Showing 54001 words to 57000 words out of 124441 words

Chapter 19 - Kazar Kwanci Hausa Novel Complete

ta je ga ajalinta. Daƙyar ta mike bayan Zahra ta yi mata ido, har lokacin atamfar da ta sanya na kamu ne a jikinta, fuskarta fayau don ta ce ita sam ba za ta yi kwalliya ba. Ta yafa gyalenta ta fito. Ba ta kula zolayar su Adda Ruƙayya da wasu a ƴan uwan Malam dake soye-soye da yanke-yanke duk na shirin yinin gobe ba, ta yi hanyar falon Malam da sallama ɗauke a saman harshenta sannan ta sa kai ta shiga. Tana kuma ji a ranta ta shirya karɓar dukkan wani abu da zai zo da shi a wannan dare.


"Wannan ma ai zancen banza da wofi ne. Shi wani abu yake sha a can Indiyan da zai kawo mana wannan wasan kwaikwayon? Ina aka taɓa haka? Daga kan Yaya ka koma kan ƙanwarta? Ba zai yiwu ba, bari na je na sami shi Alhajin, sai na dawo."

Malam ke maganar cike da tsantsar ɓacin rai da mamaki don abin akwai ɗaure kai kafin ya sa kai ya fice daga falon. Inna dake zaune ta kasa ce mishi uffan har ya fita balle kuma wata Yayar Malam ɗin Inna Asabe da Ƙanwarsa da suke zaune a falon cike da jimami. Husna dake gefe kuka take yi kamar wacce aka aikowa da saƙon mutuwa.
Sadiya kuwa kallo kawai take bin kowannensu da shi. Babu baka sai kunni, ji take idan ta dage akan sai ta ce wani abu, wannan karon kukan ba zai yiwu ba wataƙila ta shiga kwarara amai tsabar yanda zuciyarta ke tashi sanadin kukan da ta sha. Idanun sun kumbura fuskarnan ta yi jawur da ita. A hankali ta lashi busassun leɓɓanta tana ji kanta na mugun sarawa da ƙarfi, bakinta gaba ɗaya babu ɗanɗano. Tun a daren ta ke kuka har wayewar garin yau da ya kama na yinin bikinta. Ta kai duba ga kujerar da Huzaif ɗin ya zauna a jiya, komai ya shiga dawowa a kwakwalwarta.

Sadda ta shiga falon bayan an sanar da ita zuwan Angon nata, sallama ne ɗauke a saman leɓɓanta. Ya amsa bai amsa ba, ba za ta iya fahimta ba tunda ba ta ji ba, kuma ba kallonsa tayi ba balle ta yanke hukunci a kallon lebbansa. Har ta zauna ba ta ji ya yi magana ba, sai ta ɗago kanta kaɗan ta dube shi, kallon inda take ma ba ya yi, ya wani haɗe girar sama da ta ƙasa yana dunƙule yatsunsa.

"Ina wuni, an zo lafiya?"

Ta tsinci kanta da furtawa. Dama kuma hakan ya kamata ita ta fara gaida shi.

"Lafiya." Shi ne amsar da ya ba ta a taƙaice, shiru ya ƙara samun matsuguni tsakaninsu na ƴan daƙiƙa kafin ta ji muryarsa ya soma magana a kaushashe.

"Sadiya, zan fara da ba ki haƙuri, da kuma roƙonki wata alfarma."

Duk da faɗuwar gaban da ta ji sai ta daure ta haɗiyi miyau tana dubansa, har a lokacin nasa idanun ba sa kanta. Wannan ya ba ta dalilin kallonsa sosai, ya ƙara kyau ya murje abinsa tamkar ba wanda ya je karatu ba. Ba ta ga alamun yana tattare da wata damuwar ba.

"A farkon ganin da na yi maki, na yaudari kaina da sunan sonki nake yi. I am sorry to say, ban san soyayya ba, wataƙila shi ne dalilin da ya sa na ji kamar a raina sonki nake yi. Amma kuma a hankali na soma fahimtar babu wannan son a tsakanina da ke, ba na jinki a raina. Kuma..."

Ya kasa ƙarasawa ya yi ɗan shiru yana furzar da huci. Ita kuma ga mamaki sai ta shiga wani murmushin da ko ba a faɗi ba za ka fahimci zallar yaƙe ne. Don kansa kuma ya ɗora zancensa.

"Ba ke nake so ba, ban taɓa sonki ba Sadiya. Husna nake so da aure, da ita na zaɓi ƙarasa sauran rayuwata ta duniya a matsayin matata."

Anan ne ta ji kamar an buga mata ƙaton guduma a tsakar kai, so take ta tuna wace ce ma Husna? Ji ta yi kamar a ranar ta soma sanin sunan, zuwa yanzu har wani bibbiyu take ganinsa don haka ta riƙe kanta sakamakon jirin da ya soma kwasarta daga zaune. Wannan ba shi ne damuwarta ba, babban burinta ya ba ta haske, ya fahimtar da ita wace Husnar yake so?

"Ina nufin Husna ƙanwarki. Ita nake son aure. Ina neman alfamarki don Allah Sadiya ki taya ni roƙon su Malam su bar ni da abin da nake so. Na rantse maki ji nake idan ban auri Husna ba zan iya rasa raina."

Ya ƙarashe yana mai zamewa daga saman kujerar, sai a lokacin ne kuma ya dube ta dakyau, ita ma ta maida dubanta gare shi. Magiya da roƙo har da hawaye a saman fuskar Huzaif yana mai tabbatar mata idan ya rasa Husna to shi ma mutuwa zai yi. Kawai sai ta ji kuka ya tahomata, ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta ta shiga rerawa. Shi ma gaba ɗaya ya ƙara fita hayyacinsa, wannan magiya da roƙon bai fasa ba kuma ba ta sauya zani ba. Ta gaji da sauraronsa don haka kawai ta share fuskarta ta miƙe, a hankali ta saka hannunta ta zare zoben da ya taɓa yi mata kyautarsa ta ajiye a gefen kujerar. Harafi ɗaya ta kasa furtawa wannan ya sa ta ficewa a falon amma kuma tana jin sautin muryarsa yana bin bayanta yana kiran sunanta. Ga mamakinta har ta zo tsakar gidan yana biye da ita, waɗanda suka soma zolayarsa da kirarin Ango suka yi shiru jin magiyar da yake zubawa Sadiya cewa ta yafe masa Husna yake son aure har wai yana yi wa Inna magana dake gefe akan ta sanya baki. Salati da salallami matan suka ɗauka. Huzaif gaba ɗaya ba ya cikin nutsuwarsa. Meenat idanu waje take bin Yayan nata da kallon mamaki da tsoro. Anya kuwa lafiyarsa ƙalau? Husna yake so? Wannan wane irin abu ne? Husna dake kallonsa a can ƙasan ranta ji take kamar ta yi tsuntsuwa ta gan ta a gaban Antinta ta rungume ta su yi rawa da juyi, a fili kuwa gaba daya ta marairaice har da kuka.

Adda Ruƙayya ce ta yiwa Huzaif tas ta ce ya tashi ya fice a gidan tun ba ta ɗauke shi da mari ba, haka gwuiwa a sake ya fice. Nan fa aka shiga tattaunawa, Inna Asabe ce mai kiran Malam a waya ta fesa mishi. Wasu fadi suke kodai ƙwaya yake sha. Sadiya kuwa ɗakin Innarta ta shiga ta dinga kuka kamar babu gobe. Inna dai sunayen Allah kawai take jerowa a ƙasan ranta jikinta har rawa yake don mamaki. Meenat a guje ta bi bayan Yayanta sai dai ya bar gidan wannan yasa ta komowa ta ɗauki jakarta da waya ta bi sahunsa. Tun ma a hanya ta kira gidan ta labartawa Maminsu komai.


"Ki yi haƙuri Sadiya. In sha Allahu ko baki auri wannan munafukin ba, to rayuwarki ba za ta tagayyara ba."

Muryar Gwaggo ce ta maido ta hayyacinta, ta sauke ajiyar zuciya gami da janye idanu daga kallon mazaunin Huzaif a daren jiya da ma tuna diramar da ya yi musu a gidan. Ba ta ce musu komai ba ta miƙe ta fice a falon Malam, ta san dai koda Malam da Abba sun tsaida magana kan lallai sai Huzaif ya aure ta, ba za ta taɓa bari ta aure shi ba. Koda an mata dole tana ji a jikinta za ta iya bar musu gidan a neme ta a rasa. Idan da abin da ya fi ficewa a rai, to Huzaif ya yi a ranta.

***
Marin da Abba ya ɗauke shi da shi ne ya katse sauran kalaman da yake zuba musu duk domin su fahimci nisan da ya yi a ƙaunar Husna. Da yatsa yake nuna shi cike da ɓacin rai mai yawa.

"Ƙarya kake yi Huzaifa! Ƙarya ka ke yi ka maida mu ƙananan mutane a wannan rana da na gayyaci dubban mutane domin su shaida ɗaurin aurenka. Mu za ka kawo wa zancen banza da wofi?!"

Huzaif hawayensa kawai suke fita, bakinsa kuwa ya ƙi mutuwa.

"Wallahi Abba ina sonta. Ina ƙaunar Husna. Don girman Allah..."

Ya zube gwuiwoyinsa a ƙasa yana mai cigaba da roƙo.

"Ku aura min Husna. Ni fa ban taɓa son Sadiya ba, kuskuren fahimta aka samu. Ita ma Husna a tambaye ta, tana sona mun jima muna son junanmu."

Kalaman da suka dira a kunnuwan Malam kenan sadda ya sanyo kai falon saukar baƙi na Aminin nasa da sallama ɗauke a bakinsa. Mami ta kara gyara zaman mayafinta, ita gaba ɗaya tausayin ɗanta ta ji. To mene ne bambancin Sadiya da Husnar? Ita a nata ganin kawai a maida auren kan Husna.

Abba zai yi magana Malam ya dakatar da shi. Sai a lokacin ma ya kula da shigowar Malam falon. Babu ko kunya Huzaif ya koma gare shi da magiya ya yi hakuri ya yafe masa ya ba shi auren Husna domin suna son junansu sosai.

"Ya isa haka, Husna da Sadiya dukkansu abu guda ne. Amma kuma ba zamu yanke hukunci kai tsaye ba sai an haɗu gaba ɗaya."

Ya ƙarashe yana jin ciwon abin a ransa, sai dai kuma ya sani, iyalan Alh Abubakar sun fi ƙarfin komai a wurinsa.

"Wannan zance ne kawai kake yi Sa'ad, kai ma sanin kanka ne ba..."

"Zai yiwu Abubakar, zai yiwu. Amma bari na yi musu magana kowa ya hallara anan, mu ji ta bakin dukkansu."

Daga haka ya fiddo waya, Inna ya kira ya ba ta umarnin taso Husna da Sadiya gaba su zo sannan ya yi kiran babban ɗansa akan su zo gidan Abba.

Kowa ya hallara har Hafsatu da Hajara da Safiyya waɗanda duk suke can gidan sun shigo biki. Hajara zyciyarta wasai, ta sani kuma komai zai tafi daidai kamar yanda Bokanta ya ce hakan yasa hankalinta a nutse babu wata fargaba ko damuwa.

***

Tarin mutanen da ke zaune a babban falon saukar baƙi na gidan Abba, bai hana ta kuka har da sheshsheƙa ba. Yin sa ta ke iyakar ƙarfinta.

"Ya isa haka Husna, ya isa. Share hawayenki. Ai yanzun komai ya zo ƙarshe da yardar Allah."

Faɗin Abba kenan yana maida duba ga Huzaif dake zaune tanƙwashe da ƙafafu yana satar kallon Husna yayinda ya ke jin sautin kukan nata har tsakiyar kwanyarsa. Ji ya ke inama yana da damar ƙarasawa kusa da ita ya rarrashe ta.

Hajara ce ta ja ta a jiki ta kwantar da kanta saman cinyarta tana shafawa a hankali wannan ne ya haifar da shiru na lokaci ya ratsa a falon. Malam zai yi magana amma Abba ya hana shi. Inna kanta na ƙasa, a gefenta Sadiya ce da ke fitar da na ta hawayen masu ɗumi, kanta har sarawa yake yi don rabonta da abincin kirki tun jiya, uwa uba baccin da ba ta iya ta yi sa ba.

"Huzaif, yanzu ba anjima ba, ina so ka faɗamana gaskiyar wa ka ke so tsakanin Sadiya da Husna? Ka fitar da mu cikin duhu don mu san abin yi a gaba. Ka daina haifar mana da wannan ruɗanin, mu ba yara ba amma kana wasa da kwanyarmu."

Huzaif da ke jin ƙirjinsa na bugu da ƙarfi, ya ɗan dubi gefen da Sadiya ta ke, aka yi sa'a suka haɗa idanu. Ta kasa dauke su a kansa, so take ta gano kodai dukkan abin da ke afkuwa a mafarki ne, yanzun furucin bakinsa zai sauya. Kokwanton da wani sashi na zuciyarta ke yi ne take son kawar da shi, ina makomar waɗannan zafafan gwala-gwalan kalamin da ya dinga yi mata a baya suke? Me ya ke nufi da kiran waya ya hana ta bacci ta hanyar sauraron daɗaɗan zantukansa masu ƙara narkar da zuciyarta a kaunarsa? A hankali kuma ta sauke idanunta ƙasa yayinda tsikar jikinta ke tashi yarr. Hawayenta suka ɗiga saman lallen da ta sha na bikin aurensu wanda yau da ya kasance ranar ɗaurin aure amma kuma reshe na nema ya juye da mujiya. Kamar daga sama ta tsinci muryar Huzaif na magana.

"Abba ni Husna ce zaɓina, ita zuciyata ta aminta kuma nake so. Ban taɓa son Sadiya ba. Mun jima muna soyayya da Husna a ɓoye, mun kasa fitowa fili mu bayyana ne, dalilin kenan da ya sa na rage shiga harkar Sadiya. Na rasa ta yaya zan bayyana mata ba ita nake so ba, Husna ce zaɓina tun farko, akasi aka samu da rashin fahinta."

Akasi? Rashin fahimta? Waɗannan ke yawo a kwakwalwarta. Hannun Inna ta ji a saman nata, wannan hannun da ke yawan ƙarfafa mata gwuiwa da jin cewa ba fa ita kaɗai ce ba a duniyarta, a yanzun ma jin wani ƙarfin gwuiwar ta yi sai ta tsinci kanta da ambaton Allah da ma dukkan addu'ar da ta zo bakinta. Tana ji Malam da Abba na faman buɗewa Huzaif wuta a dalilin wasan kwaikwayon da ya yi da ita, can kuma ta tsinkayi muryar  Hajara na fadin.

"Abba laifi fa na Sadiya ne ba Huzaif ba, dama tun farko bai ce yana sonta ba. Ita ce dai ta dinga shigewa lamarinsa amma ko gidan ya je babu wacce ya fi maida hankali kanta face Momina."

Haka dai maganganun suka yi ta tashi, Abba ya dage kan lallai Huzaif bai isa ya maida shi ƙaramin mutum ba, shi kuwa Malam ya ma kasa cewa uffan a wannan karon sai kallon ɗiyarsa Sadiya da yake yi.

"Abba."

Sassanyar muryar Sadiya ta shiga dodon kunnuwansu, sai falon ya yi tsit aka maida hankali ga abin da take son cewa. Ga hawaye a fuskarta amma wani murmushi ta ke yi mai tarin ma'anoni. Ta ɗan dubi Huzaif shi kuma ya kauda kai sannan ta kalli Abba.

"Na haƙura da Huzaif. Ina roƙon Allah ya musanya min da wanda ya fi shi. Don Allah kuma ku bar shi ya auri ƴar uwata. Husna jinina ce, da ni da ita duka ɗaya ne. Wallahi na haƙura."

Tana kai wa nan ta sadda kanta. Nan Abba ya yi shiru, a karshe ya dinga yiwa Sadiya addu'a da kuma fatan alheri.

"Na rantse maki Sadiya da ace ina da wani ɗan da ya kai shekarun Huzaif, da babu abin da zai sa na sharemaki hawayenki. Amma ina maki fatan Allah ya ba ki wanda ya fi Huzaif komai na rayuwa. Allah ya albarkaci rayuwarki."

"Ba amin ba." Wannan furucin da Hajara ta yi ƙasa-ƙasa ya shiga kunnenta, ta yi murmushi karo na biyu. Wai kuwa akwai ranar da Hajara za ta ƙaunace ta? Ta ba kanta amsa da a'a.

Ita dai daga wannan ta miƙe ta bar musu falon ta kama hanyar fita. Anti Hafsatu ce ta biyo ta da sauri tare da su Radeeya da Lubna yayyun Huzaif. Haƙuri da ban baki suka shiga ba ta, ta nuna ita fa komai ya wuce. Anti Hafsatu wacce har su din ma haushinsu take ji kawai ta janye Sadiya suka fice daga gidan. Ba ta ma koma gidansu da ita ba kai tsaye gidanta suka wuce a motarta.

A can ne Sadiya ta ci wani sabon kukan, Anti Hafsatu na rarrashinta har Safiyya wacce ita ma ta biyo su. Ƙarfe ɗayan da aka tsara za'a ɗaura aurenta da Huzaif, yana bugawa labari ya sauya, aka ɗaure auren Huzaif da Husna.
Sabo turken wawa, wannan karin magana ta Malam Bahaushe shi ya taka rawa a rayuwar Sadiya, wannan ƙwallafa ran da ta yi akan Huzaif da kuma cin amanar da ya biyo baya sai da ya yi sanadiyyar kwanciyarta a gadon asibiti. Ta fi ƙarfin sati uku kafin komai ya soma wucewa rayuwarta ta fara daidaita.

Sama-sama ta ji a wani yammaci, Inna da Anti Hafsatu da Baba Habu suna zancen karatun Husna da ba ta kammala ba don a lokacin ne za ta je SS1, Inna ke faɗamusu hukuncin Malam inda ya yi rantsuwar Husna ta gama karatu ta yi zaman aure kawai. Hirar Husnar ma ba son ji take ba dalili kenan da ta ɗauko wani tsohon littafi na Hausa mai suna Darasi Ne ta shiga maimaicin karatu, ita ɗin ba gwanar karance-karance ba ce, amma kuma tun sadda wata ƴar ajinsu Nabila Muneeb ta ba su labarin littafin ta ji nan duniya tana kaunarsa. Har ta kasa hakuri sai da ta tara kudi ta ba ta ta siyomata. Ta karanta ya fi a ƙirga amma duk sadda ta ɗauka sabo fil take jin sa.

Tafiya na tafiya har aka ci watanni biyu da auren Huzaif da Husna. Lokacin bai fi saura kwanaki ya rage a fara azumi ba. Sadiya ta rage walwala amma kuma ta soma dawowa nutsuwarta. Gaba ɗaya ta tattara soyayya ta yi watsi da ita. Babu ko burɓushin kaunar Huzaif ko tunaninsa a zuciyarta. Ta maida hankali ƙwarai wajen neman ilimin addininta, zuwa lokacin tana ji babu sauran dama a wurinta na yin karatun boko. Malam sosai yake jan ta a jiki yana lallaɓa ta. Haka ma yayyunta maza da wasu a cikin matansu don har a sannan ba kowaccensu suke ɗasawa ba.

Babban labari na farin cikin da ya same su a lokacin bai wuce na samun cikin Safiyya ba bayan dogon lokacin nan. Murna sosai Inna da Sadiya suka taya ta. Yanzun babu komai tsakaninsu face zumunci da kyautatawa. Sadiya kusan rabin azuminta a gidan Safiyya ta yi sa. Sosai ta ɗauke mata dukkan wasu ɗawainiya, Safiyya ke faɗi mata wai Hajara da mijinta sun tafi Umara. Ba ta ma ƙara bi ta kan zancen ba, ai ta ji Inna na faɗawa wata yar uwarsu wai Husna ta kira ta tana neman gafara za su wuce Umarah mijin Anti Hajara ya biyamusu ita da Huzaif. Kenan tare suka wuce gaba ɗaya. Ta san gudun jefa ta damuwa ya hana Safiyya yin maganar Husna, abin da kuma ba ta sani ba, ita har a zuciyarta yanzun babu ko ɗigon ƙaunar Huzaif, ta ma mance da komai tana kuma ji a ranta ta yafe wa ƙanwarta.

Sai da ana saura sati ɗaya bikin ƙaramar sallah sannan ta tattara ta koma gidansu. Mijin Safiyya ne ya kai ta da kansa har da sha tara na arziki, atamfarta har da leshi duka ɗinkakku don tun sadda aka kawo suka je kai ɗinki da Safiyya. Kasancewar yanzun komai ya ƙara daidai tsakanin Safiyya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login