ina yini, fatan ka iso lafiya?" Zazzaƙar muryarta ya sanya shi ɗagowa kansa yan dube ta. Kanta yana ƙasa tana kallon ƙafafunsa waɗanda sai ka rantse ba su taɓa taka ƙasa ba don har wani sheƙi ta ga suna yi. Sai a sannan ta ɗago kai ta ɗan dube shi.
"Lafiya ƙalau sister..."
Sai ya rasa sunan da zai ambata don har ga Allah ya ga ta fita daban da ƴan gidan. Tana da kyau mai haifar wa da mutum faɗuwar gaba, ga wani irin duka da ya ji ƙirjinsa na yi kamar zai fito. Ya kasa kauda kai daga kallonta kamar yanda ya shiga tunanin ko wace ce a ahalin gidan.
"Sadiya ce fa Yaya. Ba ka gane ta ba ko?"
Cewar Amira wacce ta yi caraf da zancen. Tabbas sai yanzun ya tuno akwai Sadiya a gidan. Ya shafi sumarsa yana murmushi.
"Oh, na gane ta yanzu."
"Ina wuni." Ya ƙara jin wata gaisuwar daga Husna da ke durkushe ita ma tana kokarin ajiye abin hannunta. Sai lokacin ya dubi kannensa yana murmushi.
"To kun ga wannan ko a hanya na gan ta zan san ƙanwata ce. Wannan kuwa idan muka jeru fa za'a yi tsammanin sato ta na yi."
Aka yi dariya har Malam idan ka cire Sadiya da ta tsuke baki. Huzaif ya kauda kai yana wani murmushi, ba ya son ya cigaba da kallonta, ba zai ce ga abin da kallon ke haifar masa ba. Amma ko mene ne, ya sa ni ba yau ne zai zama ƙarshensa ba. Ƙila akwai tarin abubuwa da yawa da za su iya biyo wa baya.
An ɗan taba hira da Malam kafin ya shige zuwa ɗakinsa, Husna kuwa ji ta yi nan duniya ta samu mijin aure. Wani irin son Huzaif ta ji ya mata dirar mikiya ba tare da ta shirya wa hakan ba. Ita kuwa Sadiya tuni ta fice don kwaso sauran kayan, ganin Husna ba ta da niyyar miƙewa ya sa ta duban Meenat, cikin rashin sa'a kafin ta kai ga duban Meenat din idanunta suka sauka kansa. Wani murmushi ya yi mata da ya jefa ta cikin jin nauyinsa don haka ta fasa kiran Meenat ɗin ta fice daga falon kirjinta na lugude.
*Kazar Kwanci...*
"Lafiya?" Tambayar da Inna ta yi wa Sadiya kenan ganin yanda gaba ɗaya jikinta ya yi la'asar kamar wacce ta rasa sukuni. Sadiya ta yi yaƙe gudun kar Inna ta fahimci komai ta ce.
"Babu komai Inna."
Nan ta soma ɗaukar kulolin abincin guda biyu manya ta yi gaba. Kirjinta sai bugu yake don ta sani ko ba ta kalle shi ba, jikinta ya ba ta cewar idanunsa na yawo a kanta.
"Meenat, zo mu taya Sadiya mana."
Faɗin Amira kenan tana duban Meenat da ta shiririce a dole sai ta tabbatarwa Yayansu ta fi kowa ƙokari da maida hankali a gidan. Sai a sannan ita ma Husna ta bi bayan su, Sadiya tuni ta yi gaba har da su tuntuɓe tsabar saurin ta fita. Kamar ta cewa Meenat wannan yayan naku ya fiye kallon tsiya amma sai ta yi tunanin ba lallai hakan ya yi mata daɗi ba wannan ya sa ta bar wa ranta. Amma fa ba karamin takura yake mata da kallo ba.
Har suka kammala kawo komai suka shiga zubawa Huzaif rabin hankalinsa na ga Sadiya yayinda rabin kuwa ya ke latsa wayarsa. Da uhum da uhm uhm kawai ya ke bin su Affan da Zee Mama don bai taɓa jin hirarsu ta gundure shi ba sai a lokacin. Husna ce ta ajiye mishi komai da aka yi wanda Sadiya ta zuba. Su kuwa matan suka haɗu wuri guda, mazan ma haka. Ya dubi na sa kafin ya ɗan haɗe gira da shagwaɓe murya yana duban Sadiya ya ce.
"Wai meyasa ni za'a ware ni daban? Ni fa ba na cin abinci sosai idan ni kaɗai ne."
Sadiya ta ɗago kai ta dube shi kaɗan, ganin ita ɗin yake kallo sai ta tsuke baki hakan ya sa shi murmusawa. Sau biyu ta yi hakan, kuma shi a wurinsa kyau sosai take masa.
"To Yaya kuma a can ya ka ke yi?" Faɗin Amira kenan.
"Ai ba ni ɗaya ba ne. Akwai abokan karatuna da muke ɗaki guda su biyu, tare muke ci."
"To na zo mu ci tare?"
Husna ta furta ba tare da ta shiryawa hakan ba, ganin kowa ya kalle ta ne ya sanya ta saurin gyara kalamanta.
"Oh, ina nufin ku ci tare da su Yaya Amir?"
Huzaif ya girgiza kai gami da ɗan murmushi. Bai ƙara kula kowa ba ya yi bismillah ya kai lomar farko na dambun bakinsa. Wani daɗi ya ratsa shi, sai ga shi ya zage sosai ya ci abincin, Sadiya rabin hankalinta na kansa, shi kuwa na sa yana kan abincin da ya ji daɗinsa sosai. Haka nan ma kazar ya ci ba laifi, kunun aya kuwa tana kallo sai da ya tsiyaya kusan sau uku yana kurɓewa. Haka nan ta ke yaba tsarinsa, a nutse yake komai, su ma tuni sun kammala sun miƙe. Ita kaɗan ma ta ci saboda rashin sakewa da Huzaif a wurin. Amma don ta su Amira da Meenat, tsaf suke cin abinci tare duk sadda suka haɗu.
"Kai wallahi girkin nan ya yi daɗi sosai. Ni nasan Inna ce ta yi abin ta." Faɗin Meenat tana duban Inna da Malam waɗanda a sannan sun shigo falon. Dariya suka yi, Inna ta amsa.
"Rabin girkin dai ƴar uwarki ce ta yi. Abin da na taimaka mata da shi kaɗan ne."
"Wai Sadiya?" Ta ƙara tambaya tana fiddo ido waje, Sadiya da ke ƙoƙarin kwashe sharar da ta tattare ta fice ta ɗan dubi Meenat ƙasa-ƙasa tana harararta. Meenat kuwa dariya ta yi don dama tsokana ce, ita ta san Sadiya ta iya girki sosai, yawanci idan sun je lesson Antinsu Zulfa'u ba ta nan, ita ke musu girki a ɓangaren kuma su kwashi gara don baiwa kam ta girki Allah ya ba ta shi.
Sadiya ta fice ɗauke da tsintsiya da makwashin shara a hannu tana jin sadda Amira ke ba Meenat amsa da fadin.
"Allah ya shiryeki Meenat, ni dai na san ko iyakar dahuwar indomie ne, ba za ki yi mai daɗin na Sadiya ba. Amma ba wacce ki ka raina sama da ita. Ki yi kamun ƙafa ta koya maki girki Malama."
Ta dai ji wannan amma ba ta ji amsar da Meenat ta ba ta ba. Ta fice tana murmushi. Koda ta koma Huzaif ba ya nan, ta dai hango shi ta tagar falon yana tsaye yana waya ya ba su baya. Kauda kai ta yi. Can ba jimawa ya shigo, nan kuma ya ce su shirya zasu wuce.
"Ba za ku bari a yi Magriba ba? Kar ta risƙe ku a hanya." Faɗin Malam bayan ya kai duba ga agogon dake maƙale a bangon falon. Huzaif ya amsa da toh, so ya ke ne ya bar gidan, ya kasa tantance me yake ji a kan Sadiya. Ya na ƙaryata wani sashi na zuciyarsa mai tabbatar masa cewa wannan shi ake kira Love At First Sight. Bai yarda ba, bai kuma aminta ba. Yana son ya ɗan ƙauracewa ganinta ko zai samu nutsuwar tunani.
Ana ta hira amma shi kuwa jifa-jifa yake sa musu baki. Sadiya gaba ɗaya ta kasa sukuni duk kuwa da cewa ta ɗago kai fiye da sau biyu amma ba ta ƙara kama shi yana kallonta ba. Ta ɗan samu nutsuwa kaɗan, sai ita ma ta sako fuskarta har ake hirar bikin Amira wanda bai fi sauran sati huɗu ba.
Kiraye-kirayen sallar Magriba ce ta katse musu hirar, matan gaba daya suka shige cikin gida. Amira da ke fashin sallah sai ta yi zamanta tana danna waya, su kuwa kowannensu ya ɗora alwala. Mazan ma daga can suka wuce masallaci. Nan kuma suka yi shirin tafiya, Husna sai rawar kai take yi ta kasa sukuni, babba burinta ta mallaki lambar Huzaif ɗin hakan ya sa koda ake ta sallama bayan an taka musu ta miƙa masa wayarta. Ya kai duba ga wayar kafin ya dube ta da alamar tambaya.