Showing 33001 words to 36000 words out of 124441 words

Chapter 12 - Kazar Kwanci Hausa Novel Complete



"Lambarka za ka saka min Yaya. Zamu dinga gaisawa."

Babu musu ya karɓa ya saka lambarsa ya miƙa mata. Sai ya kai duba ga Sadiya dake gefe jikin ƙofa ta ɓuya, kanta kawai da hannun da ta dafe ƙofar ake gani.

"Ita ba ta da waya?" Ya tambaya yana duban Sadiya har lokacin, ta ji tambayar amma sai ta kauda kai daga gare su. Husna ta ɗan juya, ganin da Sadiya yake ta ji wani haushi ya turnuƙe ta amma kuma a yau sai ta ji daɗi na rashin mallakar wayar Sadiya.

"Tab, ai wannan yanda ka san wata kifin rijiya haka take. Ba ta fiye fita ba sai Inna ta matsa mata sai kuma dole, wayar ma ba za ta riƙe a yi hira da ita ba. Idan a na son gaisawa da ita sai dai ko ta wayar Husnar ko Inna."

Meenat ta ba shi amsa.

"Ya fiye mata ai, tunda babu ruwanta da haukan da ku ke yi a tiktok." Faɗin Amir. Meenat ta turo baki, sau ɗaya ne ta taɓa kuskuren ɗora wani bidiyonta da ƙawayenta a Tiktok, shikenan abin ya zagaya inda ba ta yi zato ba, sanadin haka har wayarta Abba ya ƙwace, daga baya kuma ya ba ta bayan ya gargaɗe ta sosai. Tun daga wannan lokacin Amir ke kiranta da ƴar tiktok.

Shi dai Huzaif murmushi ya yi.

"Ku shiga mu tafi, dare na yi. Gaba ɗaya suka shige motar bayan sun yi sallama da su Sadiya karo na biyu, su Malam dama ba su fito ba daga gida. Har zai shige ya juyo ya ƙara duban Sadiya, ido huɗu suka yi wannan karon don ta fito sosai daga bayan ƙofa suna sallama da su Amira da Meenat. Idan dukkansu suka ce ba su ji wani lamari sabo na gewaye su ba da ba su da fassararsa to sun yaudara kansu da gangar jikinsu. Daƙyar ta janye idanunta ta juya ta koma ciki, sai a sannan ya sauke ajiyar zuciya mai karfi ya ya dubi Husna da murmushin ƙarfin hali.

"Sai wani jiƙon sister. Mu kwana lafiya."

Daga nan ya shiga motar, Amir ya ja suka tafi. Husna jiki a matuƙar sanyaye ta juya ta shige cikin gidan.

***
Takan tsinci muryar Husna cikin dariya da kuma hira suna yi, tana jin abu ya yi mata tsaye a ƙoƙon rai, to ko dai ita kaɗai ke jin yanayin da ta ke ciki a kansa? Ko dama yaudarar kanta take yi da har ta fassara kallon da ya dinga bibiyarta da shi da wani abu na daban? Anya akwai hakan shi a ransa? Kwanaki bakwai da zuwansu gidan, amma gaba ɗaya ta rasa abin da ke mata daɗi. Za ta ji Husna na kyakyata dariya idan suna hira, ko kuma ta yi masa saƙon muryarta, amma shi ba ta taɓa ji ko sau ɗaya ya mata nasa ba. Sannan ba ta ji ko sau ɗaya Husna ta ce ya tambayi inda take ba. Hatta da Inna sun gaisa har sau wajen uku ta waya, nan ma ba ta ji ya tambaye ta ba. Sai gaba daya ya ba ta haushi, watakila ita kaɗai ce ta ji bambancin yanayi a kallon, zai yiwuwa ita kaɗai ke muradin ƙara sanya shi a idanunta da ma jin sautin muryarsa.
Ganin suna ta shirye-shiryen zana jarrabawarsu ta mock (jarrabawar sharar fage da makarantun kuɗi ke yi kafin fara ssce exams) wanda daga shi babu jimawa za su yi soma Waec ya sanya ta maida hankali ga karatunta gami da watsi da al'amarin da take da tabbacin gaibu ne. Ba zai taɓa faruwa ba.

***
A ɓangaren Huzaif kuwa, zuwa lokacin ya gama fahimtar me yake ji game da Sadiya. Ƙaryata kansa da zuciyarsa ya ke yi kawai don a tunaninsa, bayan tsohuwar budurwar da ya yi a Indiya, Ummu-Aimana, ba ya jin akwai gurbin son kowa a zuciyarsa. A lokacin ya yi wa Aimana so mai yawa, sai dai kuma yana ji yana gani aka aura mata wani ɗan uwanta. Allah kaɗai ya san da ya ya mance lamarinta a rai. Tun kuma daga kanta ne ya yi watsi da tarkacen so.
  Murmushinta, yanayin yanda take tsuke baki idan abu bai mata daɗi ba, har ma da yanayin kallonta gaba ɗaya sun gewaye nasa tunanin sun hana shi sakat ta yadda ko idanu ya rufe to Sadiya ke mishi gizo a cikinsu.
Ba ya so ya shiga rayuwarta kai tsaye gudun kar ya yi mata katsalandan a je ko akwai wanda ta ke so, komai a sannu ya fi. Dalili kenan da ya maida Husna abokiyar hirarsa a waya, ya kula tana da wauta iri-iri da kuma iya ba da labaran da mutum zai dara sosai. Hakan ba ƙaramin kewa ya ɗebe masa na Sadiya ba. Koda wasa bai taɓa tambayarta ina Sadiya ba, ko kiran Husna ya yi babban fatansa bai wuce a samu akasi wayar ta kasance a hannunta ba, amma kuma muryar Husna ce ko yaushe ke karaɗe dodon kunnensa, haka ma idan Inna ya kira.

Ya ji dagaske ba zai jure ba, wannan ba irin wacce zai gani ya kauda kai ya haƙura ba ne ko kuma ya yi sanyi. A yadda ya wayi gari daƙyar a wannan ranar na Alhamis, ba ya jin zai jure wucewarsa matuƙar da ransa da lafiya bai sanya Sadiya a ido ba. Don haka ƙarfe uku da mintoci ya yi shirinsa tsaf cikin ƙananan kaya jeans da ruwan madarar tshirt, kamar koyaushe dama tun zuwansa yanayin shigarsa kenan zai wahala ka gan shi da manyan kaya. Turarukansa masu tsada da ƙamshi ya fesa kafin ya fito riƙe da wayoyinsa. Cikin gidansu ya soma shiga kai tsaye ɓangaren Maminsa ya faɗa da sallama. Mami dake zaune suna lissafi ita da Lubna da Radeeya waɗanda dawowarsu kenan daga kasuwa duka kayan an buɗe su ana kuma ƙirgen waɗanda suka yi saura a dangin kayan kicin da ba su siya ba.
 
  "A'a, manya gatan wasa. Wannan wankan kuma sai ina?" Faɗin Lubna fuskarta a sake tana kallon ƙanin nasu. Huzaif da ya maida hankali ga yin cilli da Noor ƴar gidan Radeeya da ba ta fi watanni huɗu a duniya ba, ya zauna yana murmushi gami da shafar sumarsa. Mami da ke bin sa da kallo ita ma murmushin kawai ta yi, da ace ma zancen zai je ai za ta so hakan. Ta san akwai sauran watanni kusan shida da zai ƙara a Indiya kafin ya dawo nan baki ɗaya, amma kuma za ta so ya kasance akwai maganar aure a kansa sai dai ba ta da matsawa yaro, tana cigaba da nema musu zaɓin Allah.

"Sis Deeya, ki shiga tsakanina da yayarmu, na faɗamata har yanzu yaron Mami ne amma ta ƙi rabuwa da ni da zancen auren nan."

Radeeya ta yi dariya.

"Ai shikenan, sai ka yi ta zama haka Huzaif tunda ba ka so mu zo gidanka mu ɗauki ɗanka. Ni na bar ɓata bakina ma, idan ta yi wari ai dole za mu ji." Lubna ta faɗi tana taɓe baki.

"Yauwa, za ku ji tabbas idan ta yi warin. Mami."

Ya ƙarashe da maida akalar zancen ga Mamin tasu.

"Zan ɗan fita, ba nisa zan yi ba."

Mami ta gyaɗa kai tana kokarin maida wasu tukwane gidansu.

"Allah ya tsare ya maido ka lafiya. Ya haɗa ka da dukkan alkhairai, ya tsare ka dukkan sharri."

Wani murmushi ya yi har ka na hango fararen haƙoransa. A duniya yana son Mami ta yi mishi addu'a. Ya amsa da amin yana mai miƙewa.

"Af, amma sai dai ka ɗauki motar Abbanku, Malam Bukar ya kai Antinku Zulfa'u unguwa da Honda."

Ya ɗan jan ya tsaya.

"Ok, muƙulli fa?"

"Za ka iya tuƙin garin nan?" Radeeya ta tambaya da alamar gargaɗi a fuskarta.

Ya yi dariya daidai sadda Mami ke miƙewa ta shiga ɗaki don ɗauko masa muƙulli ya na amsawa Radeeya zancenta.

"Har wannan ƙauyen unguwar taku sai na kai ki."

"Huzaif da karambani, ko sadda suka zo gidana ai shi ya tuƙo."

Cewar Lubna. Shi dai bai kara tanka musu ba sai kallo, a tunaninsu saboda sauyin da titunan suka samu zai iya rasa nutsuwarsa yayin tuƙi. Yana karɓar muƙullin ya yi musu sallama ya fice.

***
Tun daga nesa ta hango kamar mota a gaban gidan nasu.

  "Yau kuma wa muka samu?" Ta faɗi tana ƙara duban ƙofar, Zahra'u wacce suke tare ita ma kallon motar ta yi.

"Ko dai Amarya ce ta kawo ziyara?"

Taɓe baki Sadiya ta ɗan yi.

"Anya? Zai wahala ta zo gidan nan. Na ji ma fa Yaya Zakari ya ce wai za ta je Makkah. To ko ita ta..."

Sauran maganar ta maƙale a fatar bakinta sa'ilin da ta hango shi ya fito daga motar yana amsa waya bai ko lura da su ba. Ta ji miyan bakinta ya ƙafe. Zahra kuwa ido ta ɗan zaro gami da cewa.

"Wow, masha Allah! Ke wannan waye haka? Ko shi ne yayan su Meenat ɗin da kike faɗa ya dawo? Wannan blackbeauty haka?"

Ita dai Sadiya ba baka sai kunni, ita kaɗai ta san yanda kirjinta ke faman lugude. Ba ta iya ta amsawa Zahra ba har sai da ta ƙara magana. Da ƴan rawar murya ta amsa mata.

"Yes, shi ne." Iyakar abin da ta ce kenan ta sunkuyar da kai da sauri ganin suna dab da ƙarasawa kusa da inda yake tsaye kuma ta tabbata zuwa lokacin ya lura da su.

"Ina wuni." Sai da Zahra ta gaida shi sannan ita ma ta gaishe shi. Ya amsa yana kokari ya ga sun haɗa idanu.

"Kin san kuwa zuwan domin ki na yi Sadiya. Ina fatan za ki ban aran lokacinki?"

Sadiya suka dubi juna da Zahra wacce ke maƙale dariyarta. Kafin ta ce wani abu ta riga ta lokacin da ta sa hannu ta karɓi ledar dake wurin Sadiya.

"Bari na shiga na kai wa Inna saƙonta, zan sanar da ita ki na waje."

Ido a buɗe Sadiya ke duban Zahra gami da riƙo hijabinta ganin dagaske tafiyar za ta yi.

"Ina za ki je? Don Allah jira ni. Ka yi hakuri Yaya Huzaif, ka shigo cikin gidan. Idan Inna ta ji mun tsaya a waje faɗa za ta yi, kuma ma za'a yi tunanin wani abin."

Ya haɗe hannayensa a ƙirji yana bin fuskarta da kallo.

"To amma kuma ni gurinki na zo. Ki na tunanin idan mun tattauna a cikin gidan babu matsala?"

Ta gyaɗa masa kai da saurinta kamar ma a firgice ta ke. Ya yi murmushi.

"Ok, mu je."

Daga haka suka yi gaba yana biye da su. Sai da ya jira suka shiga suka sanar da Inna zuwansa kafin ta ce Sadiyar ta ce ya ƙaraso.

"Haba Huzaifa, gidan nan ai ba baƙonka ba ne. Ka na da ƴancin shigowa kanka tsaye. Bismillah, shigo falon."

Huzaif wanda har a sannan murmushi bai ƙaura a saman fuskarsa ba, ya bi umarnin Inna zuwa falon nata.

Ita kuwa Sadiya ɗakinsu ta faɗa da saurinta, Husna ba ta gidan ta je gidan Safiyya dubo ta, ba ta jin daɗin jikin.

"Ke, wai ko dai akwai wani abu tsakaninku? Ni kam gaskiya kun dace sosai. Don Allah kar ki wulaƙanta shi Sadiya. Na sanki sarai ba kya sakarwa samari fuska. Amma wannan na gida ne kuma ya fita daban ma a halitta da ma yanayi."

Faɗin Zahra kenan cike da zumuɗi. Sadiya ta yi shiru tana kallonta, wani irin sanyi take ji a ƙasan ranta ga kuma murmushin da ba ta san ta na yin sa ba. Ko babu komai yau ta ba idanunta abincin da suka jima su na marmari. Ko iyakar ganin aka tsaya ta ji daɗi.

"Ah, ƙawata ta harbu. Sai fatan Allah ya sa kar ta zurma da yawa, kai ni ina tunanin ma gaba ɗayanki ki ka dulmiya." Zahra ta ƙarashe da dariya. Sai kunya ta kama Sadiyar ta kuwa shiga maka mata hararar borin kunya. Kiran da Inna ta ƙwala wa Sadiya ya sa dole ta miƙe ta fito har Zahra na dakatar da ita wai ta cire hijabin ta saka mayafi amma ko kallo ba ta ishe ta ba.

A tsakar gidan ta ci karo da Inna. Cikin ɗan haɗe rai Inna ke faɗin.

"Ku yanzu idan mutum ya zo har sai an ce ku kai masa ruwa?"

Kai Sadiya ta girgiza mata gami da ba ta hakuri ta nufi kicin ɗin. Ruwa da lemu mai sanyi na zoɓo wanda Inna ke siyarwa tun sadda ta yi firij su ta haɗo masa. A jug ta tsiyaye zoɓon dake ɗaure a ledoji har guda biyar sannan ta rufe ta ɗora komai saman ƙaton faranti ta nufi falon Inna ƙirjinta na bugu ta shiga ambaton sunayen Allah.

Da sallamarta ta shiga ta ajiye ba tare da ta dube shi ba ta tsiyaya mishi ruwan roba a kofi ta miƙa, ya karɓa. Daga haka ta miƙe da zummar bar mishi falon ya yi saurin katse hanzarinta.

"Kin ce za ki saurare ni."

Dole ta tsaya cak gami da juyowa ta dube shi. Ya ɗan karkata kai cikin alamun roƙo ya ce.

"Please." Sai ta tsinci kanta da jin kunya da murmusawa duka lokaci guda. A dole ta koma ta zauna. Sallamar Zahra ce ya hana shi furta komai, suka amsa mata. Ita ma wani babban tray ne ɗauke da flask na abinci. Allah ya taimaka ma shinkafa ce dafaduka da ya ji busasshen kifi Innar ta yi.

"Thank you. Mene sunanki ke kam? Ke ma a nan gidan ki ke?"

Huzaif ya watsawa Zahra tambaya yana dubanta fuska a sake. Ita ma da fara'arta ta amsa.

"A'a, ni makwafciyarsu ce kuma aminiyar Sadiya."

Ya jinjina kai.

"Na yarda yanzu ke aminiyarta ce, amma kuma nan gaba kaɗan zan ƙwace maki wannan matsayin. Ni zan zama amininta har ƙarshen rayuwarmu. Right?"

Yanda ya rufe zancen da tambaya ya na maida akalarta ga Sadiya lokaci guda kuma ya na marairaice muryar ya sa ta ji wani masifaffiyar kunya ta rufe ta. Zahra kuwa dariya kawai ta yi gami da fadin.

"To, abin babba ne. Allah ya tabbatar mana da alheri. Zan jira na ga wannan ranar in sha Allahu."

"Ina fatan ba a riga ni ba?" Huzaif ya ƙara faɗi ya na duban Zahra a wannan karon.

Ta dubi Sadiya wacce duk ta rasa sukuni ta kuma fahimci dagaske dai wannan Huzaif ɗin a na yin sa tunda kunya ta gama rufe ta sai ta ba shi amsa.

"Idan magana ta gaskiya zan faɗamaka, Sadiya tana da masoya da yawa. Ka san masu sunanta akwai farin jini masha Allah, amma kuma ina maka albishir da cewa, babu wanda ta ba shi damar zuwa inda ta ke. Mai yiwuwa kai za'a buɗewa ƙofar zuciyar."

Ta ƙarashe da ƴar dariya ba ta jira amsarsa ba ta fice ta bar musu falon. Shi kuwa Huzaif sai ya rasa me zai yi don jin daɗin wannan farin albishir ɗin daga bakin wacce ya tabbatar Sadiya ba ta mata rufa-rufa tunda ta kira kanta da sunan Aminiya. Ita ko Sadiya ji ta je kamar ta miƙe ta bar falon, sai wasa ta ke da yatsun hannunta ta kasa kataɓus.

"A taimaka a kalle ni ko ya ya ne."

A hankali ta saci kallonsa, caraf suka haɗa ido, da sauri ta janye nata ƙwayoyin idanuwan. Ta ji sadda ya sauke ajiyar zuciya.

"Ko ban ƙara wani dogon bayani ba Sadiya, na sani kin fahimci manufata a kanki. Daga kallo ɗaya idan aka yi min a gabanki, an san ni Huzaif na gama kamuwa da sonki. Soyayya mai tsafta nake son mu yi wanda zai ƙarfafa zumuntar iyayenmu da mu kanmu. Irin wacce na ke fatan ta kai mu ga aure. Sai dai duka waɗannan fata da burin daga ɓangarena ne, ban sani ba ko ba na cikin tsarinki."

Shiru ya ƙara biyo baya, Sadiya jin kalamansa take yi kamar a na mata yayyafin ruwa. Ta kasa magana, ta kuma rasa dalilin shirunsa na tsawon daƙiƙa, kamar yanda ta rasa dalilin da ya hana Innarta shigowa alhalin idan dai ta yi baƙo, bini-bini koda aiki ta ke yi takan shigo su taɓa hira kaɗan.

Ba ta yi aune ba sai ganin Huzaif ta yi ya yi wani durƙuso a gabanta, wuya a ɗan karye ya ke leƙa fuskarta. Duk yanda ta so kaucewa kallon fuskar a wannan karon hakan ya faskara, dubansa ta ke yi kamar yanda shi ɗin ma ita ya zubawa idanu yana ji tamkar idan ya rabu da kallonta, wani abin zai faru ga rayuwarsa.

"Kin amince da ni Sadiya? Kin san Allah idan har ba ki yi min magana ba yau ba zan iya runtsawa ba. Ba kuma na jin koda na koma Indiya, zan maida hankali kamar a baya na ƙarasa abin da ya yi min saura. Tun ganin farko da na yi maki a zuwana gidan nan, na ji a jikina ba ranar ce za fa zamo mana ƙarshen haɗuwa ba. Jikina ya ba ni cewar akwai alaƙa mai karfi da zai iya giftawa tsakaninmu. Ban taɓa jin yanayin da nake ji a kanki a kan wata ɗiya mace ba, ban ware maki duk ƴanmatan da suka kawo min hari ko kuma waɗanda muka ɗan yi soyayya da su ba a baya. Sadiya dagaske nake, dagaske na zo wajenki. Nan ba gidan da Huzaif zai zo da wasa ba ne. Ina son jin ra'ayinki a kaina."

Ta ɗan ciji ƙasan leɓɓanta kafin ta sauke ajiyar zuciya, wannan kusancin ya yi mata yawa, ga ƙamshin turarukansa da suka buɗaɗe ƙofofin hancinta. Ta yi narai-narai da fuska ta na dubansa karo na biyu da yake a gabanta.

"Na ji, zan ba ka amsa, amma don Allah ka koma kujerarka."

Ya yi wani murmushi kafin ya ce "Ooookay." Ya na mai jan harafin farkon kalmar sannan ya miƙe ya koma inda ya ke. Madadin ya ga ta ce wani abu, sai ya ga akasin haka. Zamowa ta yi ta ja filet ta shiga zuba mishi abinci ta ajiye masa saman madaidaicin teburin da ke a tsakiyar falon kusa da farantin lemu da ruwa. Kallonta kawai yake yi ya ma rasa me zai ce sai ƙirjinsa da ke faman bugu da sauri-sauri. Idanunsa har wani kaɗawa suka ɗan yi, idan Sadiya ba ta karɓi tayin soyayyarsa ba, ya zai yi? Ina zai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login