Showing 114001 words to 117000 words out of 124441 words
ta ba har ta kai aya, duk da ya ji babu daɗi a yawan munana zaton da ta ke yi ga abokan zamanta musamman Mai babban ɗaki amma kuma jin abin da ta ce a ƙarshe ya sa ya ɗan murmusa. Mamaki yake yi idan Fulanin na faɗin yana son Sadiya, kuma duk da ya sani babu hakan a ransa, amma kuma idan ta faɗi yana jin daɗin abin. Ba kuma don ya san dalili ba.
"Allah ya huci zuciyarki." Ya ƙara furtawa bayan duka waɗanda ya yi ta faɗi sadda suka yi waya. Ta ja guntun tsaki. A hankali kuma ta sanya hannu ta ɗauko wata rufaffen kwanon sha na silba ta miƙa masa.
"Maza shanye ka ba ni. Tsari ne na jiki don ban yarda da dangin matarnan taka ba. Ba kuma na son na ji komai. Umarni ne nake ba ka."
Jikinsa duk a sanyaye ya sa hannu ya karɓa ya sha da bismillah. Yana kammalawa ya ajiye ya dube ta.
"Zan shiga na gaishe da Mai Martaba."
"Daga nan idan ka so ka shige ɗakunansu ma. Kuma ka saka a rai ba za ka dauwama da yarinyarsu ba muddin ni Kausar ina raye sai ka auri zaɓina ni ma."
Ya ji kalaman kamar sukar kibiya, duk yadda ya ke kauda kai ba ya son yi wa Mahaifiyarsa zancen da zai sosa ranta sai da ya yi magana.
"A tun farko kun sani ba ni da ra'ayin aure yanzu amma kuma don na samar maku da farin ciki, na baku zaɓin ku nemo min matar aure idan na ga tana da ɗabi'un da zan iya zaman aure da ita, zan amince. Ko sati bamu yi da maganar ba kuma wannan abu ya faru. Ummi ku saka a rai ita ce zaɓin da Allah ya yi min. Please kar ku ƙaƙaba min wani auren da ina ji jikina ba zan tsinci komai a rayuwa da mace sama guda ɗaya ba face tarin zunubai."
Nan da nan Fulani ta hau buga salati kafin kuma ta shiga girgiza kai tana huci.
"Shikenan, ta faru ta ƙare. Tun ba a je ko'ina ba ka soma ji a jikinka za ka iya rayuwa da Sadiya kaɗai a duniyarka. Yaushe ne aka yi daren Ibraheem da har garinku ya waye? Ashe wayewar garin har ya ci ace an juyar min da kanka har haka? Toh na rantse maka sai ka ƙara aure ko ba nan kusa ba. Mu zuba ni da kai!"
"Ki yi haƙuri." Maina ya ƙara nanatawa karo na ba adadi. Wani irin mutum ne da ba ya gajiya da ba wanda ya yi wa laifi haƙuri balle kuma wacce ta haife shi. Ya yi mata sallama ya miƙe ya fice ta bi bayansa da kallo. Wani ƙwafa ta yi. Wayarta ta ɗauka ta danna kira ba jimawa ya soma ƙara.
"Fulanin Gombe, ranki ya daɗe. Fatan kina lafiya?" Abin da aka faɗi kenan. Fulani ta yamutse fuska.
"Ina fa na ga lafiya Haj Falmata. Kwana ɗaya yaron nan ya yi da wannan ƴar talakawan amma har wuyansa ya yi kaurin da ina faɗa yana ba wa aurensa kariya?"
"Uhum, ai ni na san irin waɗannan ba sa shigowa haka kawai. Ke ce tun farko ki ka tsaya jin ta bakinsa akan Zainab. Da tuni ba an wuce wajen ba. Da ace na taɓa haihuwa a duniyarnan babu abin da zai hana ni ɗaukar abin da na haifa mu aura masa. Ya fiye mana sau dubu akan auren nan da Mai Martaba ya yi masa."
Jikin Fulani ya yi sanyi. Ta tuna kukan da Zainab ta kira ta na rusa mata a jiyan akan wanda bai san tana hauka a kansa ba don Maina ko kallo ba ta ishe shi ba. Asalima a wurinta take samun sukunin hira, amma shakkar Maina ya hana ta ma neme shi da zancen so. Ita ɗin ƙanwa ce ga Haj Falmata, dukkansu yaran Galadiman Katsina ne kuma Haj Falmata ta kasance aminiya ga Fulani tun zamanin ƙuruciya, ita Fulani ɗiya ce ga Sarkin Katsina. Ba ta da abokiyar shawarar da ta wuce Falmata, wasu gani suke yi ma kamar shakkarta take yi domin komai za ta yi sai ta jira ta ji ta bakinta.
"Fulani ko kin sauka a kan layin ne? Na ji ki shiru. Yanzu me kika tsayar za ki yi a kai?"
Maganar Falmata ya maido ta nutsuwarta, ta sauke ajiyar zuciya.
"Ke zan yi wa tambayar Haj Falmata. Sai na ga kamar ma ya fara son yarinyar nan."
Wata dariya Falmata ta sheƙe da ita kafin ta ce.
"To asiri ai ba ƙarya ba ne, ke a tunaninki za su shigo gida irin wannan ba tare da babban shiri ba? Hum! Ai kalle su kawai. Idan ma kin ga ya so ta to fa ki shaida ba a cikin hayyacinsa yake ba. Yanzu dai ki kwantar da hankalinki, kar ki ƙara matsa mishi da batun aure. Idan ma matsi da takurar ce, ki dinga yi ga ita yarinyar. Shi kuwa ki bari sai nan gaba zamu ɓullo masa da zancen auren Zainab ta yadda ba zai ƙi bin umarninmu ba."
Fulani ta jinjina kai.
"Hakan ma shawara ce. To amma ta ya ya zan addabi rayuwarta? Ta wace hanya?"
Tsaki Haj Falmata ta ja.
"Ke fa daɗina da ke wani bin kamar 'yar fari, ki yi tunani sosai, ba za ki rasa wata hanyar ba. Kuma duk sadda ta zo wajenki, ki tabbata kin mata wulaƙancin da sai ta ji ta tsani rayuwar gidan."
Fulani ta jinjina kai.
"Hakan ya yi. Zan gwada ko zamu dace."
Daga nan suka yi sallama.
A gefen Haj Falmata dake zaune saman kujerar tangameman falonta ta yi wata dariyar mugunta kafin ta yi ƙwafa, a fili ta ke faɗin.
"Ai Kausar sai na lalata maki dukkan wani nishaɗinki ke da yaranki, yadda na haddasa ƙiyayyar abokan zamanki a zuciyarki, haka zan saka ki tsani surukarki tsanar da har ɗanki sai ya fara bijirewa umarninki. Muje zuwa!"
Zainab dake zaune a gefe cikin shiga ta riga da wando ta yarfo da gashinta saman kafaɗa ta dubi Haj Falmata idanunta cike taf da ƙwalla ta ce.
"Amma Anti bakya tunanin cutar da Maina kamar cutar da ni ce? Na rantse maki dagaske nake sonsa, a ture ma ƙudurin da ki ke da shi na wai na mallake shi ta yadda zai gagari Fulani. Ina kaunarsa ne ba na jin zan iya..."
"Ke! Rufe min baki ko na tashi na ɗauke fuskarki da mari! Shashasha! Wa yake ta wata soyayya? Ni wannan ƙudurina ne tun da jimawa sai na ga bayan dukkan wani abu da zai yi wa Fulani daɗi a duniya. Tana murnar ta haihu ta huta ko? Toh kuwa ba ta huta ba. Tun muna yara rayuwarta ta fifitu akan tawa, ubanta Sarki, nawa uban da yake matsayin yaya a wurin ubanta ya kasance a ƙarƙashin ikon ubanta. Kausar ta fi ni kyau da farin jinin jama'a! Ta zo ta fi ni dace da auren ɗan Sarki wanda a yanzu yake riƙe da kambun sarautar gaba ɗaya, na ƙare a auren wannan soloɓiyon Tafidan Bauchi wanda bai san komai ba sai boko ba kuma ya sha'awar mulkin sai wanda a ka ƙaƙaba masa a dole. Ta haihu, ta san daɗin haihuwa, ni kuwa ban san ko guda ba. Komai na rayuwarta tamkar ita ta tsarawa kanta, ki faɗa min toh Zainab, ta ya ya zan samu nutsuwar zuci?"
Haj Falmata na kai wa nan ta hau share hawaye, ita ma Zainab na ta hawayen ta share, ba wai na tausayin 'yar uwarta kawai ba, a'a sai na ƙara hango bambancin da ke tsakanin nata manufar ta son auren Maina da kuma na 'yar uwarta. Ta rantse ba za ta cutar da shi ba muddin ya aure ta sai dai duk abin da Falmata za ta yi mata to ta ji ta gani ta kuma shirya mata.
***
Misalin ƙarfe takwas da mintuna na dare motar Maina ta shigo gidansa. A lokacin Sadiya ta yi sabon wanka ta baɗaɗe gidan da turaren wuta yayin da ita kuwa ta yi wa kayanta turare na musamman da ma jikinta, ba ta yini ita kaɗai ba don Mai babban ɗaki ta karɓi roƙonta ta bar mata mata biyu, Karima za ta ɗan girme mata wacce aka ba ta domin girke-girke, sai ko Bintu da ba ta fi shekarunta ba, ita za ta dinga taimaka mata da gyaran sashenta. Ta saki jiki da su kwarai, girki kuwa abin da ya sa ba ta hana ba saboda bisa shawarar Anti Hafsatu ta jira ta koyi duk wani abu da ba ta sani ba, ta san me Maina ke ci da wanda ba ya ci. Sai dai yinin ranar kawai hira suka ɗan taɓa da su an riga da an kawo abinci daga can gidan. Bayan haka ma wasu a cikin ƴan uwan Maina sun shishshigo an gaisa da masu bin ta da kallo mai kama da harara, da kuma masu sakar mata fuska. Ita dai dukkansu ta karɓe su da shimfiɗar fuska.
Ta ji sadda ya murɗa ƙofar falon na farko ya shigo, ta tsinci muryar wani bayan shi a nan ta fahimci ba shi kaɗai ba ne, sai ta ji kamar ta miƙe ta zura a guje. Kunya ta ke ji kada ya ce ta zaƙe da yawa tunda ga shi har ado ta ke masa. Ita kuwa a yanzu sosai ta kwantar da hankalinta ta haƙura da komai.
Aka buɗe falon da take ciki aka shigo. Sallamarsa ce ta fara dira a dodon kunnuwanta kafin ta ɗaga idanu ta dube shi tana amsa sallamar. Ta sunkuyar da kai sadda suka haɗa idanu.
Bayan ya ƙaraso ciki, ya rasa dalilin da ya tsayar da shi a falon har da neman wurin zama. Farko dai zai iya cewa ƙamshi, wani irin ƙamshi ke tashi mai daɗin gaske, sai ko kwalliyar da ya ga ta yi na doguwar rigar atamfa ya sha adon stones daga wuya. Niyyarsa kawai ya wuce ɓangarensa, idan an mishi tayin abinci ya ci, idan ko ba ta yi ba ya share.
"Barka da zuwa."
Muryarta ya katse shi.
"Barka dai. Ya ki ka wuni?"
Ta ɗan ɗago kai ta wulƙa gefensa kaɗan na tare da ta kalle shi ba, sai abin ya zo da wani salo kai ka ce da gayya ta yi.
"Lafiya lau, na gode Allah."
Ya gyaɗa kai. Sai kuma ya rasa me zai ce don haka ya miƙe ya nufi hanyar tafiya ɓangarensa.
"Ko kana buƙatar abinci yanzu?"
Ya ɗan dakata ba tare da ya juyo ba ya ba ta amsa.
"Kina iya kawo min ɓangarena?"
Sai da kirjinta ya ɗan ba da ras, sai kuma ta amsa da toh. Daga haka ta ga ya yi gaba abin sa. Ta miƙe ta ɗan zauna da nufin jinkirtawa kaɗan kafin kuma ta ƙarasa wajen teburin. Kicin ta shiga ta ɗauki ƙaton kwanduna biyu da aka sanyo fulasan abinci a ciki ta maida su ciki ta kama hanyar saman. Ba ta gan shi a falon ba, ta ajiye ta komo ƙasa ta tattaro farantao da duk abin buƙata. Haka ta dinga hawa da sauka tana nishi har ta kammala bai fito daga ɗaki ba. Jikinta ya ba ta wanka yake yi sai kawai ta zauna ta shiga danna wayarta. Status din wata ƙawarsu ta makaranta ta gani da ke murnar test din ranar ta yi mata daɗi. Zuciyarta ta ji tana neman tsinkewa sai kawai ta ajiye wayar, ita kam a ta sani ta yi bankwana da karatu. Babu wani ko wata da ya yi mata zancen, hakan ya ba ta tabbacin ba za'a bari ta yi ba.
Ƙamshin turarukansa ne suka fara sauka a kofofin hancinta kafin ta kalle shi ta kuma sauke kai lokaci guda. Riga da wando ne na pyajamas a jikinsa baƙi da maroon colour sun karɓe shi ƙwarai. Waya yake amsawa yana zuba turanci kamar wani rainon Ingila. Ita ba ta taɓa ganin wanda turancinsa ke burgeta ba irin Maina duk da wannan ne karo na biyu da ta tsince shi yana wayar. Na farko sadda suke a Airport zasu taho garin, sai ko yau ɗin.
A wayar ta gane kamar tafiya ma zai yi nan da sati biyu kamar yadda ya sanar da abokin wayar tasa da ya kira da suna Mr John. Ganin ya zauna ta buɗe flask din farko, cous-cous ne da ya aka dafa sai ƙaramin filas din na miyar kayan lambu da kaza. Ta shiga zuba wa a faranti, ta yi zubi huɗu za ta yi na biyar ya dakatar da ita lokacin ya kammala waya.
"No kar ki ƙara, ya isa haka."
Ta kuwa maida wanda ta ɗebo sannan ta zuba miyar ta saka cokali ta ajiye a saman centretable din dake gabansa. Hatta da ruwa da kunun ayar da aka kawo sai da ta ajiye masa. Gefe ta samu ta zauna cikinta na ƙugi amma tana jin nauyin cin abinci a kusa da shi ta gwammace idan ya kammala ta sauka ƙasan ta ci.
"Kin ci abinci ne?" Tambayar ta zo mata a bazata, sai ta kasa cewa eh tunda ƙarya ba ya daga cikin ɗabi'unta, ba ta ma iya ba.
"A'a."
Ya ɗan ƙara kai idanunsa kanta, sai ya ji duk ta ba shi tausayi. Ita ma fa ba wai da son ranta aka yi auren nan ba, ya sani kuma har yanzun ba ta gama warkewa daga tabon da AbdulMajid ya bar mata a zuciya ba. Shi sai ya ji ma ba ta ba shi haushi, ya ƙudurta a rai zai kyautata zamantakewarsu koda kuwa wata mu'amalar aure ba zai gifta tsakaninsu ba. Zan ba ta kulawa kamar yadda zai yi ga ƙannensa.
"Ɗauko plate ki ɗiba ki ci. Ki na wasa da lafiyarki ashe?"
Sadiya ta ɗan ji abin banbarakwai, wannan kulawa har haka? Sai ta ɗan yi murmushin rashin sabo da hakan. Ba ta yi musu ba ta zuba a wani farantin ta soma ci a nan saman kafet ɗin tana kaffa-kaffa kada ta ɓata wurin. Shi kuwa bai ƙara kula maida hankali gareta ba, ya ci abincinsa sosai. Dama kaɗan ta zuba wa kanta don haka kusan a lokaci guda suka kammala. Tana cikin tattara kwanukan ne ta tsinci muryarsa.
"Kin shigo nan ne bayan fita ta?"
"Eh. Na shigo na gyara."
Ta ga ya yi wani murmushin gefen kumatu da ya yi matuƙar yi mishi kyau. Ita ba ta taɓa ganinsa yana murmushi ba sai yanzu. A ɓangarensa kuwa tunani yake wai wannan ƴar yarinyar har ta san gyara ɓangaren miji, ya tuna a gabansa Hindu ke faɗawa Mai babban ɗaki saƙonta na ba ta buƙatar masu hidima da yawa, ciki kuwa wato har da na ɓangarensa kenan. Sai ya ji ta burge shi, yana son girmamawa, ko babu komai ta girmama abin da ya shafe shi. Amma kuma duk da haka so ya ke ya ji ta bakinta don haka ya ce.
"Akwai masu hidimar da za su yi. Ki daina wahalar da kanki "
Sadiya ta russuna kanta a ladabce kuma cikin sanyin murya ta ba shi amsa.
"Ban ɗauki aikin lada ba matsayin wahalar da kai. Ni da kaina na nuna ba na son wata ta sanya min hannu a aikin da ya rataya a wuyana. In sha Allahu ba zai gagare ni ba a koyaushe muddin da lafiyata."
Ya ƙara kallonta sosai yana nazarin kaifin kwakwalwa da tunani irin nata.
'Sadiya Sa'ad Shagari sunanta. Iyayenta asalinsu garin Kano, mahaifiyarta ƴar nan Gombe ce gidan marigayi Muhammadu Liman. An mata shaida mai kyau a unguwa, haka nan kowa ya shaida ba silarta ne aurenta ake fasawa ba. Kaddara ce. Tana karatu a jami'ar bayero a shekararta ta farko tana karantar Medicine.'
Ya tuna kaɗan a cikin bayanan da Khamees ya ba sa nata, bayan binciken da ya sa a yi a mishi a kanta.
"Dama ki na da niyyar barin makaranta bayan aure ne ko kuwa sanadin wannan ƙaddarar ce?"
Tambayar ta zo mata a bazata hakan yasa da wani irin zumuɗi ta ɗago kai ta dube shi fuskarta ɗauke da murmushi sosai. Shi ma ya lula cikin tunanin dama ta fi kyau idan ta yi murmushi? Ita kuwa ta ma mance da komai a lokacin face hango tabbatuwar mafarkanta.
"A'a dama akwai niyyar karatun. Amma saboda..."
Sai ta kasa ƙarasawa ta sadda kai ƙasa tana wasa da siraran awarwaron da ke hannunta. Maina ya murmusa.
"That means idan kin samu damar karatun za ki yi?"
Sadiya ta ƙara kallonsa lokacin har wasu hawaye sun zubo mata na tsantsar farin ciki ta shiga gyaɗa mishi kai don ta ma rasa me za ta ce. Maina ya ji ta ƙara ba shi tausayi don haka ya tausasa murya.
"Kar ki yi kuka. Ba na son kuka."
Ta kuwa share hawayenta.
"Toh." Ta furta kamar a shagwaɓe har sai da ya bi ta da wani kallo kaɗan.
"Za ki yi karatu, sai dai ki yi haƙuri ba yanzu ba. Amma na miki alƙawarin za ki yi in sha Allah."
Koda yace ba yanzu ba, ba ta ji zafi ba. Ko babu komai ai ya gama magana tunda ya saka Allah a lamarin. Kuma ya shayar da ita tsantsar mamaki. Dama ba a fidda rai da rahamar Allah. A sadda ta ke ganin kamar shikenan ta bar karatu, sai ga dama ta ƙara zuwar mata.
"Nagode. Allah ya saka da alheri, ya ba da ikon cika alƙawari."
Murmushi ya yi yana kai kofin kunun aya bakinsa. Sai da ya yi kurɓa uku sannan ya sauke kofin.
"Bayan karatu ki na da wani burin?"
Kai ita fa Sadiya sai mamaki Maina ya ke ba ta a daren. To ko dai dagaske su Nudrat suke da suke ta yabawa da ɗabi'unsa? Dama yana da magana? Sauƙin kai? Kulawa?
Sai ta kasa cewa komai.
"Na yi alƙawarin kula da ke, rashin sanayyar juna da bamu yi ba, ba zai sauya komai ba. Idan kin saka a ranki zaman ibada za ki yi da ni, ni kuma me zai sa na kasa ba ki kulawa? Ki ɗauke ni matsayin wani abokin shawara kuma ɗan uwa, ni ma zan riƙe ki tamkar yar uwa."
Shi ne kuma ƙarshen maganar da ya yi mata a daren. Ta yi mishi godiya da addu'a, ganin ma ya shiga amsa waya ne ya sa ta miƙewa fuskarta a sake