Showing 45001 words to 48000 words out of 124441 words

Chapter 16 - Kazar Kwanci Hausa Novel Complete

zuciya, yanzun ma da tunanin ya faɗomata sai ta tsinci kanta da jan guntun tsaki.

Wayarta da ta hau ƙara ya sa ta kai idanunta saman screen ɗin, sunan Yaya Huzaif ne muraran ya bayyana, murmushi ta yi kafin ta kai hannunta jawo ta. Ta ɗaga sannan ta soma magana.

"As..."

"Da wa ki ke waya Bebi?"

"Inna ce ke waya da Adda Ruƙayya, wayarta batir ya ƙone shi ne na..."

"Ya isa please Bebi, ba na son ƙaryar banza da wofi. Na san wani ƙaton ki ka ba lambarki, idan ba haka ba ki rantse da Allah cewa Inna ke amfani da wayar sannan ki yi min screenshot lambar ki turo min ta whatsapp na gani."

Sai ta rasa me za ta ce, gaba ɗaya kanta ya ƙulle tamau. Ganin komai take tamkar a mafarki, daƙyar ta haɗiyi miyau cikin sanyin murya ta ce.

"Na rantse? Rantsuwa fa ka ce Yaya Huzaif? Meyasa zan ba wani lambata alhalin na san da sanya rana a kaina?"

Tsaki ta ji ya ja.

"An faɗamaki ni mahaukaci ne kenan Bebi, zan yarda ni kaɗai ki ke kulawa ne alhalin ina da labarin duk sadda ki ka fita sai an samu mazan da suke biyo ki gida da sunan suna sonki? Ke na rantse ban yarda Inna ke amfani da wayarki ba. Ƙarya ki ke yi Bebi tunda har kin kasa rantse min. Ni za ki ci amana?"

Tana jin alamar ɓacin rai a muryarsa, sai ta ji ƙwalla sun cicciko mata.

"Wai Yaya Huzaif lafiya? Wane ya ɓata maka rai?"

"Haka ki ka ce ko? Laifi ne don na nuna kishi a kanki? To ki je ko da waye ki ke magana Allah ya isa ban yafe ba. Da na san hakane wallahi ba zan siyamaki wayar ba idan ya so sai na ga ta hanyar da za ki ci amanar soyayyata. Amma bakomai, nagode."

Yana kai wa nan ta ji kit, ya kashe wayar. Ta fiddo wayar a kunne tana ƙura idanunta. Hawayenta tuni sun zubo saman kuncinta. Yaya Huzaif dai? Ƙaryatawa? Zargi? Ja mata Allah ya isa?

'Meke faruwa ne?' Ta tambayi zuciyarta, ba ta sani ba. Ta ji ranta ya ɓaci sosai, ba ta kai ga tunanin komai ba ta ji ƙarar shigowar saƙo a wayar, da hanzari ta duba. Shi ne ya rubuto.

"Dama an ce ka kiyayi mai kyau, babu abin da kuka iya sai yaudara. Za ku yi amfani da mutum ne don samun wani cikar burinku, a ƙarshe ku watsar da shi a kwandon shara. Babu yadda za'a yi Inna ta karɓi wayarki ta yi wanda ya zarta mintuna biyar tunda ba cinikin fili za ta ƙulla ba ai. Ni ki ka maida ɗan iska da bai san me yake ba. Shikenan, kar ki ƙara nemana a waya, ki rufe lambata kamar yadda ni ma zan rufe naki. Sai anjima."

'Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un!' Kalmar da Sadiya ta ambata kenan, hawayenta ya ƙaru, ya cigaba da zuba tamkar ruwan famfo. Sosai kalamansa sun yi mata zafi, ta ƙara karantawa, ta ji wani abu na taso mata na jin haushinsa don haka ta kashe wayar gaba ɗaya. Ranar karatun da ta kasa ƙarasawa kenan.

Inna ta bi ta da kallo sadda ta fito a falon rataye da jakar karatunta za ta shige zuwa ɗakinsu.

"Ke, lafiya na ga fuskarki ta sauya?"

Ta ɗan rike kanta.

"Bakomai, kaina ke ciwo sosai."

Ta faɗa ne don kare damuwarta, amma kuma dagasken kukan da ta ci a dalilin wannan kalaman marasa daɗin ji da Huzaif ya fesa mata, su ne babban dalilin da ya haɗu da rashin cin abincin da ba ta yi ba na rana ya haifar mata da azababben ciwon kan.

"To ai dole kanki ya yi ciwo Mamana, kin zauna za ki kashe kanki da boko alhalin ko abinci ba ki ci ba. Je ki ki ajiye jakar ki zo ki ɗebi abinci."

Kamar ta ce ta ƙoshi, amma kuma ta san idan har ba ta bi umarnin Innar ba, to hakan zai sa ta fahimci ba lafiya ba don haka sai kawai ta amsa da toh ta shige ɗakin. Husna dake amsa waya ganin ta shigo ta koma amsa wayar da uhm da kuma uhm uhm. Ita sam hankalinta ma ba a kanta yake ba, abin da ke cin ranta ya ishe ta wannan ya sa koda ta ajiye jakar ta fita don ɗebo abinci.

Husna ta ɗan leƙa ganin ta shiga kicin ne yasa cikin raɗa-raɗa ta ce.

"Antina, na rantse fuskarta gaba ɗaya ta yi ja kamar kuka ta yi ma. Kinsan ita haka fuskar ke komawa idan ta ci kuka."

"Eh Anti, ai ni ya kira sadda Inna ke wayar sai nace masa ni ina ɗakina, wataƙila Sadiyar ita ke yin waya."

Husna ta yi dariya ta ƙara da faɗin.

"To shikenan Anti, zan ƙara takatsantsan. Sai mun yi magana."

Daga haka suka yi sallama ta katse kiran tana ƴar dariya. Tana kallon Sadiya ta shige falon Innar, kwanciyarta ta yi iskar fankar da ke kaɗawa yana mata daɗi. Zuciyarta kuwa wani irin sanyi ta ji yana yi. Huɗubar da Antinta Hajara ta yi mata ne ya shiga dawomata.

"Zan taimaka maki, amma ke ma sai kin haɗa da irin namu makircin na mata. Kin ga dai na ce maki ki kula da duk wani taku naki da zai sa a zarge ki ta kowace fuska, yauwa, to kuma ina son duk sadda wani abun ya tashi wanda ki ka san zai iya haddasa hayaniya ko rikici tsakanin Sadiya da Huzaif, ki yi iyakar yin ki don ganin kin ƙara kunna wutar rikicin madadin ki kashe shi. Kuma ki dinga bi ta sigar da ba wanda zai maki kallon zargi. Idan har aka tafi a haka ina mai tabbatar maki komai zai zo mana da sauƙi. Za mu yi nasara kan ƙudurinmu."

Tana kai wa nan a tunaninta ta buɗe idanun da ta lumshe su a farko, ajiyar zuciya ta saki. Kaunar Yayarta da ba ta da kamarta wato Hajara yana ratsa ta. Ta tabbata daga yanayin fuskar Sadiya akwai magana sosai. Wani tunani ne ya faɗomata a rai don haka ta yi saurin jawo wayar Sadiya da ta ajiye a gefen gadon ta duba, ganin a kashe sai ta mayar, murmushi sosai ta shiga yi, wayarta ta ɗauka gami da shiga cikin whatsapp. Kai tsaye saman lambar Huzaif ta tafi, ta ci sa'ar ganinsa a online kuwa. Don haka ta shiga rubutu.

"Hi, Yayana akwai wata damuwar ne?"

Kamar jira yake yi ta ga ya soma rubutu, can sai ga saƙon ya shigo.

"Hum, babu komai ƙanwata, kawai yayarki ke neman ɓatan rai ne. Amma shikenan."

Husna ta riƙe dariyar dake cin zuciyarta ta ba aikamasa da ɗan dodon da ya zaro ido na waya. Ta ɗora da faɗin.

"Ya Salam, meke faruwa? Na ga Sadiya ta na ta cika da batsewa ta kashe wayarta. Wa ya ɓata wa wani tsakanin kai da ita."

Ta ga sadda ya buɗe amma kuma an ɗauki mintuna kusan uku kafin ya tura mata martanin zancen.

"Ƙila da ni ne ba ta son magana. Zan tambayeki ki faɗamin iyakar gaskiyarki please."

Husna ta miƙe zaune sosai ta dubi ƙofar shigowa, har sannan babu alamun Sadiya sai ta cigaba da hirarta.

"Zan faɗamaka, na yi alƙawari."

"Bayan ni, akwai mazan da Sadiya ke kulawa?"

Ta yi wata dariya kamar yana ganinta, ba komai ba ne face na nishaɗi. Wato dai tarkon da ta ɗana a ɗazun har ya harbu, a wautarta gani take yi shi ne ummul aba'isin na soma faɗansu, ba ta da masaniyar wancan aikin da Antinta ta ƙullo.

"Gaskiya Yaya Huzaif idan nace maka hakane to na yi ƙarya, ba kuma zan ce ba haka ba tunda ni dai ba ma taɓa wayar juna da Sadiya tun sadda ka siyo mata nata. Amma ni dai don Allah koma hakan ne ka yi hakuri ka share. Me zai dameka tunda dai ka sani taka ce kai ɗaya, ka kwantar da hankalinka"

Ta aika saƙon tana jin haushin kanta da fatan da ta yi mishi a ƙarshen rubutun hakan yasa da sauri ta ba kanta amsa a zuciya da cewa ba amin ba.

"Jibi zan bar ƙasar nan Husna, a haka ki ke cewa na kwantar da hankalina? Kai ni ƙaryar da ta yi min ce ta rainin wayo ta tsaya min a zuciya, wato ta maida ni wani baho, tana waya da ƙato ta cemin Inna ke waya da Adda Ruƙayya. Hum. Anyways, shi kenan sai anjima."

Tana gani ya sauka ya bar online ɗin, dariya sosai Husna ta yi, ta aika masa da fuskar dodo mai nuni da kuka, ita ba ta ce Sadiya na da gaskiya ba kuma ba ta ƙaryata shi ba. Nan take ta yi hoton hirar tasu ta aikawa Antinta Hajara. Ganin ba ta kan layin sai ta bar mata da zummar idan ta hau ta gani. Zuciyarta fari fes ta shiga kalle-kallenta a tiktok, har Sadiya ta shigo ɗakin ta ɗauki wayar tana kallonta ta gefen ido. Ta gani kamar za ta kunna sai ta fasa ta maida ta cikin sif ta adana can ƙasan kayanta.

'Allah yasa kun fara samun saɓani kenan.'

Cewar Husna a ƙasan ranta.

***
Abin ɗaure kai ga Sadiya, har ranar tafiyar Huzaif ya zo bai neme ta ba koda ta wayar Husna, hatta wayarta da ta kunna saboda kasa jurewar rashin kiranta da bai yi ba, nan ma ko saƙon whatsapp bai turomata ba. Abin kum sai ya ƙara ɓata mata, a gefe ga soyayyarsa dake nukurkusarta, sai dai ta rantse ba za ta kira shi ba muddin bai tuna da ita ba don kansa. Tana sane da cewa daren ranar zai tafi kuma zai zo gidan sallama da Inna hakan yasa tun dawowarta daga boko ta maƙale a gidan su Zahra wacce ta san komai. Ita kanta abin bai mata daɗi ba.

"Amma hakan da kika yi za ki cutar da zuciyarki ne Sadiya, don Allah ki shiga gidan watakila idan ya zo ki ga kun shirya. Yau fa zai koma karatunsa."

Faɗin Zahra kenan bayan sun kammala cin ɗan waken da Umman Zahra ta zuba musu. Daƙyar ma ta cusa abincin gudun kar Zahra ta fahimci ta damu amma ita kaɗai ta san me take dannewa, zumuɗin ta ga Huzaif ne yasa hatta da lesson ɗin da suke yi a tashi karfe huɗu ta kasa zama. Cike da son basarwa ta ja guntun tsaki.

"Toh ya yi ta komawar mana Zahra, dama can da shi nake rayuwa ne? Ai ban san da zamansa ba. Duk abin da Allah ya zaɓa min zan karɓa da hannu bibbiyu."

Ta karashe murya a raunane, kawai sai hawayenta suka zubo. Tana son Huzaif sosai, ta san da hakan. Amma fa ba za ta ɗauki cin fuska a tarayyarsu ba. Sam ba za ta yarda ya wulaƙanta iyayenta ko ma ita da kanta ba. Zargi tun kafin su kai ga zama a ƙarƙashin inuwar aure? Ta yi ƙwafa kawai.

Kafin Zahra ta samu bakin magana suka ji muryar Meenat na gaida Umma, da sauri Sadiya ta share hawayenta. Ta tabbata tunda Meenat ta zo gidansu, to tare suke da Huzaif. Ƙila Inna ce za ta aikota ta duba ko tana nan ɗin.
Meenat ta ƙaraso ta zauna gefenta tana leƙen fukar kafin ta yi dariya.

"Kai jama'a, yau na ga sabbin shiga. Shi Yaya Huzaif gaba ɗaya jikinsa ya mutu kamar wanda aka watsawa ruwan sanyi, ke kuwa kallo ɗaya za'a yi maki a gane kin sha kuka."

Ta kauda kai gami da jan guntun tsaki tana murmushin da bai kai zuci ba.

"To ai wannan dole ne Meenat, rabuwar masoya ko kaɗan babu daɗi sai don ba yadda aka iya." Faɗin Zahra tana dariya. Ita Meenat dariyar ta yi sannan ta miƙe tana kamo hannun Sadiya.

"Ki taso muje kar ya ƙara balbale ni saboda na jima. Shi ya ce lallai ƙafata ƙafarki wai na taimaka masa ki fito."

Mamaki ya sa Sadiya da Zahra kallon juna, Huzaif da kansa yake zumuɗin ganinta? Sai ta kasa gasƙatawa don haka ta miƙe saboda magiyar da Meenat ke mata ba don komai ba. Hijabinta ta zura suka fito har Zahra.

Ƙananun kaya ne a jikinsa gaba daya sai ta ga kamar ya ɗan yi rama. Shi ɗin ma kallonta yake yi kafin ya maida hankali ga amsa gaisuwar Zahra.

"Tafiya kuma ta zo, to Allah ya tsare ya ba da sa'ar abin da za'a je nema."

Huzaif da ɗan murmushi yana satar kallon Sadiya dake faman wasa da gefen hijabinta ya amsa da amin. Daga haka Meenat da Zahra suka bar falon Malam zuwa can tsakar gida wurin Inna suka bar su.

Shiru ne ya biyo baya, sai ta ga abin da ta yi babu dacewa ciki don haka ta gaishe shi a sanyaye. Ya amsa da saurinsa kuwa kafin ya ɗora da faɗin.

"Bebi mu yafewa junanmu, mu manta da gabar nan mai haifar da rashin nutsuwa da walwala a rayukanmu. Na kasa samun nutsuwa, ni ban san wane irin kishi ne ya motsa min ba ranar amma ke ma ba ki kyauta min ba. Kin san dai ba zan faɗi marar daɗi akan Innarmu ba. Ba zan taɓa haka ba."

"Ka yi haƙuri." Shi ne abin da kawai ta furta, so take yi komai ya wuce, babban burinta su dawo da kyakkyawar mu'amalarsu. Ba ta son wata damuwa musamman a wannan ranar da ya kasance zai tafi ya bar ta, ba ta san sadda kuma zai dawo ba.

Tana ji ya sauke ajiyar zuciya.

"Shikenan Bebi, ya wuce. Amma fa ki shirya tare zamu je Airport, sai kin min rakiya."

Ta ɗan dube shi, suka yi wa juna murmushi, wannan ƙaunar ta dawo mata sabuwa fil. Nan ya shiga jan ta da hira mai nuni da tsantsar kewarta.

Malam da kansa ya yi wa Sadiya da Husna iznin bin su domin rakiya. Sadiya ta yi ado da ruwan tokar abayarta mai kyau da Anti Hafsatu ta kawo mata da jimawa, ya karɓe ta kwarai. Ita ma Husna abayar wajen Anti Hajara ta saka sai dai kuma ganin yadda Sadiya ta fito fes ya sosa ranta ba kaɗan ba. Ta daure dai ta shanye suka kama hanya. Sai da suka koma gidan Abba, Huzaif ya ƙara sallama da Mami da Anti Amarya sannan suka wuce.

A hanya sai jan Sadiya yake da hira ita kuwa nauyi take ji sosai, daga yadda yake ta kallon Sadiyar yana magana ƙasa-ƙasa ya sa Husna samun tabbacin sun shirya, AC ne a motar ta ko'ina amma Husna gumi ke tsastsafo mata. Sam ba haka ta so ba, ba ta shirya ganin hakan ba ma kwata-kwata. Ta ji inama ta yi zamanta a gida.

"Na yarda da ke ɗari bisa ɗari, ba na zarginki. Wancan abin ma da ya faru, kishi ne ya haifar da shi. Amma ina ba ki haƙuri, ina jaddada maki cewa ina sonki. Ki riƙe min amana Bebi, ki kula min da kanki."

Waɗannan su ne zantukan da Huzaif ya yi mata sadda ya juya bayan ya buɗe tafin hannunta na dama ya sanya mata wani ɗan gida ƙarami na zobe a ciki. Ta janye hannun a hankali. Hawaye a saman fuskarta ta bi shi da kallo, shi kansa sai da ya ji idanunsa sun kada kamar ya fitar da hawayen. Haka suka rabu zuƙata babu daɗi.

A hanya duk zolayar da Meenat ke jan ta da shi ba ta kulata ba, lumshe idanu kawai ta yi, a ranta tana jaddada cewa babu abin da zai sa ta ci amanar Huzaif. Kuma da yardar Allah ba ta da miji sai shi. Har abada babu wanda za ta kula da zummar soyayya. Mutum ɗaya take so, kuma Huzaif ne, dama ai tsakanin harshe da haƙori akan saɓa. Balle ma faɗa na masoya.

Sai dai kuma ga rashin sanin Sadiya, wannan ne mafarin da Huzaif zai nisanta gare ta, irin nisan da dawowarsa zai zama jan aiki.

***
Lamura suka daidaita tsakanin Sadiya da Huzaif, yakan kira ta ta whatsapp duk sadda ya samu sukuni, haka kuma suna taɓa hira. Soma jarrabawar Waec da suka yi ya sa hirar ta ragu tsakaninsu.

Karatu sosai take yi, a gefe kuma ga Husna ƙanwarta da suke ɗasawa sosai don yanzu abin tun yana ba ta mamaki har ya daina. Za ta zauna su yi hira da dariya, hakanan tsakaninta da Inna. Inna ta ji daɗi sosai, kullum buri da addu'arta bai wuce na ganin yaran nata sun zama tsintsiya maɗauri ɗaya ba. Malam kansa ya kula da yanayin sauyi na jituwa tsakaninsu.

A haka Sadiya ta kammala zana jarrabawar Waec sai kuma Neco da ke tahowa. A wannan ɗan taƙi na hutun da ta samu ne, Inna da su Dada da Adda Ruƙayya suka yi tafiya Gombe. Ganin haka Sadiya ta soma shiri kamar yanda aka tsara za su koma gidan Yaya Hashim. Husna na zaune tana kallonta sai ta yi ɗan gyaran murya hakan yasa ta dubanta.

"Wai ke ba za ki je gidan Anti Hajara ba? Ba ki taɓa zuwa ba fa. Ko dai mu je can mu.."

"Aa Husna, ke dai ki je. Amma kar ki ƙara sanya ni ciki ba na so."

Husna ta yi murmushi, dama ta san ai hakan ce za ta faru. Ta ɗaga kafaɗa.

"Ai shikenan."

Sai dai ga Husna zancen bai tsaya a nan ba, Malam na dawowa gidan ta same shi da batun kamar yanda Antin nata ta tsara mata.

"Malam me zai hana muje gidan Anti Hajara? Ka ga har yanzu Anti Sadiya ba ta kula ta sosai, sai na ke ga idan ta je gidanta komai zai wuce tsakaninsu."

Malam da ɗan mamaki yake kallon Husna.

"Toh amma rashin jituwar daga Sadiya ce yanzu ko? Ɗazu Autar Mamar ta kira tana magiya ku je gidanta hutu, ba ta ware min ke ko Sadiya ba. Akwai wani abu dake faruwa tsakaninsu ne?"

Husna ta girgiza kai. Dama ai ta san Antin ta kira.

"Aa, kawai dai babu wani sabo tsakaninsu shiyasa na ce ko zamu je can."

"Shikenan hakan za'a yi Auta. Ku kammala shiri sai na sauke ku."

Cike da zumuɗi kuwa Husna ta miƙe. Ba ta ce wa Sadiya komai ba. Ita ma Sadiya kasancewar hankalinta na ga waya tana duba saƙon da ta tura ga Huzaif tun a jiya amma bai buɗe ba gaba ɗaya ba ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login