Showing 108001 words to 111000 words out of 124441 words
Kallon ɗakunan ya tsaya yi, zai rantse bai san wanda take a ciki ba tunda kowanne babu inda ba a zuba kaya ba. Can dai ya zaɓi wanda ya ke tunanin zai iya kasancewa nan ne ya murɗa ya shiga da sallamarsa ƙasa-ƙasa.
Sadiya da ke zaune gefen gado ta yi shiru ta ɗan zabura ta kalle shi, idanunsu ya sarƙe wuri guda. Kusan kuma lokaci guda suka janye daga kallon juna. Ya ƙaraso a hankali ya ajiye ledojin saman teburin dake gaban gadonta. A hankali ita kuwa ta ɗan zame daga saman gadon kafin murya a tausashe ta ce.
"Barka da dare."
Maina wanda bai motsa daga inda yake ba, ya zura dukkan hannayensa a cikin aljihun wando yana kallonta son rai har jelolin kitsonta da suka zubo a kafaɗa.
"Barka dai. Akwai abin da ki ke buƙata?"
Ta girgiza kai.
"A'a. Ba na buƙatar komai. Nagode."
Godiyar ya ji daɗinta hakanan, hancinsa ya saba da jin ƙamshin turaruka iri daban-daban, sai ya ji wanda ke tashi a ɗakin ya bambanta da waɗanda ya san, ya kuma yi mishi. Sadiya jin shirun ne ya sa ta ɗago kai ta dube shi, idanunsu suka sarƙe wuri guda karo na biyu. Bai kauda na shi ba sai ita ce da sauri ta yi ƙasa da nata kan.
"Ki na iya amfani da abin da ke cikin ledar. Allah ya tashe mu lafiya."
Ta san dama hakan ce za ta faru, ba ta kuma kawo zai kwana ɗakinta ba. Ita ma kuma kwanan zai haifar mata da rashin sakewa da ɗari-ɗari. Kafin ma ta kai ga amsawa har ya juya ya soma tafiya. Bayan fitarsa ta sauke ajiyar zuciya na samun cikakken 'yanci a lokacin don tsayuwarsa a ɗakin ya sa ta kasa nutsuwa sosai. Yana da qualities na suffa wanda kowace mace za ta yi kwaɗayin ya kasance mijinta sai dai hali ne ba ta sani ba sai zama ya yi zama. Ya dai shayar da ita mamaki don ba ta zaci ko hanyar inda ta ke ma zai kalla ba balle ya nuna kulawa. Miƙewa ta yi ta rufe ɗakin da muƙulli, ba ta kalli inda ledojin suke ba duk da tarin yunwar da ta ƙunsa don tun rana kasa nutsuwa ta yi ta ci abinci tsabar fargaba da ta shiga jin wai za ta tare a ɗakinta. Sai da ta rage kayan jikinta ta zuwa doguwar riga mai taushi wanda tsawonsa da kaɗan ya wuce ƙaurinta, ta rufe gashinta da hula. Ta tattare kayan wuri guda ta ajiye su inda ya dace sannan ta zauna ta kara bin ɗakin da kallo. Murmushi ta ji ya suɓuce mata da ta tuna wai gidanta ne, kuma ita ɗin mata ce ga matashi kamar Ibraheem Tafida. Ta ɗan lumshe idanu tana tunano shigar da ya yi na kufta ruwan madara. Ya karɓe shi sosai. Ga maganarsa da ke fita a nutse kuma muryar ba a sama ba, ƙasa-ƙasa wanda sai ka nutsu za ka ji. Ta lura haka yake magana tunda ba wannan ne karon farko da ta ji ya yi ba.
Ta yi saurin buɗe idanunta tana mai jin haushin kanta, ko mene ne toh na tsayawa wassafa Maina har haka? Ta ɗan cije leɓbanta cike da takaicin kanta, idanunta suka sauka a kan ledojin da ya ajiye, nan kuma ta tuna da yunwar da ke cin ta, ta miƙe ta ƙarasa ta janyo ta buɗe ta farko. Soft drinks ne sai ko ɗayan ledar da ta buɗe, gashin kaji ne har guda biyu. Na ukun kuwa tarkacen su brush da toothpaste, mouth wash da sauransu.
Ta miƙe ta buɗe ƙofar gami da murɗawa a hankali ta fito, falon shiru an kashe fitilun amma kuma akwai hasken waje da ma ɗan hasken dake gefen hawa bene da ya ratso cikin falon. Ta koma ta ɗauko wayarta, da taimakon hasken ta gane inda makunnan suke ta kunna ɗaya, ya ba da kalar blue, an zuba kayan ƙawa a cikinsa. Ta ƙarasa ga ƙofar da ke jikin dining table, aikuwa kicin ɗin ne kamar yadda ta yi tsammani. A zatonta ƙarami ne sai ta gan shi da girma wanda a wata duniyar zai iya zama madaidaicin falon wata. Ta ƙara godiya ga Allah da wannan ni'imar da ya yi mata, ta kuma yi fatan Allah ya sa aurenta ya zame mata haske da zai haskaka duniya da lahirarta. Ta shiga ciki, a jerin farantai dake jere a plates rack irin wanda ke manne jikin bango, guda daya ta ɗauka sai kofi ta ɗauraye su ta kashe fitilun ko'ina ta koma dakin. Ta yi tunani ya fi a ƙirga ko ta zuba ta miƙawa Maina, amma kuma tana jin fargabar kar ya ji haushin ganinta a ɓangarensa. Ita dai ta san ya mata yawa don ko rabi ba za ta iya ci ba balle a kai ga kaza biyu. Haka ta ɗiba ta ci ta kora da ruwa ko lemun ba ta sha ba ta tattara a dole ta buɗe ƙofa karo na biyu ta koma kicin. A firij ta saka kazar da sauran lemukan wanda ta tarar ma akwai lemun a ciki, ta rufe komai ta koma ta yi alwala sannan ta kunna karatun kur'ani a wayarta. Tun tana bin karatun a hankali har dai bacci ya yi awon gaba da ita cikin lallausan gado da abin rufarta.
Ƙarar alarm ɗin dake wayarta ne ya farkar da ita ta kuma gane asuba ce ta yi. Fitowarta daga banɗaki ba jimawa ta ji ana ƙwanƙwasa ƙofar, ba ta yi dogon tunani ba don ta sani rai biyu ne a cikin gidan idan ka cire ma'aikatan waje. Hijabi ta zura a gaggauce ta ƙarasa ta buɗe ƙofar. Sanye yake cikin doguwar rigar jallabiya fara ƙal, ko ba a faɗa ba shirin sallah ya yi.
"Oh kin tashi ashe." Hakan kawai ya faɗi bai kuma saurari cewarta ba ya yi gaba zuwa masallaci. Sadiya ta bi shi da kallo sannan ta rufe ƙofar ta koma tana tunani kenan tashinta ya zo ya yi. Murmushi ta ɗan yi don har a zuci ta ji daɗin haka. Ɗan ƙaramin wuri ko kuma ace masallaci da aka ɗan kewaye mata, an saka darduma sai ɗan gini da aka yi aka ajiye kur'ani har uku kowanne da wajensa ga kuma wani abin ƙamshi mai daɗi da aka ajiye a gefe. Duk a wajen babu inda ya fi burgeta kamar nan ɗin, ba buƙatar ta nemi gabas a gidan, yanayin da aka shimfiɗa dardumar ma ya sa ta fahimta. Bayan ta idar ta yi karatun kur'ani kafin ta shiga azkar na safe. Koda rana ta fito ji ta yi baccin ma ya fice mata a idanu don haka ta gyara gadonta ta faɗa wanka. Zama ta yi ta murje jikinta da zazzafan turaren da Antinta ta bayar takanas aka kawo mata daga Kaduna wanda Safiyya Jibril ke haɗawa. Ba ta shafa mai a jiki ba sai tafin ƙafafu da hannunta. Ta shirya cikin atamfarta super holland ruwan masara sai ko kalolin da aka ƙawata zanensa da ita. Ɗinkin riga da siket ne, ya zauna ɗabas a jikinta ya kuma fiddo surarta ainun. Hoda kawai ta shafa da man leɓe.
Baƙin mayafinta ta yafa a kafaɗarta ta zura takalmi flat ta fito zuwa falon. Kamar jira ake ta fito aka shiga kwankwasa ƙofa don sai da ta saurara sosai ta iya ji. Ta ƙarasa har falon farko sannan ta buɗe. Wata baiwar gidan ta gani ɗaya daga cikin masu yi musu hidima tun zuwansu a sassan Haj Saratu. Su uku ne, suka ɗan russuna suka gaishe ta. Ta amsa har lokacin ta kasa sabo da wannan girmamawar da ake mata, son samunta ne ma su daina a dinga gaisawa kamar 'yan uwa.
Hanya ta ba su suka shiga har falonta na biyu bayan neman iznin hakan a wurinta, nan suka ajiye kwandunan da suka shigo da su da aka shaƙe da kayan kari.
"Saƙo ne daga Mai babban ɗaki."
Abin da suka ce kenan. Ta yi godiya, bayan tafiyarsu ta fiddo. Ta jera komai saman tebur, ta shiga kicin ta ɗauko farantai da cokula har ma da kofin tangaraye guda bibbiyu ta ɗauraye ta goge su ta ajiye.
Ta haɗa shayi ta sha da soyayyar agada da ƙwai don ko farfesun ma ba ta sha ba ita. Ta tattare ta kai kicin ta wanke su tas ta goge ta maida inda ta ɗauko har a sannan Maina bai fito ba balle ta zuba masa abin kari. Ta gaji da zaman ta koma ɗakinta ta fiddo waya ta kira Anti Hafsatu amma wayarta ba ta shiga, hakan ya sa ta kira Zahra. Jin su kamar a hanya yasa da sauri ta tari numfashin Zahra mai tsokanarta da cewa Amarya.
"Wai ban gane ba, kun wuce ne? Ina Anti Hafsatu?"
"Muna hanya har mun fara nisa, Anti Hafsatu kin san ta jirgi ta koma, dama zuwa da komawa aka biya mata."
Ran Sadiya ya ɓaci, kwalla har sun tarar mata ta ce.
"Shi ne ba ku zo mun yi sallama ba Zahra? Har da ke? Haka za ku yi min don kun daina sona?"
Kawai sai ta fashe da kukan gaba ɗaya ma. Ta dai ji Zahra na faɗawa sauran wai kuka take, sai kuma ta ji muryar Dada.
"Sadiya, yi shiru bana son kukan nan. Toh ai kin ji, wannan kukan naki ne yasa muka watse gaba ɗaya ba tare da mun maki sallama ba. Ki nutsu ki yi saurare ni kin ji ko?"
Ta kuwa bi umarninta, nan Dada ta yi mata ƴar gajeriyar nasiha ta kuma ƙarashe da addu'a da faɗamata irin karamcin da aka yi musu na haɗa su da sha tara na arziki don kowannensu sai da aka ba shi manyan atamfofi guda biyu ga kyautar turaruka da kuma kuɗi da Maina da kansa ya yi musu. Wai a daren jiyan ya shiga sun gaisa ya kuma yi sallama da su.
"Ke dai ki dage da addu'a sosai Jikata."
Wannan shi ne kalaman ƙarshe a safiyar da Dada ta furta gareta. Ya kuma shige ta sosai, ta yi musu fatan isa lafiya daga nan suka yi sallama bayan Zahra ta tabbatar za ta kira ta idan sun isa.
Miƙewa ta yi ta koma falon don gani take kamar babban laifi ne ta bar Mijinta ya fita ba tare da ya karya ba. Ba ta wani jima ba sai ga ƙarar takunsa yana saukowa daga bene sai ko muryarsa da ta ɗan tsinkaya yana magana dab da zai ƙarasa saukowa.
Ya zuge gilashin da ya raba benen da falon ya fito, nan da nan ƙamshi ya gauraye falon. Zai iya rantsewa bai ankara ma da ita ba har ya zauna hankalinsa na ga wayar da yake amsawa mai muhimmanci da ya shafi kamfaninsu. Ita kuwa duk ta takure a wurin, sai kuma a lokacin ne ta tuna da mayafin da ta laluba da idanunta ta ga ba ya nan, wato a ɗakin ta bar shi.
Maina yana kammala wayar ya ɗago kai yana duba kiran Fulani da ya shigo sa'ilin da yake kan wani layin. A lokacin ne kuma hankalin ya kai gare ta.
'Masha Allah.' Ya yi furucin a zuci, a gaggauce ya kauda kansa ya hau danna wayar da zummar bin bayan kiran Fulani sai dai hakan ya gagara.
"Barka da asuba fatan an tashi lafiya?"
Ya tsinci muryarta, dole ya ƙara kai dubansa kanta, ba wai wani sashi ne ya bayyana a tare da ita ba, ko kaɗan, amma fa kayan sun yi wani irin zama a jikinta. Amma kuma tunani yake haka surar take ko kuwa dai irin abin nan ne da ya ji ana kira da acuci maza?
Sai da ta ɗan kai hannunta da ya sha lalle ta sosa goshinta kaɗan sannan ya tuna bai amsa gaisuwarta ba. Ɗauke idanun ya yi.
"Barka dai, lafiya. Kin tashi lafiya?"
Tambayar ta mata daɗi, ba ta zaci zai damu da sanin ya ta tashi ba.
"Lafiya Alhamdulillah."
Shiru ya ɗan biyo baya.
"Ga abin kari, nan za'a kawo ko kuma a can za'a zuba?"
Ya ɗan kalleta, ya kula kamar kallo ma bai ishe ta ba. Toh ba ta ga abin kallo a tattare da shi ba ne ko me? Ya yi wa kansa tambayar da ba shi da amsa.
"No, can ɗin ma is ok."
Ta miƙe ta juya ta fara tafiya ba tare da ta jira shi ba. Runtse idanu ta yi gaba daya kunya take ji, tafiyar ma yin ta kawai take duk da ta san ba ta wani ishe shi kallo ba amma sai ta ke ji kamar idanunsa na kanta.
Kamar kuwa ta san haka ɗin ne.
Ya bi bayanta da kallo a hankali tun daga kan jelolin kitsonta da suka bayyana ta saman ɗankwalin da bai kammala rufuwa ba har zuwa yadda ta ke tafe bayanta na wani juyi kamar da gayya. Ya kauda kai ya shafi goshinsa.
'It's all fake.' Ya faɗi a ƙasan ransa kafin kuma ya ja istigfari da sauri na yanke hukuncin abin da bai sani ba, kuma ma ya ga mene ne amfanin sa mata ido har haka? Ya miƙe ya soma takawa har ya ƙarasa inda Sadiya ke tsaye ta dai ɗauki kofi amma kuma ta rasa ya za ta yi tunda ba ta san me da me yake ci ba. Zama ya yi saman kujera daidai inda ta ke a tsaye, ta kuwa ja baya kadan. Daga yanayinta ya karanci duk ta diririce ƙila ta rasa me za ta yi ne. Don haka ya ce,
"Haɗa min tea ba madara."
"Toh." Ta amsa, ta zuba sugar na ɗaya, na biyu ya ɗan dakatar da ita daga ɗiban na uku ta hanyar ɗan ɗaga hannunsa. Ta rufe ta ajiye, ita jikinta har wani rawa yake ma tsabar rashin sabo da kuma tsoron kar ta yi ba daidai ba.
Ta janyo faranti ta zuba mishi suyar da aka yi haɗe da sauce ɗin hanta a gefe sai ta ga bai ce uffan ba, ta sanya fork a gefe ta ajiye. Farfesun ma da ta zuba a bowl ba ta ji ya ce wani abu ba. Tana kammalawa ta ji ya yi magana.
"Nagode." Sai da ta ɗan yi murmushi, ashe bai da girman kan da ta ke yawan kallonsa da shi. Falo ta ƙarasa ta zauna a kujerar da ta ba dinning area din baya. Wayarta ta shiga latsawa kawai tana kallon hotunan status, anan ne ta ga Husna ta mata magana ta saƙon whatsapp. Ta buɗe, tun ma asuba ne.
"My sis, i am so sorry nikam na so na shigo mu yi sallama amma hakan ba zai samu ba. Antinmu ta hana wai za mu saka ki kuka. Flight ɗaya zamu hau da Antin da Antina, zan kira ki idan mun isa lafiya. Allah ya albarkaci rayuwar aurenki. Ameen. "
Ta yi murmushi, nan ta shiga ba ta amsa kafin ta fito. Kamar daga sama ta ga saƙon Nudrat wanda bai kai ko mintuna uku da shigowa ba. Ta kuwa buɗe da sauri don babu ranar da tunaninta ba ya faɗo mata a rai.
"Hi my besty, ya kike? Koda dai nasan ki na lafiya, kin ji ni shiru ko? Kunya Sadiya, kunyar abin da Hammana ya maki na ke ji, na kasa zuwa inda kike, na kuma kasa taɓo ki a waya. Sai na ke jin kamar kowa zai min kallon munafuka, za'a ga kamar na san komai saboda irin kusancinmu da shi. Sadiya na rantse babu abin da na sani a abin da ya faru. Abin da ya sa ma Nene kasa zuwa gidanku kenan sai a jiya suka je da yan uwa aka ba da haƙuri. Nene ta shiga damuwa ƙwarai don har kwanciya rashin lafiya ta ɗan yi. Amma Alhamdulillah, sai kika ga kunya da tozarcin da Hamma ya so ya yi mana gaba daya, Allah bai nufe shi da aikatawa ba. Sai ki ka samu wanda ya fi shi."
Sadiya ta sauke ajiyar zuciya, a hankali ta ɗan juya kai ta dubi Maina, idanunsa ba ya kanta yana amsa waya kamar kuma da Fulani inda yake kawai ambaton Allah ya huci zuciyarta, ba ta ma son jin me suke tattaunawa don haka ta maida kai ta tafi saƙo na biyu da Nudrat ta aiko cikin guda uku.
"Ibraheem Tafida, kar ki ga ina cewa na tsani halayyarsa, wallahi Triple kin yi dace. Ni kin fi kowa sanin na fi son mutum mai sakewa da shiga lamurana, idan muna da kusanci da kai amma kana nuna seniority a komai to fa haushinka ya zame min dole. Haka ɗabi'ata take. Amma a ture wannan, zan ba ki kyakkyawar shaida akan Maina wanda kowa ke yabonsa a zuri'armu. Kyauta, kyautatawa da girmama ɗan adam, ba ya raina su, ban kuma taɓa jin ya wulaƙanta wani ba. Shi dai haka halayyarsa ta ke, ba ya shiga sabgar mutane. Ya fi ganewa wasu lokutan ya yi rayuwa da waɗanda suke shiga sabgarsa kuma ya aminta da su ɗari bisa ɗari. Na san da haka saboda amintarsu da Hamma. Ɓata baki ne idan na ce maki ya haɗa dukkan abin da mace ke son mijinta da shi tunda kin shaida wasu, ya fi Hamma kyau, aji, ilimi, kuɗi, nasaba mai kyau, uwa uba kuma gudun ɓacin ran iyaye."
Sadiya ta numfasa, meyasa kowa ke son nuna mata Mainan nan mai kyau ne wai? Ita fa koda zai shiga ranta ba ta fatan ta so shi saboda kyawun nasa, fatanta Allah yasa yana da halaye masu kyau. Koda dai ko a yanzun da yake lallaɓa Fulaninsa ai ya ci ace ta gane yana bin iyayen.
Ta ƙarasa zuwa saƙo na ƙarshe da Nudrat ta turo.
"Humm, ba ina zuzuta Maina don ki ji a ranki ya fi Hamma saboda son kawar da laifinsa a zuciyarki ba, a'a Triple. Ina mai ba ki tabbacin za ki ga zahirin abin da nake faɗamaki idan ku na tare. Ina maki addu'a da fatan alheri, ina roƙon Allah ya haɗa kawunanku. Ya sanya wa Maina so da kaunarki a zuciya, ke ma kuma ya sa ki ƙaunace shi fiye da dukkan wani ɗa namiji da ki ka taɓa so a rayuwarki. Ameen. A ƙarshe ina ƙara neman