Showing 111001 words to 114000 words out of 124441 words

Chapter 38 - Kazar Kwanci Hausa Novel Complete

gafararki."



Ta numfasa tana dannawa saƙon sitika na Love. Kafin ta ɗan juya kaɗan ta kai duba ga Maina, wannan karon karaf suka haɗa idanu yana shirin kai kofin ruwa bakinsa, da sauri ta juya kanta tana ɗan runtse idanu irin na ta kwafsa. Sai ta kasa ma bai wa Nudrat amsa a lokacin, hakan ya sa ta fita gaba ɗaya a whatsapp din ta ma ajiye wayar a gefen kujera. Tana nan zaune ta ji takunsa zuwa tsakar falon. Wannan karon ba ta yi karambani ɗago kai ba balle su haɗa idanu. Shi kuwa ya ɗan dakata ya dube ta sosai ya ce.



"Ki na buƙatar wani abu?"



Kai ta girgiza kafin a hankali ta amsa.



"A'a."



Shiru ya ɗan biyo baya, can kuma ta ji ya ce.



"Ok, sai na dawo."



"Allah ya tsare ya kiyaye hanya."



Leɓɓansa suka motsa a hankali ya ce ameen sannan ya soma tafiya. Ta bi bayansa da kallo tana ɗan murmushi har ya fice. Ita ba ta ɗauka za ta same shi da sauƙin kai har haka ba, ta fi zaton yana da mugun girman kai da wulaƙanci. Amma abin mamaki shi ke amsa gaisuwa, addu'a da ma maganarta. Tana roƙon Allah ya sanya mata soyayyarsa a zuciya kamar yadda masoyanta ke taya ta roƙo, ita ma kuma ta ƙaunace shi su zauna lafiya tunda shi ne zaɓin da Allah ya yi mata.



Ta tattara komai ta kai kicin, ta wanke waɗanda aka ɓata, sauran abincin ta bar su da zummar idan an zo tafiya da kwanukan sai su ɗauka.



Ba ta jima da komawa falon ba aka shiga ƙwanƙwasawa. Koda ta buɗe ta yi arba da wasu ƴanmata su biyar. Wacce ta fara tozali da ita, kallon sama da ƙasa ta shiga bin ta da shi ta a taunar cingam. Sadiya ta ba su wuri suka shigo fuskarta ɗauke da ɗan murmushi.



"Sannunku da zuwa."



Ta furta. Ta san dai wasu sun amsa amma ba ta tunanin dukkansu. Suka ƙarasa shigowa suka zauna a falon. Wacce ta fi sauran gaba ɗaya sakin fuska ta cikinsu ce ta fara magana.



"Barka da safiya Anti Sadiya." Da haka sauran ma suka gaishe ta, ta kula wannan mai taunar cingam din sai da mai maganar ta farko ta ɗan zungure ta sannan ba tare da ta dube ta ba ita ma ta gaida ta. Ta amsa musu kuwa ta mike ta kawo musu ruwa da lemu a saman tray.



"Anti da kin bar shi ma, daga gida muka fito. Amma mun gode."



"Babu komai." Ta ƙara ba ta amsa.



"Ni suna na Hindatu, sai wannan (ta nuna wata ƴar baƙa mai ɗan ƙaramin jiki) sunanta Mabruka, sai wannan (ta nuna baƙar cikinsu gaba ɗaya don dukkansu farare ne ƙal) sunanta Nasiba. Wannan kuwa Ummulkhair autarmu. Wannan kuma (ta yi nuni da mai taunar cingam da harare-harare) ita ce Najma. Dukkanmu ƙannen Maina ne."



Sadiya ta ƙara yi musu kallon tsaf tana ƙara faɗaɗa murmushinta. Dama daga ganin Hindatun ka san cewa yar uwa ce ga Maina don za ta iya cewa ma kaf cikinsu babu wanda ta ga sun yi kama da shi kamarta. Ƙila kuma kammanin Mai Martaba ne ba lallai sun haɗa ɗaki ba don ta ji Anti Hafsatu ta ce mahaifiyar Maina mace ɗaya ce a gabanta ba ta aurar ba.



"Masha Allah, nice to meet you all sisters." Ta faɗi suka amsa da godiya da maida martani, Najma ta ja guntun tsaki kafin ta ce.



"Wai ku ba za ku tashi mu wuce ba? Oh, ashe ba mu ga gida sosai ba jiya, bari mu shiga."



Daga haka ta miƙe, Sadiya na kallonta ta soma shiga ɗakuna, ba ta ce uffan ba.



"Kai Najma wai mene ne haka?" Cewar Hindatu tana harararta bayan ta fito daga ƙuryar ɗakin Sadiya cike da jin haushin babu wani abin ƙazantar da Sadiya ta bari don so ta yi ta ga wani abu na ba daidai ba ta dara.



"To mene ne laifi? Dama gidan Amarya ba ko'ina ake shiga ba?" Ummulkhair ta amsawa Hindatu cike da tsiwa.



"Za ki rufe mana baki ko sai na gurje shi yanzu? Ku tashi ma tafiya zamu yi ai Mai babban ɗaki ma ta ce kar mu daɗe." Faɗin Mabruka wacce suke sa'anni da Najma, duka sun girme musu.

Ita dai ba ta ce musu komai ba, idanunta ya kai ga Najma da ke ƙoƙarin zuge gilashin bene wai za ta hau. Anan ne kuma ta miƙe ta ƙarasa.



"Ki yi hakuri, za ki iya shiga ko'ina na gidan nan ki kalli abin da ba ki gani ba, amma ban da nan." Mamaki tsantsa ya bayyana saman fuskar Najma. Ranta kuma ya ɓaci har wani huci ta shiga yi. Sadiya ta kauda kai daga dubanta gami da jan gilashin ya rufe ruf sannan ta koma mazauninta.



"To ni kuma sai na shiga na ga me za ki yi."



"Najma wallahi ke da Maina, kuma sai na faɗawa Mai babban ɗaki muddin ki ka buɗe. Ba tun jiya an faɗamana ɓangaren Maina ba ne?"



Faɗin Hindatu a zafafe. Najma ta fasa ta yi ƙwafa, haushin Sadiya ta ji ya ninka na farko a ranta. Tana mata kallon kamar wata wawiya ashe da wayonta.



"Sai ki je ki yi ta faɗa uwar sharri. Mts." Daga haka ta yi gaba ta zura takalmanta ta fice har tana ƙoƙarin buge Hindu da isowarsu kenan bakin ƙofar tare da bayi har huɗu suna shirin ƙwanƙwasawa.



"To ita kuwa lafiyarta?" Hindu ta faɗi tana bin ta da kallo kafin ta girgiza kai kawai ta yi sallama zuwa ciki bayan an amsa.



Nan da nan su Mabruka suka yi wa Sadiya sallama.



Ita ko ta gaisa da Hindu, bayin su ma suka gaida ta.



"Ranki ya daɗe, waɗannan hadimai ne daga Mai babban ɗaki. Ga Zuwaira, Karima, Bintu da Jamila. Bintu aikinta shi ne girki, Karima kuwa kula da ɓangarenki, Zuwaira za ta dinga taimaka maki da gyaran ɓangaren Maina. Ita kuwa Jamila an ba ki ita ne saboda kula da dukkan abin da zasu yi, sai ko taya ki hira."



Ta ji abin sam bai mata ba, toh ita zaman me take? Kawai ta ci ta miƙe ƙafafu?



'Duk gatan da za su nuna maki, kar ki sake kwanon mijinki ya fita a hannunki, haka nan ɓangarensa. Ki zama ke za ki dinga ba shi dukkan wasu kulawa. Komai nasa ya kasance ke ce za ki yi da kanki ba wata baiwar ba. Hakan zai ƙara maki ƙima da kankaro mutuncinki a wajensa.'



Maganganun Anti Hafsatu suka faɗo mata a rai. Shirunta ya sa Hindu dubanta dakyau.



"Gimbiya Sadiya ko ba su yi maki ba ne a sauya maki da wasu?"



Ta girgiza kai da sauri.



"A'a Baba Hindu, ba haka ba ne. A taya ni miƙa godiya ga Mai babban ɗaki, a ce kuma na yaba da kyautarta gare ni. Sai dai ina neman alfarma su zama mutum biyu kawai madadin huɗu idan har babu damuwa."



'Baba Hindu', wannan sunan da Sadiya ta kira ta da shi ya faranta mata rai sosai, girma ne da za ta iya rantsuwa bayan Maina da Saudatu babu masu ba ta shi a gidan. Maina kan kira ta da Inna ko kuma Innar Jibril, yayinda Gimbiya Saudatu ita ma ke kiranta Inna. Sai ko yanzun da Sadiya ta raɗa mata suna duka don darajta tsufanta. Murmushi ta yi, ta yaba sosai da hankalinta, dama a yadda ta ke kallon yarinyar, ba ta da matsala sam. Ta fahimci ga dukkan alamu ba ta son wasu bayi su yi ta mata hidima, kuma ya dace a ba ta wuri su shaƙu da mijinta kafin duka wannan.



"Shikenan zan isar da saƙonki Gimbiya. Suna iya kwashe kwanukan safe?"



Sadiya ta gyaɗa kai tana murmushin ita ma.



"Eh. Nagode."



Su kansu bayin sun ji dadi, yarinya ƙarama amma akwai alamun tana da hankali. Bintu da Karima suka shige kicin ɗin bisa umarnin Hindu suka fara fiddo kwanukan suna ɗorawa a kwandon da aka kawo ɗazu. Tunawa da kajin dake a firij yasa ta miƙewa, ta fiddo ta miƙa musu ta ce su yi amfani da shi. Nan suka shiga godiya.



Bayan tafiyarsu tunanin gyara ɓangaren Maina ya zo kanta amma kuma tana jin fargabar kar ta yi mishi ba daidai ba, kar ya zo ya kushe. Ƙarshe dai ta bi shawarar zuciyarta a kan ta hau ta gyara masa. Nan ta zuge gilashin tana tuna diramarsu da yarinyar da ta aka kira da Najma, ba ta san matsayin yarinyar ba a wajen Maina, amma ta karanci tsanarta a fuskarta. Koda dai har wacce ta ji sun kira da auta wato Ummulkhair alamu sun nuna itama ba ta wani marhaba da ita.



Ta sauke ajiyar zuciya tana kallon gefen bangon, wani ƙaton madubi ne mai adon silver a gefensa har da wata fulawa ta ado. Ta cigaba da takawa har ta ƙarasa falon farko da ke saman.



"Ya Allah." Ta yi furucin a fili, ashe ita ba komai ta gani a wajenta ba. Nan ɗin ƙamshin ma na daban ne. Madadin faluka guda biyu, shi nasa guda ɗaya ne mai girma sosai. Ta sani ba za ta iya ƙiyasta kuɗaɗen da aka narka a falon ba, don ko ba a faɗa ba an san komai na ciki zai yi tsada. Shi komai fari da baƙi ne a falon, hatta da tayils ɗin farare ne tas. Labulayen ma adon fari da baƙi ne. Wurin tsaf ta iske shi. Ta buɗe wata ƙofa, babu komai a ciki sai kayayyakin motsa jiki, ta ja ta rufe. Ta can gaba kuwa study room ne. Nan ma komai a tsaftace. Rufewa ta yi. Sai da ta bi wani ɗan ƙaramin corridor, nan ne ta ga ƙofa na kallonta, ta murɗa a sannu ta buɗe. Daga yanayin ɗakin ta gane nan ne ɗakin baccinsa. Gadon duk a hargitse, hatta da kayansa da ya cire a saman wata ƴar kujera ya bar su. Ɗakinsa shi ma yana da girma irin nata, shi gadonsa wani mai zagaye ne a dunƙule. Ta soma tunani anya mutum biyu za su iya rayuwa a kansa?



"Bari dai na gwada."



Aikuwa ta faɗa gadon ta kwanta a gefe, sai ta ga akwai fili sosai da mutum biyu ma zasu iya kwanciya ba tare da sun matsu ba. Daddaɗan ƙamshin turarensa ta shaƙa a jikin filon da ma bargon, da sauri ta miƙe tana tsoron kar ƙamshin ya mamaye jikinta har a ƙarshe ya gane ta shigar masa ɗaki. Nan ta watsar da komai ta hau aikin da ta shigo dominsa. Hatta banɗakin ya burgeta, nan ma ta wanke shi tas ta sanya turare. Ta fito ta dawo falon, duk da bai yi wani datti ba sai da ta goge. Ta ga har wata baranda yake da ita har da kujeru ya saka sai a gefe shukoki ƙanana guda biyu a tukunyar ƙasa. Idan kana tsaye kana iya hango har hasumiyar masallacin Mai Martaba wanda ya ɗan yi nesa kaɗan da gidan nasu. Hatta da filin gidan da ma mai shigowa ko fita kana iya gani. Wurin ya burge ta sosai, ganin bai yi ƙura ba sai ta tattara ta dawo falon. Nan ma ta jona burner ɗin da ta gani ta zuba turaren wuta. Benen ma sai da Sadiya ta bi ta goge tas sannan ta rufe masa.



***

Ina labarin Hajara?
  KANO

Fuska a turɓune Alh Nuhu ke bin Hajara da kallo, ita kuwa idanunta ta shiga wulƙawa a ɗakin kafin ta gane a asibiti take. Da wani sauri ta yi yunƙurin miƙewa ta ji an riƙe ta gam. Ta dube shi, kallon da yake watsa mata ya sa ta jin shakkarsa na shigar ta, ƙirjinta sai da ya buga da ƙarfi.

"Me za ki yi idan kin miƙe? Umarnin likita ne ki kwanta ki sami hutu."

Ta koma ta kwanta tana ɗan satar kallon mijin nata. Ya ɗan yi taku zuwa ƙofar ɗakin sannan ya juyo ya nuna ta da yatsa murya a kausashe ya ce.

"Kar ki ƙara yin gangancin da ki ka yi a yau, wai shaye-shaye har ki yi overdose? Har ki rasa sadda za ki afa kayan mayenki saboda wata banzar damuwar da ki ka saka a ranki na auren ƙanwarki ki dinga sumbatun banza da wofi sai yanzu? Sai yanzun da kike ɗauke da gudan jinina? Toh na rantse maki ki ka yi kuskuren da cikin nan ya bi rariya ki saka a ranki a ranar zan sake ki. Ranar aurenmu zai ƙare! Ke ko mutuwa za ki yi a wurin haihuwa ni dai Nuhu ina buƙatar abin da za ki haifa min ya zo da rai! Don haka ki sani ina maki gargaɗi da babban murya kar ki ƙara gangancin wasa da lafiyarki muddin akwai ajiyata a jikinki! Idan kuwa kin ƙi ji toh ki shiryawa abin da zai biyo baya! Shashashar banza kawai! Mts!"

Yana kai wa nan ya sa kai yana baza babbar riga ya fice daga ɗakin har da banko ƙofar. Hajara ta runtse idanunta don har a lokacin kanta bai bar sarawa ba. Ta tuna dai bayan shigowarta gidan a hankali tashe ta yi kuka ta kuma yi ihu, a ƙarshe ta fiddo ajiyarta na kayayyakin maye da Waleedah ta siyo mata ta shiga sha babu ƙaƙƙautawa har sai da ta daina gane me ake yi a duniyar. Sai yanzun da ta farka, ba ta san hawa da sauka ba amma kuma ta dai tsinci wani ɓangare na katoɓarar da ta yi ba a hayyaci ba daga maganganun mijin nata.

Ajiyar zuciya kafin ta buɗe idanun, hawayenta suka kwaranyo saman fuska. Ta kai hannu saman mararta ta shafa. A dalilin Sadiya ta ke shirin yi wa kanta illah? Ina! Ba za ta ƙara gangancin shan wani abu da zai jaza mata fushin mijinta ba. Yanzu idan ya sake ta wa za ta kama? Ina take da ikon yin yadda ta so a gidan Malam? Za ta tattara lamarin Sadiya ta ajiye gefe guda tukunna amma fa ba don ta haƙura ba, sai don cikinta ya ɗan yi ƙwari. Ta dai kula da wulakantaccen kallon da wacce ake kira Fulani Kausar kuma mahaifiya ga Maina ke musu, ga dukkan alamu daga su har wacce suka kawo ba su samu karɓuwa ba a wajenta. Wani murmushi ne ya suɓuce mata duk kuwa da yanayin da take ciki. Fatanta Sadiya ta ɗanɗana baƙin ciki a hannun uwar miji.

Shigowar Inna da wasu yan uwan Malam su huɗu da Baba Habu da su Yaya Hashimu ne ya katse tunaninta. Ta rantse har ba ta kaunar ganin Inna don sai ta ke ga kamar ma murmushi ne shimfiɗe a saman fuskarta.

"Sannu Hajara, Allah ya ba ki lafiya. Ashe kuma tsautsayin da ya afku gareki kenan? Faɗuwa daga bene? To Allah ya tsare ya kiyaye. Sai ki dinga kula."

Abin da ya fito daga bakin Baba Asabe kenan. Ta gane ya ɓoye musu ainahin abin da ta aikata, hakan ya mata dadi.

Nan kowa ya shiga jajanta mata, a ƙarshe dai wata ma'aikaciyar asibitin ta ce su taimaka su tafi saboda ba a son ta da hayaniya. Haka suka bar ta don asibitin akwai masu jinya ita ma ta fi buƙatar hakan. Daƙyar ta iya cusa abinci  kafin daga bisani bacci ya ƙara awon gaba da ita cike da mafarkin Sadiya da irin matsayin da ta taka a yanzun.

***
Nene ce zaune ta zuba uban tagumi ta yi shiru gaba ɗaya zuciyarta a jagule. Ta share hawayen dake saman fuskarta ya fi sau a ƙirga sai dai ba su rabu da zuba ba.

"Haj Aziza."

Ta ji muryar Baffa a kusa da ita, ko kusa ba ta ji sadda ya shigo falon ba don haka ta ɗan razana kafin ta numfasa.

"Sannu da zuwa. Yanzu ka shigo?"

Madadin ya ba ta amsa sai ya girgiza kai cike da takaici ya ce.

"Haba Azizat, ki raba kanki da wannan koke-koken da ba zai maido hannun agogo baya ba, abin da fa ya faru ya riga ya afku. Da ace yaron nan ya damu da lamarinki kamar yanda ki ka damu da shi, toh da bai tsallake umarninmu ba har ma ya zaɓi wasu iyayen da suka fi mu ba. To muddin ki na son mu zauna lafiya da ke sai kin bi umarnin likita kin ragewa kanki damuwa a kan wanda bai san mutunci da ƙimarmu ba. Mun rasa Maryama yarinya mai tsananin biyayya ma mun haƙura balle wani AbdulMajid?"

Nene ta ɗauke hawayenta.

"Ka yi haƙuri. Duk yadda na so na kawar da tunaninsa na kasa ne. Ka yi min alfarmar kai zuciyarka nesa ka ƙara tuntuɓar iyayen yarinyar nan inda ɗanmu ya tafi da ɗiyarsu. Mu yi hakuri mu manta da abin da ya faru, ƙila dama ba matarsa ba ce Sadiya. Ƙila..."

"Azizat mene ne haka ki ke yi? Idan kin rasa AbdulMajid ba ki da Muneeb da sauran yara?"

Nene kawai sai ta fashe da kuka sosai, kwanakin nan gaba ɗaya kewar AbdulMajid take yi, duk da ta yi fushin amma tana ji har ta huce. Ita dai burinta ya dawo su dinga ganinsa.  Allah ne shaidarta, ta so Sadiya ta kuma ji zafin rashin aurenta da ɗan nata, sai dai tana gudun ta yi masa baki ya zo ya lalace ko kuma ya haɗu da bala'i iri-iri a rayuwa. A yanzu ba ta da addu'a sai nema masa gafarar Allah kan kada ya hukunta shi a kan ɓacin ran da ya haifar a zuƙatansu na fifita son zuciyarsa da watsi da haƙƙoƙinsu da ke rataye a wuyansa.

Baffa ya yi ta lallaɓa ta da kuma yi mata alƙawarin zai bincika ya ji inda yake. Hakan ya ɗan nutsar da zuciyarta.

***
GOMBE

Fuskarta ɗaure ta ke bin sa da kallo kamar mai son karantar zuciyarsa. Ba ta iya gane komai ba don haka ta soma magana murya a kausashe.

"Sai yanzu ka ga damar shigowa wurina Kakana? Me suka ba ka ka ci da yau ɗaya ka manta da kwanonka na wajena? Har akwai girkin da Saratu za ta sanya a naka da nawa hadiman ba su iya ba? Kuma ka rasa ina za ka yi zaman ci sai wajen matarka? Ni na rasa gane wannan lamari, auren na dole aka maka ko kuwa na so ne?"

Maina da ke sauraron Fulani bai katse

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login